Ticker

6/recent/ticker-posts

Wakar Baba Tsoho Ya Sauka Ga Fa Tsoho Ya Sauka Ta Dauda Katuhu Rarara

DAUDA KATUHU RARARA - BABA TSOHO YA SAUKA GA FA TSOHO YA SAUKA

Jagora: Masu Fatar mutuwar ka

 Yanzu haushi ya qaru

 

Amshi: Baba tsoho ya sauka

 Damana gatan tsirrai

 

Jagora: Ga fa tsoho ya sauka

Amshi Damana gatan tsirrai

 

Jagora: Masu fatar mutuwarka

 Baba haushi ya aru

 

Amshi: Ga fa tsoho ya sauka

 

Jagora: Damana gatan tsirrai

 

Amshi: Masu fatar mutuwarka

 Yanzu haushi ya ƙaru

 

Jagora: Ku dubi tsoho ya sauka

Amshi Damana gatan tsirrai

 

Jagora: Ko me ye ka ga a tsaida gaskiya

Amshi: Halin baba

 Baba tsoho ya sauka

 

Jagora: Ga tsoho ya sauka

 Damana gatan tsirrai

Amshi: Masu fatar mutuwar ka

 Yanzu haushi ya ƙaru

 

Jagora: Khaliƙin Sarki mai iyawa kowa

 Allah ne

Amshi: Baba tsoho ya sauka

 

Jagora: In ko an ce makaɗin

 Kahutu rara Dauda ne

Amshi: Baba tsoho ya sauka

 

Jagora: Ilahu kai ne farkon batunmu

 Neman sa’a ne

Amsa: Gaskiya halin baba

 

Jagora: Don ko kai ne ke bamu

 Garkuwa in mun taru

Amsa: Ga fa tsoho ya sauka

 

Jagora: Damana gatan tsirrai

Amshi: Masu fatar mutuwarka

 Yanzu haishi ya ƙaru

 

Jagora: Baba duk mai noma da gatari

 Shi yay hauka

Amashi Baba tsoho ya sauka

 

Jagora: Wahala ta riske ku

 Masu yin bangon toka

Amshi Damana gatan tsirrai

 

Jagora: Kun aje mota

 Ku da kanku kun ɗauko jaka

Amshi: Gaskiya halin baba

 

Jagora: Darajar ta a gun talaka har ma ta ƙaru

Amshi: Baba tsoho ya sauka

 

Jagora: Damana gatan tsirrai

Amshi: Masu fatar mutuwarka yanzu haushi ya ƙaru

Jagora: Baba duk wanda ya ƙi ka

 Mai halin ‘yan wawa ne

Amshi: Baba tsoho ya sauka

 

Jagora: Wanda yake gaba da baba

 ɗan CLC ne

Amshi: Baba tsoho ya sauka

 Damana gatan tsirrai

 

Jagora: Mu ko tun farko masu yin mu

 Sun san LD ne

Amshi: Gaskiya halin baba

 

Jagora: Arziki kashi ne ya yanzu

 Mun tako baba

Amshi: Eah baba tsoho ya sauka

 

Jagora: Damana gatan tsirrai

Amshi: Masu fatar mutuwar ka

 Baba haushi ya ƙaru

 

Jagora: Ah! Zuwan baba janar

 Cuwa-Cuwa ya kauda ta

Amshi: Baba tsoho ya sauka

 

Jagora: Masu koyon tafiya

 Ku yanzu sai dai tatata

Amshi: Damana gatan tsirrai

 

Jagora: It has beenstory ne

 Da gaskiya kun san muryata

Amshi: Gaskiya halin baba

 

Jagora: Haihuwar mai tsidau

 Ba za ku kasa fahimta ba

Amshi: Baba tsoho ya sauka

 

Jagora: Damana gatan tsirrai

Amshi: Masu fatar mutuwarka

Yanzu haushi ya ƙaru

Jagora: Baba Barka da zuwanka

 Ga mu nan mun zo tarbo

Amshi: Baba tsoho ya sauka

 

Jagora: Ga Buhari sannu da hanyar zuwa

 Taron tsoho baba

Amshi: Damana gatan tsirrai

 

Jagora: Wanda duk ke haushinka

 Bai ruwan ‘yan sunnah ba

Amshi Gaskiya halin baba

 

Jagora: Je ka aike wa na sabuwa?

