MURTALA MAMSA JOS - WAƘAR APC I
Jagora: Da na je taron
jari,
Na gano abin mamaki al’umma
Amshi: mu ji mansan waka,
Wai dawa da wa kaje,
Ka gano kafada mana
Jagora: janar Buhari ya zo
taro
Bola tunubu ya zo taro
Amshi: To
Jagora: Asuwaji ya zo taro
Almakura ya zo taro
Amshi: Eye
Jagora: Okorocha ya zo
taro
El-rufa’i ya zo taro
Amshi: To
Jagora: Adam Oshumole ya
zo taro
Baba tunde ya zo taro
Amshi: Eye
Jagora: Fashola yazo taro
Eke odoma yazo taro
Amshi: To
Jagora: Christ ngege yazo
taro
Ogunnaye yazo taro
Amshi: Eye
Jagora: Obita yazo taro
Jolabi ya zo taro
Amshi: To
Jagora: Ane okonko yazo
taro
Dom okibe yazo taro
Amshi: Eye
Jagora: Abdulsalami yazo
taro
Audu obe yazo taro
Amshi: Too
Jagora: John ogege yazo
taro
Kasiru gaya yazo taro
Amshi: Eye
Jagora: Shekarau yazo taro
A halliru yazo taro
Amshi: Ehe
Jagora: Bafarawa yazo taro
Garda gadi yazo taro
Amshi: Too
Jagora: Tod abiti yazo
taro
BubaGaladima gun taro
Amshi: Eye
Jagora: Enginiya bajoga a
taro
Hadi sirika yazo taro
Amshi: Too
Jagora: Ebike Amos yazo taro
Kayode Fayomi gun taro
Amshi: Ehe
Jagora: Gwamna Rufa’i yazo gun taro
Ibrahim gaidam gun taro
Amshi: Uhm
Jagora: Kashim shattima
yazo taro
Tunde bakari yazo taro
Amshi: Eye
Jagora: Sun taru ne su
ceto ‘yan Najeriya
Sabuwar jam’iyya ,
APC mai ceton Najeriya
Kowa ya bi.
Amshi: Sabuwar jam’iyya
APC
Gaskiya ta zo
Jagora: Ku zo mu kama
gaskiya
Ta zo Najeriya
Amshi: Gaskiya ta zo
Mun karɓe ta
Mun riƙa hannu biyu ‘yan Najeriya,
da hannu bi-biyu.
Jagora: Mun karɓeta hannuwa bi-biyu
‘Yan Najeriya, kowa ya bi
Amshi: Sabuwa ta zo,
APCnmu mun amince
‘Yan Najeriya,
Sabuwa tazo
Jagora: Sabuwa ta zo
Mun karɓeta mun amince
‘Yan Najeriya kowa ya bi
Amshi: Gaskiya ta zo mun
karɓeta
Ƙauyuka,
birni Najeriya, Kowa ya bi
Jagora: Mun amince ‘yan
Najeriya
Mun karɓe ta hannu bi-biyu
Amshi: Gaskiya ta zo, mun
karɓe ta
Mun amince ‘yan Najeriya
Kowa ya bi
Jagora: Ubangiji Allah
Sarki taimake ni
Yau na ɗauko baituka
Wajibi ne Sarki yau ya
sami
Ƙwarkwara
ya yi sa-ɗaka
Taimakamini Sarki Allah
Tabara wahid kai mani ɗaukaka
Zan yi waƙar jam’iyyar nan
Da za ta ceto ‘yan Najeriya
Amshi: Sabuwa ta zo APCnmu
Mun amince ‘yan Najeriya
Jagora; Na kira Allah
sarkin nan
Da yai saman nan har da qasan bakwai
Na sako Manzon Allah
Xan Amina wanda ya bi ka saman bakwai
Kwanakin nan Allah ne
Duk ya yi su in ka qirga su bakwai
Taimakonka muke neman Juljalalu
Talakawan duk Najeriya.
