YAU NIGERIYA RIƘO SAI MAI GASKIYA
BABA BUHARI KAI MUKE SO
NAJERIYA
ANPP 2003 WADDA YA JUYA TA ZUWA CPC.
Ibrahim Yala Hayin Banki
Bakandamiyar Buhari 2003
2011 CPC
Turke/
Amshi: Yau Najeriya Riƙo sai mai gaskiya
Baba Buhari Kai Muke So Najeriya.
Amshi: Yau Najeriya
Riƙo sai mai gaskiya
Baba Buhari Kai Muke So Najeriya.
Amshi: Yau Najeriya
Riƙo sai mai gaskiya
Baba Buhari Kai Muke So Najeriya.
Jagora: Allah Khaliƙu da yay yo duka duniya
Mu riƙon da za mu yi mu duka bai
ɗaya
Bai wa Buhari mulkinmu duk Najeriya
CPC ta zo ta rungumi
Najeriya
Amshi: Yau Najeriya
Riƙo sai mai gaskiya
Baba Buhari Kai Muke So Najeriya.
Jagora: Salli ala
Muhammadu Annabi Shugaba
Mai cetonmu ran da kowa ke fargaba
Annabi ran ƙiyama ka
samu sahun gaba
Mun bi rasulu ɗan Amina mai gaskiya
Amshi: Yau Najeriya
Riƙo sai mai gaskiya
Baba Buhari Kai Muke So Najeriya.
Jagora: Ka zo ka fitar da
mu a ƙunchin da muke ciki
Yau mun sha wuya a kullum sai farmaki
Ana satar kuɗinmu a yau ba shamaki
Kaji halin da mu muke ciki
Najeriya
Amshi: Yau Najeriya
Riƙo sai mai gaskiya
Baba Buhari Kai Muke So Najeriya.
Jagora: Su Tanko da Babalola sun
tabka abin tsiya
Sun gama kwashe dukiyar ‘yan Najeriya
Shi yasa muke biɗar yau mai gaskiya
Wanda idan ya zo za ya
gyara Najeriya
Amshi: Yau Najeriya
Riƙo sai mai gaskiya
Baba Buhari Kai Muke So Najeriya.
Jagora: Allah wadan ku tun
dai kun cucemu mu
Kun kashe rayuwar mutane kun sai damu
Don Allah Buhari mu zo ka fitar da mu
CPC ta zo ta rungumi
Najeriya
Amshi: Yau Najeriya
Riƙo sai mai gaskiya
Baba Buhari Kai Muke So Najeriya.
Jagora: Na tuna sanda ka
yi mulkin Najeriya
Sanda ka kau da dogowar hula mai danniya
Don gyaran ƙasa da
kishin Najeriya
Dawo Buhari kai muke so
Najeriya
Amshi: Yau Najeriya
Riƙo sai mai gaskiya
Baba Buhari Kai Muke So Najeriya.
Jagora: Randa ka karɓi mulki Buhari a nan ƙasar
Duk ka ta da hancin ya komai nan ƙasar
Sai ka gyara komai da ke a cikin ƙasar
Yau me zai hana mu so ka a
Najeriya
Amshi: Yau Najeriya
Riƙo sai mai gaskiya
Baba Buhari Kai Muke So Najeriya.
Jagora: Buhari a lokacin
yaƙƙi bashin Ingila
Da su da Amerika masu halin basila
I.M.F ya ce ba ya so don matsala
Mun gode Buhari mai kishin
gaskiya
Amshi: Yau Najeriya
Riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari Kai Muke So Najeriya.
Jagora: Duk ya kama yan
Jihar can da suke ƙasa
Masu kuɗin da ba su zakka sun bar ƙasa
Kaji a lokacin tattali ya bunƙasa
Kowa ya taso a faɗin Najeriya
Amshi: Yau Najeriya
Riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari Kai Muke So Najeriya.
Jagora: Na rantse a
lokacin ba ma yin tsiya
Tun da akwai Buhari mai aiki da gaskiya
Mun ci abinci har da nama basua wuya
Zamanin Buhari mai kishin
gaskiya
Amshi: Yau Najeriya
Riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari Kai Muke So Najeriya.
Jagora: A wancan lokacin
farar hula sun gudu
Domin sun yi ɓarna dole su zan gudu
Yanzu idan ka hau dole wancan na gudu
Zai tsere ya bar ƙasar don bai gaskiya
Amshi: Yau Najeriya
Riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari Kai Muke So Najeriya.
Jagora: Ke Lema baƙar daga kin mana yau tsiya
Ba kya maganin ruwa duk mun sha wuya
Kun haɗa kai da masara bakwa
gaskiya
CPC taho ki rungumi
Najeriya
Amshi: Yau Najeriya
Riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari Kai Muke So Najeriya.
Jagora: Wanda ya ja da kai
Buhari zai sha wuya
Domin ka fi wancan mai halin ‘yan giya
Mai fuska kamar ana mutsika taliya
Kai hanga su cima zaunen Najeriya
Amshi: Yau Najeriya
Riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari Kai Muke So Najeriya.
Jagora: Lalle Daura ta yi ɗa wanda yake da kyau
Wanda idan na gan shi ni bana zudda yau
Ku zo jama’ar ƙasa ku
rungumi wai gaskiya
Shi ne za ya fidda mu ƙuncin Najeriya
Amshi: Yau Najeriya
Riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari Kai Muke So Najeriya.
Jagora: Tarkon mutuwar da
PDP tai mana
Halin ha’ula’i da ta jejjefa mana
Bala’in shawa da tak kokoya mana
Baba Buhari ne za ya fidda
Najeriya
Amshi: Yau Najeriya
Riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari Kai Muke So Najeriya.
Jagora: Dubi halinsu yasa
mu mun koma baraa
Maula mutuwar zuci da
halin kaugora
Rashin aiki ya sa ɓarayi sun gagara
Kowa na abin da ya so
najeriya
Amshi: Yau Najeriya
Riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari Kai Muke So Najeriya.
Jagora: Na sama basu
tausayin na ƙasa Najeriya
Sun danne mu sun koma ba sua waiwaya
Allah shugabannin ga ba su da gaskiya
Sun gutsura mana a faɗin Najeriya
Amshi: Yau Najeriya
Riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari Kai Muke So Najeriya.
Jagora: Don haka zo ka ja
mu Buhari Shige gaba
Mu duk a za mu bika don ba ma fargaba
Mu a ƙasarmu kai muke so yau
shugaba
Zo ka riƙe my kar mu kauce ta da gaskiya
Amshi: Yau Najeriya
Riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari Kai Muke So Najeriya.
Jagora: Ga zakaran da
Rabbana Sarki yannufa
Dole a ƙyale mai gida koko a
ragwama
Don haka ka da ku ja da shi balle ku zurfafa
Yau Allah yana a bayan mai gaskiya
Amshi: Yau Najeriya
Riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari Kai Muke So Najeriya.
Jagora: Eh, zan yi kiran ku dukkanin
yan Najeriya
Kar mu bari a sake cutar mai gaskiya
Ku zo mu tsaya muna da ƙarfin
Allah ɗaya
Kar da mu sake ƙyale PDP
tai murɗiya
Amshi: Yau Najeriya
Riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari Kai Muke So Najeriya.
Jagora: Eh Bana kowa ya ƙwace zaɓenmu ya tabbata
Zai rashin uwa, uba yaya har mata
Har shi kan shi har da mai sashi ya yo cuta
Za mu gama da jahili bama kauciya
Amshi: Yau Najeriya
Riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari Kai Muke So Najeriya.
Jagora: Eh mun gaji mu da
ku a mulkin Najeriya
Zaluncinku ya ƙure mu a
Najeriya
Cin zarafi da cin amanarku gaba ɗaya
Ya sa ba mu tsoron ku yau Najeriya
Amshi: Yau Najeriya
Riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari Kai Muke So Najeriya.
Jagora: Eh bana ƙarya kuke ku sake rubuta mana
Kuma kun daina sanya kowa musgun a mana
Kun rantse da wanda yai ka’aba Rabbana
Kun gama murɗiya yau a duk Najeriya
Amshi: Yau Najeriya
Riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari Kai Muke So Najeriya.
Jagora: Ina kuke rundunar
matsan Najeriya
Mu tashi mu ƙwaci ‘yanci cikin Najeriya
Mata kar ku yarda yau a yi muku murɗiya
Sai mu zage mu kai Buhari mai gaskiya
Amshi: Yau Najeriya
Riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari Kai Muke So Najeriya.
Jagora: Ba mai ƙara ba mu ƙwaya ko shalisho
Wiwi benalin roti mun daina sha
Sai dai ku baiwa ‘ya’yanku duka su je su sha
Mu yanci muke biɗa faɗin Najeriya
Amshi: Yau Najeriya
Riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari Kai Muke So Najeriya.
Jagora: Mun gano ku masu
mulkin Najeriya
Kun mai she mu jahilai ba mu da tarbiya
Ku kun tura ‘ya’yanku Turai gaba ɗaya
Ku kun ba mu gariyo mui muku kariya
Amshi: Yau Najeriya
Riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari Kai Muke So Najeriya.
Jagora: Mutun ɗaya na da dukiya ta wuce
hankali
Ya tara ta babuu zakka ko jangali
Ya hana ‘yanuwansa don renin hankali
Sai ‘ya’yansu ke bushesha cikin duniya
Amshi: Yau Najeriya
Riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari Kai Muke So Najeriya.
Jagora: Su ke yanka
‘ya’yanmu ba wani tausayi
Ga neman matan aure sun yi dabaibayi
Sai bidi’a da asharanci suke ta yi
Wai su ne fa shugabannin Najeriya
Amshi: Yau Najeriya
Riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari Kai Muke So Najeriya.
Jagora: Duk wani wanda ba
ya jin tsoron Rabbana
To mun daina girmamashi ya cuta mana
Mai rawani da jiniya Allah isar mana
Za mu buga daku dana faɗin Najeriya
Amshi: Yau Najeriya
Riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari Kai Muke So Najeriya.
Jagora: Sai ƙarya kuke da addini
mayaudara
Da kun shiga jama’a ku rinƙa faɗin kabbara
Bayan zukciyarku kun sa ta ta wut
tsira/guttsura
Ba kwa tausayin talakka Najeriya
Amshi: Yau Najeriya
Riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari Kai Muke So Najeriya.
Jagora: Yau Najeriya Riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari Kai Muke So Najeriya.
Jagora: Wasu ma sun yi
mulki a baya Najeriya
Sun
kashe wanda bas u so sun cirri dukiya
Sun raba kammu sun yi mulki ba waiwaya
Kaji su baba dan gajere maras gaskiya
Amshi: Yau Najeriya
Riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari Kai Muke So Najeriya.
Jagora: Su suka rusa ilimi
yau Najeriya
Su usuka ɓata tattalin ‘yan Najeriya
Lantarki ƙasarmu
yau yaz zama najiya
Allah ya isa macutan Najeriya
Amshi: Yau Najeriya
Riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari Kai Muke So Najeriya.
Jagora: Su suka sanya
rasshawa yau tay yo yawa
Su suka tsaida arzikin ‘yan Najeriya
Su ke kulle kamfani don har sun saya
Sun raba tallaka da aiki ‘ya’yan tsiya
Amshi: Yau Najeriya
Riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari Kai Muke So Najeriya.
Jagora: Su ne gamji
Sardauna yai wa sutura
Shi ya tsaya sukai ficce ba wata takura
Wani ma ba tsawo na Sardauna aka gutsura
Don kishin arewa shi yai masu kariya
Amshi: Yau Najeriya
Riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari Kai Muke So Najeriya.
Jagora: To amma su
tsawonmu yau duk sun rarrage
Sun koma da mu da su sai ga mu yo hange
Da Sardauna za ya dawo ya ga ɗan mage
Wanda suka ta cin amanar Najeriya
Amshi: Yau Najeriya
Riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari Kai Muke So Najeriya.
Jagora: Su ne suke ta
sukan Buhari Uban ƙasa
Su ne sun ka ƙwace
Petur da kuɗin ƙasa
Don tsabar rashin mutunci a cikin ƙasa
Har ma dukiyar marayu sun murɗiya
Amshi: Yau Najeriya
Riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari Kai Muke So Najeriya.
Jagora: Eh Allah jiƙan Abacha mai kishin gaskiya
Kaji maza na Maryam Sani mai gaskiya
Ka bar baya ta yi kyau ba wani tautsiya
Muhammadu Abacha ya biyo
layin gaskiya
Amshi: Yau Najeriya
Riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari Kai Muke So Najeriya.
Jagora: Buhari fiya fiya
da ba ya yin murɗiya
Zo ka kawar da saibat mai fuskar saniya
Har da na Joɗa tanki da shi aka yi murɗiya
Duk sun cuci rayuwar ‘yan
Najeriya
Amshi: Yau Najeriya
Riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari Kai Muke So Najeriya.
Jagora: Eh da a ƙasarmu babu yunwa in kuntuna
Sai ku tuna abinci da ga shi a ko’ina
Ba mu faɗa a lokacin kowace fitina
Yanzu idan ka gammu kau duk mun sha wuya
Amshi: Yau Najeriya
Riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari Kai Muke So Najeriya.
Jagora: Ch Allah wadan ku
masu halin na Baturiya
Wannan ɗan baƙin da ƙira ta yan giya
Can gona yake yana halin murɗiya
Ko ko in ka bishi lalle ka sha wuya
Amshi: Yau Najeriya
Riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari Kai Muke So Najeriya.
