RARARA KAHUTU WAQA TA HUXU: Maraba Da Tsoho Oyoyo
Jagora:/Amshi: Maraba da
tsoho Oyoyo
Amshi: Wandara sai ciwon baki
Jagora: A suna ta
hayagagar wofi
Wasu na galatsi sai ga baba
Amshi: Maraba da tsoho
Oyoyo
Jagora: Su wandara sai
ciwon baki
Amshi: Suna ta hayagagar
wofi
Wasu na galatsi sai gababa
Jagora: Maraba da tsoho
Oyoyo
Amshi: Su wandara sai
ciwon baki
Jagora: Wasu na kuka, wasu
na murna
Ana haka sai kuma ga baba
Amshi: Maraba da tsoho
Oyoyo
Jagora: Suna ta hayagagar
wofi
Wasu na galatsi sai ga baba
Amshi: Maraba da tsoho
Oyoyo
Su wandara sai ciwon baki
Jagora: Nn ƙaya suka hau mai tsido
Ya ƙyautu su nemo takalmi
Amshi: Maraba da tsoho
Oyoyo
Jagora: Ku ne kuka hau hanyar bori
Ya kyautu ku nemo mai gurmi
Amshi: Su wandara sai
ciwon baki
Jagora: Masu kama kifi na
tsoro taba shi
da dama mai tsini.
Amshi: Maraba da tsoho
Oyoyo
Jagora: Magana muka wa
‘yan ca nan ga
Su tuba su daina riƙon gaba
Amshi: Maraba da tsoho
Oyoyo
Jagora: Su wandara sai
ciwon baki
Amshi: Suna ta hayagagar
wofi
wasu na gatsali sai ga
baba
Jagora: Na roƙi tabaraka mai iko
Ya raba mu da ‘yan mugun baki
Amshi: Maraba da tsoho
Oyoyo
Jagora: Komai girman sa
gobe
Warhaka ya ƙyale
carki
Amshi: Su wandara sai
ciwon baki
Jagora: An yi gaskiya an
gyara ƙasa
Su algaza
Amshi: Maraba da tsoho
Oyoyo
Jagora: Allah masani shi
yai dattijo
Ya sa mana tsohon rana gaba
Amshi: Maraba da tsoho
Oyoyo
Jagora: Su wandara sai
ciwon baki
Amshi: Ana ta hayagagar
wofi
Wasu na gatsali sai ga baba
Jagora: Ya taɓe zuman ƙasa
Zomo ta ruga
Amshi: Maraba da tsoho
Oyoyo
Jagora: Duk wanda ya sai
yaɗin wando
Ya kyautu ya sai yadin riga
Amshi: Su wandara sai
ciwon baki
Jagora: Ruwa aka wa hanya ɗoɗar
In da ta ɗauro ai
Amshi: Maraba da tsoho
Oyoyo
Jagora: Ana haka ko mulkin
wancan
Su wandara sun so su yi zamba
Amshi: Maraba da tsoho
Oyoyo
Jagora: Su wandara sai
ciwon baki
Amshi: Ana ta hayagagar
wofi
Wasu na gatsali sai ga baba
Jagora: Wasu na azumin
samun lada
Wasu na azumin kamun baki
Amshi: Maraba da tsoho
Oyoyo
Jagora: Gwamnatinmu da
adalci muka zo
To ka ga akwai canjin kaki
Amshi: Su wandara sai
ciwon baki
Jagora Hayyi: mun yarda
Buhari ya maimaita
Kar ka yi mana tawaye carti ee! hayya
Amshi Maraba da tsoho
Oyoyo
Jagora Na Kahutu akwai
Launin zance
Wataƙilla ka gane baba
Amshi Maraba da tsoho
Oyoyo
Jagora Su wandara sai
ciwon baki
Amshi Ana ta hayagagar
wofi
Wasu na gatsali sai ga baba
Jagora Dukiyar ƙasarmu a inganta
Amshi Maraba da tsoho
Oyoyo
Jagora Dattijo ka damƙe da gaskiya
Ka baje muna ƙaryar
mai zamba
Amshi Su wandara sai ciwon
baki
Jagora Aiki ka tsaya kai
mana
Kai na yarda da kai baka gaba
Amshi Maraba da tsoho
Oyoyo
Jagora .................
General
Kibiya ta mai ƙin adalci harba
Amshi Maraba da tsoho
Oyoyo
Jagora Su wandara sai
ciwon baki
Amshi Ana ta hayagagar
wofi
Wasu na gatsali sai ga baba
Jagora Nn suna ta
hayagagar wofi
Wasu na gatsali sai ga baba
Amshi Maraba da tsoho
Oyoyo
Jagora Maganar ciki sai da
tsoro ce
A fito mana fili ai zance
Amshi Su wandara sai ciwon
baki
Jagora Ba na cika kallon
mai waina
In dai akwai layin fanke
Amshi Maraba da tsoho
Oyoyo
Jagora Na gaya wa jemage
in dai
Ya zo ƙasa sai dai yai koke
Amshi Maraba da tsoho
Oyoyo
Jagora Bana mun ƙure ƙaryar mai malfa
War haka sai layin baba
Amshi Maraba da tsoho
Oyoyo
Jagora Su wandara sai
cowon baki
Amshi Ana ta hayagagar
wofi
Wasu na gatsali sai ga baba
Jagora Amma wasu za su ci
indomin ƙarshe
Amshi Maraba da tsoho
Oyoyo
Jagora Nn huɗu ga huɗu
Kun ga takwas ke nan
Jagora Ganduje Buhari
A ko yaushe
Amshi Su wandara sai ciwon
baki
Jagora Ganduje a dole ka
kau da biri
Shi na ya zamo hujjar ƙarshe
Amshi Maraba da tsoho
Oyoyo
Jagora Ganduje Buhari muna
tare
Ku za ku yi maimaici baba
Amshi Maraba da tsoho
Oyoyo
Jagora Su wandara sai
ciwon baki
Amshi Ana ta hayagagar
wofi
Wasu na gatsali sai ga baba
Jagora Gaba dai dattijo
muje
In za mu rabon takin taro
Amshi Maraba da tsoho
Oyoyo
Jagora Sabon abu ni dai na
shaida
Darajarsa ta zarce gyauro
Amshi Su wandara sai ciwon
baki
Jagora Doki in dai har
natsere ne
Ya kyautu a nemo mai horo
Amshi Maraba da tsoho
Oyoyo
Jagora Naroƙi tabaraka mai komi
Ka taya mana ya Allah rabba
Amshi Maraba da tsoho
Oyoyo
Jagora Su wandara sai
ciwon baki
Amshi Ana ta hayagagar
wofi
Wasu na gatsali sai ga baba
Jagora: Maraba da tsoho
Oyoyo
Amshi: Su wandara sai
ciwon baki
Jagora: Ah Suna ta
hayagagar wofi
Wasu na gatsali sai ga baba
Amshi: Maraba da tsoho
Oyoyo
Jagora: Su wandara sai
ciwon baki
Amshi: Suna ta hayagagar
wofi
Wasu na gatsali sai ga baba
Jagora: Maraba da tsoho
Oyoyo
Amsa: Su wandara sai ciwon
baki
Jagora: Wasu na kuka wasu
na murna
Ana haka sai kuma ga baba
Amsa: Maraba da tsoho
Oyoyo
Jagora: Suna ta hayagagar
wofi
Wasu na gatsali sai ga baba
Amshi: Maraba da tsoho
Oyoyo
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.