Ticker

6/recent/ticker-posts

Wakar Guguwar Sauyi Ta Aminu Abubakar Ladan

AMINU ABUBAKAR LADAN – ALAN WAƘA: WAƘA ƊAYA – “GUGUWAR SAUYI”

Jagora: In ya Allah kaɗa guguwar Sauyi

Buhari Janar ya karɓi ƙasaaa

Jagora: Ku aje kube sauyi ya zo

Ku aje kube sauyi ya zo

Ku aje kube sauyi ya zo

Ku aje kube sauyi ya zo

 

Masu Sanduna sauyi ya zo

Mai barandami sauyi yazo

Bana ƙuria fa za ta aje manufa

Bana ƙuri’a fa za ta aje manufa

 

Sai godiya hamdullahi

Allah alhamdullahi

Allah alhamdullahi

Allah alhamdullahi

 

Amshi: Baƙar malfa, baƙar Jarfa

Mai shanye jinin jikin talaka

Allah kaɗa guguwar sauyi

Buhari Janar Karab da gari

 

Amshi: Baƙar malfa, baƙar Jarfa

Mai shanye jinin jikin talaka

Allah kaɗa guguwar sauyi

Buhari Janar Karab da gari

 

Jagora: Baƙar malfa, baƙar Jarfa

Mai shanye jinin jikin talaka

Allah kaɗa guguwar sauyi

Buhari Janar Karab da gari

 

Jagora: Ya karɓi gari

Mutum na gari

Mu zamna gari yah!

Mu bar sukari, yaah!

Mu samu gari, yaah!

Sahibul Sabari yaah!

Ɗa nagari yaah!

Maras haɗari

Amshi: Baƙar malfa, baƙar Jarfa

Mai shanye jinin jikin talaka

Allah kaɗa guguwar sauyi

Buhari Janar Karab da gari

 

 

Jagora: Subuhanaka Rabbu mun gode

Mun jaddada godiya gunka

Baƙar malfaah

 

Amshi: Baƙar malfa, baƙar Jarfa

Mai shanye jinin jikin talaka

Allah kaɗa guguwar sauyi

Buhari Janar Karab da gari

 

Jagora: Allah alhamdulillahi

Gwanin Sarki abun bauta

Buwayi

 

Amshi Baƙar malfa, baƙar Jarfa

Mai shanye jinin jikin talaka

Jagora: Duk yadda ka so da bayinka

Ba mai tuhuma abin ƙinka

Amshi Baƙar malfa, baƙar Jarfa

Mai shanye jinin jikin talaka

Jagora: Muna tuba da aibunmu

Ka yafe mana laifukka

Amshi: Mai shanye jinin jikin talaka

 

Jagora: Allahu ka dubi bayinka

An tashi hana mu Bautarka

Amshi Baƙar malfa, baƙar Jarfa

Mai shanye jinin jikin talaka

Allah kaɗa guguwar sauyi

Buhari Janar Karab da gari

 

Jagora: Masifu sun buwaye mu

Ka saukar mana jinƙanka

Amshi: Baƙar malfa, baƙar jarfa

 

Jagora: Baƙin mulki na zalunci

Ake a ƙasarmu ba shakka

Amshi: Mai shanye jinin jikin talaka

 

Jagora: Baƙar Jam’iyya mai malfa

Tana son kada bayinka

Amshi: Baƙar malfa, bakar Jarfa

 

Jagora: Muƙami in da adalci

Yana yiwuwa da yardarka

Amshi: Mai shanye jinin jikin talaka

 

Jagora: A kan ce ko da kafirci

Kana yarda ya ɗaukaka

 

Amshi Baƙar malfa, baƙar Jarfa

Mai shanye jinin jikin talaka

Allah kaɗa guguwar sauyi

Buhari Janar Karab da gari

 

Jagora: Muƙami in da zalunci

Kana rusa shi ba shakka

Amshi: Baƙar malfa, baƙar Jarfa

 

Jagora: Akan ce ko da Musulunci

Kana hana yay yi albarka

Amshi: Mai shanye jinin jikin talaka

 

Jagora: Muƙamin nan da zalunci

Da kafurci na saɓon ka

Amshi: Baƙar malfa, Bakar Jarfa

 

Jagora: Muƙamun nan da zub da jini

Ana halakkar da bayinka

Amshi: Mai shanye jinin jikin talaka

 