Amshi; Sabuwa ta zo
APCnmu mun amince ‘yan Najeriya
Jagora‘Yan’uwa ‘yan Najeriya muna ta
bacci
Ta sako gangara
Riƙon amana ba ɗan kishiya
Wanda yai haka sai ya
kassara
Maƙiyan
talakawa sun take mana
Iska sai mu yi hattara
Ba rashin kunya ba manyan
kasarmu
ba sa aikin gaskiya
Amshi: Sabuwar jam’iyya
APCnmu
Mun amince ‘yan Najeriya
Jagora: Tun tana ƙarama Najeriya
Tarawa ke yi mata hassada
Ta zamo ingarma ta girma
Sannu dutse gatan ɗanbura
Sun buga sun bar ta tana
nan
A yanzu har sun gaji da
hassadar
Ta zamo kafuwar Allah
Rabbana yana kallon ku a
duniya
Amshi: Sabuwa ta zo APCnmu
Mun amince ‘yan Najeriya
Jagora: Babatu na zuga ba
Mai son karo ya zo
Ga rago a kara
Kaji giwa bukkan daji kin
wuce harbi
Koko tokara
Sannu maliya baki ƙafewa dukkan ruwa
A cikinki ya tattara
Jam’iyyar talakawa APC mun
amince ‘yan najeriya
Amshi: Sabuwa ta zo APCnmu
Mun amince ‘yan Najeriya
Jagora: Dole ne mai tarkon
tsuntsu ya kau da
Kai ya bi sa da lalama
In ya ci da zucci tsuntsu
ya gan shi
Tashi za sui sama
Dole ne in ya da maɗaci na je
In ɗauko mai ƙwaryar zuma
Jam’iyyar APC, Allah ya
bamu mui
Kishin Najeriya.
Amshi: Sabuwa ta zo APCnmu
Mun amince ‘yan Najeriya
Jagora: Sannu maliya ba ki
ƙafewa duk jama’a
Sun ɗiba sun bari
Shi manomi ƙauye shi za ya ba mu
Labarin ɓarnar biri
Wai ina sunan mugun da
yassai ashana
Yab baiwa biri
Mun shiga uku ‘yan
Najeriya ɗan Neja
Kai ka dafa mana taliya.
Amshi: Sabuwa ta zo APCnmu
Mun amince ‘yan Najeriya
Jagora: Duka jam’iyyun
Najeriya sun haɗa kai
Talakawa kun jiya
Tun da sun haɗa kai talakawa mu bi su
Kar mu yi tambaya
Kar mu yarda da duk wani
wanda za ya
Zo ya ce muna shi ne ɗan’iya
Sabuwar jam’iyyar ta zo
mubi ta
bai ɗaya ‘yan Najeriya.
Amshi: Sabuwa ta zo APCnmu
Mun amince ‘yan Najeriya
Jagora: Shi biki ka san
mai zuciya ake gaya ma
Ko ɗan zai zo maka
Ka kira mai naira wawa
idan ya zo
Naira zai sammaka
Kuma in ka karɓa bawa yake ganin ka
a kullum don haka
Kurciya kukanki jawabi
akwai cikinta
ga ‘yan Najeriya
Amshi: Sabuwa ta zo APCnmu
Mun amince ‘yan Najeriya
Jagora: Tafiyar yanci
talakawa mu kama APC Najeriya
‘yan amana sun haɗa kansu sun fito da
jam’iyya mai tarbiya
Kun ji wancan ma babban
cikinsu y ace da tasu bat a da tariya,
Su da kansu suke furucin
haka ba ta zuwa
na zauna lafiya.
Amshi: Sabuwa ta zo APCnmu
Mun amince ‘yan Najeriya
Jagora: Zan kira Manyan
Jam’iyyar na karrama su
na yo masu jinjina
Zan kira babban jirgi mai
riƙon amana
Sarkin dangana
Ga ni fa alaramma ba
kuskure idan na yi
Ku yi mana magana
Innallaha Ma’assabirina ya
fi son wannan
mai duniya.
Amshi: Sabuwa ta zo APCnmu
Mun amince ‘yan Najeriya
Jagora: Janar Buhari ikon
Allah ka zudda
Kwallakan Najeriya
Kun ci zaɓe an murɗe mana hayaniya
Za mui kai ka tsaya
Ka hana mu mu ɗau doka a hannu
Al’ummar Najeriya
Lokaci in ya yi uban
kuturu kaɗan ya yi
yai mana fariya.
Amshi: Sabuwa ta zo APCnmu
Mun amince ‘yan Najeriya
Jagora: Ɗan amana yau na zo gare ka ga shi zan
doka maka tambura
Ka riƙe Allah
Sarkin aiki El-Rufa’i
yau ka gagara
Maƙiyanka
suna ta fushi El-Rufa’i ka
sa duk sun tunzura
El-Rufa’i minista ne a
lokacin su wancan
Kai an gauraya.
Amshi: Sabuwa ta zo APCnmu
Mun amince ‘yan Najeriya
Jagora: Ka riga ka kai
sama duk maƙiyanka
Gwamna sun koma ƙasa
Ga shi kun yi sake ɗan zaki ya girma
dole ku dudduƙa masa
Tun da ya riƙe Allah ‘yan Jahar
Nasarawa suna gode masa
Tanko Almakura ‘yan Jahar
Nasarawa
mun zauna lafiya.
Amshi: Sabuwa ta zo APCnmu
Mun amince ‘yan Najeriya
Jagora: Yau Jahar Nasarawa
mun sami
Lafiya ga aiki kai mana
Kai kaɗai ne tilo gwamna a
jam’iyyar
Sarki mai dangana
Kafi mai allo da ƙafafunsa basu
mai rana sai jingina
Ba batun son kai na yi ba,
Nasarawa dole mu zauna
lafiya.
Amshi: Sabuwa ta zo APCnmu
Mun amince ‘yan Najeriya
Jagora: Kuma duk haɗamar mai handama
Wallahi bai iya ɗaukar duniya
Mai yawan bacci in ya sha hura ku
duba
kar ku yi tambaya
Wadda ya yi biyayya haƙƙin uwa, uba
ya zauna lafiya.
Amshi: Sabuwa ta zo APCnmu,
Mun amince ‘yan Najeriya.
Jagora: Yau ina Sardauna
Sir Ahmadu Bello
Gamji ka ji firimiya
Yau ina gwarzo Nnamdi
Azikiwe
duk sun bar duniya
Sir Abuabkar Tafawa Balewa
shi ma ya bad duniya
Mun yabawa Akintola ‘yan ƙasa
mu dudduba Najeriya.
Amshi: Sabuwa ta zo APCnmu
Mun amince ‘yan Najeriya
Jagora: Wai ina takwara
Janar Murtala Ramat ya bar duniya
Ba su Awolowo, Aminu Kano,
Bakin zuwo
Sun bar duniya
Da a ce mun kwaikwayi
tsarinsu da
Ƙasa ta
zauna lafiya
Dole zan koka Najeriya ƙasa ta gado
Ta hau kan ƙaya.
