𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaikum malam. Shin waɗanne irin abubuwa ne suke iya halatta wa mace ta nemi saki a wajen mijinta?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumusalam
warahmatallahi wabarakatuh.
Asali dai a
shari'ance a na yin aure ne da nufin sai dai mutuwa ta raba auren ba wai da
nufin a rabu ba, shiyasa idan ya kasance Ma'aurata suna irin zamanda a
shari'ance babu wata cutuwa a tsakaninsu, to baya halatta ga Mace tanemi saki a
wajen Mijinta kamar yadda Mαnzon Allαh(Sallallahu Alaihi Wasallam) ya faɗa cewa:
"أيما
إمرأة سألت زوجها طلاقا في غير ما بأس، فحرام عليها رائحة الجنة" (رواه
الترمذي/1187)
MA'ANA: Dukkan wata
Mace da ta nemi saki a wajen Mijinta ba tare da wani tsanani (sababi) ba, to an
haramta mata taji koda ƙanshin Aljanna.
Danhaka asali a
shari'ance Mace ba ta da ikon ta nemi saki a wajen Mijinta, to amma idan ya
kasance akwai wani sababi ko wata larura da shari'a ta yarda da su to babu
laifi idan Mace tanemi saki a wajen Mijinta ba tare da ta biya shi wata
fansaba, akwai yanayin ma da yake iya zama wajibi akan Mace ta nemi a sake ta ɗin.
Danhaka Malamai
sukace ya halatta Mace ta iya neman saki a wajen Mijinta idan ya zamana
rayuwarta tana cikin wani garari a zamantakewar auratayya tsakaninta da
Mijinta, kamar Misali idan ya kasace Mijin yana munana mata, ko yana ƙauracemata ya dena
saduwa da ita ba tare dawani dalili da shari'a ta aminta dashi ba. Malamai sun
ambaci waɗansu abubuwa waɗanda a dalilinsu Mace
za ta iya neman saki a wajen Mijinta, kamar Misalin :
1. dan ba ya iya
ciyar da ita yadda ya kamata.
2. Idan ya kasance
Miji yana dukan Matarsa.
3. Idan ya kasance
Miji yana zagin Matarsa ko kuma zagin Iyayenta.
4. Idan ya kasance
Miji baya iya biyawa Matarsa buƙatar aure kuma tana cutuwa a dalilin
hakan.
5. Idan ya kasance
Matar ta ga wani aibu a tare da shi ko wata cuta.
6. Idan yakasance
yana wasa da Sallah sai yaga dama yakeyi ko kuma ba ya Azumi.
7. Idan ya kasance
mai aikata kaba'ira ne kamar shan giya ko sata ko neman Matan banza ko luwaɗi.
8. Idan ya kasance
yana ɗauke da wata cuta da
za ta iya shafar ita Matar.
9. Idan ya kasance
yana tilastawa Matar akan dole sai tayi wani abu na Saɓon Allαн(ﷻ).
10. Idan yakasance
yana ɗauke da wata cuta da
za ta iya hanawa Matar haihuwa.
11. Idan ya kasance
ba ya barin Matar taje ta sada zumunci da iyayenta da kuma 'Yan'uwanta.
12. Idan ya kasance
Matar ta ƙyamaci ɗabi'ar Mijin saboda mummunan halinsa.
13. Idan ya kasance
ba ya adalci a tsakanin Matansa wajen rabon kwana ko zamantakewarsu.
14. Idan ya kasance
sana'ar da yake yi ta haramunce kamar saida giya ko gumaka ko kuma caca.
15. Hakanan wasu daga
cikin Malamai sukace idan ya kasance Miji sunyi sharaɗi da Matarsa akan ba
zai yimata kishiya ba kuma sai yayi, ko sukayi sharaɗi akan ba zai ɗauke ta daga garinsu
ya kaita wani garinba kuma sai yakaita ɗin, to Malamai sukace idan har Miji ya saɓa ire-iren waɗannan sharuɗɗa to ya halatta Mace
ta nemi a saketa.
Danhaka kenan a yayin
da Mace ta samu kanta a wasu daga cikin sabuba makamantan waɗanda aka ambata, to
idan za ta iya yin haƙuri da juriya a hakan tare da shi, to babu laifi su
cigaba da zamansu tare, amma idan taga ba za ta iya jurewaba to alal-haƙiƙa ya halatta tanemi
Mijin ya saketa, amma idan ya kasance Mijin ba ya yin sallah ne ko azumi ko
kuma wasu abubuwan da Allαн(ﷻ) ya wajabta masa, to da farko ya kamata
tayi masa wa'azi ko tasa ayi masa, idan kuma yaƙi denawa to bai
halatta ta cigaba da zama da shi ba, danhaka wajibi ne ta nemi ya saketa dan
tatsira da addininta awajen Allαн(ﷻ)
шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.