Ticker

6/recent/ticker-posts

Auren Bazawara Ga Saurayi

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum malam mene nee illa da kuma amfanin auren bazawara ga namiji saurayi wanda bai taɓa yin aure ba? Sannan kuma me yasa iyayenmu mata da abokai da sauran yan'uwa suke nuna kyamarsu tare da tsoratar da saurayi idan yace zai auri bazawara?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumussalam warahmatullahi wabarakatuhu

Auren bazawara ga saurayi wanda bai taɓa yin aure ba yana da amfani da nasarori masu yawa na rayuwa, amma kuma yana iya zuwa da wasu ƙalubalen na daban. Ba laifi ba ne a addinance ko a al'adance. Babban misali shi ne Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) wanda ya auri Sayyida Khadijah (R.A) tana bazawara shi kuma yana saurayi. Babu wani illa ga saurayin da bai taɓa aure ba idan ya auri bazawara. Sai dai zaurawan sun kasu Kashi daban daban.

Akwai mai shekaru akwai mara su. Akwai wacce take da yara akwai wacce ba ta taɓa haihuwa ba don haka ya dangancin wacce kake son ka aura kuma da yawan kai naka shekarun.

Auren bazawara ga saurayin ba ace masa yana da illa sai dai ace akwai wasu matsalolin da suke iya biyo bayan aure. Idan mace mai 'ya'ya ce kuma manya dole ne ka iya jimre gani-ganin da zasu rika yi maka. Saboda ba dukanninsu suke ganin ka cancanci auren mahaifiyarsu ba. Idan kuma kanana ne kuma a gabanta suke dole kayi jimirin daukar dawainiyar su daidai karfin ka. Idan a gaban mahaifinsu suke to ka sani dole watarana zasu kawo muku ziyara na kwana ko na yini yana da kyau ka amshe su hannu biyu-biyu. Idan kuma irin wacce ake cewa sauta ga wawa ce wannan ba ta da matsala sosai.

Amfanin auren bazawa ga wanda Bai taɓa aure ba shine ta riga ta san gwagwarmayen rayuwar aure. Tasan yadda zata kula da miji da abunda ke kewayen mijinta. Ta riga ta san dadi da wahalar zaman aure. Wannan yasa ta san yadda ake biyayya da kiyaye mutuncin miji. Ta riga ta kware wajen girki, tsabtan gida, tarbiyyar yara, da kuma kula da buƙatun miji na yau da kullum.

Yawancin gwauraye mata suna da babban buri na ganin aurensu na biyu ya zauna daram. Suna da rage yawan shagwaba ko neman abubuwa na ƙyalƙyali da 'yan mata samari ke yi. Galibi auren bazawara ba ya da yawan bukatar kuɗaɗe masu yawa irin na budurwa, wanda hakan ke sauƙaƙawa saurayi mai ƙaramin ƙarfi.

Babban matsalar auren bazawara ga wanda bai taɓa aure ba shine ta riga ta ginu akan wani tarbiya data samu wajen mijinta na baya. Kai kuma sabon shiga ne, don haka yanada wuya ka iya sauketa daga kan wannan layin. Da yake saurayin bai taɓa aure ba, fari ne sol a harkar zamantakewa. Ita kuma ta dahu. Wannan bambancin na iya haifar da rashin fahimta idan ba a yi hankali ba. Idan rabuwar auren fari ta faru ne saboda matsalar halinta, akwai yiwuwar ta dawo da wannan halin gidan sabon mijin. Akwai fargabar cewa mace na iya tunawa da tsohon mijinta, musamman idan ya kasance yana da wata sifa ta kirki da sabon mijin ba shi da ita. Muddin zaka auri bazawarar da mijinta ya mutu ya barta sai ka haɗa da hakuri, domin duk abunda zaka mata sai ta nuna maka wancan ba haka yake Mata ba koda kuwa bai mata kamar yadda kake Mata.

Iyayenmu mata sun fi son ganin ɗansu saurayi ya auri mace budurwa kamarsa, domin su yi rigo guda su girma tare, kuma duka su zama sabbi a harkar aure. Mutane da yawa suna tsoron cewa bazawara za ta juya saurayi rawar gata saboda ta ninka shi gogewa a harkar rayuwar aure. Suna tsoron tsegumin abokai da makwabta masu cewa "Wane ya kasa samun budurwa sai bazawara". Wannan tsoron abin magana yana damun iyaye sosai. Iyaye suna tsoron kar auren ya janyo wa ɗansu rigima da dangin tsohon mijin matar, ko kuma nauyin riƙon 'ya'yan wani ya fada wuyansa tun yana matashi. Iyayen kan shiga fargabar cewa ko matar tana da matsalar dabi'a ko rashin ji da ya sa aka sake ta a auren farko.

Akwai wasu dabi'un mutane da suke yi ba tare da hujja ba. Kushe auren bazawara yana cikin su. Mutane suna amfani ne da ance kace ba da hujja ba. Sau da dama ana tsoratar da samarin da ke son auren zaurawa ba da hujja ba. Kamata yayi kamin ka kushe bazawarar da saurayi ke son aure, ka tabbatar wacce yake son auren itace take da wani illa amma ba wai ka yanke mata hukunci da wata bazawarar data yi wani laifi a can ba. Suma zaurawa mutane ne. Don haka kowacce da hakinta da dabi'unta su za a duba amma ba zawarcin nata ba.

Shawara Ta Ƙarshe a musulunci da ma hankali, babban abin dubawa a aure shi ne addini, hali, da soyayya ta gaskiya, ba wai ko mace budurwa ce ko bazawara ba. Idan har ka gamsu da tarbiyyarta kuma kuna son juna, abin da ya rage shi ne ka zauna da iyayenka cikin lallashi da girmamawa don nuna musu amfanin zabinka da kuma kwantar musu da hankali.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

  ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments