J - I, Ba za mu faɗin a yi gangami
A zo a ceci ƙasar nan
ba
Ba za mu faɗin a yi gaskiya
Wajen yin zaɓen nan ba
Ba zamu faɗin a zo a yi gangami
A ceci mutane ba
Wanga duk ahadunfa Aliyu
Yana kiran Jama’a duba
Gaskiya dokin ƙarfe
Ce fa anta hawa fa ta daure fa
Ina masoyan Baba Buhari
Ku tashi ko ba ku falka ba
Muna cikin tafiyar APC
Ba za mu barta ta watse ba
Ba za mu barta ta watse ba
APC za mui babba
Mai Bola Tunibu baba
BC Akande mu je baba
Najeriya sai baba Buhari
Ka ji gaskiya dokin ƙarfe
Tah!
A - Ku zo mu ƙara faɗa masu dai
‘yan ƙasarmu
APC muka yi
In za ai zaɓe a yi gaskiya
Ba za mu yarda da runtu ba
Najeriya sai baba Buhari
Gaskiya dokin ƙarfe
J - Ku zo mu ƙara faɗa masu dai
‘yan ƙasarmu
APC muka yi
In za ai zaɓe a yi gaskiya
Ba za mu yarda da runtu ba
Najeriya sai baba Buhari
Gaskiya dokin ƙarfe
A - Ku zo mu ƙara faɗa masu dai
‘yan ƙasarmu
APC muka yi
In za ai zaɓe a yi gaskiya
Ba za mu yarda da runtu ba
Najeriya sai baba Buhari
Gaskiya dokin ƙarfe
J - Najeriya sai Baba
Buhari
Gaskiya Dokin ƙarfe
A - Ni Najeriya kuka ni ke
Na rasa wane zai share man
‘Ya’yana Hausa, Yoruba, Ibo
Ku tashi ku duba man
Wanene zai jure ɗawainiya
Da ku cikinku ku zaɓa man
A kudu na ko a Arewa
Dawa-dawa kuka zaɓa man
J - Ga Buhari Uba babba
Jarumi gwarzo babba
Janar Buhari mazan Fama
Kin ji gaskiya dokin ƙarfe
A - Ku zo mu ƙara faɗa masu dai
‘yan ƙasarmu
APC muka yi
In za ai zaɓe a yi gaskiya
Ba za mu yarda da runtu ba
Najeriya sai baba Buhari
Gaskiya dokin ƙarfe
J - Ba za mu faɗin mu yi gangami
Mu zo mu gyara ƙasarnan ba
Ba za mu faɗin a yi gaskiya
A lokacin zaɓen nan ba
Ba za mu faɗin APC ta zo
TA gyara ƙasar nan ba
Ba za mu faɗin a cikin ƙasa
A daina yi muna wawa ba
Ba za mu faɗin a shi-shigo
Jam’iyyar APC ba
I, bata zo don wawa ba
Ba ta zo don kwabsi ba
Ta zo ta yi adalci a
tsaida
Gaskiya dokin ƙarfe
A - Ku zo mu ƙara faɗa masu dai
‘yan ƙasarmu
APC muka yi
In za ai zaɓe a yi gaskiya
Ba za mu yarda da runtu ba
Najeriya sai baba Buhari
Gaskiya dokin ƙarfe
J - In jama’a in ma barci
ku kai
Ku tashi ga maja babba
Kun san duk mai so ya hau
sama
Ba zai ƙi nemo tsane ba
Tsalle ɗaya ake yi a faɗa
A rijiya ba a gane ba
Amma sai kay yo tsalle
dubu
Ya ma wuce baka fito ba
Magana niy yo babba
Wani ba zai gane ba
A kusa a tsare shi ne
A yi gaskiya dokin ƙarfe
A - Ku zo mu ƙara faɗa masu dai
‘yan ƙasarmu
APC muka yi
In za ai zaɓe a yi gaskiya
Ba za mu yarda da runtu ba
Najeriya sai baba Buhari
