CITATION: Mujaheed, A. (2025). “Gudummawar Gasa Wajen Bunƙasar Rubutun Gajerun Labaran Hausa” Tauraruwa Journal of Hausa Studies, Vol. 4, No. 1 December, 2025. Department of Nigerian Languages Federal University of Lafia. Pg 92-104, ISSN: 2814-0222.
GUDUMMAWAR GASA WAJEN BUNƘASAR RUBUTUN
GAJERUN LABARAN HAUSA
Daga
Abdullahi Mujaheed, PhD
Sashen Harsunan Nijeriya da Kimiyar Harsuna,
Jami’ar Jihar Kaduna
mujaheedabdullahi@gmail.com
+2348069299109, +2348156747550
Tsakure
Gajerun
labaran Hausa a rubuce sun fara samuwa ne tun daga lokacin da aka yanke wa harkar
ɗab’i cibi a ƙasar Hausa ta hannun hukumomin inganta adabi. Duk da cewa an
gudanar da wasu nazarce-nazarce a fagen gajerun labaran Hausa da kuma gasannin rubutun
gajerun labarai bisa manufofi daban-daban, har yanzu ba a sami wani nazari da ya mayar da hankali kacokam a kan rawar
da gasa ta taka a fagen gajerun labaran Hausa ba. Wannan dalilin ne ya haifar da gudanar da wannan bincike bisa manufar daddale
gudummawar gasa wajen bunƙasar rubutun gajerun labaran Hausa. Hanyoyin da aka bi wajen gudanar da
binciken sun haɗa da neman bayanai tare da bibiya da halartar tarurruka da
shirye-shiryen gasannin rubutun gajerun labaran Hausa. An tuntuɓi masana da manazarta
da kuma marubutan gajerun labarai. An yi amfani da kafar intanet wajen
tattaro wasu bayanan. Haka kuma, an yi amfani da Ra'in Fagen Adabi (Literary Field Theory) na Pierre Félix
Bourdieu (1930–2002) wajen bayyana yadda gasa take zama wani fage na samar
da adabi da samun lambobin yabo, sai kuma Ra'in Zamantakewa da Al’adu (Sociocultural Theory) na Lev Semyonovich Vygotsky (1896–1934) wanda aka yi amfani da shi
wajen bayyana yadda hulɗa da haɗin gwiwa a cikin gasa ke ƙarfafa koyo da
ƙirƙira da bunƙasar adabi. Binciken ya gano cewa gasa tana taka muhimmiyar rawa
wajen bunƙasa rubutun gajerun labaran Hausa tare da fito da sababbin marubuta
da labaransu masu ƙunshe da saƙonni mabambanta daidai da ƙa’idojin da kowace
gasa ta shimfiɗa.
Fitilun
Kalmomi: Gudummuwa, Bunƙasa, Gasa, Gajeren Labari, Rubutun Hausa.
1.
Gabatarwa
Gajeren labari
kamar yadda sunansa ya nuna, taƙaitaccen labari ne wanda galibi yake ƙunshe da
manyan taurarin da ba su wuce uku ba, cikin kalmomi ƙalilan da ba su gaza dubu
ɗaya (1,000), kuma ba su wuce dubu bakwai da ɗari biyar (7,500) ba. Yana ƙunshe
da wasu batutuwa na rayuwar zahiri ko ƙirƙirarru domin isar da wani saƙo cikin
zubi sassauƙa. A ire-iren waɗannan labaran, ana warware ƙulli cikin sauri, ko
kuma akan ƙare labari a buɗe, a bar mai karatu da yanke hukunci.
Gajerun labarai waɗanda
aka wallafa su cikin littafi ko intanet da sauran hanyoyin rubutu da karatu na
zamani, sun samu ne bayan samuwar rubutu da karatu a cikin duk al’ummar da aka
same su. Haka kuma, fasahar samar da gajeren labari a matsayin nau’in adabi, ya
daɗe a sassan duniya, ciki har da ƙasar Hausa. Duk da yake, gano asalin gajeren
labari na baka zai yi wuya, amma bincike ya gano cewa wanda ya fara ƙirƙiro
rubutun da ake iya gani a siffar gajeren labari (na adabi) shi ne Nicola
Vasilievitch GoGol wanda aka haife shi a Sorochintsky ta ƙasar Rasha a shekarar
1809, shekarar da aka haifi Edgar Allen Poe a Baltimore. Daga waɗannan mutane
ne za a iya riskar tushen samuwar rubutattun gajerun labarai (Bates 1972: Shf.
6 cikin Abdo El-Rahman, 1996: Shf. 7).
Gasa kuwa
wani al’amari ne da ake shiryawa kuma a gudanar a tsakanin mutum biyu ko fiye a
kan wani abu guda ɗaya domin fitar da gwani daga cikin gwanaye a kan wani abu
ko al’amari. Kuma an ɗauki gasa a matsayin siyasa wadda kan sanya wani abu ya
bunƙasa, ya watsu tare da barbazuwa a cikin al’umma ko ana so ko ba a so
(Ɗan’amarya, 2012: Shf.50).
Saboda haka,
gasa tana daga cikin muhimman hanyoyin da suka bunƙasa rubutun ƙagaggun labarai
ƙasar Hausa. Shi ya sa wannan nazari ya keɓanta ga fito da gudummawar gasa
wajen bunƙasar rubutun gajerun labaran Hausa. Baya ga shimfiɗa, Aikin ya ƙunshi
ra’o’in bincike da hanyoyin gudanar da bincike. Akwai kuma waiwayen yadda gasar
rubutun ƙagaggun labarai ta faro a ƙasar Hausa. Daga nan aka tuƙe da daddale
bayanan gudummawar gasa a fagen bunƙasar gajerun labaran Hausa.