Amshi: Baba tsoho ya sauka

 

Jagora: Damana gatan tsirrai

Amshi Masu fatar mutuwarka

Yanzu haishi ya ƙaru

Jagora: Baba Sojoji naka ga shi

 Ka san ‘yan sanda

Amshi: Baba tsoho ya sauka

 

Jagora: Gaskiya ce gyaranka

 Baba kowa ya yarda

Amshi: Damana gatan tsirrai

 

Jagora: Su O’O ta ƙare

 Sai hada-hadar kifi banda

Amshi: Gaskiya halin baba

 

Jagora: Wanda zai yi siyasa da gaskiya

 Shi ab babba

Amshi: Baba tsoho ya sauka

 

Jagora: Damana gatan tsirrai

Amshi: Masu fatar mutuwar ka

 Yanzu haishi ya ƙaru

 

Jagora: Wanda ke dafa ma Buhari

 Sarki Allah ne

Amshi: Baba tsoho ya sauka

 

Jagora: Baba ku ne da nutso su

 Zabuwa sai dai zane

Amshi: Damana gatan tsirrai

 

Jagora: Gaskiya ce jarinka

 Gwargwadon adalci ne

Amshi: Gaskiya halin baba

 

Jagora: Mai hali na ƙwarai

 Ba cuwa-cuwa sai kai baba

Amshi: Baba tsoho ya sauka

 

Jagora: Damana gatan tsirrai

Amshi: Masu fatar mutuwarka

 Yanzu haushi ya ƙaru

 

Jagora: Gaskiyarka kaɗai ke riƙe mu

 Kowa ya gamsu

Amshi: Baba tsoho ya sauka

Jagora: Eh duk mutanen Najeriyarmu

 Kai ka haska su

Amshi: Damana gatan tsirrai

 

Jagora: Baba ko maƙiyan gwamnatinka

 Ma ai sun gamsu

Amshi: Gaskiya halin baba

 

Jagora: Ga fa tsoho ya sauka

 Kwarjini ma ya ƙaru

Amshi: i Baba tsoho ya sauka

 

Jagora: Damana gatan tsirrai

Amshi: Masu fatar mutuwarka

Yanzu haushi ya ƙaru

Jagora: In ana shishi da shi

 Ƙurciya shi ad dodo

Amshi Baba tsoho ya sauka

 

Jagora: Ka sako jamfata da

 taƙama dogon wando

Amshi: Damana gatan tsirrai

 

Jagora: Yau su san ajiyarmu

 Baba ya ƙaro ƙwazo

Amshi: Gaskiya halin baba

 

Jagora: Tattali za’a yi ba

 Cuwa-cuwa sai kai baba

Amshi: Baba tsoho ya sauka

 

Jagora: Damana gatan baba

Amshi: Masu fatar mutuwarka

Yanzu haushi ya ƙaru

Jagora: Zan yi baitin Ganduje

 Baba ɗan gatan baba

Amshi: Baba tsoho ya sauka

 

Jagora: Khadimul Islam namu

 Kaji mai ƙaunar baba

Amshi: Damana gatan tsirrai

Jagora: Mu fa aiki muka zo

 Ba aika-aika za mu yi ba

Amshi: Gaskiya halin baba

 

Jagora: Ga Buhari da Ganduje

 Ka ga aiki ya ƙaru

Asmhi: Baba tsoho ya sauka

 

Jagora: Damana gatan tsirrai

Amshi: Masu fatan mutuwarka

 Yanzu haushi ya ƙaru

 

Jagora: Tankaɗe bar shiga rariya

 Kunu sai dai kogo

Amshi: Baba tsoho ya sauka

 

Jagora: Al’ummar birni ƙauyuka

 Akwai wani ɗan saƙo

Amshi: Damana gatan tsirrai

 

Jagora: Baba yace a gaya wa ɗan gari

 Ko kuma baƙo

Amshi: Gaskiya halin baba

 

Jagora: Muita noma kiyo

 Abinci ba zai yanke ba

Amshi: Baba tsoho ya sauka

 

Jagora: Damana gatan tsirrai

Amshi: Masu fatan mutuwarka

Yanzu sauki ya ƙaru

Post a Comment

0 Comments