Gaskiya dokin ƙarfe
J - Ita gaskiya dokin ƙarfe
Hawanta ba kowa ke ba
Gaskiya rigar-ƙarfe ce
Sakata ba kowa zai ba
Duniya ta yarda Janar
Ya sa rigar ba zai tuɓe ba
Shi tuwo sunansa tuwo
Har yau haka ne ba a canza
ba
Haka ne ba wai ne ba
Ba za ku musa man ba
Yau ƙasar nan
shi take Jira
Buhari mai dokin ƙarfe
A - Ku zo mu ƙara faɗa masu dai
‘yan ƙasarmu
APC muka yi
In za ai zaɓe a yi gaskiya
Ba za mu yarda da runtu ba
Najeriya sai baba Buhari
Gaskiya dokin ƙarfe
J - A, da tambaya na taho
me ƙarfi
Na san ba zan rasa amsa ba
Wanene zai taimaki tattali
na arziki
Bai rushe ba
Wane ne zai taimaki ilimi
Ya tafi sak bai noƙe ba
Wanene zai tallafi lafiya
Uwar jiki bata lauye ba
Wanene zai zo da haɗin kan
Ƙasa ya
zan bata watse ba
Ku duba tun daga samun
yancin
Ƙasa zuwa
yau na duba
Demakuraɗiya aka ce a nai
Mu yan ƙasa ba mu gane ba
Dame-dame aka ce za ai
muna
Zuwa a yau ba mu samu ba
Ai ba zan rasa ansa ba
Ga uba da rabin baba
Ai ƙasar nan
sai baba
Janar Buharii mai dokin ƙarfe
A - Ku zo mu ƙara faɗa masu dai
‘yan ƙasarmu
APC muka yi
In za ai zaɓe a yi gaskiya
Ba za mu yarda da runtu ba
Najeriya sai baba Buhari
Gaskiya dokin ƙarfe
J - I, Suna ganinmu ƙasarmu a hargitse
Ba za su tashi a gyara ba
Ana ta sace kuɗinmu
Suna gani, amman kamar ba
su gane ba
Idan ka hango kai magana
Kuma ba za su barka ka
zauna ba
Su ɓata rai in mun faɗi gaskiya
Saboda su ba su saba ba
Gata nan ba mu ɓoye ba
Gaskiyar ba mu ɓoye ba
Gaskiyar ba mu ɓoye ba
Gata nan fili sarari APC
Gaskiya dokin ƙarfe
A - Ku zo mu ƙara faɗa masu dai
‘yan ƙasarmu
APC muka yi
In za ai zaɓe a yi gaskiya
Ba za mu yarda da runtu ba
Najeriya sai baba Buhari
Gaskiya dokin ƙarfe
J - I, Ina masoyan Baba
Buhari
Dake jahar Lagos ku fito
Ina, masoyan Baba Buhari
Dake Kano kuma ku fito
Ina masoya Baba Buhari
Dake Kaduna sai kufuto
Ina masoyan baba Buhari
Dake Inugu sai ku futo
Ina masoyan Baba Buhari
Dake Adamawa, ku futo
Ina masoyan Baba Buhari
Dake Sakkwato sai ku futo
Ina masoyan Baba Buhari
Da Ke Borno kuma ku futo
Ina masoyan Baba Buhari
Dake Osun kuma ku futo
Ina masoyan Baba Buhari
Dake Ribas kuma ku futo
Ina masoyan Baba Buhari
Da ke Ondo kuma ku futo
Ina masoyan Baba Buhari
Da ke Jahar Yobe ku futo
Ina masoyan Baba Buhari
Dake Nasarawa sai ku futo
Ina Masoyan Baba Buhari
Dake Jahar Naija ku futo
Ina masoyan Baba Buhari
Dake Fulato Sai ku futo
Ina masoyan Baba Buhari
Dake Bayalsa se ku futo
Ina masoya Baba Buhari
Dake Imo kuma ku futo