2.
Ra’in
Bincike
Ra'o’i biyu aka ɗora kan
wannan bincike, su ne Ra'in Fagen Adabi (Literary
Field Theory) na Pierre Félix Bourdieu (1930–2002) da kuma Ra'in
Zamantakewa da Al’adu (Sociocultural
Theory) na Lev Semyonovich Vygotsky (1896–1934). Dukkansu sun dace da bayyana rawar da gasa ke takawa wajen bunƙasa
rubutun gajerun labaran Hausa.
Ra'in Fagen Adabi na Bourdieu, kamar yadda ya nuna a cikin aikinsa mai suna The Field of Cultural Production: Essays on Art and Literature (1993),
ya jaddada cewa adabi yana
bunƙasa ne a cikin wani 'fage' na samar da al'adu da adabi inda marubuta da cibiyoyi
da masu sharhi kan adabi da masu karatu suke mu’amala da juna (Bourdieu, 1993).
A cikin wannan fage, irin tarin al’adun da suke tattare da fagen, kamar bayar da lambar yabo
da samun ƙima da kyaututtukan adabi, suna taka rawa wajen bunƙasa nau’o’in rubutu.
A mahangar adabin Hausa, gasa tana zama dandalin da matasa marubuta ke samun
ƙima da yabo da sahalewa. Gasa tana ba da dama ga marubutan gajerun labarai su
fafata, su nuna fasaha, su kuma samu amincewa daga takwarorinsu da masana.
Wannan tsari yana taimakawa wajen kafa ƙa’idoji masu inganci tare da samar da
sababbin marubuta da kuma tabbatar da gajerun labarai a matsayin muhimmin nau'i
na adabin Hausa.
A ɗaya ɓangaren, Ra'in
Zamantakewa da Al’adu na Vygotsky kamar yadda ya ɗabbaƙa a cikin aikinsa mai
suna Mind in Society: The Development of
Higher Psychological Processes (1978), yana bayani ne a kan yadda hulɗar
zamantakewa da al’adu suke taka muhimmiyar rawa wajen haɓaka ilimi da ƙirƙira.
Vygotsky (1978) ya bayyana cewa, bunƙasar mutum tana da alaƙa kai-tsaye da
ƙwarewarsa ta al’adu da hulɗar zamantakewa. Gasa a matsayin wata al’ada ta
haɗin kai, tana samar da wani yanayi ga marubuta wanda yake ba su damar koyo
daga junansu tare da musayar ra’ayi da inganta ƙwarewarsu ta rubutu. Baya ga
bunƙasa ƙirƙira, tsarin rubutu don gasa yana ƙarfafa alaƙa da zumunci tsakanin
marubuta. Hakan kuma ke taimakawa wajen ɗorewar rubutun
gajerun labaran Hausa.
A taƙaice, waɗannan ra'o'i biyu sun samar da
cikakken ginshiƙi ga wannan bincike. Yayin da Ra'in Fagen Adabi ya bayyana
yadda gasa take zama wani fage na samar da adabi da samun lambobin yabo, shi
kuma Ra'in Zamantakewa da Al’adu yake bayyana yadda hulɗa da haɗin gwiwa a
cikin gasa ke ƙarfafa koyo da ƙirƙira da bunƙasar adabi.
3.
Hanyoyin
Gudanar da Bincike
Hanyoyi na kai-tsaye aka
bi domin gudanar da wannan bincike. Hanyoyin sun haɗa da yawon neman bayanai tare
da bibiya da halartar tarurruka da shirye-shirye da suka shafi gasannin rubutun gajerun labaran Hausa. An tuntuɓi masana da manazarta da kuma marubutan gajerun labarai. Har ila yau, an yi
karance-karance daga rubutattun bayanai da kuma amfani da na’urorin zamani da
kafafen intanet da sauransu.
4.
Gasa da Bunƙasar
Rubutattun Gajerun Labaran Hausa Bisa Faifai
Bincike ya
tabbatar da cewa, gasar samar da ƙagaggen labarin Hausa tana da daɗaɗɗen
tarihi, kusan ana iya cewa ita ce tushe na samuwar rubutaccen ƙagaggen labarin
Hausa. Kuma abin sha’awa, ana jin an
fara ƙoƙarin shirya gasa domin samar da ƙagaggen labarin Hausa tun a shekarar
1927 a Kwalejin Katsina, inda aka nuna cewa Abubakar Imam yana cikin waɗanda
suka shiga gasar kuma ya yi nasara, amma fa abin da aka rubuta ɗin bai zo hannu
ba. Duk da haka, ana danganta shekarar 1927 da mafarin rubutun labarin Hausa (Malumfashi,
2009).
4.1 Gasar Hukumar Ƙasa
da Ƙasa ta Nazarin Harsuna da Al’adun Afirka
A shekarar 1929 Hukumar Ƙasa da Ƙasa ta Nazarin Harsuna da Al’adun Afirka
mai mazauni a Ingila ta gudanar da wata gasa domin samar da littattafan zube
daga harsunan Afirka ciki har da Hausa. A wannan gasa an samu labaran Hausa
waɗanda suka sha yabo, wato Hausa Stories guda biyu na H.B.G Nuhu da na Malam Dodo, sai Zaman Dara na Malam Ahemed Mettedden da Littafin
Karatu Na Hausa na Malam Bello Kagara da Takobin Gaskiya na
Malam Nagwamatse sai kuma Labaran Hausa
na Ɗan Malam Alƙali Sokoto (Ɗan’Amarya,
2012: Shf. 78). Duk da yake ba a samu labaran a hannun ba, amma ko daga jin sunayen wasu daga cikin waɗannan labarai, an gane cewa kundaye
ne na gajerun labarai, misali Hausa
Stories da Labaran Hausa. Bugu da
ƙari, idan aka yi la’akari da littafin Hausa
Stories na Malam Dodo za a tarar cewa ya rubuta shi ne ta hanyar harhaɗa
tatsuniyoyin Hausawa. Saboda haka, wannan ya tabbatar da cewa tun a shekarar 1929 aka
fara jin ɗuriyar rubutun gajerun labaran Hausa waɗanda gasa ta samar.
Daga wannan lokaci, an cigaba da samun gasa domin samar da ƙagaggun
labaran Hausa. Misali, gasar da Hukumar fassara ta shirya a shekarar 1933, da
wadda Hukumar NNPC ta shirya a shekarar 1978, sai kuma gasar da Hukumar Kula Da Nazarin Al’adu ta Tarayya a shekarar 1980 da ta Hukumar Kula da
Kyautata Fasaha da Al’adu ta Jihar Kaduna a shekarar 1988 (Ɗan’Amarya, 2012).
Sai dai duk waɗannan sun samar da dogayen labarai ne, ba gajerun labarai ba.
4.2 Gasar Gidauniyar
Bashir Ƙaraye
Gidauniyar Injiniya Muhammad Bashir Ƙaraye ta shirya gasa
domin samar da rubutun zube tsawon shekaru uku a jere 2007 zuwa 2009. A cikin
labaran da suka yi nasara a shekarar 2008 ne aka samu littafin Saba Ɗan Sababi na Hafsat M.A Abdulwaheed
wanda ya zo na uku a gasar. Littafin ya kasance kundin gajerun labarai ne guda 12
masu alaƙa da juna, inda marubuciyar ta tsara su da zubi irin na littafin Magana Jari Ce 1-3 na Abubakar Imam,
wato ta gina gajerun labaran da suke cikin littafin ne daga uwar labarin da ta
ƙulla tun daga farko (Faruk, 2018). A taƙaice dai, littafin gajerun labarai ne
masu ɗauke da darussa na nishaɗantarwa da tarbiyyantarwa waɗanda aka tsara
domin samar da abokin hira ga masu sha’awar karatun littattafai. Ita kanta
marubuciyar ta jaddada hakan a gabatarwar littafin:
“...wannan littafi na ɗaya ne kuma yana ɗauke da labarai goma sha biyu. Ina
fatan wannan littafi zai zama abin koyon tarbiyya da kuma nishaɗantarwa ga masu
karanta shi a cikin makarantu ne ko a wajen jama’ar gari, fatana kwalliya ta
biya kudin sabulunta.” (Abdulwahid, 2008: Shf.7).
Daga wannan lokaci, an cigaba da gudanar da gasa jefi-jefi don samar da
rubutattun gajerun labaran Hausa har zuwa lokacin da hukumomi da ƙungiyoyi da
ɗaiɗaikun mutane suka rungumi sanya gasanni don rubuta gajerun labaran Hausa. Ana
iya cewa abin da ya sake farfaɗo da rubuce-rubucen ƙagaggun labaran Hausa shi
ne rungumar rubutun gajeren labari, wanda cikin batutuwan da suka bunƙasa shi
akwai gasa wadda ita ce kan gaba, in ma ba a ce gasar ce kanwa-uwar-gami ba.
4.3 Gasar Makarantar Malam Bambadiya
A shekarar 2013 ne aka fara shirya gasa, musamman domin samar da
rubutattun gajerun labarai lokacin Makarantar
Malam Bambadiya (wani dandali a kafar intanet ta Facebook) a ƙarƙashin jagorancin Farfesa Ibrahim Malumfashi. Wannan
makaranta ta shirya gasar rubutun gajerun labarai a kan matsalar bara a ƙasar
Hausa, wadda aka yi bikin bayar da kyaututtuka a watan Satumbar 2014 a Jami’ar
Jihar Kaduna. An tsara za a buga labaran da suka shiga gasar kuma suka ƙayatar
daga na 1 zuwa na 20 cikin littafin da aka raɗa wa suna Jamhuriyar Mabarata, sai dai har zuwa yau(2025), ba a samu buga
wannan littafi ba.
Daga wannan lokaci, sai aka shimfiɗa tabarmar ware wani jigo na musamman
domin sanya gasar rubutun gajerun labarai a kan shi.
4.4 Gasar Pleasant Library, Katsina
A shekarar 2018 an gudanar da gasar gajerun labarai a kan jigon talauci wanda Makarantar Malam Bambadiya suka haɗa gwiwa da Pleasent Library,
Katsina suka ɗauki nauyi. Ita ma wannan gasar, ba a samar da littafi
bugagge na labaran da suka yi nasara ba. Sai dai an bayyana labarai
guda uku waɗanda suka lashe gasar, su ne;
i. “Matalauciyar Rayuwa” na Kabiru Yusuf Fagge (Anka)
ii. “A Sasanta” na Hassana Abdullahi Hunƙuyi
iii. “Da Sandar Hannunka” na Zakariyya Haruna Ɗanladi.
4.5 Gasar BBC Hausa
Tun daga shekarar 2016 hukumar gidan rediyon BBC da ke
Landan suke sanya gasar Hikayata ta mata zalla domin rubutun
gajerun labarai. Babbar manufar wannan gasa ita ce fitar da
matsalolin da suke addabar mata daga bakin mata ‘yan’uwansu, kamar dai yadda
Bahaushe ya ce ‘ciwon ‘ya mace na ‘ya mace ne.’ To sai dai ba a keɓe wani jigo
na musamman da za a rubuta labaran a kai ba. Duk da haka, a bisa wannan
fasalin, duk shekara ana fitar da labarai 100, sai a tace 25 waɗanda a cikinsu
ne ake zaɓen 3 waɗanda suka yi zarra a matsayin na 1 zuwa na 3, tare da karrama
marubutan nasu, inda na 4 zuwa na 12 kuma ake karanta su tare da ɗora su a
kafafe da shafukan yanar gizo na BBC Hausa ɗin, irin su youtube da sauransu. Daga 2016 zuwa 2024, duk shekara ana fayyace
labarai 3 da suka yi zarra a kowace shekara kamar haka:
Shekarar 2016:
i. “Sansanin ‘Yan Gudun Hijira” na A’isha Muhammad Sabitu
ii. “Sai Yaushe?” na Amina Alhassan Abdulsalam
iii. “In Da Rai” na Amina Gambo.
Shekarar 2017:
i. “Bai Kai Zuci Ba” na Maimuna Sani Beli
ii. “Zawarcina” na Bilkisu Sani Makaranta
iii. “Sana’a Sa’a” na Habiba Abubakar da Hindatu S.N.
Shekarar 2018:
i. “ ‘Ya Mace” na Safiyya Jibril Abubakar
ii. “Sunanmu Ɗaya” na Sakina Lawal
iii. “Zaɓina” na Bilkisu Muhammad Abubakar.
Shekarar 2019:
i. “Maraici” na Safiyya Ahmad
ii. “Ba A Yi Komai Ba” na Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo
iii. “A Juri Zuwa Rafi” na Jamila Babayo
Shekarar 2020:
i. “Rai Da Cuta” na Maryam Umar
ii. “Numfashin Siyasa” na Surayya Zakari
iii. “Farar Ƙafa” na Rufaida Umar Ibrahim.
Shekarar 2021:
i. “Haƙƙina” na A’isha Musa Dalil
ii. “Butulci” na Nana Aicha Hamissou
iii. “Rahmat” na Zulaihat Alhassan.
Shekarar 2022:
i. “Gudun Gara” na Amira Souley
ii. “Haihuwar Guzuma” na Hassana Labaran Ɗanlarabawa
iii. “Al’ummata” na Maryam Muhammad.
Shekarar 2023:
i. “Rina a Kaba” na A’isha Adam Usaini
ii. “Baƙin Kishi” na A’isha Abdullahi Yabo
iii. “Tuwon Ƙasa” na A’isha Sani Abdullahi
Shekarar 2024:
i. “Amon ‘Yanci” na Hajara Ahmed Hussaini
ii. “Kura a Rumbu” na Amrah Auwal Mashi
iii. “Tsalle Ɗaya” na Zainab Muhammad Chubaɗo.
Shekarar 2025:
i. “Tsalle Ɗaya” na Fadila Lamiɗo
ii. “Gobena” na Jamila Lawal Zango
iii. “Samarin Shaho” na Hafsat Tanko.
A ƙarshen gasar BBC Hikayata ta kowace shekara, ana karrama marubutan labaran da suka lashe gasar da kyaututtuka. Sai dai har yanzu ba a taɓa tattara waɗannan gajerun
labarai cikin littafi ba, saboda
manufarsu ita ce a saurara, ba a karanta ba. Sai dai ana wallafa su kuma ana sanya sautin murya na karatun labaran a
shafin www.bbchausa.com.
4.6 Gasar Kamfanin Media Trust
A shekarar 2020 kamfanin Media Trust da haɗin gwiwar Gandun
Kalmomi da Open Arts sun shirya gasar
rubutun gajerun labarai kan siyasa wanda sakamakon gasar ya samar da wani
littafi na gajerun labarai mai suna Dambarwar
Siyasa a shekarar 2021. Littafi ne da ya ƙunshi gajerun labarai 15 waɗanda
aka tace daga cikin labarai 285 da suka shiga. Gajerun labaran da suka yi zarra
a wannan gasar, wato waɗanda suka zo na 1 da na 2 da na 3, su ne:
i. “Dimokuraɗiyyar Talaka” na Rufaida Umar Ibrahim
ii. “Tufka da Warwara” na Mubarak Idris Abubakar
iii. “Ranar Ƙin Dillanci” na Ubaida Usman.
Sai kuma sauran labaran wato daga na 4 zuwa na 15, su ne “Komai Nisan
Dare” na Yaseer Kallah da “Hassada Ga Mai Rabo” na Mustapha Sufyanu Jikan Malam
da “Baki Guba Ne” na Basira Sabo Nadabo da “Tsaka Mai Wuya” na Salim Yunusa.
Haka kuma, akwai “Kawalwalniya” na Mujaheed Ameen Lilo da “Kazar Kwanci” na
Maryam Umar Sakkwato da “Ci Ga Rashi” na Isma’il Gambo da “Igiyar Linƙaya” na
Hajara Ahmed Hussaini da “Kotun Allah Ya Isa” na Rufaida Abubakar Adam. Bayan
haka, akwai “Zaɓin Allah” na Faridat Husain Mshelia da “Tsalle Ɗaya” na Nasiru
Kainuwa Haɗejia da kuma “Yanayi” na Habib Sani Yahaya.
4.7 Gasar Gidauniyar Ɗangiwa
Arc. Ahmed Musa Ɗangiwa, a ƙarƙashin gidauniyarsa ta Ɗangiwa Literary Foundation, ya bayar da
gudummawa gaya wajen bunƙasar rubutun gajerun labaran Hausa ta hanyar shirya
gasa tun daga shekarar 2020, lokacin yana rike da matsayin Shugaban Bankin Kula
da Muhalli da Tsarin Yanka Filaye na Tarayya (Federal Mortgage Bank), har zuwa 2024 da yake a matsayin Ministan
Gidaje da Tsara Birane na Tarayyar Nijeriya a yanzu(2023-2027).