Jagora: Ƙanilanci, dalilanci

Da banbanci ake shuka

Amshi: Baƙar malfa, baƙar Jarfa

Mai shanye jinin jikin talaka

Allah kaɗa guguwar sauyi

Buhari Janar Karab da gari

 

Jagora: Arewa ƙasarmu ya Allah

Ta zama kufai kamar bukka

Ana ta bugu a kan taiki

Shi kau jaki yana hauka

 

Jagora: Ana ta kisa kamar fari

Ba wanda ake ganin shakka

Dattawan ‘yan arewarmu

Ciki ba wanda ke shakka

 

Jagora: Ana karkashe maluma namu

Sarakai ma ana ɗauka

Amshi : Baƙar malfa, baƙar Jarfa

Mai shanye jinin jikin talaka

Allah kaɗa guguwar sauyi

Buhari Janar Karab da gari

 

Jagora: Siyasar yau da cin zarafi

Da muzanci da cin fuska

Da zaran an ji sunanka

Musulmi ka shige sarƙa

 

Jagora: A yau taken musulminmu

Ta’addanci yake ɗauka

Rufewa ta zukatanmu

Ta sa ba wanda ke shakka

 

Jagora: A sa sawu a take mu

Baubayi babu mai shakka

Amshi: Baƙar malfa, baƙar Jarfa

Mai shanye jinin jikin talaka

Allah kaɗa guguwar sauyi

Buhari Janar Karab da gari

Jagora: A sa riga ta Islamu

A yo wauta ga zantarka

Sannan fa a jingina kanmu

Wakilai babu mai tanka

 

Jagora: Mu yi gurin mutuwa bayi

Idan mun take alhaƙƙa

Tutar atabau ba za mu yi

Saboda abun da mun shuka

Mu bai Allah buƙatarmu

Mafi girma da ɗaukaka

 

Amshi: Baƙar malfa, baƙar Jarfa

Mai shanye jinin jikin talaka

Allah kaɗa guguwar sauyi

Buhari Janar Karab da gari

 

Jagora: Mun dogara yau da wayonmu

A toka yau muke shuka

Amshi: Baƙar malfa, Baƙar jarfa

 

Jagora: Ba a ma ai fara komai ba

Sai ka gyara bautarka

Amshi: Mai shanye jinin jikin talaka

 

Jagora: Mu dubi Arewa Lardinmu

Irin gawa muke shuka

Amshi: Baƙar malfa, baƙar jarfa

 

Jagora: Abin kaico da ‘ya’yanmu

Ake markar kisan hauka

 

Amshi: Mai shanye jinin jikin Talaka

 

Jagora: Mu yunƙura gyara kayanmu

Ku zaɓi Buhari yai mulka

Amshi Baƙar malfa, baƙar Jarfa

Mai shanye jinin jikin talaka

Allah kaɗa guguwar sauyi

Buhari Janar Karab da gari

 

Jagora: Arewar babu mai twari

Suna tsoron gidan sarƙa

Amshi: Baƙar malfa, baƙar Jarfa

 

Jagora: Sun zamanto Damisar faɗi

Har su yayyaga hotonka

Kyanwar Lami cikin ɗaki

Ba cizo babu bautarka

 

Amshi: Baƙar malfa, baƙar jarfa

 

Jagora: Ruɓuɓɓu a cikin namu

Suna kuma ci da bautarka

 

Amshi: Mai shanye jinin jikin talaka

 

Jagora: Suna inuwa ta addini

Suna cutar da bayinka

Amshi Baƙar malfa, baƙar Jarfa

Mai shanye jinin jikin talaka

Allah kaɗa guguwar sauyi

Buhari Janar Karab da gari

 

Jagora: Suna miƙa wuyayarmu

Ga mai ƙin a yi bautarka

Amshi: Bakar malfa, bakar jarfa

 

Jagora: Kamar dabba suke janmu

Da zalunci muna kuka

Amshi: Mai shanye jinin jikin talaka

Jagora An kone wajen karatunmu

Ana kishin mu ɗaukaka

 

Amshi: Baƙar malfa, baƙar jarfa

Jagora: An ƙone kasuwancinmu

A yau baƙi suna shakka

Amshi: Mai shanye jinin jikin talaka

 

Jagora: Ba mai sha’awar ya zo gunmu

Da hulɗar kasuwa barka

Amshi: Baƙar malfa, baƙar Jarfa

Mai shanye jinin jikin talaka

Allah kaɗa guguwar sauyi

Buhari Janar Karab da gari

 

