RARARA KAHUTU WAQAR BUHARI TA BIYU: Ga Dattijo Ya Dawo
Jagora: Ga Dattijo ya dawo
Amshi: Mu yi rawa, mu yo tsalle
Jagora: Karɓi ka ja mu je baba
Alfaharin talakawa
Amshi: Mu yi rawa, mu yo tsalle
Jagora: Mu yi rawa mu yo tsalle
Amshi: Baba Buhari zaɓunmu
Alfaharin talakawa
Jagora: Ga dattijo ya dawo
Amshi: Mu yi rawa mu yo
tsalla
Jagora: Baba Buhari ya sauka
Alfaharin talakawa
Jagora: Ga dattijo ya dawo
Mu yi rawa mu yo tsalla
Jagora: Karɓi ka ja mu je baba
Alfaharin talakawa
Amshi: Ga dattijo ya dawo
Mu yi rawa mu yo tsalle
Jagora:/Amshi Karɓi ka ja mu je Baba
Alfaharin talakawa
Jagora: Masu faɗar halin ka
Bai yi kama da gyara ba
Amshi: Ga dattijo ya dawo
Jagora: Duk faɗin ƙasar
tamu
Banga guda kamar kai ba
Amshi: Alfarin talakawa
Jagora: Baba Buhari kwaɗo
Bai zai yi kama da zoma ba
Amshi: Baba ubanmu ya dawo
Jagora: Wanda ya ke tushinka
Bar shi muna fuki wwa
Amshi Ga dattijo ya dawo
Jagora: Mu yi rawa mu yo
tsalle
Amshi: Baba Buhari zaɓunmu
Alfaharin talakkawa
Jagora: Allah wadai karambani
Ka ba shi kin boka
Amshi: Baba Buhari ya dawo
Jagora: Wanda ya kyale gaskiya
War haka za ya sha kuka
Amshi: Alfaharin talakawa
Jagora: Mena saya da ɗan bajo
ɗan ajiye- nakai yinka
Amshi: Baba ubanmu ya dawo
Jagora: Mu mun zaɓi dattijo
Mai ra’ayi ga talakkawa
Amshi: Ga dattijo ya dawo
Jagora: Mu yi rawa mu yo tsalle
Amshi: Baba Buhari zaɓunmu
Alfaharin talakkawa
Jagora: Ka kulaƙauyuka
baba
Alfahari ga ‘yan birni
Amshi: Ga dattijo ya dawo
Jagora: Takin zamani an raba mana
Ko’ina har ni
Amshi Alfaharin talakawa
Jagora: Noman damina ne muke yi
Kar a kai rani
Amshi Baba Buhari ya dawo
Jagora: Baba Ubanmu gatanmu
Alfaharinmu xan baiwa
Amshi: Ga dattijo ya dawo
Jagora: Mu yi rawa mu yo
tsalle
Amshi: Baba Buhari ɗan baiwa
Alfaharin talakkawa
Jagora: Nm mu yi rawa da murna ta
Baba ubanmu ya dawo
Amshi: Ga dattijo ya dawo
Jagora: Baba zuwanka murna muke
Ta halinka ya dawo
Amshi: Alfaharin talakkawa
Jagora: To barka da sauka
Muke maka namu ya dawo
Amshi: Baba ubanmu ya dawo
Jagora: Murna muke sannu
Sannu ubanmu ɗan baiwa
Amsa: Ga dattijo ya dawo
Jagora: Mu yi rawa mu yo
tsalle
Amshi: Baba Buhari zaɓunmu
Alfaharin talakawa
Jagora: Cikin waƙa ta baba
Ya kyautu na gaida gwamnnona
Amshi: Ga dattijo ya dawo
Jagora: Na sami iri na
sukar ga
In ajiye na kai gona
Amshi: Alfaharin talakkawa
Jagora: Oga mai Malabu, nakai
sha’aninka gwarzona
Amshi: Baba Ubanmu ya dawo
Jagora: Ka ji mai mana tun da
sassafe
Ya fi munafiki wawa
Amshi: Ga Dattijo ya dawo
