Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Hirar Batsa (Sex-Chat)

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalmu alaikum, Mene ne hukuncin Mutanen da sukeyin Sex-Chat, wato hirar batsa ta hanyar rubutun Text ko ta hanyar rubutu a Social-Media musamman ta WhatsApp? Malam wallahi na Shiga bala'i Ka taimakeni Nidai mutum ne Wanda Allah ya jarabceni da karfin sha'awa Kuma ban taɓa yin zina ba To Amma wannan WhatsApp ɗin ya haɗani da mutanen banza an shigar dani wani group na batsa hotunan banza da videos ɗin banza Duk ina ganinsu Rana ɗaya sheɗan yayi tasiri a kaina wlh Malam wata yarinya da muka haɗu da ita har hoton farjinta ta turomin nima na tura mata nawa, Sai da na Riga na aikata hakan Abin yaketa damuna Na tuba Malam Allah zai yafe min kuwa? Sannan kuma Malam wane abu zan dage da yi Wanda Allah bazai kamani da laifin ba Wallahi nayi nadama.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumussalam warahmatullahi wabarakatuhu

To itadai hirar da akeyi ta batsa atsakanin Namiji da Mace ta hanyar Ƙiran Waya ko rubutaccen saƙo kamar yadda aka fi saninta da sunan Sex-Chatting, ko Shakka babu wannan wata Musibace da Fitina wacce ta addabi Al'ummar wannan Zamani damuke cikinsa, tun daga kan Maza har Mata, masu aure da marasa aure, wasuma daga cikinsu za ka samu cewa Ɗaliban Ilimine, danhaka al'amarin dai sai wanda Aʟʟαн ( ) Ya tsallakar kawai, itadai wannan hirar batsa takasune gida biyu.

1. ko da yakasance Namiji zai yi irin wannan hirarne da Matarsa itama Mace tayi da Mijinta.

2. Kokuma ya kasance Mutum zai yi irin wannan hirarne da Matar da ba tasaba ko Mijin da ba nataba

Idan ya zamana Mutum zai yi irin wannan hirarne da Matarsa ko Mace tayi da Mijinta, to yakan iya zama Halal amma Saida Sharuɗɗa guda biyu:

1. Sharaɗi nafarko yakasance babu wani Mutum akusa dasu ta yadda zai iyajin hirar dasukeyi atsakaninsu idan yazamana suna hirarne ta hanyar Ƙiran Waya, idan kuma ta hanyar rubutune to ya kasance sunkiyaye ta yadda babu wani wanda zai iyaganin hirar dasukayi acikin rubutun, kokuma yaga irin hotunan sassan jikinsu da suka aikawa junansu, balle kuma Mutum yace zaije ya nunawa abokansa ko ita ta nunawa ƙawayenta irin hirar da sukeyi.

2. Sharaɗi nabiyu, ya kasance tsakanin Matar da Mijin dukkansu sun aminta da kansu cewa wannan hirar da sukeyi bazata kaisu ga aikata dukkan wani abu ta hanyar wasa da jikinsu wanda hakan zai iya kaisu ga sunfitar da Maniyyinsu ba, wato abinda da aka fi sani da suna istimna'i (Masturbation) idan waɗannan Sharuɗɗa guda biyu suka cika to ya halatta ma'aurata suyi atsakaninsu, amma idan hirar zata iyasa wani daga cikinsu kokuma suduka sukai ga sunkasa iya mallakar kansu harsai Mutum yayi abinda zai sashi yafitar da Maniyyinsa to anan suma kansu ma'auratan yazama haramun suyi irin wannan saboda wancan mummunan aikin da hirar zata iya kaisu ga aikatashi, domin a Shari'ance akan iya Haramta abinda yake Halalne idan yakasance zai iya kai Mutum ga aikata Haramun, amma idan yakasance hirace kawai sukeyi atsakaninsu har Sha'awar Mutum takai Ƙololuwa yayi Inzalin-Maniyyi batare da yayi amfani da hannunsa ba ko wani abu dabam to wannan babu laifi ya halatta,

Amma idan yakasance ita wannan hirar ta batsa maisuna Sex-Chatting, tana gudanane atsakanin waɗanda ba ma'aurataba wanda kuma dama galibi ita wannan hirar anfi yintane ko da tsakanin Samari da 'Yammata, ko Samari da Matan aure, ko Maza masu aure da 'Yammata, kokuma Mazan aure da wasu Matan auren da ba nasuba, danhaka wannan ko kokwanto babu akancewa yin wannan hirar Haramunne Ƙaulan-Wahidan, danhaka wajibine akan masu wannan aiki suyi gaggawar tuba zuwa ga Aʟʟαн( ).

Maganar yafewa Kuwa: Allah yana yafe kowanne zunubi da bawa ya ke aikatawa, idan ya tuba, amma banda shirka wato hadashi da Wani bawansa wajan bauta. Kamar yanda Ayoyi da hadisai ingantattu da dama Suka nuna, Amma akwai sharudan tuba:

1. Dena zuzunubi.

2. Nadama Akan saɓon.

3. Ya Qudurci niyyar, bazai sake aikata aikin ba.

Idan aka rasa ɗaya daka cikin ukun nan tuba bai tabbata ba. Sannnan kuma banda hakki mutane iyaka hankinka tsakaninka da Allah. Sannan kuma kadege da neman gafarar Allah, ka nesanci duk abinda zai kai ka ga aikata zantukan da zasu tada maka sha'awa, Sannan ka lizimci azumin lafila saboda sha'awa da take damunka, da ya waita istgfari.

Allah ya tsaremu.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments