Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Barin Sallah A Daren Amarci

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum warahmatullah wabarakatuh malam. Tambaya nake da ita, shin ya halatta amarya taƙiyin sallah a ranar da aka daura mata aure saboda yawan aikace-aikace da rashin lokaci, ko kuma a daren amarci sai na ki yin sallar asuba, shin hakan ya halatta? Malamai ina so aja ma amare kunne akan hakan domin gaskiya mata da yawa basayin sallah a daren amarci saboda wani dalili na daban, Allah ya saka maku da Alkhairi.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumussalam warahmatullah wabarakatuh.

A'a bai halatta ba ga amarya ta bar sallah a ranar daurawa aurenta ko daren amarci saboda aiki ko rashin lokaci. Rashin lokaci ko yawan hidima ba sa zama dalilin barin sallah, kuma Fara rayuwar aure da saɓon Allah yana janye albarka daga auren.

Sallah tana ɗaya daga cikin rukunai na Musulunci da babu rangwame a kansu matukar mutum yana da hankali da lafiya.

Magana ta gaskiya ita ce wajibi ne a gareku Amarya da Ango su sallaci sallolin su na farillah da Allah ya wajabta ma musulmai yin waɗannan salloli.

An tambayi commitee na malamai masu bada fatawa na kasar saudiyya cewa "Yaya hukucin yin sallah ga mace a daren amarci?

Sai suka Amsa da cewa " Ya wajaba a gareta ta sallaci sallolin ta na farillah saboda babu wani sassauci akan barinta wai saboda daren amarci, sai dai idan da wani dalili da zai hanata sallah kamar tana a halin haila (jinin dabi'a) ko kuma jinin haihuwa"

Domin neman karin bayani duba acikin littafin (LAJNATUD-DAA'IMAH 7/343)

Wajibi ne Amarya da Ango ku kasance kun sallaci sallolin ku a ranar da aka daura maku aure, kuma ku nisanci saɓon Allah maɗaukakin sarki, ku kiyaye daga dukkan wani aiki da zai kai ku zuwa ga saɓa ma Allah, lallai babu wani dalili na daban wanda shari'a batayi magana akansa ba da zai hana mace yin sallah, matukar ba waɗannan da aka lissafa ba, kai kuwa Ango dolene baka da wani dalili Don haka dukkan wanda ya nisanci sallah to sheɗan yayi galaba akansa, irin waɗannan ma'auratan sai ayi masu nasiha, musamman iyayenmu sai suyi kokarin kwaɗaitar dasu dangane da gyara tsakanin bawa da mahaliccin sa.

'Yar uwata kiji tsoron Allah maɗaukakin sarki ki sallaci sallolin ki, kaima Ango kaji tsoron Allah maɗaukakin sarki domin kuwa Allah yayi tanadi na azaba ga wanda yabar sallah da gangan, Allah maɗaukakin sarki ya shiryar damu, Allah yasa mudace.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu. . .

  ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam  

Post a Comment

0 Comments