𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaikum. Tambayata ita ce shin akwai banbancin kabli da ba'adi tsakanin sallolin na farilla da nafila kuma ya ake gane kabli da ba'adi Kuma ya ake gyara su?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumusalam
warahmatallahi wabarakatuh.
Da farko mu sani cewar duk
abinda yake farilla ne a sallah kuma akabarshi to kabaliyyah ko ba’adiyyah bata
gyarashi, to haka hukuncin yake a salloli na nafila. Haka kuma duk abinda
mustahabbine a sallah to shima ba’a yi masa kabaliyyah ko ba’adiyyah.
Dukkan rafkannuwa da aka yi
ta a lokacin da ake ramuwar sallah to hukuncinta kamar sallar da ake yinta ne a
cikin lokaci, kenan ba banbanci da sallolin ramuwa da kuma waɗanda
ake yinsu cikin lokaci.
Yin rafkannuwa a sallar
nafila hukuncinsa kamar yin ranfannuwa ne a sallolin farilla in banda mas’aloli
guda shida ananne nafila ta banbanta da farilla, sune kuma kamar haka:
1. KARATUN FATIHA: Duk wanda
ya manta da karatun fatiha a sallar nafila bai tunaba sai bayan ya yi ruku’u
sannan ya tuna to anan zai cigaba da sallar shine sai bayan ya kammala ya yi
kabaliyyah, saɓanin sallar farilla da zai cire wannan
raka’ar ya kawo wata makwafinta sannan ya yi ba’adiyyah idan ba’a biyun farko
bane, ko kabaliyyah idan hakan ya farune a biyun farko na farilla.
2. KARATUN SURA.
3. BAYYANAWA.
4. SIRRANTAWA.
Idan mutum ya manta karatun
sura bayan fatiha a cikin sallar nafila, ko kuma ya bayyana a inda ake asurtawa
ko ya sirranta a inda ake bayyanawa kuma bai tunaba sai bayan da ya yi ruku’i
to zai cigaba da sallar shine, amma duka a cikin nafila to babu komai akansa,
wato ba kabaliyyah kuma ba ba’adiyyah, saɓanin
inda sallar farilla ce.
5. TASHI ZUWA RAKA’A TA UKU:
Duk wanda ya kammala raka’o’i biyu a sallar nafila sai bai zauna ba ya mike
zuwa raka’a ta uku to idan ya tuna kafin ya kulla ruku’u to anan zai dawo ya
zauna ya yi tahiya ya yi sallama, sannan kuma ya yi ba’adiyyah, amma har idan
ya kulla raka’a ta uku to zai cigaba ne da sallar sai ya kara ta zama raka’o’i
huɗu
sannan sai ya yi kabaliyyah, saɓanin sallar farilla.
6. MANTA RUKUNI: Duk wanda
ya manta rukuni a sallar nafila kamar ruku’i ko sujjada kuma bai tuna ba har ya
yi sallama kuma abin ma ya yi tsawo to anan ba zai sake sallar ba, saɓanin
sallar farilla, domin inda farillace to da zai sake sallarne har abada .
Waɗannan
sune wuraren da aka dan sami banbanci tsakanin salloli na farilla da salloli na
nafila akan abinda ya shafi hukunce-hukuncen rafkannuwa, da fatan Allah yasa ya
anfanar da mu.
WALLAHU A'ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.