Jagora: Ya cuce ni da da
yanzu na hankale
Kar ka sake ka zo wuri na ba ma tare
Kai da na yamma yaronka mai halin kare
Na riƙe ni Buhari don shi ne mai
gaskiya
Amshi: Yau Najeriya
Riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari Kai Muke So Najeriya.
Jagora: Allah jiƙan wada Nas mai kishin
gaskiya
Okadibo ya wuce yana kishin gaskiya
Sun kashe har mashal mai kishin gaskiya
Kaji waɗanda su suke son mai
gaskiya
Amshi: Yau Najeriya
Riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari Kai Muke So Najeriya.
Jagora: Sannu Rufa’i an ga
mai kishin gaskiya
Kai ne shugaba na jam’iyya Najeriya
Yau CPC ta game duk Najeriya
Dole a jinjina muku an ga
mai gaskiya
Amshi: Yau Najeriya
Riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari Kai Muke So Najeriya.
Jagora: Buba galadima a
gaishe ka da ƙoƙari
Kai ne Jarumin da ke sa mu yi hanzari
Sannu Sulaiman Hamma gaishe ka da ƙoƙari
Kun riƙe dai Buhari mai kishin
gaskiya
Amshi: Yau Najeriya
Riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari Kai Muke So Najeriya.
Jagora: Ga wani jarumi a
yaƙi bai fargaba
Hadi Sirika yaƙinmu ban
ga kamarsa ba
Sannu Uban Mujahid da Fatima ja gaba
Hadi Sirika ya riƙe na kan
gaskiya
Amshi: Yau Najeriya
Riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari Kai Muke So Najeriya.
Jagora: Sha’aban Sani Nawa
mai kishin gaskiya
Jagoran rundunar talakka ga baki ɗaya
Wasu sun ce CPC ya ƙi ki zo
jiya
Sai ga Sani Sha’aban ya zo gaba ɗaya
Amshi: Yau Najeriya
Riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari Kai Muke So Najeriya.
Jagora: Ga wani Malamin
jami’a mara danniya
Doctor Bashir na Kurfi mai kishin gaskiya
Sannu Air Vice mashal Mukhtari mai juriya
Yusha’u Armaya’u ma ya riƙe
gaskiya
Amshi: Yau Najeriya
Riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari Kai Muke So Najeriya.
Jagora: Yau a Kaduna an
sami babban shugaba
Amadu Yaro Koka-Kola bai fargaba
An yo zaɓen CPC an san cigaba
Ya buge ɗan agwagwa yau mai faɗin tsiya
Amshi: Yau Najeriya
Riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari Kai Muke So Najeriya.
Jagora: Kabiru Tanimu ya
shigo ba fargaba
Shi ɗan takara na gwamna mara
fargaba
Eh Dan masani na Gwandu mason a ga cigaba
Kabiru Tanimu ya shigo ba ya Kauciya
Amshi: Yau Najeriya
Riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari Kai Muke So Najeriya.
Jagora: Akwai wasu jaruman
matasa na gaida su
Musa, Hore, Jauro su ma na san da su
Suleiman Dauda Daura shi ma na sa da su
Abdullahi Lema nawa mai gaskiya
Amshi: Yau Najeriya
Riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari Kai Muke So Najeriya.
Jagora: Tanko dattijo mai
son gaskiya
Haruna Sa’idu ya taho ba ya kauciya
Janaral Sale sannu mai kishin gaskiya
Shehu Namiji ma ya riƙe
gaskiya
Amshi: Yau Najeriya
Riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari Kai Muke So Najeriya.
Jagora: Eh Garba Attahiru
yana kishin gaskiya
Sannu na mairo nawa mai aiki da gaskiya
Ih cewa ya ga ya kyale ‘yan murɗiya
Nasan kai a yi haka da ka cika dauriya
Amshi: Yau Najeriya
Riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari Kai Muke So Najeriya.
Jagora: Akwai wani jarumin
matashi mai juriya
Shi ne Yusuf Jelani mai kishin gaskiya
Wanda ya Sami duniya ya riƙe al’uma
Nasa garkuwar rigasa mai gaskiya
Amshi: Yau Najeriya
Riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari Kai Muke So Najeriya.
Jagora: Eh Malam
Shitu nawa mai kishin gaskiya
Wahala bata ka kauce wa mai gaskiya
Kullum in nazo Katsina ban shan wuya
Malam Shitu ke riƙe ni mai
gaskiya
Amshi: Yau Najeriya
Riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari Kai Muke So Najeriya.
Jagora: Ga Abdulmunaf na
Daura na sa da kai
Mai aiki a kan Buhari na gaida kai
Sannu mijin Walima yalal na gaida kai
Ina magana a wadda ka je nai dubiya
Amshi: Yau Najeriya
Riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari Kai Muke So Najeriya.
Jagora: Dacta Muhammad Dan
Tanko mai son gaskiya
GA mai lore shi Kaduna mara danniya
Dacta Mustapha na Zariya na gaida kai
Har Dact Modibbo ma ya riƙe
gaskiya
Amshi: Yau Najeriya
Riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari Kai Muke So Najeriya.
Jagora: Mannir Yakubu a
gaishe ka da ƙoƙari
Ga Nuhu Dan Magaji ma ya cika ƙoƙari
Sanata Audu Yandoma ya zo da wuri-wui
Mu gaida Lawal ma ya cika gaskiya
Amshi: Yau Najeriya
Riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari Kai Muke So Najeriya.
Jagora: Shehu Barau na
Ningi yau dole na sa da kai
Akwai wani baba mai alƙalami na
gaida kai
Fatiri yala ma yau na sa da kai
Mustapha Kwaliti a Borno yau juriya
Amshi: Yau Najeriya
Riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari Kai Muke So Najeriya.
Jagora: Eh sannu Aminu
Adamu ba ka kauciya
Kaji magayaƙi Gusau
baya danniya
Shi ne Shugaba na CPC Zamfara
Aminu Dankwangila yana kishin gaskiya
Amshi: Yau Najeriya
Riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari Kai Muke So Najeriya.
Jagora: Na tuna sanda ka
yi mulkin Najeriya
Sanda ka kauda doguwar hula mai danniya
Dan gyaran ƙasa da
kishin Najeriya
Dawo Buhari kai muke so Najeriya
Amshi: Yau Najeriya
Riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari Kai Muke So Najeriya.
Jagora: Dan zago can Kano
kana kishin gaskiya
Kai ne shugaba na CPC gaba ɗaya
Jafari Isah Sannu mai kishin gaskiya
Danbalki Kwamanda ma ya riƙe gaskiya
Amshi: Yau Najeriya
Riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari Kai Muke So Najeriya.
Jagora: Har injiniya
magaji na sa da kai
In ƙaunar Buhari ne dole a sa
da kai
Awwal A ya Laɓe ke gai da kai
Allah taimaka ku kauda mara gaskiya
Amshi: Yau Najeriya
Riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari Kai Muke So Najeriya.
Jagora: Faruku Adamu
Jigawa an sallama
Kai ne maganin wanda ya rena al’uma
CPC Jigawa kai ne ke hikima
Ukashatu Shugaba a gaishe ka da juriya
Amshi: Yau Najeriya
Riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari Kai Muke So Najeriya.
Jagora: Eh Yakubu Lado
Sanata ma na sa da kai
Tuntuwa in kayo shiri dole a tai da kai
Aminu Masari Dan Bello ma na gaida kai
MT Liman yau sun da wo ma gaskiya
Amshi: Yau Najeriya
Riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari Kai Muke So Najeriya.
Jagora: Eh Dan Chaina na
Bauchi kai ma ban barka ba
Alƙawarin da ka yi Daura ban
gan shi ba
Naga rabi amma rabin ni ba a ba ni ba
Gara ka bincika in gano mara gaskiya
Amshi: Yau Najeriya
Riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari Kai Muke So Najeriya.
Jagora: Akwai wata juruma
a mata ban barta ba
Altini yar Haruna Potaskum mu je gaba
Ki je ki gaya wa mata su bar yin fargaba
Altine yan gari tana kishin gaskiya
Amshi: Yau Najeriya
Riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari Kai Muke So Najeriya.
Jagora: Eh Yala zan tsaya
a nan sai kuma nan gaba
Hali babu yau kiɗan ba wata fargaba
Wacce ka rera amshin gare ni Maryam baba
Ni ne ɗan hayin banki kawo gaba ɗaya
Amshi: Yau Najeriya
Riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari Kai Muke So Najeriya.
Jagora: Yau Najeriya Riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari Kai Muke So Najeriya.
Amshi: Yau Najeriya
Riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari Kai Muke So Najeriya.
Amshi: Yau Najeriya
Riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari Kai Muke So Najeriya.
Amshi: Yau Najeriya
Riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari Kai Muke So Najeriya.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.