Cikin kwanakin nan ana ta tattaunawa a kan mas'alar halasci ko rashin halascin fitowar mace takarar kujerar majalisa, inda aka hakaito fatawar wasu Malamai da suka tabbatar da halasci, sai kuma aka samu wani Malami ya saɓa musu, har ya wallafa takarda, yana mai yi musu raddi, ya kuma karantar da takardar da ya rubuta.
Ni a iya bincike na, na fi
gamsuwa da rashin halascin fitowar mace takaran kujerar majalisa, balle kuma
kujerar Gomna, balle kuma Shugaban ƙasa.
Saboda dalilai da suke nuni da cewa; harkar shugabanci na maza ne ba na mata
ba. Shi ya sa Malamai da yawa suke ƙirga
"الذكورية" wato kasancewa namiji a cikin sharaɗin
shugabanci.
To amma ni abin da ya ja
hankalina a cikin raddin da Malamin ya yi wa waɗancan
Malaman shi ne, yadda ya sanya saɓani
a kan mas'alar -wai- saɓani ne tsakanin Ahlus Sunna
da ƴan bidi'a, alhali mas'alar babu Nassi a
kanta. Kuma ban san wata Aƙida
ta bidi'a da aka gina a kanta ba. Kuma ba a san wata ƙungiyar bidi'a da ta yi fice da hakan a
tsakanin sauran Musulmi ba.
Saboda haka iya abin da za a
ce shi ne; wannar mas'ala ce "Ijtihadiyya", saboda babu Nassi a
kanta. Saboda Hadisin Abu Bakrah (ra):
"لن
يفلح قوم ولّوا أمرهم امرأة".
صحيح
البخاري
"Duk al'ummar da suka
shugabantar da mace a kansu ba za su rabauta ba".
Nassi ne a kan babban
shugabanci, kamar Shugaban ƙasa
ko Gomna. Saboda "ولاية" (Wilaya) da ke cikin Hadisin ba
dukkan nau'o'i na shuganbanci ba ne, kamar na ƴan
majalisa, saboda idan mun duba ma'anar da Malamai suke bai wa
"Wilaya" za mu ga ƴan
majalisu ba su da ita. Malamai suka ce:
"الولاية
هي القدرة على إنشاء العقود والتصرفات النافذة، من غير توقف على إجازة أحد".
الموسوعة
الفقهية الكويتية (٧/ ٢٠٥)
"Mulki shi ne samun iko
a kan kulla yarjejeniya da zartas da aiyuka, ba tare da jiran sahhalewan wani
ba".
Shi ya sa Ibnul Atheer ya
ce:
"الولاية
تُشعر بالتدبير والقدرة والفعل، وما لم يجتمع ذلك فيها لم ينطلق عليه اسم الوالي".
النهاية
في غريب الحديث والأثر (٥/ ٢٢٧)
"Mulki yana nuna
gudanarwa da iko da aiki, duk mulkin da waɗannan
ba su haɗu a
cikinsa ba to ba za a kira shi da shugaba mai mulki ba".
Idan mun lura da wannan
ma'ana ta "Wilaya" za mu ga cewa; ba za ta dace da kowa ba cikin
kujerun da ake takara a kansu sai kujerar Shugaban ƙasa ko Gomna. Amma ƴan majalisa ba su da wani zartarwa da
suke yi a kan talakawa, shi ya sa wani ɗan
majalisar, idan an zaɓe shi ya tafi Abuja, ba za a
ƙara ganinsa ba sai lokacin wani zaɓen.
Ala ayyi halin, wannar
mas'ala mas'ala ce "Ijtihadiyya", mas'ala ce da babu laifi idan an yi
saɓani
a kanta. Duk wanda ya yi Ijtihadi ya yi fatawa da halasci, to wanda ya yi
Ijtihadi ya yi fatawa da haramci ba zai zargi wanda ya yi fatawa da halascin
ba. Saboda ba a zargi a mas'alolin Ijtihadi. Wanda ya dace yana da lada biyu,
wanda ya yi kuskure yana da lada ɗaya.
To saboda haka, wani dalili
ne zai sa a taƙaice mas'alar
tsakanin Ahlus Sunna da ƴan
bidi'a?
Har jahilai da yara, ko
Malamai marasa wara'u su fara zargin wanda ya saɓa
musu, suna bidi'antar da shi?!
Saboda haka yana da kyau a
bi a hankali, a ajiye abubuwa a muhallinsu.
~ Dr. Aliyu Muh'd Sani (H)
Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.