Jagora An zaɓu ruba-ruba namu

Da sunan wai waƙiltarka

A ba su kuɗi su miƙa mu

Hannu kwarya, hannu baka

Tunanensu iyalansu su tara

Abin da ba tamka

Suna tsoron talaucewa

Suna shakkar zamon talaka

Su zaɓi zama talakawa

A ranar komuwa gunka

 

Amshi Baƙar malfa, baƙar Jarfa

Mai shanye jinin jikin talaka

Allah kaɗa guguwar sauyi

Buhari Janar Karab da gari

 

Jagora: Sun maishemu kamar kaji

A ba ka hatsi kasa bakka

Da an buga tambarin zaɓe

Mutanen babu tsoron ka

Su sa riga su sa hula

Su ɗau hoto suna baka.

Su ce ma je a Mammanna

A ɗau na abinci a baka

Da sun hau karagar mulki

Da ƙyar su gane sunanka

 

Amshi Baƙar malfa, baƙar Jarfa

Mai shanye jinin jikin talaka

Allah kaɗa guguwar sauyi

Buhari Janar Karab da gari

Jagora: Duk wanda ya hau kujerar nan

Abin ƙinsa a ce sauka

Ya hau ɗamara ta shiryawa

Da zango ya yi zai sauka

A hau fasali da tsarawa

Ana son sabuwar doka

Ana wai za a sabonta

A yo doka da ba ƙinka

Kun daina gudanuwar mulki

Su samo sabuwar doka

 

Amshi Baƙar malfa, baƙar Jarfa

Mai shanye jinin jikin talaka

Allah kaɗa guguwar sauyi

Buhari Janar Karab da gari

 

Jagora: Su daidaita da son ransu

Kawai don kar a ce sauka

Amsa: Baƙar malfa, baƙar jarfa

 

Jagora: Cikin dimokuraɗɗiya ake son

Rai ake hauka

Amshi: Mai shanye jinin jikin talaka

 

Jagora: A mulkin nan na al’umma

Na zaɓen ra’ayin sonka

Y/Amshi Baƙar malfa, baƙar Jarfa

Mai shanye jinin jikin talaka

Allah kaɗa guguwar sauyi

Buhari Janar Karab da gari

 

Jagora: Mulki daga al’umma ake

cikin zaɓe na son ranka

Amshi: Mai shanye jinin jikin talaka

 

Jagora: Ana yi don mutane ne

Misalin ba ka ‘yancinka

Amshi: Baƙar malfa, baƙar jarfa

Jagora: Amma kuma ko mulukiya

Ba ta yi kama haka hauka

Y/Amshi Baƙar malfa, baƙar Jarfa

Mai shanye jinin jikin talaka

Allah kaɗa guguwar sauyi

Buhari Janar Karab da gari

 

Jagora: Ko tsarin gurguzu Malam

Ya kai haka ba a tauye ka

Amshi: Mai shanye jinin jikin talaka

 

Jagora: Nm Jari – hujja ake yi muna

Muƙami na saman doka

Amsa: Baƙar malfa, baƙar jarfa

 

Jagora: Da masu kuɗi da mai mulki

Sai yadda su kai a kan doka

Amshi: Mai shanye jinin jikin talaka

 

Jagora: An yunƙura mai da mu bayi

Kana bauta da ‘yancinka

Amshi: Baƙar malfa, baƙar jarfa.

 

Jagora: Hm ‘yanci na faɗi da bakinka

A yau in ka yi kai kuka

Amshi: Baƙar malfa, baƙar jarfa

 

Jagora: Sai kai sa’a a ƙyale ka

Da nunfashi a ɗaure ka

Amshi: Mai shanye jinin jikin talaka

 

Jagora: Idan suka so su bautar ka

Ka rayu kamar taɓin hauka

Amshi: Baƙar malfa, baƙar hauka

Jagora: Koko ɗauri na talala

Kana raye kamar baka

Amshi: Mai shanye jinin jikin talaka

Jagora: Ana raba hankula namu

Kamar ƙwallo a taka ka

Amshi: Baƙar malfa, baƙar Jarfa

Mai shanye jinin jikin talaka

Allah kaɗa guguwar sauyi

Buhari Janar Karab da gari

Jagora: Ya taka sai ya ba wancan

Da ya taka ya miƙa ka

Amshi : Baƙar malfa, baƙar jarfa

Jagora: Suna ruɗin tunanenmu

Suna hila da ƙuri’arka

Amshi: Mai shanye jinin jikin talaka

Jagora: Suna ƙarya ta alkawali

Suna raba kawunan talaka

Amshi: Baƙar malfa, baƙar jarfa

Jagora: A yau kowa ya ɗau wuifon

Makamin ƙuri’a taka

Amshi: Mai shanye jinin jikin talaka

Jagora: Mu zaɓi Buhari al’umma

Ya gyara ƙasarmu ba shakka

Amshi: Baƙar malfa, baƙar jarfa

Mai shanye jinin jikin talaka

Jagora: Jininmu da martaba tamu

Ya zam fansa a mulkinka

Amshi: Mai shanye jinin jikin talaka

Jagira: A yau kan mage ya waye

Talaka ka san matakanka

Amshi: Mai shanye jinin jikin talaka

Jagora: Ka gane ƙuri’a taka

Muhallinta muƙaminka

Amshi: Baƙar malfa, baƙar jarfa

Jagora: Makamin yanke zalunci

Da duk mai kai wulayarka

Amshi: Mai shanye jinin jikin talaka

Jagora: Wakilai har da dattijai

Ku zaɓo masu ƙaunarku

Amsa: Baƙar malfa, baƙar jarfa

Jagora: Matakin kansila har kan

President zaɓu mai sonka

Amsa: Baƙar malfa, baƙar jarfa

Jagora: Ku lura da kyau talakawa

Kuna zangon tsaka-tsakka

Amshi: Mai shanye jinin jikin talaka

Jagora: Muna dama ta ƙarshe ne

Gaba ɗai ba ragin ɗakka

Amshi: Baƙar malfa, Dokar Jarfa

Jagora: ƙwayaye ƙwarkwata tamu

An yo zaɓe a fanshe ka

Amshi: Mai shanye jinin jikin talaka

Jagora: Da kunne ya ji mun tsira

Da zalunci na yan iska

Amshi: Baƙar malfa, baƙar jarfa

Jagora: Ka lura janar cikin tafiya

Akwai kaska da ke bin ka

Amshi: Baƙar malfa, baƙar jarfa

Jagora: Waɗannan masu fifiko

Su raɓe a inuwarka

Amshi: Mai shanye jinin jikin talaka

Jagora: Waɗansun su mazalunta

Suna tafiya a ƙuri’arka

Amshi: Baƙar malfa, baƙar jarfa

 

Jagora: Su sam dama su yo mulki

Su cuci talakawanka

 

Amshi: Mai shanye jinin jikin talaka

 

Jagora: Allahu ka yo muna maganin

 Katsittsince ɗiyan iska

Amshi: Baƙar malfa, baƙar jarfa

 

Jagora: Ka yi mana kariya Allah

Da dangina masoyanka

Masoya masu jin waƙa

Su sa lura da sambarka

Allah ga janarar namu

Ka karɓi nufinsa bawanka

Kayo sanadi na cetonmu

Ta hanyar ba shi mulkinka

Ya share muna kukanmu

Mu bar ƙangin jinin kaska

 

Amshi Baƙar malfa, baƙar Jarfa

Mai shanye jinin jikin talaka

Allah kaɗa guguwar sauyi

Buhari Janar Karab da gari

Jagora: Allah ka amsa roƙonmu

Muna kuka da roƙonka

Masifu sun buwaye mu

Muna kwaɗayi na tanyonka

Anan zan sa ɗigon aya

a kan nusar da bayinka

Ka sa waƙar da nittsara

Ta zan ƙaimi ga bayinka

Ala mai waƙe al’umma

Masoyina Sahibi naka

Amshi Baƙar malfa, baƙar Jarfa

Mai shanye jinin jikin talaka

Allah kaɗa guguwar sauyi

Buhari Janar Karab da gari

Jagora:

Amshi Baƙar malfa, baƙar Jarfa

Mai shanye jinin jikin talaka

Allah kaɗa guguwar sauyi

Buhari Janar Karab da gari

Jagora: Ya karɓi gari

Mutum nagari

Mu zam nagari

Mu bar sukari

Mu zam nagari

Abin fahari

Sahibul Sabari

Da na gari

Post a Comment

0 Comments