Shekarar
2020
A shekarar 2020, gidauniyar Arc. Ahmed Musa Ɗangiwa ta shirya gasar samar da gajerun labarai na Hausa waɗanda za su haska mafita ga
matsalolin muhalli irin su yanka
fili ba bisa ƙa’ida ba da matsalolin gidan
haya da matsalar mallakar muhalli a wuraren da ba su dace ba, da kuma yanayin aikin bankin bayar da lamunin gina gidaje na ƙasa.
Gajerun labaran da suka yi zarra, wato na ɗaya zuwa na uku su ne:
i. “Abun Da Ka Shuka” na Bashir Adamu
ii. “Laifin Wa?” na Bilkisu Muhammad Garkuwa
iii. “Sanin Hanya” na Aliyu Rabe Aliyu.
Akwai kuma labaran da suka samu yabo kuma aka bi su da
kyaututtuka, su ne “Tushen Farin Ciki” na Ɗanladi Haruna da “Alaƙaƙai na Fatima
Bello Bala da “Muhallinka Rayuwarka” na Kabir Yusuf Anka da “Gyara Kayanka” na
Bello Sambo da “Awon Igiya” na Hafizu Koza Adamu. Sauran su ne “Kufcewar
Salo” na Bamai Dabuwa da “A Rashin Sani” na Halima K. Mashi da “Labarina” na Binta Rabi’u Spikin da “A Yankinmu” na Fiddausi Musa, sai kuma
“Rashin
Jini...” na Ibrahim Mustafa Habib.
An fitar
da sakamakon wannan gasa kuma an bayar da kyaututtuka ga waɗanda
suka sami nasara a watan Disamba na shekarar 2020. Sannan an
buga waɗannan gajerun labarai a cikin littafin da aka raɗa wa suna Muhalli, Sutura.
Shekarar
2022
Baya ga 2020, a shekarar 2022 ma Gidauniyar Arc. Ahmed Musa Ɗangiwa ta
sake sanya gasa ta biyu domin rubutun gajerun labaran Hausa a kan matsalolin
matasa, musamman abin da ya shafi taɓarɓarewar tarbiyya da zaman kashe-wando da
ɗaukar makami da kuma safara da shaye-shayen kayan maye. Wannan gasar ta samar
da littafin gajerun labaran Hausa wanda aka sanya wa suna Ɗaukar Jinka. Littafi ne da yake ɗauke da gajerun labarai 15, tun
daga labaran da suka zo na 1 da na 2 da na 3, wato:
i. “Tun Ran Gini” na Amrah Auwal Mashi
ii. “Son Zuciya” na Rufaida Umar Ibrahim
iii. “Sara Suka” na Fatima Bello Bala da “Ka Fi Ɗan’uwa” na Jibrin Adam
Jibrin Rano
Sauran labaran su ne “Alhaki Kwikuyo” na Rabi’atu Sani Katibu Mashi da
“Sakaci” na Rahma Muhammad Kabir da “Maraici ko Son Zuciya” na Lantana Jafar da
“Sanadi” na Khadija Lawan Daura. Sai kuma “Damar Tuba...” na Abu-Ubaida Sani da
“Wanda Bai Ji Bari Ba...” na Nana Aicha Hamissou da “Ƙaddarata” na Ahmad
Muhammad Adam da “A Dalilinsa Ne” na Adamu Ahmad Yarma da “...Wutar Ƙaiƙayi” na
Ruƙayya Ibrahim Lawal da “Gadar Zare” na Maryam Umar Sokoto da kuma “Gobarar
Daji” na Salim Hassan.
Shekarar
2024
A shekarar 2024
kuwa, gasar Ɗangiwa ta samar da littafi mai
suna Burina mai ƙunshe da gajerun
labarai 16. Labaran da suka yi zarra a matakin na 1 da na 2 da na 3, su ne:
i. “Kabarin Burina” na Abu-Ubaida Sani da A’ishatu Muhammad Bazango.
ii. “Tarnaƙi” na Firdausi Muhammad Sodangi
iii. “Sauyin Tunani” na Lawan Muhammad PRP
Sauran labaran su ne “Maryamu” na Zainab Abdulrahman Aminu da “Sauyin
Launi” na Faisal Haruna Hunƙuyi da kuma “Rai da Buri” na Lubabatu Isah Ingawa.
Sauran sun haɗa da “ Zanen Ƙaddara” na A’isha Abdullahi Yabo da “Ɗan Hakin da
ka Raina” na Hauwa Adam Sulaiman da “Babu Rashi ga Allah” na Fauziyya Sani
Jibril da “Cikar Buri” na Faridat Husain Mshelia da “Matar Manya” na Nafisa
Auwal Ƙaura Goje. Sai kuma “Mafarki” na Safna Aliyu Jawabi da “Labarina” na
Salisu Tukur Gaiwa da “Burin Fatima” na Mubarak Idris Abubakar da “Haka, ba Haka
ba” na Jamila Abdullahi Rijiyar Lemu da kuma “Duniyar Shahara” na Haruna
Birniwa.
4.8 Gasar
Gidauniyar Mun Gani a Ƙasa Foundation
Hada-hadar siyasa da yaƙin neman zaɓe, su ma sun taimaka wajen shirya
gasar rubutun gajerun labarai na Hausa domin kuwa a shekarar 2022, gidauniyar Mun Gani a Ƙasa Foundation a jihar
Katsina, ƙarƙashin jagorancin Injiniya Surajo Yazid Abukur, ta sanya gasar rubutun
gajerun labarai da rubutacciyar waƙa a kan ɗan takarar gwamnan jihar Katsina na
jam’iyyar APC, wato Dikko Umar Raɗɗa. An tattara labarai da waƙoƙin da aka zaɓa
waɗanda suka yi zarra da kuma waɗanda suka sha yabo a cikin littafin da aka
raɗa wa suna Mizani, wanda aka buga a
shekarar 2023. Daga cikin gajerun labarai 10 da suka fito cikin littafin, waɗanda
suka zo na 1 da na 2 da na 3, su ne:
i. “Rawar Gani” na Fatima Bello Bala
ii. “Tudun Tsira” na A’isha Adam Hussain
iii. “Shugaba Nagari” na Amrah Auwal Mashi.
Sai kuma sauran labarai 7 waɗanda suka sha yabo su ne, “Ɗan Takara ko Ɗan
Siyasa” na Aliyu Rabe Daura da “Murnar Mata” na Hassana Labaran Ɗanlarabawa da
“Adali” na Maryam Naseer da “Wanda Bai Ji Bari Ba” na Mubarak Idris. Sauran su
ne “Da Mai Kama Ake Ƙota” na Salisu Abdullahi da Sadiƙ Abubakar da “Nagari
Nakowa” na Rabi’atu Abubakar Umar sai kuma “Cancanta Kawai” na Amina Dan’azumi.
Duk labaran da waƙoƙin na siyasa ne, amma ko ba komai, wannan gasa mai ruhin
siyasa ta taimaka wajen bunƙasar rubutun gajerun labaran Hausa. Kuma an dubi
abin da ya shafi tsarin shugabanci, wato zaɓen shugaba nagari abin koyi, aka
turke jigon gasar rubutun gajerun labaran a kai.
4.9 Gasar Bukukuwa
Daga lokacin da gasar
rubutun gajerun labarai ta zama jiki, sai ta kasance wata kafa ta sada zumunci
tsakanin marubutan, musamman a lokacin bukukuwansu. Ta haka ne idan wani
marubuci yana bukin murnar zagayowar ranar haihuwarsa ko bukin aure, ko wani
bukin, nan ma sai ya sanya gasar rubutun gajerun labarai, musamman ga marubuta
masu tasowa domin ƙarfafa masu gwiwa.
A irin wannan fasalin ne
a shekarar 2020 aka sanya gasar rubutun gajerun labarai domin murnar bukin
Fadila Aliyu Kurfi. Sakamakon gasar ya samar da gajerun labarai 10 waɗanda aka
tattara aka samar da littafin Alƙalami...
Labaran cikin littafin su ne “Ƙanin Miji” na Abdulkarim Papalaji da “Maza
Gumbar Dutse” na Abba Abdulahi Gumel da “Ilimin ‘Ya Mace” na Zaidu Barmo da “Da
Ban Haɗiya Ba” na Mubarak Muhammad da “Mugun Ƙawance” na Rahma Ahmad Muhammad
da “An Daina Kiwon Dabba...” na Amina Dauda Abubakar da “Biyu Babu” na Idris
Sa’id da “Ungulu Kazar Kowa” na Nasiru Kainuwa Haɗejia da “Kunne Ya Girmi Kaka”
na Sadisu Shu’aibu Nguru da kuma “Shu’umar Ƙawa” na Sadiya Salisu Aliyu.
Bugu da
ƙari, a shekarar 2022 lokacin da aka naɗa Aminu Alan Waƙa sarautar Sarkin Ɗiyan
Gobir, ya sanya gasar rubutun gajerun labarai wadda ya raɗa wa suna “Gasar
Tsibirin Gobir.” Gajerun labaran da wannan gasar ta samar daga na 1 zuwa na 10,
sun haɗa da “Tsayuwar Wata” na Rahama Ahmad Muhammad da “Gidan Gandu2” na
Hassana Labaran Ɗanlarabawa da “Gyara Kayanka...” na Rufaida Umar da “Maraina
Kaɗan” na Bilkisu Muhammad Garkuwa da “Wake Ɗaya” na Jibrin AJR Adamu da “Kifi
Na ganinka...” na Hadiza D. Auta da “Kakata” na Nasiru Kainuwa Haɗeja da “Kowa
Ya Bar Gida...” na Muhammad Bala Garba da “Al’adata Darajata” na A’isha Sani
Abdullahi da “Ɗan Hakin Da Ka Raina...” na Hauwa’u Suleiman.
A
shirye-shiryen Bukin Ranar Marubutan Hausa ta Duniya da aka gudanar a jihar
Jigawa a ranar 31/12/2025, an shirya gasar rubutun gajerun labaran Hausa a kan
gudummawar fasahar AI wajen inganta
tsaro da tattalin arziƙi. Sakamakon gasar ya samar da littafi mai ƙunshe da
gajerun labarai 28 mai suna Ninki Biyu.
Labarai uku da suka yi zarra a matakin na 1 zuwa na 3, su ne:
i. “Riba Biyu” na Safnah
Aliyu Jawabi
ii. “Ɗinkin Kwalba” na
Nana Aicha Hamissou Abdoulaye da A’isha Sani Abdullahi
iii. “Idon Basira” na
Muttaƙa A. Hassan da “Magani a Gonar Yaro” na Hassana Labaran Ɗanlarabawa
Duk labaran da ke cikin
littafin, ruhinsu shi ne gudummawar ƙirƙirarriyar basira(AI) ga tsaro da tattalin arziƙi. Kuma gasa ce ta samar da su.
4.10 Gasar Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano
A shekarar 2024, Hukumar
Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano ta shirya gasar rubutun gajerun labaran
Hausa. A zagayen farko an fitar da labarai 50 waɗanda aka tace aka fitar da 15
daga cikinsu waɗanda a cikinsu aka fitar da 3 waɗanda suka yi zarra, waɗanda su
ne:
i. “Bahaushiyar Al'ada”
na Zubairu Musa Balannaji
ii. “Gadon Gida Sai Da
Horo” na Dalladi Z. Haruna
iii. “Bahaushe Mai
Arziƙi Ne” na Hauwa Shehu
Sauran labarai 12 daga
cikin 15 ɗin su ne, “Tushiya Masomin Dawa” na Aisha Adam Hussain da “Ɗanyen
Kasko” na Fauziyya Sani Jibril da “Tsalle Ɗaya” na Fa'iza Muhammad Sajo da
“Sakayya” na Habibu Muhammad Ayagi da “Bikin Fari” na Hassana Labaran
Ɗanlarabawa da “Gida Nesa Gida” na Isma'il Gambo da “Allon Kwaikwayo” na Maryam
Abdullahi da “Dahuwar Ƙaho” na Nana Aicha Hamissou da “Kowanne Tsuntsu” na
Rahama Ahmad Muhammad da “Sana'ata” na Rufaida Umar Ibrahim da “Ciki Mai Manta
Kyautar Jiya” na Zubairu Abdulrahman Kasim da kuma “Wankan Jego” na Zuwaira
Dauda Kolo. Ita ma wannan gasar, har yanzu ba a kai ga buga waɗannan labarai a
littafi ba.
4.11 Gasar Bashir Tofa
A shekarar 2025, Kano Book Club tare da haɗin gwiwar The Third Space, sun gudanar da gasar
rubutun gajerun labarai wadda aka raɗa wa suna, “Gasar Gajerun Labarai ta Bashir
Tofa.” Manufar gasar ita ce bunƙasa al’adu da adabin Hausa ta hanyar haɓaka
rubutun Hausa da samar da adabi. Har zuwa lokacin da wannan bincike ya kammala,
ba a kai ga samar da bugaggen littafin da ya ƙunshi gajerun labaran da wannan
gasar ta samar ba, sai dai labaran da suka yi zarra a matsayin na 1 zuwa na 3 a
wannan gasar, su ne:
i. “Ilimi Kogi” na Hamza
Sadiq Adam
ii. “Kazar Amarci” na
Muntasir Shehu
iii. “Yaro Masomin
Babba” na Hassana Abdullahi Hunƙuyi.
Sauran labaran su ne,
“Ribar Adabi” na Rufa'i Abubakar Adam da “Wutar Kara” na Lantana Ja'afar da
“Budurwar Zuciya” na Usman Ibrahim Ali da kuma “Tsaka Mai Wuya” na Madina Bala
Hussain. Har ila yau, an bayyana cewa za a cigaba da tattarawa da tantance labaran
ne har sai an sami adadin da ake buƙata domin buga littafin da zai ƙunshi
labaran da suka cancanci bugawa daga cikin labaran da suka shiga gasar.
4.12 Sauran Gasanni
Baya ga waɗannan ma, ana iya cewa yanzu, gasar rubutun
gajerun labaran Hausa ta zama ruwan dare, ta inda wasu zauruka na marubuta a
kafafen sada zumunta ma sukan sanya gasar rubuta gajerun labarai cikin wani
ƙanƙanin lokaci su ɗan bayar da na goro ga waɗanda suka yi nasara. Akwai kuma
wasu gasannin da ake kan gudanarwa, ba a kai ga kammala su ba, ballantana a
fitar da labaran da suka yi nasara. Daga cikin ire-iren waɗannan gasanni, akwai
gasar gajerun labarai kan matsalar
tsaro a Arewacin Nijeriya. Wannan gasa ce da Jami’ar Tarayya ta Dutsin-ma ta shirya a
shekar 2024. A zagayen farko an tantance labarai 77 daga cikin 275 da suka shiga gasar.
Daga cikin 77 ɗin ne aka tace 30 waɗanda
suka dace da abin da aka nema.
A cikin waɗannan labarai 30 ɗin ne za a sake tankaɗe da rairaya a ɗauki 20. Daga ƙarshe za a fitar da na 1 zuwa na 3 da kuma na 4 zuwa na 20 waɗanda za a karrama da kyauta da takardar karramawa, sannan kuma a buga labaran a matsayin littafi. Sai dai har zuwa lokacin tattara bayanan
wannan bincike, ba a kammala fitar da sakamakon ƙarshe na gasar ba.
Akwai kuma gasar rubutun
gajerun labarai da Ƙungiyar Marubutan Jihar Katsina (KMK) ta sanya a shekarar
2025. Duk da cewa har zuwa lokacin tattara bayanan wannan bincike, ba a kammala
wannan gasar ba, amma a zagayen farko an fitar da labaran da za a fitar da
zakaru a cikinsu a ɓangarori uku da aka shirya gasar a kan su, wato:
i. Hanyoyin Magance
Matsalar Tsaro a Jihar Katsina
ii. Illolin
Tallace-tallace ga 'Ya'ya Mata
iii. Hanyoyin Kawar da
Ciwon Sankarar Mama.
Sauran ƙungiyoyin
marubuta da suka ba da gudummawa wajen shirya gasar rubutun gajerun labarai sun
haɗa da:
i. Hazaƙa Writers
Association, a shekarar 2023
ii. Kyauta Daga Allah
Foundation, a shekarar 2023
iii. Marubuta Whatsapp
Group, a shekarar 2024, gasar da ta samar da littafin Abin Cikin Ƙwai...., mai
ƙunshe da labarai 33.
iv. Arewa Writers
Association, a shekarar 2025 da sauransu.
