Ticker

6/recent/ticker-posts

Babbar Matsalar Ibnu Taimiyya Koyar da Ta'addanci!

Shin Ibnu Taimiyya shi ne ya koyar da ta'addancin da yake faruwa a wannan zamani?

Ibnu Taimiyya ya rayuwa da Malaman Bidi'a masu yawa; Sufaye ƴan Ash'ariyya, masu ƙarfin faɗa-a-ji a wajen sarakunan zamaninsa. Kuma sun yi husuma mai zafi da shi. Kuma sun yi adawa da shi, adawa mai tsanani, saboda mas'aloli masu yawa. Kai, har kafirta shi sun yi, amma duk da haka shi bai taɓa kafirta wani ba.

Waɗannan Malamai - saboda adawarsu da shi - sun sa an ɗaure shi, har sau bakwai (7), amma duk cikinsu ba a taɓa ɗaure shi bisa tuhumar koyar da ta'addanci ko kafirta musulmi ba.

An ɗaure shi a kan kafirin amana da ya zagi Annabi (saw), mas'alar ziyara, mas'alar Istigatha, mas'alar Siffofin Allah, mas'alar saki uku. Don haka - duk da ƙiyayyar da maƙiyansa suke masa - ba su taɓa tuhumarsa da kafirta musulmi ko koyar da ta'addanci ba. Da a ce sun samu ra'ayin ta'addanci a tare da shi, da lallai sai sun sa an ɗaure shi. Amma ba su yi ba, saboda babu.

Daga cikin abin da zai nuna maka cewa; jahilai ne suke tuhumar Ibnu Taimiyya da ta'addanci, ko masu son zuciya, shi ne Manhajin Ibnu Taimiyya a mas'alolin Imani da Kafirci:

1- A wajen ƴan bidi'a; Sufaye da Khawarijawa da ƴan Shi'a da Sayyid Qutub da sauransu, Imani abu ɗaya ne ba ya rarrabuwa, shi ya sa a wurinsu abu ɗaya mutum zai aikata - wanda bai kai kafirci ba - su fitar da shi daga Muslunci.

Amma a wajen Ibnu Taimiyya Ibnu, Imani yana rarrabuwa. Yana da tushe, yana da rassa. Duk cikinsu, rabuwa da Tushen Imani ne kaɗai zai fitar da mutum daga Muslunci.

Wannan ya sa fitar da mutum daga Muslunci yake da wahala a wajen Ibnu Taimiyya.

2- Hatta Nassoshin da suka zo da kalmar kafirci, a wajen Ibnu Taimiyya, nassoshi masu yawa ƙaramin kafirci ake nufi, ba kafirci mai fitar da mutum daga Muslunci ba. Kamar faɗin Annabi (saw):

(سباب المسلم فسوق وقتاله كفر).

"Zagin Musulmi fasiƙanci ne, yaƙarsa kuma kafirci ne".

Da ire - iren wannan Nassi.

3- Idan kuma aiki ya tabbata babban kafirci ne, kafirci mai fitar da mutum daga Muslunci, to za ka samu Ibnu Taimiyya ya sanya ƙa'idoji masu ƙarfi da suka hana saurin kafirta mutum ayyananne. Saboda aikata kafirci daban, zamowa kafiri daban. Saboda mutum zai iya aikata kafirci amma bisa jahilci, ko kuskure, ko tawili da makamancin haka. Don haka ba a kafirta mutum ayyananne har sai an tsayar masa da hujja, an yaye masa shubuha, an yanke masa dukkan hanzari.

Kuma zartas da hukuncin kafircin haƙƙin hukuma ne, ba a hannun talakawa yake ba.

Don haka duk inda ka ga Ibnu Taimiyya ya ce: mai ra'ayi kaza kafiri ne, ko wanda ya aikata kaza kafiri ne, wannan hukunci yake faɗi, ba ɗora shi yake yi a kan kowa ba. Kamar dai yadda za mu ga Aya ko Hadisi ya ce: wanda ya yi kaza kafiri ne, ko makamancin haka.

Wannan kawai hukunci ne a sake, ba a ɗora shi kan kowa ba.

