𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Mene ne hukuncin karatun Alqur'ani acikin waya, irin application dinnan uzu sittin, yaya hukuncin macen da ba ta da tsarki ta dau wayar tai karatu aciki.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Alqur'anin
Application Na waya rubutacce wanda ake karantawa, kona sauti wanda ake saurara
baya ɗaukar hukinci
Alqur'ani cikakke wanda ke rubuce acikin takardu. Ya hallata taɓashi acikin wayar ko
karantashi batare da tsarki ba, kuma ya halatta shiga banɗaki da wayar, saboda
rubutun Alqur'anin dake cikin waya ba kamar rubutunsa bane dake cikin takardu,
Kawai wasu na'urorine suke bijirowa sannan saisu gushe, ba haruffa bane
tabbatattu, waya kuma ta haɗa Qur'anin dawasu abubuwan.
An tambayi shaik
Abdurrahman bin Nasir mene ne hukuncin karanta Alqur'ani na cikin waya batare
da tsarki ba?
Saiya Amsa: Abune
sananne karatun Alqur'ani wanda mutum ya haddace ba sharadi bane sai mutum yana
da tsarkin kari karami harma da babban kari, Saidai karanta Alqur'ani tare da
tsarki koda tilawa mutum zaiyi karatun shine yafi, domin zancen Allah ne, yana
daka cikin girmama zancen Allah kada akaranta sai anada tsarki.
Amma karantashi
acikin takardu sharadine kai tsaye sai idan mutum yanada tsarki, Saboda Abunda
yazo acikin hadisi shahararre ( Baya halatta aɗauki Alqur'ani ko shafarsa sai wanda
yake da tsarki) Dakuma abunda yazo na maganganun sahabbai da kuma tabi'ai akan
haka jamhurdin malamai suka tafi akai, Shine wanda yake da hadasi haramunne ya
taɓa Alqur'ani saboda
tilawa kowanin tilawa.
Abisa wannan zai
bayyana garemu cewa Alqur'anin dake cikin waya da sauran na'urori wanda ake
taskance abubuwa acikinsu baya ɗaukar hukuncin Alqur'anin dake rubuce acikin takardu,
domin rubutunsa ya saɓa da wanda yake
acikin takardu, ba zaka samesu da siffofinsu da'ake karanta su ba, saidai
asamesu asifar yanada na'urar ke bayarda haruffan yayinda aka nema, saita
bayyanar dashi a screen idan kuma ka tsallaka kan wani abun acikin wayar sai
haruffan su kau, Abisa wannan yahalatta ɗaukar wayar ko shafarta, ko wani kaset da'aka
taskance Alqur'ani acikinsa, ya halatta karantashi, koda mutum baida tsarki.
Shaik Salih Alfauzan
yace: Alqur'anin dake rubuce acikin takardu Bai hallata shafarsa ko taɓa shi ba saiga wanda
yakeda tsarki kamar yanda yazo acikin hadisi, Amma waya ba'a kiranta Alqur'ani.
Karanta Alqur'ani
acikin waya saukakawane ga mai haila, da kuma wanda ɗaukar Alqur'anin gaba
ɗaya yake masa wahala,
ko yake wajan da zai masa wahala yin alwala, saboda rashin tsarki.
Saboda haka ya
halatta macen da ba ta da tsarki ta karanta Alqur'ani na appilication, ba
haramun bane dan ta ɗauki wayar ko tayi
karatu dashi lokacin da batada tsarki.
WALLAHU A'ALAMU
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.