Ina masoyan Baba Buhari
Dake Oyo Kuma ku fito
Ina Masoyan Baba Buhari
Dake Bauchi Kuma ku futo
Ina masoyan baba Buhari
Da ke Katsina Dikko ku
futo
Ina Masiyan Baba Buhari
Dake Zamfara sai ku futo
Ina masiyan baba Buhari
Dake Kebbi kuma ku futo
Ina masoyan Baba Buhari
Dake Taraba sai kufuto
Ina masoyan baba Buhari
Dake garin Gombe ku futo
Ina masoyan baba Buhari
Dake Jigawa se ku futo
Ga Buhari uba babba
Ga shi nan yazo baba
Ku futo in ji faruku Adamu
Mai gaskiya dokin ƙarfe
A - Ku zo mu ƙara faɗa masu dai
‘yan ƙasarmu
APC muka yi
In za ai zaɓe a yi gaskiya
Ba za mu yarda da runtu ba
Najeriya sai baba Buhari
Gaskiya dokin ƙarfe
J - Aye, duk abinda yai yo
zafi
Allah ka magani ba ƙato ba
A da muna neman mufuta
Sai gashi ta futo ba su gane
ba
Jam’iyu suka haɗu guri ɗaya
Suka yi maja ba gaba
Saboda kishi domin dawowa
Da martaba aka sa duba
Maƙiya ba su so ai ba
Ba su so a yi maja ba
Suka ce dokin ƙarfe ce
Ga shi ta zamo dokin ƙarfe
A - Ku zo mu ƙara faɗa masu dai
‘yan ƙasar mu
APC muka yi
In za ai zaɓe a yi gaskiya
Ba za mu yarda da runtu ba
Najeriya sai baba Buhari
Gaskiya dokin ƙarfe
J - Ba za mu daina yabama wanda
Suka assasa a yi maja ba
Ba za mu daina yabama Bola Tunibu
Mai kishin nan ba
Ba za mu daina shi Janar Buhari
Mai alhairi ba
Ba za mu daina yabama B.C Akande
Namu ciyaman ba
Ni ba su yarda da rinto ba
Ba su yarda da ruxi ba
Sun yarda a yo zaɓe na gaskiya
Kamar dokin ƙarfe
A - Ku zo mu ƙara faɗa masu dai
‘yan ƙasarmu
APC muka yi
In za ai zaɓe a yi gaskiya
Ba za mu yarda da runtu ba
Najeriya sai baba Buhari
Gaskiya dokin ƙarfe
J - Aye, ga wasiƙa nan buɗaɗɗiya
A je a kai wa mai malfa
Bara ta riga ta wuce
Bana ƙarfa-qarfa ba za ai ba
Ya mutun yana da gida
A ce ya je ya kwana cikin
rumfa
Zalunci karya ce mai ita
taka bi
Bai tsere ba
Zaɓen bana ba zan ba
Ba za a yi rinto ba
Mu Buhari muke fata
Shi ne da gaskiya dokin ƙarfe
A - Ku zo mu ƙara faɗa masu dai
‘yan ƙasarmu
APC muka yi
In za ai zaɓe a yi gaskiya
Ba za mu yarda da runtu ba
Najeriya sai baba Buhari
Gaskiya dokin ƙarfe
J - Two o tawuzan an tari zaɓen da aka yo a ƙasa
Duka an zaɓa
‘yan kudu sun futo ran zaɓe
Janar Buhari sun zaɓa
A arewa dukan mu mun futo
Janar Buhari mun zaɓar
Alokacin kana faɗuwa ƙasa
Tai war-was
Nasara bata samu ba
Maguɗi ba su kasa ba
Ku faɗawa mai malfa
Yau mun taho akan dokin ƙarfe
A - Ku zo mu ƙara faɗa masu dai
‘yan ƙasarmu
APC muka yi
In za ai zaɓe a yi gaskiya
Ba za mu yarda da runto ba
