RARARA KAHUTU WAQAR BUHARI TA UKU: Tsoho Kai Ne Sama
Amshi: Tsoho gyara zama kai ne
sama
Jan zaki bajimi ɗan gagara.
Jagora: Jan Zaki bajimi ɗangagara
Bera kan ka shigo ya firgita
Amshi: Tofa mai jimirin
jure fari
Jagora: Tsoho gyara zama
kai ne sama
Jan zaki bajimi dangara, ɓera kan ka shigo ya
firgita
Amshi: Bera kan ka shigo
ya firgita
Jagora: Xan wawa tuni har ya
firgita
Amshi: Tsoho gyara zama
kai ne sama
Jagora: Kowaye ya faxi yai ƙarya
Jemage ya ci dambun taliya
Jagora: Tofa mai jimirin
jure fari
Amshi: Tsoho gyara zama
kai ne sama
Jagora: Jan zaki bajini na
gyara
ɓera kan kafuto ya firgita
Amshi: Tofa mai jimirin
jure fari
Jagora: Yai maza kan ka shigo
Ya shige ɗaka
Amshi: Jan zaki bajini
dangagara
ɓera kan ka shigo ya firgita
Jagora: Ya kai mai jimirin kai aike
Ko an ce tafi ai ba ya zuwa
Amshi: Tsoho gyara zama
kai ne sama
Jagora: Ai yaro a yi
kankanba daɗa
Na game su da halin laduwa
Amshi: Jan zaki bajini
dangargara
Jagora: Sun kama kunkuru
sun hau sama
Tsoho kam tuni ya hau taguwa
Amshi: Tsoho gyara zama
kai ne sama
Jagora: Ayashe tana tsare
sarkin fallasa
Kai kuwa sake wuri ɗan Zamfara
Amshi: Tsoho mai jimirin
jure fari
Jagora: Ka saba da ruwa
tun kan haka
Don ku ne a ciki malam bado
Amshi: Tsoho gyara zama
kai ne sama.
Jagora: A sara wa ngira
ko baki
An shaida ki wurin kare ido.
Amshi: Jan zaki bajimi
xangagara
Jagora: Tun tafiya baki
ta qare mashi
In ya sami quli sai yai kwaxo
Amshi: Tsoho gyara zama
kai ne sama
Jagora: Kun lalata wuri
‘yan adawa
An yi kiran ku kuna kunyar zuwa.
Amshi: Tofa mai jimirin
jure fari
Jagora: Tsoho gyara
zama kai ne sama
Amshi: Jan zaki bajimi
xangagara
Vera kan shigo ya firgita
Jagora: Buzu da raqumi
yake buzu
In babu raqumi sai yai vata.
Amshi: Tsoho gyara zama
kai ne sama
Jagora: Yau mu ke da
gida mu ke da waje
Yau ‘yan vata gida sun firgita.
Amshi: Jan zaki bajimi
xangagara
Jagora: Shi wancan day
a yi ma sheri jiya
Ya rave tuni ya faxa kwata.
Amshi: Tsoho gyara zama
kai ne sama
Jagora: Rani da damina
ni Koran qarya ne
Na bi ‘ya’yan guguwa
Amshi: Tsoho mai
jimirin jure fari.
Jagora: Tsoho gyara zama kai ke sama
Amshi: Jan zaki bajini xangagara
ɓera kan ka shigo ya firgita
Jagora: Kura tauna ƙashi an gamsu
Giwa a bar ta wurin karye icce
Amshi: Jan zaki bajini
dangagara
Jagora: Daɗa an tattaushi wurin wawa
Dole su wane su zan kace-na-ce
Jagora: Ga Sakatarenmu na
zo na fati
Maza-maza bani rabona in wuce
Amshi: Tsoho gyara zama
kai ne sama
Jagora: Na san ba ka da
rowa idan
Na zo tilas ka yi mun ko ba yawa
Amshi: Tofa mai jimirin
jure fari
Jagora: Tsoho gyara zama
kai ne sama
Amshi: Jan zaki bajimi ɗangagara
ɓera kan ka shigo yafirgita
Jagora: Mai gaskiya irinka
daban ne
Na yi na’am tuni na sara maka
Amshi: Tsoho gyara zama
kai ne sama
Jagora: Duk tsananin
wahala ko daɗi
Sai na ambaci turmi sha daka
Amshi: Jan zaki bajimi ɗan gagara
Jagora: Almajirin Mawaƙa Kamilu
Mun gode da halinɗaka
Amshi: Tsoho gyara zama
kai ne sama
Jagora: Zan kushe wa halin
nasu ɗan gabu
In an ce tafi shi ba ya zuwa
Amshi: Tofa mai jimirin
jure fari
Jagora: Tsoho gyara zama
kai ne sama
Amshi: Jan zaki bajimi ɗangagara.