Jagora: Mu yi rawa mu yo
tsalle
Amshi: Baba Buhari zaɓunmu
Alfaharin talakawa
Jagora: Baba riƙa da kyau
Kar ka damu da tsegumin
mayu
Amshi: Ga dattijo ya dawo
Jagora: Ka riƙe rabbana
Su su ja’e su je su ɗau layu
Amshi: Alfaharin talakawa
Jagora: Ba mu da ja a
motarka
Yanzu akwai cikar tayu
Amshi: Baba Ubanmu ya dawo
Jagora: Masu fushinka in
Sun faka da jaware tsattsewa
Amshi Ga Dattijo ya dawo
Jagora: Alfaharin talakawa
Amshi: Baba Buhari zaɓunmu
Alfaharin talakawa
Jagora: Saƙon mai
Malabunu
Mai ra’ayin talakawa
Amshi: Ga dattijo ya dawo
Jagora: Hasken Yobe duk wanda ke
Da fushinka yai gawa
Amshi: Alfaharin talakawa
Jagora: Sakatre na Fatinmu
Mai ra’ayin uban Kowa
Amshi: Baba Ubanmu ya dawo
Jagora: Mun yaba mai Malabunu
Bai iya furta karya ba
Amshi: Ga dattijo ya dawo
Jagora: Mu yi rawa mu yo
tsalle
Amshi: Baba Buhari zaɓunmu
Alfaharin talakawa
Jagora: Baba Buhari
dattijo
Ga kilishi ku wanke shi
Amshi: Ga dattijo ya dawo
Jagora: Oga namu ya dawo
Ga shi jikinshi yai ƙarfi
Amshi: Alfaharin talakkawa
Jagora: Kowaye ya kwame ya kula
Ya sha zafi
Amshi: Baba Ubanmu ya dawo
Jagora: Baba ka ƙara kwa zo
Kana kauda cutawa
Amshi: Ga dattijo ya dawo
Jagora: Mu yi rawa mu yo
tsalle
Amshi: Baba Buhari zaɓunmu
Alfaharin talakkawa
Jagora: Saƙon mai mala buni ne
Isiyaku yak kawo
Amshi: Ga dattijo ya dawo
Jagora: Kai ni Isiyaku goron
da mai tsidau da yak kawo
Amshi: Alfaharin talakkawa
Jagora: Waƙa ce ta
murna
Ta baba ubanmu ya dawo
Jagora: Je ka abinka dattijo
Sannu ubanmu ɗan baiwa
Amshi: Ga dattijo ya dawo
Jagora: Mu yi rawa mu yo
tsalle
Amsa: Baba ubanmu zaɓunmu
Alfaharin talakawwa
Jagora: Baba na ƙauye sun yaba ka
da ‘yan birni
Amshi: Ga Dattijo ya dawo
Jagora: Buhari maza da matanmu
na ta yabon ka har ma ni
Amshi: Alfaharin talakawa
Jagora: Wanda ya kushe mulkinka
Ya yi fushi da tsantseni
Amshi: Baba ubanmu ya dawo
Jagora: Duk wanda ya kushe halinka
Bai taɓa yin kamar kai ba
Amshi: Ga dattijo ya dawo
Jagora: Mu yi rawa, mu yo
tsalle
Amshi: Baba Buhari zaɓunmu
Alfaharin talakawa
Jagora: Baitin baba
Ganduje
Zan yi yabon uban kowa
Amshi: Ga dattijo ya dawo
Jagora: Zan yabi khadimul
Islamu
da ba ya gaggawa
Amshi: Alfaharin talakawa
Jagora: Ka san mai kula ne
Da ba shi da nuna bambarwa
Amshi: Baba ubanmu ya dawo
Jagora: Shi aiki yake
Ba aika-aika ba a bar wa
kwakwawa
Amshi: Ga dattijo ya dawo
Jagora: Mu yi rawa mu yo
tsalle
Amshi: Baba Buhari dakonmu
Alfaharin talakkawa
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.