Najeriya sai baba Buhari
Gaskiya dokin ƙarfe
J - A ka zo twu tawuzan an sabum
Amma rawar bata canza ba
Aka zo twu tawuzan Ilabun
Ba su bar muna zaɓan ba
Sai janar yace jiki magayi
Wasu ba su gane ba
Kukan kurciya yai yo mai
hankali
Ba zai ya gane ba
Ga shi yau ba mu huta ba
Mutan ƙasa basu runtsa ba
Mu kasa mu tsare a bana
Ayi gaskiya dokin ƙarfe
A - Ku zo mu ƙara faɗa masu dai
‘yan ƙasarmu
APC muka yi
In za ai zaɓe a yi gaskiya
Ba za mu yarda da runtu ba
Najeriya sai baba Buhari
Gaskiya dokin ƙarfe
J - Yau dai mulkin son kai
su kai
Ƙasarmu
ba ƙarya ne ba
Tunda ga shi Obasanjo
Da kansa ya faɗa bai ɓoye ba
Wanda shi ɗannan kuma ya kafa su
Ba ƙarya ne
ba
Amma ya ce mulkin wariya
suke
Bai dace ba
Gaskiya ta futo duba
Ba ƙarya ya
faɗi ba
Gaskiya dokin ƙarfe
Ga shi ta futo dokin ƙarfe
A - ku zo mu kara faɗamasu dai
J - A ba za mu daina yabama gwabnonin ga
Da suke APC ba
Wanda duk ya fuce daga APC
Bai zam mai kishi ba
In mutun kishin Arewa yake
To ba zai bar maja ba
In mutum kishin kudu yake
Ba za ya bar APC ba
In mutum kishin gyaran ƙasa yake
Ba zai bar maja ba
Ya Allah duk mai son ataimaki ƙasa
Ba sherri ba
Ya Allah duk mai son a gyara al’umma
Ba wawa ba
In yana yin APC ka bashi a
ciki
Bai kucce ba
Wanda kuma yake a waje
Ka shigo da shi Allah
Rabba
Ga waɗannan Jajirtattu
Ba za mu daina yaba masu ba
Ba za mu daina yabama
Gwamnan Zamfara mai
alhairi ba
Abdul-Aziz Yari Gwamnan
Zamfara ne babba
Ba za mu daina yaba ma Gwamnan Lagos
Su Fashola ɗin ba
Ba za mu daina yaba ma Kwankwaso
Dakta Rabi’u Musa ba
Ba zamu daina yaba ma Rotumi Ameci
Gwamnan Ribas ba
Ba zamu daina yabama Inyaku
Gwamnan Adamawa ba
Ba zamu daina yaba ma Kashim Shattima
Gwamnan Barno ba
Ba za mu daina yaba ma Gwamnan
Yobe Ibrahim ba
Ba za mu daina yaba ma Almakura
Gwamnan Nasarawa ba
Ba zamu daina yaba ma Rocas
Gwamnan Imo Site ba
Ba za mu daina yaba ma Gwamna
Edo Adam Ashemule ba
Ba za mu daina yaba ma gwamnan
Osun Adisola ɗin ba
Ba za mu daina yaba ma Gwamnan
Ogun Ebukulle namu ba
Ga Gwabnan Oyo Abiyola
Ajimobi
Gwarzo babba
Ba za mu daina yaba ma Gwamnan
Sakkwato Wamako ba
Ba za mu daina yaba ma Gwamnan
Kwara abdulfata namu ba
Ba za mu daina yaba ma Faruku Adamu
Aliyu
Gwarzo ba
Aji Jigawa ana yin sa
Jama’arsa suna sonsa
Ya kira a futo a yi sak
Buhari za mu yo dokin ƙarfe
A - Ku zo mu ƙara faɗa masu dai
‘yan ƙasar mu
APC muka yi
In za ai zaɓe a yi gaskiya
Ba za mu yarda da runtu ba
Najeriya sai baba Buhari
Gaskiya dokin ƙarfe
