Akwai 'Yan Bidi'a saboda suna dangantuwa ga kungiyoyin Bidi'a, kamar Sufanici da Shi'anci da sauransu, akwai kuma Ahlus Sunna saboda suna dangantuwa ga tafarkin Sunna, wanda ya ginu a kan Akidun Ahlus Sunna wal Jama'a.
Sau da yawa wadanda suke
dangantuwa ga Sunna suna ruduwa, kullum suna kan zargin 'Yan Bidi'a suna musu
inkarin Bidi'o'in da suka kara a cikin Ibada, kamar Bidi'o'i a Zikiri, a
Sallah, da sauran aiyukan Ibada, alhali sai ka samu su kuma masu dangantuwa ga
Sunnar suna sakaci wajen aikata Sunnonin Annabi (saw), na yawaita Zikiri, da
yawaita Ibada, da Siffantuwa da kyawawayen halayen Annabi (saw). Sai ka samu
mai dangantuwa ga Sunna yana da kaushin hali wajen mu'amala, da cin mutuncin
mutane, amma a hakan yana tinkahon shi Ahlus Sunna ne. Ta yadda da yawa irin
wadannan halinsu ya fi muni a kan halin 'yan bidi'a da suke aikata Ibada amma
tare da Bidi'a.
Ibnu Taimiyya ya ce:
((كثير
من المنكرين لبدع العبادات والعادات تجدهم مقصرين في فعل السنن من ذلك، أو الأمر
به. ولعل حال كثير منهم يكون أسوأ من حال من يأتي بتلك العبادات المشتملة على نوع
من الكراهة)).
اقتضاء
الصراط المستقيم لمخالفة أصحاب الجحيم (2/ 126)
((Da yawa daga cikin masu
inkarin Bidi'o'i a cikin Ibada da al'ada za ka same su sun gaza wajen aiki da
Sunnonin Annabi (saw) a Ibada da al'adar, ko yin umurni da shi. Kai, ta yiwu
halin da yawa daga cikin irin wadannan masu inkarin Bidi'o'in ya fi muni fiye
da halin wadanda suke aikata Ibadun da suke kunshe da karhanci)).
Saboda haka don Allah ya
waffaqa ka ga bin tafarkin Sunna, mai inkarin Bidi'a, to bai kamata a samu
sakaci wajen aikata Sunnoni da aikin Ibada, musamman wadanda kake yi wa 'Yan
Bidi'a inkarin sun shigar da Bidi'o'i a cikinsu ba, kamar Zikrori da Nafilfili
na Sallah da kuma abin da ya shafi aiki da kyawawan halaye.
Shi ya sa aka ruwaito daga
al-Hassan al-Basriy ya ce:
«إن
الإيمان ليس بالتحلي ولا بالتمني، إنما الإيمان ما وقر في القلب، وصدقه العمل»
مصنف
ابن أبي شيبة (6/ 163)
((Imani ba yin ado ba ne, ba
buri ba ne, Imani kawai shi ne abin da ya tabbata a zuciya, aiki ya gaskata
shi)).
Saboda haka Ahlus Sunna na
gaskiya shi ne mai aiki da Sunnonin Annabi (saw) a Akida da Ibadu; na Zikirori,
Nafilfilin Sallah da Azumi da Sadaka, kuma ya siffantu da kyawawan halaye,
halayen Annabi (saw), ba wanda idan aka ga halayensa na cin zarafin mutane za a
kasa banbance shi da 'yan daba ba.
Dr. Aliyu Muh'd Sani (H)
Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.