Ticker

6/recent/ticker-posts

Siffar Ramukon Sallah

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalam da fatan malam na lafiya, ya ibada da hakuri da jama'a? Ina da wasu tambayoyi da nake so a taimaka min da amsoshinsu.

1. Nine na makara sallar asubah, ban tashi daga barci ba har sai 7 oclock (karfe bakwai) rana ya fito kuma naji ance alokacin ne shaiɗan yake matso da kahonsa kusa da rana, idan mutum na sallah alokacin tamkar shi Shaiɗan ɗin yake bautawa. To awani lokaci ne ya kamata mutum ya rama wannan sallan?

2. Akwai salloli da ake bina bashi na shekaru 2 Wanda nake so in fara biya. misali idan alokacin sallar magrib ne bayan na idar sai kuma nake so in biya azahar na bashin da ake bina yaya zan biya tunda sallar zuhr a asirce ne kuma ana lokacin magrib na bayyanawa ne. shin zanyi sallar a asirce ne ko yaya.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumus salam wa rahmatullah.

Da farko dai waccen labarin da ka faɗa, ba haka yake kai tsaye ba. Amma dai abinda ya tabbata a hadisan Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) shi ne : Imamu Ahmad da Muslim sun ruwaito hadisi ta hanyar Sayyiduna Amru bn 'Abisah (radhiyallahu anhu) yace "Nace wa Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) "Ya Annabin Allah bani labari game da sallah". Sai yace "Ka sallaci sallar asubah sannan ka kame daga yin sallah har sai rana ta fito, ta 'dago domin ita tana fitowa ne ta tsakanin Ƙahon wani shaiɗani kuma awannan lokacin ne kafirai suke yi mata Sujadah ...".

Imamun Nawawiy yace "Shi shaiɗanin yana kusantar da kansa ne zuwa ga rana a irin waɗannan lokutan domin ya zamanto masu yi mata sujadah daga cikin kafirai tamkar shi suke yiwa sujadar a zahiri".

To kaga anan Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya bayyana cewa an hana yin sallah ne a irin waɗannan lokutan saboda kada muyi tarayya da kafirai cikin irin abinda suke yi adaidai lokacin. To amma wannan hanin bai shafi sallolin ramuko ba.

Mafiya yawan Maluman Fiƙhu sun tafi akan halaccin yin ramuko (Ƙadha'i) koda bayan sallar asubah ne ko bayan la'asar Sun dogara da Ingantaccen hadisin da Bukhariy da Muslim suka ruwaito Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) yace "DUK WANDA YA MANTA DA WATA SALLAH, TO YA SALLACETA IDAN YA TUNOTA".

Don haka ita sallar ramuko babu wani lokacin da aka hana yinta. Zaka iya yinta akowanne lokaci. Kuma zaka yita ne bisa yanayin da ta tsere maka, kuma akan yanayin da ake yinta.

Misali idan sallar azahar ce ko La'asar zaka yi karatunsu a Ɓoye ne koda acikin dare zaka ramasu. Sannan koda sallar asubah zaka rama, ko maghriba ko isha'i to zakayi karatunsu afili ne koda da rana zaka ramasu.

Hakanan sallar da ta tsere maka alokacin kana gida, zaka yita ne cikakkiya (ba Ƙasaru ba) koda sanda zaka ramasu ɗin kana wajen tafiya ne. Haka kuma sallolin da suka tsere maka akan yanayin tafiya ko balaguro, to zaka ramasu ne bisa yanayin sallolin tafiya (Ƙasaru) koda kuwa agida zaka ramasu).

Don Ƙarin bayani ka duba babin dake bayanin yadda ake ramukon sallah acikin littafin Risalatul Ƙairawaniy, Muƙaddamatul Iziyyah, da Matnul Ashmawiyyah, da Matnul Akhdhariy.

Anan nake so inyi maka gargadi game da barin sallah ta wuceka da gangan, ko kuma yin sakaci wajen ramasu. Wannan haramun ne domin kuwa yana daga cikin wasa da sallah. Kuma Allah yace "AZABA TA TABBATA GA MASALLATA. MASU YIN SAKACI AKAN SALLARSU".

Kaji tsoron Allah ka kiyaye dokokinsa. Sallah ita ce mafi girman dukkan ibadodi kuma ita za'a fara dubawa a ikin ayyukanka aranar Alkiyamah. Idan tayi kyau ka tsira. Idan kuma ta 'baci (saboda rashin yinta akan lokaci, ko rashin yinta da ilimi, ko rashin sanya tsoron Allah cikinta) to mutum yayi asara mai girma. (Allah shi kiyayemu).

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...

 ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments