WAƘAR YAU NIJERIYA RIƘO SAI MAIGASKIYA” WADDA IBRAHIM YALA HAYIN BANKI KADUNA YA YI WA JANARAL MUHAMMAD BUHARI A SHEKARAR (2003) LOKACIN YANA TAKARAR SHUGABANCIN NIJERIYA A TUTAR JAM’IYYAR A.P.P INDA YA CE
Y/Amshi: Ayyi ruru-rui!
Jagora: Yau Nijeriya riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari kai muke so Nijeriya
Y/Amshi: Yau Nijeriya riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari kai muke so Nijeriya
(Mai mai tawa)
Jagora: Allah haliƙu da yaiyo duka duniya
Mu roƙon da za mu yo duka bai daya
Baiwa Buhari Mulkin Nijeriya
APP ta zo ta rungumi
Nijeriya
Don shi ne muke buƙata mai gaskiya
Y/Amshi: Yau Nijeriya riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari kai muke so Nijeriya
Jagora: Salli Ala Muhammadu, Annabi Shugaba
Mai cetonmu wanda kowa ke fargaba
Annabi ran ƙiyama ka samu sahun gaba
Mun bi Rasulu ɗan Amina Maigaskiya
Y/Amshi: Yau Nijeriya riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari kai muke so Nijeriya
Jagora: Ka zo ka fitar da mu a ƙunci da muke ciki
Yau mun sha wuya a kullun sai farmaki
Ana satan kuɗinmu a yau ba shamaki
Ka ji halin da muke ciki Nijeriya
Y/Amshi: Yau Nijeriya riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari kai muke so Nijeriya
Jagora: Tanko da Baba Lola suna ta halin tsiya
Mu da kuɗin mu gashi duk an muna murɗiya
Shi yassa muke biɗan yo maigaskiya
Y/Amshi: Yau Nijeriya riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari kai muke so Nijeriya
(Mai mai tawa)
Jagora: Allah wadanku tun da bakwa ƙaunammu,
Tunda kuna ta mulkin mu ba ku kula da mu
Don Allah Buhari mu zo ka fitarda mu
Yau kai ne muke so a nan Nijeriya
Y/Amshi: Yau Nijeriya riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari kai muke so Nijeriya
Jagora: Yau Nijeriya riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari kai muke so Nijeriya
Y/Amshi: Yau Nijeriya riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari kai muke so Nijeriya
Jagora: Ni na sanka tun kana mulkin gaskiya
Kun ga alokacin Buhari bai danniya
Du ya kauda mai halin murɗiya
Sannu Buhari kai muke so Nieriya
Y/Amshi: Yau Nijeriya riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari kai muke so Nijeriya
Jagora: Sanda ya karɓi mulki Buhari nan ƙasat
Dut ya tadda‘yan cin hanci ƙasat
Duk ya gyara komai da ke a cikin ƙasat
To, mai zai hana mu so ka a Nijeriya
Y/Amshi: Yau Najeriya riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari kai muke so Nijeriya
Jagora: Kunga a lokacin yacci bashin Ingila,
Har da Amerika masu halin baɗila
Har NF ya ce baya sojan matstsala
Mun gode Buhari mai kishin gaskiya
Y/Amshi: Yau Nijeriya riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari kai muke so Nijeriya
Jagora: Ya kyautar da ‘yan ta’adda da suke ƙasa
Masu kuɗi da ba su zakka sun barƙasa
Kunji a lokacin tattali ya bunƙasa
Har a ƙasarmu mun kasance ba ma tsiya
Y/Amshi: Yau Najeriya riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari kai muke so Najeriya
Jagora: Mu wallahi lokacin ba ma yin tsiya
Tun da akwai Buhari mai halin gaskiya
Mun ci abunci har da nama ba shan wuya
Kunji a lokacin Buhari mai gaskiya
Y/Amshi: Yau Najeriya riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari kai muke so Najeriya
Jagora: Yau Najeriya riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari kai muke so Najeriya
Y/Amshi: Yau Najeriya riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari kai muke so Najeriya
Jagora: Wancan lokacin farar hulla sun gudu
Domin sun yi ɓanna dole su zan gudu
Yanzu idan ka hau dole wancan na gudu
Zai tsere ya bar ƙasar don bai gaskiya
Y/Amshi: Yau Najeriya riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari kai muke so Najeriya
Jagora Ke lema baƙaddaga kin muna yau tsiya,
Ke lema baƙaddaga kin muna yau tsiya
Ba kya maganin ruwa duk mun sha wuya
Ke Lema fa mulkinki ba kya gaskiya
ANPP zo ki tallafi Najeriya
Y/Amshi: Yau Najeriya riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari kai muke so Najeriya
(Mai mai tawa)
Jagora: Wanda ya ja da kai Buhari zai sha wuya,
Domin Ka fi wane mai halin ‘yan giya
Mai fuska kamat ana murjin taliya
Kai hangoshi baya ƙaunan Najeriya