J - A a yau ƙasar nan na da buƙatar
A taimaketa kai waye
A a yau ƙasar nan tana da buƙatar
A zo a harhaɗa hannaye
A yau ƙasar nan na da buƙatar
A tallabe ta ta bar maye
A yau ƙasar nan na da buƙatar
A taimaketa daga mugaye
Bata ƙaunar
‘yan maye
Bata neman kuraye
Ga Janar maganin janar
Janar Buhari ne gaskiya
dokin ƙarfe
A - Ku zo mu ƙara faɗa masu dai
‘yan ƙasar mu
APC muka yi
In za ai zaɓe a yi gaskiya
Ba za mu yarda da runtu ba
Najeriya sai baba Buhari
Gaskiya dokin ƙarfe
J - Iye, ga abunda ya ban
tsoro
A nan ƙasar ake karya doka
ɗauka ko ko korar ma’aikaci
Akwai tsarin doka
Ko mai za ai a ƙasa akwai tsari
A bisa doka
A ƙasar nan
yau komai
Za ai ba’a mai doka
Aye sai dai baki a ce doka
Ba a aikin doka
Komai sai yin jagajaga
Amma ku tashi ga mai dokin
ƙarfe
A - Ku zo mu ƙara faɗa masu dai
‘yan ƙasarmu
APC muka yi
In za ai zaɓe a yi gaskiya
Ba za mu yarda da runtu ba
Najeriya sai baba Buhari
Gaskiya dokin ƙarfe
J - Aye ba za mu daina yaba ma
‘Yan halat na Jama’iya APC
ba
Kano ka ɗau T. Gwarzo yana ciki
Ba za ya be –APC ba
Sannan ka ɗau Musa Gwadebe
Ciki ba za ya bar APC ba
Sannan ka ɗau Nasir Baballe,
Bai zama ɗan wawa ba
Sannan ka ɗauko Aminu Iddins
Bai zamo ɗan wawa ba
Buhari ya ce shi zai kansila
A darmanawa ba zan ba
Idan ka je Yobe a Damaturu
Ba za ka san yan wawa ba
C.D Karasuwa shi ma namu
ne
Ba za ya bar APC ba
Dukta Mustapha shi ma namu
ne
Ba za ya bar APC ba
In, ga gwaniyalga gidammu
Ba za ya bar APC ba
Jagora ne shi a matasa
Ba za ya barta ta watse ba
Mai Mala Boni yana tafiya
nan
APC bai daina ba
Kwata Goni ya APC
Ba za ya bar tafiyarnan ba
Ga zanna Mustapha APC
Ba za ya bar tafiyar nan
ba
Abdulkarim Lauwal Sifika
Ba za ya bar APC ba
Ɗan Lami
kuma babba manya
Ba za ya bar APC ba
Idan na koma Naija da baya
Akwai maza da ba su ƙare ba
Ga Sanata Ibrahim Musa
yana ciki
Bai kubce ba
Shi ne ciyaman APC a Neja
Jarumi gwarzo babba
Ga Honourabul Ado shi ma
Ba za ya barta ta watse ba
Jarumi gwarzo babba
Tafiyar bata kare ba
Da Jigawa zan ɗora
Sun kama gaskiya dokin ƙarfe
A - Ku zo mu ƙara faɗa masu dai
‘yan ƙasar mu
APC muka yi
In za ai zaɓe a yi gaskiya
Ba za mu yarda da runtu ba
Najeriya sai baba Buhari
Gaskiya dokin ƙarfe
J - Aye ba za mu daina yaba ma
Mazan ƙwarai masu kishin maja ba
Ba za mu daina yaba ma
Faruku Adamu Aliyu Gwarzo
ba
Ba za mu daina yaba ma Sa
Ba dan ya gwauce ba
Yana cikin APC hidima yake
ta yi
Bai daina ba
Da ka kira sunansa
Jigawa ce da kanta