Amshi: Sabuwa ta zo APCnmu
Mun amince ‘yan Najeriya
Jagora: Zamfarawa
AbdulAziz Yari ya yi komai
Allah taya maka
Mai amana ne Ahmad Sani ɗan Yarima
Allah taya maka
Manya gatan wasa Sanata
Yarima mun ta yaba maka
Ka yi komai mun gode maka
Al’umma duk Najeriya
Amshi: Sabuwa ta zo APCnmu
Mun amince ‘yan Najeriya
Jagora: Kariga kai riba ka
samu duniya Saura ma lahira
Kui ta cizon yatsa ya sha
gabanku jikokin yan gambara
Tun da ka yi minista
birnin Abuja
Allah yai maka Sutura
El-Rufa’i ka taka
Je ko’ina muna bayanku da
gaskiya
Amshi: Sabuwa ta zo APCnmu
Mun amince ‘yan Najeriya
Jagora: Bazawara wa zai
mata lalle
Budurwa aka wa ba a daɗi
Sabuwar Jam’iyya tamu ce
ta kira kowa don sun faɗi
Manyanmu suna lasan zuma talakawa su ko sai maɗi
Taimaka mana APC zo ki karɓi mulkin ‘yan Najeriya
Amshi: Sabuwa ta zo APCnmu
Mun amince ‘yan Najeriya
Jagora: Tun da ka riƙe Allah mai gaskiya siyasa ya ce ba daɗi
In ka hau mulki ga shawara
janar
ɓarayi kai masu damƙar biri
In ka hau mulki na tabbata
masu saɓon ma su bari
Duk rashin kunyar marashi
kunya idan ka
hau mulki tilas zai sunkuya
Amshi: Sabuwa ta zo APCnmu
Mun amince ‘yan Najeriya
Jagora: Sanata Bola Ahmad
na Tinibu yau ku ne Najeriya
Baka tsoron wancan bakinsa
sai ka ce mashin ɗin taliya
Gaskiya daɗi sanata Asuwaju Ahmad ba
ya fariya
Duk rashin kunyar marar
kunya idan ya zo tilas zai sunkuya
Amshi: Sabuwa ta zo APCnmu
Mun amince ‘yan Najeriya
Jagora: Aniyar farko APC
ta ce karatu kyauta kun jiya
Ga garaɓasa ta zo sai mu zo mu
kama ‘yan Najeriya
Mai kamar zai je aka aika
don zuciyarmu ta zauna lafiya
Gaskiya ta zo al’umma
farin ciki duka ‘yan Najeriya
Amshi: Sabuwa ta zo APCnmu
Mun amince ‘yan Najeriya
Jagora: Wanda ya riƙe Allah Sarki ba ya shirka, baya tagaiyara
Tafiyar mesa bisa tsandari
ya yi tatata ko jangora
An yaba da haɗin jam’iyyun ƙasarmu don ceton Najeriya
Amshi: Sabuwa ta zo APCnmu
Mun amince ‘yan Najeriya
Jagora: Tattalin daɗi haka mai haƙuri yakan ɗau dutsi yai miya
Dole ne mai son Najeriya
ya ɗauki APC
Najeriya
Yan uba sun ɗau Najeriya ƙasarsu ce talakawa kun jiya
Ban da zalunci a ƙasar nan, manyan macuta ne Najeriya
Amshi: Sabuwa ta zo APCnmu
Mun amince ‘yan Najeriya
Jagora: Ba tsaro a ƙasar nan
ɗansanda
yana tsoron saka yuniform
Mun shiga uku ‘yan
Najeriya ga ƙasarmu tana fama daba
Wasu na hotel kwana bakwai
sukan yi
Kwanta katifa vitaform
Ya ki zo jam’iyyar APC ki
taimaka wa ‘yan Najeriya
Amshi: Sabuwa ta zo APCnmu
Mun amince ‘yan Najeriya
Jagora: Tambaya zan yo wa
ye za ya ba da amsar wannan tambaya
Tambayar biyu ce ku haɗa sai ku bani amsa in har
kun iya
Kun ga mulki Allah shi ne
ka bai wa wanda ya so ba tambaya
Kin riga-fata kun ce ƙaddara jarabta ‘yan Najeriya
Amshi: Sabuwa ta zo APCnmu
Mun amince ‘yan Najeriya
Jagora: Shimfiɗar fuska ai ta fi a shimfiɗa maka sabon darduma
Kun ga jam’iyyar nan ta zo
da gaskiya to sai mai azzama
Ko a tarihi an yo Adam ku