Y/Amshi: Yau Najeriya riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari kai muke so Najeriya
(Mai mai tawa)
Jagora: Lalle Daura kin yi ɗa wanda yake da kyau,
Wanda idan na ganshi ni bana zudda yawu
Ku jama’a ina kira sai ku riƙe da kyau
Sannu Buhari Shugaban ‘Yan Najeriya
Y/Amshi: Yau Najeriya riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari kai muke so Najeriya
(Mai mai tawa)
Jagora: Ka ji mutan Kano, Kaduna har Katsina
Ga na Jigawa, har Barno dut sun jinjina
Sakkwato, Kebbi Zamfara dut sun jinjina
Sun ce yanzu ne ƙasar za a yi gaskiya
Y/Amshi: Yau Najeriya riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari kai muke so Najeriya
Jagora: Yobe da Bauci har da Gombe sun Sallama
Har Adamawa, ‘yan Taraba ba tantama
Su Beniwe, Pilatu suna yin Sallama
Sun ce sai Buhari mai mulkin gaskiya
Y/Amshi: Yau Nijeriya riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari kai muke so Nijeriya
(Mai mai tawa)
Jagora: Na je Naija, Kogi, Kwara sun Sallama
Sun ce sai dai kai Buhari sai Lalama
Su ‘yan Lafiya batunsu ba tantama,
Za su bi Shugaba Buharin Nijeriya
Y/Amshi: Yau Nijeriya riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari kai muke so Nijeriya
Jagora: Har na tsallaka a Lagos domin na ji
Sun ce ba su bin wanda bai yin agaji
Na ji suna Oshe Buhari mai agaji
Sarewa ka zo ka karɓe Nijeriya
Y/Amshi: Yau Nijeriya riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari kai muke so Nijeriya
Jagora: Oyo, Oshun da can Ondo su ma sun faɗa
Har Ogun da naz zaka dut sun daɗaɗa
Dut sun ce Buhari shi baya tambaɗa
Shi ne za su zaɓa a nan Nijeriya
Y/Amshi: Yau Nijeriya riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari kai muke so Nijeriya
Jagora: Har Enugu da Imo su ma sun ambata
Kun ji Anambara da su za a karon batta
Sun ce za su yi Buhari don cancanta
Sannu Buhari Shugaban ‘yan Nijeriya
Y/Amshi: Yau Nijeriya riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari kai muke so Nijeriya
Jagora: Kunji ƙasarmu ta haɗe sai mai gaskiya
Mun haɗe kai ƙasarmu duk Nijeriya
Hausawa, Ibo da Yarbawa mu ɗaya
Mun ce sai Buharinmu duka bai ɗaya
Y/Amshi: Yau Nijeriya riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari kai muke so Nijeriya
(Mai mai tawa)
Jagora: PTF da kar rinka ai mu mun gani
Kai aiki da gaskiya han ni nagani
Assibitinmu ko ina mu mun gani
Hanyoyinmu sun yi kyau duk Nijeriya
Y/Amshi: Yau Nijeriya riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari kai muke so Nijeriya
Jagora: Yau Nijeriya riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari kai muke so Nijeriya
Y/Amshi: Yau Nijeriya riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari kai muke so Nijeriya
Jagora: Yau Nijeriya riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari kai muke so Nijeriya
Y/Amshi: Yau Nijeriya riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari kai muke so Nijeriya
Jagora: Don haka zo ka jamu don kai ne jagaba
Mu a ƙasarmu kai mu ke so yau shugaba
In ka riƙe Buhari mu ba ma fargaba
Zo ka riƙemu gar mu zauce daga gaskiya
Y/Amshi: Yau Nijeriya riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari kai muke so Nijeriya
Jagora: Ga zakaran da Rabbana Sarki yan nufa
Dole a ƙyale maigida ko ko a rankwafa
Don haka gar ku ja da shi balle ku zurfafa
Yau Allah yana a bayan mai gaskiya
Y/Amshi: Yau Nijeriya riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari kai muke so Nijeriya
(Mai-maitawa)
Jagora: Zan yi kiranku Ribas Fatakol da ‘yan uwa,
Gar ku bari a cuceku da tsanin rantsuwa
Dan na Tabbata ada ba kuda damuwa
Yanzu kuma ga Buhari shi ne bai danniya
Y/Amshi: Yau Nijeriya riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari kai muke so Nijeriya
Jagora: Sannu fiya-fiya da baka yin murɗiya
Zo ka kawad da Tanko mai fuskar saniya
Har da na Baba Lola mai halin ‘yan giya
Wanda suke da ɓata tsarin Nijeriya
Y/Amshi: Yau Nijeriya riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari kai muke so Nijeriya
(Mai-Maitawa)
Jagora: Kun ga halinsu ya samu mun koma bara
Don haka nik kiram mutane kui hattara
Kan zancen da nai wadda bana ƙirƙira
Sai mu zage mu zaɓi mai gaskiya
Y/Amshi: Yau Nijeriya riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari kai muke so Nijeriya.
