Ticker

6/recent/ticker-posts

Wata Wakar: Mudassiru Kasim Kano mai suna “Ga Buhari da Osimbajo”

WATA WAƘAR: MUDASSIRƘASIM KANO MAI SUNA “GA BUHARI DA OSIMBAJO”

J- Ga Buhari da Baba Osibanjo

A- Da Buhari da Baba Osibanjo

 

J- Mun gamsu da Jagorancinku

Mun daina biye wa Oba Ojo

A- Da Buhari da Baba Osinbajo

 

J- Mun san gadon Hajja sai Fanna

Wani sanyin sai rigar gwanjo

A- Da Buhari da Baba Osinbajo

 

J- Da Baba Shugaba lafiya ta tafi

Sai mun daina yin ragwamar gwanjo

A- Da Buhari da Baba Osinbajo

 

J- Masu kashe Najeriya za su kau

Ko sun ƙi ko sun tutturjo

A- Da Buhari da Baba Osinbajo

 

J- Allah in yana sonka da alhairi

Zai yi ma kai da gidan Ojo

A- Da Buhari da Baba Osinbajo

 

J- Wanda yarriƙe son Manzon Allah

Ba’a rammai ko an tuttuji

A- Da Buhari da Baba Osinbajo

 

J- Tutul mulku mun riƙi alhairi

A zaɓen Buhari Osinbajo

A- Da Buhari da Baba Osinbajo

 

J- Bari in gaida ƙusoshin tahiyar

Babanmu Buhari da Osinbajo

A- Da Buhari da Baba Osinbajo

 

J- Wal tu ten D.G Baffa Bici

Ya ce mui Buhari da Osinbajo

A- Da Buhari da Baba Osinbajo

 

J- Wazirin Hausa Musa Gobir

Ya ce mui Buhari da Osinbajo

A- Da Buhari da Baba Osinbajo

J- Mama Fes Ladi A’isha Buhari

Ta ce mui Buhari Osinbajo

A- Da Buhari da Baba Osinbajo

 

J- Mama Hajjo ta Mama A’isha

Ta ce mui yi Buhari Osinbajo

A- Da Buhari da Baba Osinbajo

 

J- Hadda Oshi mole ya ce

Mui yi Buhari da Osinbajo

A- Da Buhari da Baba Osinbajo

 

J- Yau Iyafot na Abuja an gama

A zamanin Buhari Osinbajo

A- Da Buhari da Baba Osinbajo

 

J- An gamata fatakwal

Saura Kano da Lagos

Garin su Osinbajo

A- Da Buhari da Baba Osinbajo

 

J- Noma a ƙasa ya bunƙasa

Zamanin Buhari Osinbajo

A- Da Buhari da Baba Osinbajo

 

J- Yau a duniya mu ne na biyu

Ba ma cin Shinkahwa gwarjo

A- Da Buhari da Baba Osinbajo

 

J- Da ko mu ne bolar shinkafa

Ko ta ina za a tut tusho

A- Da Buhari da Baba Osinbajo

 

J- Makamai ko kullun kamawa ake yi

Ko ta ina in halallaujo

A- Da Buhari da Baba Osinbajo

 

J- Kamal Hamid yana kare

Mutuncin Babanmu Buhari Osinbajo

A- Da Buhari da Baba Osinbajo

 

J- Masu sace daloli EFCC

Naiwa gidajen su gwanjo

A- Da Buhari da Baba Osinbajo

 

J- Mun ga dama da mai na ruwa

Lantarki zamanin Buhari Osinbajo

A- Da Buhari da Baba Osinbajo

 

J- Baba zunge da Mambila anyi

Zamanin Buhari Osinbanjo

A- Da Buhari da Baba Osinbajo

 

J- Masu zuba hannun Jari

Duka sun yarje ma Buhari Osinbanjo

A- Da Buhari da Baba Osinbajo

 

J- Da sun gudu zamanin Ojo

A- Da Buhari da Baba Osinbajo

 

J- Ga Sha’aban na Baba Osinbajo

A- Da Buhari da Baba Osinbajo

 

J- Baba Bici ya ce waƙe

Irin na Buhari da Baba Osinbajo

A- Da Buhari da Baba Osinbajo

 

J- Mama Shatu mai dukku na Faɗa

Ta ce mui yi Buhari da Baba Osinbajo

A- Da Buhari da Baba Osinbajo

 

J- Rarara Jami’ar Waƙa

Yace mui yi Buhari da Osinbajo

A- Da Buhari da Baba Osinbajo

 

J- Yayale Mai lojikal Waƙa

Ya ce mui yi Buhari Osinbajo

A- Da Buhari da Baba Osinbajo

 

J- Kamilu Koko mai sansitif Waƙa

Ya ce mui Buhari Osinbajo

A- Da Buhari da Baba Osinbajo

 

J- Horet mai hairakial Waƙa

Ya ce mui yi Buhari Osinbajo

A- Da Buhari da Baba Osinbajo

 

J- Mudassir mai gwayas Waƙa

Ya ce mui Buhari Osinbajo

A- Da Buhari da Baba Osinbajo

 

J- Alfa zaji ma na Buhari Osinbajo

A- Da Buhari da Baba Osinbajo

 

J- Alkanawui na Buhari Osinbajo

A- Da Buhari da Baba Osinbajo

 

J- Baban Cinedu ma na Buhari Osinbajo

A- Da Buhari da Baba Osinbajo

 

J- Da Buhari da Baba Osinbajo

A- Da Buhari da Baba Osinbajo x 3

Post a Comment

0 Comments