WAƘAR MUDASSIRU ƘASIM KANO, MAI SUNA “MU AMSHI RUWA” WADDA YA YI A (2019)
J - Iye, Tunti Naintin dama ta samu
APC za mu daɗa qwani
APC Jam’iyar Buhari
A - Mu amshi ruwa mu zaɓi Buhari
J - Mu kurbi ruwa muji mu da qwari
A - Mu amshi ruwa mu zaɓi Buhari
J - Mudassiru kasim ne da ga kano ne,
Shike maku jin-jina saboda Buhari
A - Mu amshi ruwa mu zaɓi Buhari
J - Ranar zabe rana babu don makogarummu
Zai jiqa fari
A - Mu amshi ruwa mu zaɓi Buhari
J - Alamu sun nuna halin motar jatau
Bana zatayi gwari
A - Mu amshi ruwa mu zaɓi Buhari
J - Kafin la’asar mun biya allon mu,
Mun wanke mun zabi Buhari
A - Mu amshi ruwa mu zaɓi Buhari
J - Wa to cenjin yanayi na gidan Buhari,
Idan halar ne a gidan buhari
A - Mu amshi ruwa mu zaɓi Buhari
J - S.D babba bici yana muna tuni,
Kasarnan babu tamkar Buhari
A - Mu amshi ruwa mu zaɓi Buhari
J - Katin zabe yi mashi tanadi,
Adana shi ;maganin ‘yan sharri
A - Mu amshi ruwa mu zaɓi Buhari
J - Ranar zabe mu zabi Buhari
A - Mu amshi ruwa mu zaɓi Buhari
J - Wato canji goga babba bici,
Shi ka magana ka ji ka da qwari
A - Mu amshi ruwa mu zaɓi Buhari
J - Ya san kimar masoya Buhari
A - Mu amshi ruwa mu zaɓi Buhari
J - In dai baka kishin jama’a
Ba kai ba baffa ko da Buhari
A - Mu amshi ruwa mu zaɓi Buhari
J - Aji shaida wa mutun goma
ranar zabe mu zabi Buhari
A - Mu amshi ruwa mu zaɓi Buhari
J - wai to canji kungiyar alkhairi
Manufarmu kadai a zabi Buhari
A - Mu amshi ruwa mu zaɓi Buhari
J - Motoci metin na kamfen Buhari
A mu jinjinama yakubu waziri
A - Mu amshi ruwa mu zaɓi Buhari
J - Yakubu wazir muna godiya
A muna jinjina a madadin Buhari
A - Mu amshi ruwa mu zaɓi Buhari
J - Allah dafa wa baba Buhari
A - Mu amshi ruwa mu zaɓi Buhari
J - Allah kare baba Buhari
A - Mu amshi ruwa mu zaɓi Buhari
J - Duk mai kaunar a gyara qasa,
Wannan ne zaya zabi Buhari
A - Mu amshi ruwa mu zaɓi Buhari
J - Layin dogo an yi watsi da shi
Ya durfafe su baba Buhari
A - Mu amshi ruwa mu zaɓi Buhari
J - An kammala kaduna to abuja
Har mu ji guwanmu da qwari
A - Mu amshi ruwa mu zaɓi Buhari
J - Abuja to kano hanyar jirgi hanyar mota,
A naimai kwari
A - Mu amshi ruwa mu zaɓi Buhari
J - Kullun kaddamar da tituna ake yi
Aiki ne ba zancen guni
A - Mu amshi ruwa mu zaɓi Buhari
J - Na Mama A’isha Fes Ledi
Mun gaisheki uwar gidan Buhari
A - Mu amshi ruwa mu zaɓi Buhari
J - Baban Yusuf da Zara Baba Buhari
A - Mu amshi ruwa mu zaɓi Buhari
J - Shi ne Shugaban da ICC sun ka ce
Mun gaisheka ka wuce sharri
A - Mu amshi ruwa mu zaɓi Buhari
J - Kai ne shugaban da ka zo nan gun
Ba da laifi ba guiwakka da ƙwari
A - Mu amshi ruwa mu zaɓi Buhari
J - An ce had Dubai aka Je aka tattaro
Dala don kada Buhari
A - Mu amshi ruwa mu zaɓi Buhari
J - To du wanda yai yi katari da kuɗin
Ya karɓo fa ya zaɓi Buhari
A - Mu amshi ruwa mu zaɓi Buhari
J - Ya karɓi kuɗin ya zaɓi Buhari
A - Mu amshi ruwa mu zaɓi Buhari
J - Wanda yaɗɗauko manyan ayukka
Za ya zaga ƙasarmu Baba Buhari
A - Mu amshi ruwa mu zaɓi Buhari
J - Titin Kano zuwa Abuja
Ana yi ana aiki ko da ƙwari
A - Mu amshi kuɗi mu zaɓi Buhari
J - Titin Maiduguri zuwa Kano
Ana aiki aikin mai ƙwari
A - Mu amshi ruwa mu zaɓi Buhari
J - Katsina da Kano ana yi shi ma
Zamfara Kwar ana yi shi ma
Kwantagora Kebi ana yi shi ma
Lagwas Ibadan ana yi shi ma
Wari Bayelsa ana yi shi ma
Manbila hazo ana yi shi ma
A’a Zungeru ana yi shi ma
Ilori Kabba ana yi shi ma
Nasarawa Keffi ana yi shi ma
Kai Fanin Rizab ɗin mu ya cika maƙil
GDP ɗin mu ya daɗe kwarai
A - Mu amshi ruwa mu zaɓi Buhari
J - Ikwanomik ɗin mu ya daɗa haɓɓaka
Imfileshen ɗin mu ya rage sauri
A - Mu amshi ruwa mu zaɓi Buhari
J - Yau a Noma ba aimuna gori
A - Mu amshi ruwa mu zaɓi Buhari
J - To neman gama gwaguyar gori ba
Wasu yalon Bello na masu tauri
A - Mu amshi kuɗin mu zaɓi Buhari
J - To ku sallama wa baba Buhari
A - mu amshi kuɗin mu zaɓi Buhari
J - Sun saci kuɗi suna yin tayi
A - Mu amshi kuɗin mu zaɓi Buhari
J - Karɓe kwace baba Buhari
A - Mu amshi ruwa mu zaɓi Buhari
J- Koko da za a ce sai ambiya kuɗi
Za mu biya mu zaɓi Buhari
A- Mu amshi ruwa mu zaɓi Buhari
J- Na nan wajen ku ce baba Buhari
A- Baba Buhari
Baba Buhari
Baba Buhari
J- Na nan gefen ku ce Baba buhari
A- Baba Buhari
Baba Buhari
Baba Buhari
J- Na Tsakiya ku ce Baba Buhari
A- Baba Buhari
Baba Buhari
Baba Buhari
J- Bana dai kam Baba ya kashe tauri
A- Mu amshi ruwa mu zaɓi Buhari
J- A kudu da Arewan Baba Buhari
A- Mu amshi ruwa mu zaɓi Buhari
J- Babu yawan aiki na Baba Buhari
A- Mu amshi ruwa mu zaɓi Buhari
J- Ga gada ganye da Titin Baba Buhari
A- Mu amshi ruwa mu zaɓi Buhari
J- An yanken suya bar su da turi
A- Mu amshi ruwa mu zaɓi Buhari
J- A sase titin Baba Buhari
A- ‘Yan yankin suya bar su da turi
J- Mu amshi ruwa mu zaɓi Buhari
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.