Jagora: Da a ƙasarmu ba yinwa in kun tuna
Sai ku tuna abinci da gashi a ko’ina
Babu faɗa a lokacin in har kun tuna
Yanzu idan ka gammu duk mun sha wuya
Y/Amshi: Yau Nijeriya riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari kai muke so Nijeriya
(Mai-maitawa)
Jagora: Ku da ke ta sukar Buhari uban ƙasa
Ku ne kun ka kwashe fetur da kuɗin ƙasa
Don tsabar rashin mutuncinku cikin ƙasa
Har ma dukiyar marayu kun murɗiya

Jagora: Allah wadaranku masu halin Salmariya
Wannan ɗan Baƙin da ƙira ta ‘yan giya
Tun da ya hawo ya ke halin danniya
Mugun in ka gan shi kasan bai gaskiya
Y/Amshi: Yau Nijeriya riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari kai muke so Nijeriya
(Mai-maitawa)
Jagora: Yau Nijeriya riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari kai muke so Nijeriya
Y/Amshi: Yau Nijeriya riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari kai muke so Nijeriya
(Mai-maitawa)
Jagora: Kun cucemu da da yanzu mun ankare
Kar ku sake ku zo wurinmu bama tare
Don na san da kai na yamma mai halin kare
Mun riƙe mu Buhari shi ne maigaskiya
Y/Amshi: Yau Nijeriya riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari kai muke so Nijeriya
Jagora: Ka zama Jinjirin wata kai ne ake jira
Rana ta fito ta riga ta gagara
Dutse ka wuce bugu koko tokara
Har mai gatari Muhammad zai Juriya
Y/Amshi: Yau Nijeriya riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari kai muke so Nijeriya
Jagora: Ka ji wada fa Nas, yana sonka da shugaba
Mai Katsina Kabir yana sonka da shugaba
Har da na Daura Bashari shi ma ya yaba
Sun ce zo ka yi ka gyara shirin gaskiya
Y/Amshi: Yau Nijeriya riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari kai muke so Nijeriya
Jagora: Ado Bayero dole mulkin ‘yan Kano,
Yace kai suke buƙata Faɗin Kano
Ka zama ɗa dake da daɗin ɗan ɗano
Sannu Buhari Shugaban ‘yan Nijeriya
Y/Amshi: Yau Nijeriya riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari kai muke so Nijeriya
Jagora: Rabi’u Dan Tudun Garu shi ma ya yaba
Abdullahi Gwarzo wannan bai fargaba
Har da litil Aminu har shi ma ya yaba
Sun ce za su bika don tsarin gaskiya
Y/Amshi: Yau Nijeriya riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari kai muke so Nijeriya
Jagora: Ka ga Yarima can Zamfara shi ya yaba
Ka nga Yariman Zamfara shi ya yaba
Har da Bukar Abba Yobe shi ma ya yaba
Sun ce zo ka ceci Nijeriya
Y/Amshi: Yau Nijeriya riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari kai muke so Nijeriya
Jagora: Sannu Kabiru Umar Ciyaman APP Ka riƙe Gaskiya
Sannu Kabiru Umar Ciyaman APP
In a riƙe da ƙarhi a yau kai ne ka ci
Alhaji Sa’idu Ɗan Basawa kai tallafi
Don na san kana da kishin Gaskiya
Y/Amshi: Yau Nijeriya riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari kai muke so Nijeriya
Jagora: Mamman Daura ya faɗi kai ne shugaba
Har Muntari Zango yanace kai ne shugaba
Har da Lawali Bawa da ba ya yin gaba
Har da Minista Sani Mai kishin Gaskiya
Y/Amshi: Yau Nijeriya riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari kai muke so Nijeriya
Jagora; Sannu Iya bayis mashal Muktar Xan’ uwa
Abdurrahman Xan malan garkuwa
Har Muntari Shehu koko na
faskari,
Duk sun ce zo ka tallafi
Najeriya.
‘Y/Amshi Yau Najeriya riqo sai mai gaskiya
Sannu Buhari kai muke so
Najeriya.
Jagora: Ni zan dakata a nan sai kuma nan gaba
Dan Waƙa a kan Buhari ban
fargaba
Ni ne Yala na Shirya Waƙar ta Shugaba
Ni ne ɗan Hayin Banki mai son gaskiya
Sannu Buhari kai nike so Najeriya
Jagora: Yau Najeriya riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari kai muke so Najeriya
Y/Amshi: Yau Najeriya riƙo sai mai gaskiya
Sannu Buhari kai muke so Najeriya
(Mai-maitawa)
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.