4- Daga cikin manyan abubuwa da suke ƙaryata masu zargin Ibnu Taimiyya da koyar da ta'addanci, akwai cewa: a wajen Ibnu Taimiyya, ba a yaƙar kafirai don saboda kafircinsu kawai. A'a, ana yaƙarsu ne saboda suna yaƙar Musulmai, ko sun fitine su, sun hana su yin Addininsu. Wato dai ana yaƙar kafirai ne don kare kai daga ta'addancinsu.

Wannan kuwa shi ne Mazhabar Abu Hanifa, Malik da Ahmad.

Wannan ya sa Malaman Fiƙhu suke banbance tsakanin kafiri mai yaƙar musulmai (محارب), da kafirin amana (ذمي), da kafirin da aka ba shi tsaro da aminci (مستأمن). Duk cikin waɗannan, na farko ne kaɗai ake yaƙarsa.

Ashe da a ce don kafirci ake yaƙar kafirai, da duka babu wanda zai tsira a cikinsu.

Wannan ya sa Annabi (saw) ya zauna lafiya da kafirai daban - daban, ya ƙulla yarjejeniyar zaman lafiya da su. Wannan ya sa Annabi (saw) bai taɓa tilasta ma wani shiga Muslunci ba, mace ce ko namiji.

5- Wannan ya sa hatta ƴan bidi'a, za ka samu Ibnu Taimiyya ya kai matuƙa wajen yi musu uzuri. Haka kuma ba ya musu kuɗin goro, a'a, yana rarrabe tsakaninsu, yana musu adalci. Shi ya sa yake kasa ƴan bidi'a kashi uku, kuma kowane kashi yake mu'amalantarsa gwargwadon ajin da yake:

(1) Ɗan bidi'a ta kafirci:

Waɗannan su ne zindiƙai, musu hukunci irin na munafukan zamanin Annabi (saw). Kamar shugabanni da jagororin Rafidha ƴan Shi'a, da ƴan Haƙiƙa da makamantansu.

To waɗannan hukuncinsu wajen "Wala'i da Bara'i" hukuncin kafirai ne. Ba za a yi musu wala'i ba, ba za a taimake su ko a goyi bayansu ba, musamman idan sun kasance azzalumai masu yaƙar musulmai. Kamar dai Iran a yanzu.

(2) Ɗan bidi'a ta fasiƙanci (wacce ba ta kai kafirci ba):

Su ne masu bidi'a da gangan, bisa son zuciya ko neman duniya. Waɗannan hukuncinsu hukuncin masu manyan zunubai ne, wato masu kaba'ira.

Waɗannan za a yi musu "Wala'i da bara'i" rabi da rabi. A so su saboda su Musulmai ne, a ƙi su saboda fasiƙancinsu.

(3) Ɗan bidi'a mumini:

Waɗannan ƴan bidi'a ne masu son Allah da Manzonsa, masu nufin bin Allah da Manzonsa, amma saboda ƙarancin ilimi, ko kuskuren fahimta, ko tawili sai suka afka cikin bidi'a. To waɗannan hukuncinsu hukuncin Muminai ne.

Sai dai mai kira zuwa ga bidi'ar a cikinsu, za a nisance shi, za a ƙaurace masa, don kada ya fitini musulmai, da gudun shubuhohinsa.

Kamar yadda Ibnu Taimiyya yake kasa ƴan bidi'a kashi uku, daga cikinsu ya ware Sufaye ma, ya musu irin wannan kaso. Akwai kafiran cikinsu, masu guluwwi, akwai matsakaita, akwai magabatansu, waɗanda suka yi zuhudu da gudun duniya da komawa ga Allah bisa tafarkin Sunna.

Saboda haka wannan shi ne Manhajin Ibnu Taimiyya.

Shi ya sa duk wanda ya san wannan, to ya san cewa; duk wanda ya alaƙanta Ibnu Taimiyya da ta'addanci to imma jahili ne, ya jahilci waye Ibnu Taimiyya, ko maƙiyi ne, azzalumi mai son zuciya.

Don haka ka je ka karanci Ibnu Ibnu Taimiyya, don ka san cewa; Ibnu Taimiyya yaƙar ta'addanci ya yi, ba koyar da ta'addanci ba.

Dr. Aliyu Muh'd Sani (H)

Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

Post a Comment

0 Comments