HANYAR DA MIJI ZAI BI YA BIYA BUƘATARSA DA MATARSA LOKACIN DA TAKE HAILA
𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaikum. Shin ya halasta na bi wasu hanyoyi wadanda ba saduwa ba na biya wa Mijina bukata lokacin da nake jinin haila? Kuma mijina zai iya shan nonona?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus Salam
warahamtullahi Wabarkatuh
Miji yanada hurumi da 'yanci
yaji daɗi da
matarsa ta duk inda ya so ajikin matarsa, itama haka, ba'a haramta masa komai na
jikinta ba sai saduwa da ita ta dubura, wato kaciyarsa ta shiga duburar ta, da
kuma saduwa lokacin da take haila ko jinin haihuwa, banda wannan guri, da
lokuta yana da damar yaji daɗi da ita da duk abunda yaso
yaji daɗin
dashi na jikinta, kamar kiss, da kallo, da shafa, da makamantansu.
Koda zai sha nononta, ba'a
cewa ruwan nonon zaiyi tasiri idan ya sha lokacin dayake sha, ya shiga cikin
jin daɗi da
matarsa da duk inda yaso a jikinta, domin babba dan yasha nonon mace baya
tasiri wajan ta zamto haramun agare shi, shayarwar da take tasiri itace wacce
take haramta auren macen da kasha nono ɗaya
da ita shine wanda zaka sha kana dan shekara biyu ne kawai.
Shaikh Saleh Al-Uthaimeen
Rahimahullah) yace: shayarwar babba bata tasiri, Ma'ana babba yasha ruwan nonon
mace baya tasiri wajan ta zamto haramun a gareshi, shan da ya ke tasiri shine
wanda yakai sha guda biyar ko sama da haka cikin shakaru biyun farko na rayuwar
mutum kafin ayayeshi, Amma shan babba baya tasiri, abisa wannan daza'a kaddara
mutum yasha nonon matarsa kota shayar dashi, ba zai zamto kamar danta ba wajan
haramcin aure a tsakanin su.
{Fatawa Al-Islamiyya,
3/338}.
Ya halasta ga miji yaji dadi
da dukkan jikin matarsa, banda dubura da kuma lokacin da take jinin haila, da
lokacin da take jinin haihuwa, dakuma lokacin da sukai ihrami dan aikin hajji
ko umrah, har sai sun kammala aikin hajjin ko umara sun cire ihrami
(Fataawa Al-Lajnatu
Al-da'imah, 19/351-352)
Amma halaccin yaji daɗi da
dukkan jikinta ga kaɗan daka maganganun malamai:
Ibnu Qudamah {Rahimahullah}
yace: Babu laifi mutum yaji daɗi da matarsa koda
tsakankanin duburar ta ne matukar bazai sa kaciyarsa ciki ba, domin Sunnah ta
ruwaito haramcin hakan ta dubura, an keɓance
shine da kada ya sanya kaciyarsa ciki kawai, ko kuma saboda cewa wajene na
kazanta, sai aka keɓance haramcin hakan gareshi.
{Al-mughni na Ibn Qudaamah,
3/226}.
Al-kisãny yace: Yana daga
hukunce-hukuncen aure ingantacce halaccin kallan komai na mace da kuma shafawa
tun daga kanta har zuwa dun-duniyarta alokacin da take raye, domin saduwa tana
samuwa ne ta hanyar kallo da kuma shafa, sai ya kasance halaccin sa halaccin kallo
da shafa sune hanyar farko
{Bada'i'u sana'i'i, 2/231}.
Ibnu Abideen yace: Abu Yusuf
ya tambayi Abu hanifa game da mutumin dayake shafa farjin matarsa tana shafa
farjinsa dan yaji daɗi da ita shin kana ganin
hakan laifi ne?, sai Abu hanifa yace: a'a ina fatan ma ladansu ya girmama.
(Raddil mukhtaar, 6/367).
Hakika Annabi salallahu
Alaihi wa sallam ya nassanta wannan halaccin da haramta saduwa da mai haila ta
farjinta da halatta sauran gurare na jikinta, alokacin da bata haila halaccin
yafi fitowa karara.
Shaeik Saleh Al-Uthaimeen
rahimahullah yace: faɗin Annabi salallahu Alaihi
wasallam cewa mutum karyayi jima'i da matarsa intana haila, ana nufin zaiji daɗi da
ita a sauran jikinta indai ba farji ba, ya halatta yaji daɗi da
ita daga cibiyar ta dama abunda yake kasa da cibiyar ta, sai dai ya kamata tayi
kunzugu, sabida Manzon Allah salallahu Alaihi wa sallam yakan umarci Aisha tayi
kunzugu in tana haila ya rungumeta, umarnin da Manzon Allah salallahu Alaihi wa
sallam yayi na tayi kunzugu, dan kada yaga abunda baya so na jinin haila tare
da ita ne, idan mutum yaso yaji daɗi da
ita ta tsakanin cinyoyin ta babu laifi.
Idan wani yace toh yaya
zakayi da faɗin Manzon Allah salallahu Alaihi wa
sallam lokacin da aka tambaye shi menene ya halatta ga mutum ajikin matarsa
idan tana haila, sai yacewa mai tambayar _"daga cibiyar ta zuwa
sama"_ ai wannan dalili ne yake nuna abunda ya halatta ga mutum kawai
ajikin matarsa idan tana haila shine daga cibiyar ta zuwa sama.
Saika Amsa masa da wadannan
jawaban;
1. Annabi ya haramta ne dan
tsarkake mutum daga shi jinin, da kuma tsoratarwa ga abunda ake tsoran mutum ya
auka na saduwa da ita tana haila.
2. Hadisin zaka dora shi
akan saɓanin
lokuta, faɗin sa salallahu Alaihi wa sallam
_"ku aikata komai dasu idan suna haila, saduwa ce kawai baza kuyi dasu
ba"_ Wannan ga wanda zai iya mallake kansa zai iya wasa da matarsa ko tayi
masa duk abun da zatayi masa tagama, zai iya mallake kansa bazai jewa farjin ta
ba.
Faɗin
sa kuma da yace daga saman cibinta zuwa sama, ga wanda bazai iya mallake kansa
ba kodai sabida karancin addinin sa ko sabida karfin sha'awarsa.
Sharhil mumta'a, 1/417).
Sabida waɗannan
maganganu ya halatta kibi hanyoyin da zaki iya gamsar da Mijin ki idan kina
jinin haila ko na nifaasi.
WALLAHU A'ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa
Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.