ɓera kan shigo ya firgita
Jagora: Duk in da hadari
yake
In dai da walƙiya za
ai cida
Amshi: Tsoho gyara zama
kai ne sama
Jagora: Ko ‘yan hayaniyar ga sun yarda da
Tsohonmu mai gida ba ya faɗa
Amshi: jan zaki bajimi ɗan gagara
Jagora: Bayan an gama zaɓe suka ce
Saura cuwa-cuwa ta wata shida
Amshi: Tsoho gyara zama
kai ne sama
Jagora: Uwar cuku-cuku an
kawar da shi
Babu cuwa-cuwa yanzu ko na rabin awa
Amshi: Tofa mai jimirin
jure fari
Jagora: Tsoho gyara zama
kai ne sama
Amshi: Jan zaki bajimi ɗaka
ɓera kan ka shigo ya firgita
Jagora: Kan daki kake sai
an taru
Ko an taru maza shakka sukai
Amshi: Tsoho gyara zama
kai ne sama
Jagora: Idan wagambari ma
shadda ce
Ai wannan da baƙin yadi
muke
Amshi: Tsoho gyara zama
kai ne sama
Jagora: Idan tivi a cikin
falo take
Ka ga falo a uwar ɗaki yake
Amshi: Tsoho gyara zama
kai ne sama
Jagora: A’a da kuje yaƙi da maza
Don ko kun hau hanya da rago ba ya zuwa
Amshi: Tofa mai jimirin
jure fari
Jagora: Tsoho gyara zama
kai ne sama
Amshi: Jan zaki bajimi ɗaki
ɓera kan ka fito ya firgita
Jagora: Na rantse da
hukuncin mai sama
Amshi: Tsoho gyara zama
kai ne sama
Jagora: Hukunci da gaskiya
Jagora: Ku na arewa da
‘yan ɓarin kudu
Kowa na da ma’auni war haka
Amshi: Tsoho gyara zama
kai ne sama
Jagora: Na kushe wa su
dattijon biri
Su sun samu gidan mugun dawa
Jagora: Tsoho gyara zama
kai ne sama
Tofa mai jimirin jure fari
Amshi: Jan zaki bajimi ɗaka
ɓera kan ka fito ya firgita
Jagora: Su ke cikin ka
suna kushe maka
Sai na tuntuɓi gonar dankali
Amshi: Tsoho gyara zama
kai ne sama
Jagora: Shanu na ƙyama sai na hangi
Ganyena a wurin rogo tuli
Amshi: Jan zaki bajimi ɗan gagara
Jagora: Dogo canja hali in
ka ƙi
Mu yi ma bizar waje ko ba shiri
Amshi: Tsoho gyara zama
kai ke sama
Jagora: Na rena ma ƙuli na riƙo gyaɗata
Kan na yi ya kai sau nawa
Amshi: To fa mai jimirin
jure fari
Jagora: Tsoho gyara zama
kai ne sama
Amshi: Jan zaki bajimi ɗaka,
ɓera kan ka fito ya firgita
Jagora: Kura tauna kashi
an gamsu
Da giwa bar ta gurin karye icce
Amshi: Tsoho gyara zama
kai ne sama
Jagora: Aa tallaushe wurin
wawa
Dole su wane suna kace-na-ce
Amshi: Jan zaki bajimi dan
gagara
Jagora: Gun Sakatare na zo na fati
Mai mana maza bani rabona in wuce
Amshi: Tsoho gyara zama
kai ne sama Hayya
Jagora: Na san ba ka da
rowa
Idan na zo tilas ka yi mun ko ba yawa
Amshi: To fa mai jimirin
jure fari
Jagora: Tsoho gyara zama
kai ke sama
Amshi: Jan zaki bajimi ɗan gagara
ɓera kan ka fito ya firgita
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.