Wani lokacin kuma wasu
marubutan da suke da kusanci da wasu ‘yan siyasa sukan yi amfani da wannan
damar wajen shirya gasar rubutun gajerun labarai domin tallata manufofin wani
ɗan siyasa da sauransu. Misali, a shekarar 2025 an gudanar da gasar rubutun gajerun
labaran Hausa mai taken ‘Aiki Dai Malam’, a ƙarƙashin jagorancin Jigawa New
Media domin fito da ayyukan Gwamnan Jihar Jigawa Malam Umar Namadi Ɗanmoɗi. An
fitar da labarai 20 da suka tsallake tantancewa a zagaye na farko, daga cikinsu
aka fitar da 3 waɗanda suka yi zarra, su ne:
i. “Salin-alin” na
Nasiru Kainuwa Haɗeja
ii. “Malam Yana Kan
Daidai” na Rufa’i Adam Abubakar Gombe
iii. “Gwanin Na Iya” na
Hassana Labaran Ɗanlarabawa.
5. Sakamakon Bincike
Daga abin da
ya gabata, an gano cewa gasa tana taimakawa gaya wajen cigaba da samuwa da
bunƙasar rubutun gajerun labaran Hausa. Wannan ya haifar da wasu siffofi na
musamman waɗanda suka keɓanta ga rubutattun gajerun labarai na gasa. Ɗaya daga
ciki ita ce kasancewar ana keɓanta su ga wani jigo na musamman a kowace gasa. Wato,
suna da turkakken jigo. Shi ya sa dukkannin gajerun labaran gasannin da aka yi
bayani a sama, suna da jigogin da suka keɓanta gare su. Alal misali, gajerun
labaran gasar Ɗangiwa Literary ta
shekarar 2020, ta samar da gajerun labarai ne a kan jigon tsarin muhalli da
gini bisa ƙa’ida da kuma hanyoyin mallakar muhallin, yayin da a gasar 2022 aka
samar da gajerun labarai masu jigon kyautata tarbiyya ga matasa. A shekarar 2024
kuwa, an samar da labarai a kan buri. Gasar Aminiya
Trust da ta Mun Gani a Ƙasa kuwa duk sun samar da rubutattun gajerun
labarai ne masu jigon siyasa; abin da ya shafi dambarwa da turka-turkar siyasar
da kuma mizanin gane shugaba nagari cikin al’umma. Ita kuwa gasar BBC Hausa ba a keɓe mata wani jigo na
musamman da ake rubutu a kansa ba, sai dai marubuta mata ne kawai ke shiga
gasar, shi ya sa suka fi fito da matsalolin mata a labaran da suke samarwa a
gasar.
An gano cewa
gajerun labarai na gasa suna samun taciya daga ƙwararru, a yawancin lokuta
malaman jami’a, da kuma wasu fitattun marubutan Hausa. Hakan yakan sanya a
samar da labaran cikin wasu ƙayyadaddun dokoki da ake so labaran su bi kafin su
samu shiga sahun zakaru a gasar. Saboda haka, ana lura da adadin kalmomi da
ƙa’idojin rubutu da karin harshe da sauransu.
An gano cewa
‘yar ladar da ake ba marubutan da suka yi zarra a gasa tana ƙara masu ƙaimi
wajen samar da labaru masu yawa domin shiga duk wata gasa da aka sanya. Hakan
yake ba da damar bunƙasa rumbun adana rubutattun gajerun labaran Hausa cikin
littattafai. Shi ya sa a yanzu, wasu gasannin da suka samar da rubutattun
gajerun labarai ake taskace labaran cikin littattafai domin masu nazari da
al’umma gaba ɗaya. Kuma haƙƙin mallakan waɗannan littattafai, na waɗanda suka
sanya gasar ne.
6. Kammalawa
Bisa
taƙaitawa, wannan nazari ya fito da gudummawar gasa wajen bunƙasar rubutun
gajerun labaran Hausa. Baya ga shimfiɗa, an kawo ra’o’in bincike da hanyoyin
gudanar da bincike. An waiwayi yadda gasar rubutu ta faro a ƙasar Hausa,
musamman abin da ya shafi rubutun ƙagaggun labarai. Daga nan aka tuƙe da
daddale bayanan gudummawar gasa a fagen bunƙasar gajerun labaran Hausa. A
ƙarshe kuma sai aka kawo sakamakon bincike.
7. Manazarta
Abdo El-Rahman, H. E. M. (1996). The Oral in
Written: A Study of Orality in Selected West African Short Stories. Unpublished
MA Dissertation. Department of English. Ahmadu Bello University.
Abdulwaheed, H. M. A. (2008).
Saba Ɗan Sababi. Gidan Dabino Publishers.
Bates, H. E. (1972). The Mordern Short Story: A Critical Survey.
Michael Joseph Ltd.
Bourdieu, P. (1993). The
Field of Cultural Production: Essays on Art and Literature. Columbia University
Press.
Ɗan’amarya, I. A. (2012). Tarihi da Gudummuwar Gasa a Samarwa da Bunƙasa Kagaggun Labaran Hausa. Kundin Digiri na Biyu. Sashen
Nazarin Harsunan Nijeriya. Jami’ar Usmanu Danfodiyo.
Faruk, A. (2018).
Nazarin Biɗau a Cikin Littafin Saba Ɗan Sababi na Hafsat A.M Abdulwahid.
Kadaura Journal of Hausa Multi-Disciplinary Studies Vol. 1, No. 4
January, 2018. Sh. 368-385.
Malumfashi, I. (2009). Adabin
Abubakar Imam. Garkuwa
Media Service
Ltd.
Mujaheed, A. (2025). Nazarin Faruwa, Bunƙasa
da Sigogin Rubutattun Gajerun Labaran Hausa
(1929-2024). Kundin Digiri na Uku. Sashen
Koyar da Harsunan Nijeriya. Jami’ar Umaru Musa Yar’adua.
Vygotsky, L. S. (1978). Mind
in Society: The Development of Higher Psychological Processes. Harvard University Press.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.