bincika mini sam ba Adama
Ƙirƙiren wani duk mai bincike
a rayuwa shirme ne fariya
Amshi: Sabuwa ta zo APCnmu
Mun amince ‘yan Najeriya
Jagora: Shi kiran Sallah
kurma ai ba zai ba donn bakin ba hikima
Rabbu ne ya hana masa in
wani ne da kurma asha rigima
Da makaho ga kurma sun haɗa kai wai za su yi rigima
Kai kake bai wa mara gata mai sama Allah ga
Najeriya
Amshi: Sabuwa ta zo APCnmu
Mun amince ‘yan Najeriya
Jagora: Sannu Maliya ba ki kafewa
duk jama’a sun ɗiba sun bari
Sannu baya goya marayu da
mai Uwar ma sam ba ka bari
Tafiyar nan tamu da nasara
da damina ne sai ga hadari
Tafiyar APC al’ummar ƙasarmu kowa sai yai lafiya
Amshi: Sabuwa ta zo APCnmu
Mun amince ‘yan Najeriya
Jagora: Sannu ƙangi wan ganga mai buga ka sai an nemi mai ciki
Jam’iyyar APC ke za ki mai
da sojojin nan bariki
Wanga mulkin soja suke yi koko farar hula
ke shamaki
Yan uwana ‘yan Najeriya
soja suna mulkin Najeriya
Amshi: Sabuwa ta zo APCnmu
Mun amince ‘yan Najeriya
Jagora: Mun ji komai mun
gano tsiyarku ‘yan ƙasa fifti-fifti suke
Su suna tatsar nonon, shi gwanin ƙaho suka ce mashi ya riƙe
Kun shiga uku yan Najeriya
shugaban na ƙasa ko ya yaƙe
Jam’iyya ta zo ta gamayya
ke za ki ƙwato ‘yan Najeriya
Amshi: Sabuwa ta zo APCnmu
Mun amince ‘yan Najeriya
Jagora: Mutuwa rigar kowa
ce da zan iya tau kam da na kwaɓe
Mutuwa yankan ƙauna ta wuce da gwarzo Chuba Okadibo
Da ruwa yashi ko ka dunƙule kasan hannu sai ya rabe
Jarqasa APC ta dunƙule rabewa babu daliliya
Amshi: Sabuwa ta zo APCnmu
Mun amince ‘yan Najeriya
Jagora: Ga shi taro yay
taro duniya gidan daɗi inji mai kwabo
Lahira ta ɗau baƙi maza
suna can chuba Okadibo
Da ana dawowa taron ga ‘yan uwa sai
kun ga Okadibo
‘Yan uwa APC ta zo ki zo
ki ceto ‘yan Najeriya
Amshi: Sabuwa ta zo APCnmu
Mun amince ‘yan Najeriya
Jagora: Sabuwa ta zo APC
mu mun amince ‘yan Najeriya
Zamfara ma ta bi,
Abdulaziz Yari yai komai kuma mun yaba
Fashola ya zo Jihar Lagos
ki taso ai tuni mun yaba
Jahar Ogun ta bi, Amos
Adekunle shi ma ya zo mun yaba
Jahar Oyo sun bi, Kayode
Fayomi shi ma ya zo mun yaba
Jahar Osun sun bi, Ra’uf
Aribe ya zo shi ma mun yaba
Edo ma ta zo, Adam
Ashomole shi ma ya zo mun yaba
Imo ma sun bi, Rochas
Okorocha Shi ma ya zo mun yaba
Yobe ma ta zo, Gaidam
Ibrahim ya zo mun yaba
Barno ma ta zo, Kashim
Shattima ya zo shi ma mun yaba
Nasarawa ma ta zo, Tanko
Almakura shima ya zo mun yaba
Amshi: Sabuwa ta zo APCnmu
Mun amince ‘yan Najeriya
Ku zo mu kama gaskiya ta
zo Najeriya
Jagora: Gaskiya ta zo
Amshi: Mun karɓe ta ƙauyuka
birni Najeriya hannu bi-biyu
Jagora: Mun karɓe ta hannuwa bi-biyu
Najeriya
Amshi: Kowa ya bi
Jagora: Sabuwar Jam’iyya
APC
Amshi: Gaskiya ta zo
Jagora:/ Ku zo mu kama
gaskiya ta zo Najeriya
Amshi:
Jagora: Gaskiya ta zo ku
zo mu karɓe ta hannu bi-biyu Najeriya
Jagora:/ Kun karɓe ta hannuwa bi-biyu
Najeriya kowa ya bi
Amshi
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.