Ba ƙarya ne
ba
Ba za mu daina yaba ma
Badaru Jala Habis mai kishi ba
Ba za mu daina yaba ma
Hajiya Rabi Ishaka tamu ba
Ba za mu daina yaba wa
Hajiya Bunta Farin NNPC ba
Ba za mu daina yaba wa
Hajiya Rabi Burukan tamu
ba
Ba za mu daina yaba wa
Hajiya Yalwa Ringin tamu
ba
Ba za mu daina yaba wa
Tsaiyyaba Gwaram mai kishi
ba
Ba za mu daina yaba wa
Hajiya Hauwa miga tamu ba
Ba za mu daina yaba wa
Hajiya Hadiza kafin
Hausawa
Ba za mu daina yaba wa
Alhaji Yuguda Hassan
Gwarma ba
Ba za mu daina yaba wa
Alhaji Mustapha Habib namu
ba
Ba za mu daina yaba wa
Alhaji Muntari kali namu
ba
Ba za mu daina yaba wa
Alhaji Sale Auyo namu ba
Ba za mu daina yaba wa
Muhammad Dumakuri namu ba
Ba za mu daina yaba wa
Ibrahim Iro na Jahun ba
Ba za mu daina yaba wa
Injiniya Magaji Debo namu
ba
Ba za mu daina yaba ma
Bello Soje, namu
kirakasamma
Ba za mu daina yaba wa
Alhaji Gambo Garki namu ba
Ba za mu daina yaba ma
Mustapha Rabo Ringjin namu
ba
Ba za mu daina yaba wa
Auwalu Sule Kila namu ba
Ba za mu daina yaba wa
Aminu Sankara APC ba
Ba za mu daina yaba ma
Ɗayyabu
Gwalo yana APC ba
Ba za mu daina yaba wa
Muhammad na Garu Malan
Madari ba
Ba za mu daina yaba ma
Ƙanen
Idins na goje ajaba ba
Ba za mu daina yaba wa
Honorabul Yusif Abba me
zan ba
Ba za mu daina yaba ma
Barista Ringin Gabar ɗin ba
Faruku Adamu ya ce
Godiya yake ta yi bai daina ba
Tafiyar batawatse ba
Maja bata karya ba
Najeriya sai baba Buhari
Kaji Gaskiya dokin ƙarfe
A - Ku zo mu ƙara faɗa masu dai
‘yan ƙasar mu
APC muka yi
In za ai zaɓe a yi gaskiya
Ba za mu yarda da runtu ba
Najeriya sai baba Buhari
Gaskiya dokin ƙarfe
J - Isuhu rana Isihaƙa hore
Mai waƙa ban ɓoye ba
Muna cikin APC zalla
Ba za mu barta ta watse ba
Lambar waya ita zan faɗeta
A nan gurin ban fasa ba
Sufuli bakwai sufuli ukku
ukku
Takwas biyun ɗin diba
Sai huɗun tara ɗan duba
Sai tara biyun ƙarshen ba
Najeriya sai Baba Buhari
Kun ji gaskiya dokin ƙarfe
A - Ku zo mu ƙara faɗa masu dai
‘yan ƙasar mu
APC muka yi
In za ai zaɓe a yi gaskiya
Ba za mu yarda da runtu ba
Najeriya sai baba Buhari
Gaskiya dokin ƙarfe
J - Ku zo mu ƙara faɗa masu dai
‘yan ƙasar mu
APC muka yi
In za ai zaɓe a yi gaskiya
Ba za mu yarda da runtu ba
Najeriya sai baba Buhari
Gaskiya dokin ƙarfe
A - Ku zo mu ƙara faɗa masu dai
‘yan ƙasar mu
APC muka yi
In za ai zaɓe a yi gaskiya
Ba za mu yarda da runtu ba
Najeriya sai baba Buhari
Gaskiya dokin ƙarfe
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.