ƘA'IDOJIN RUBUTUN HAUSA A SAUƘAƘE: KOYARWA DALLA-DALLA A CIKIN
BIDIYOYI
Daga
Abu-Ubaida SANI,
Ph.D.
Department of
Languages and Cultures,
Federal University
Gusau, Zamfara, Nigeria
Email: abuubaidasani5@gmail.com | abu-ubaidallah@fugusau.edu.ng
ORCID: https://orcid.org/0000-0001-6447-4334 | WhatsApp: +2348133529736
Tsokaci
Sanin
ƙa’idojin rubutun Hausa yana ɗaya daga cikin ƙalubalen da suka daɗe suna ci wa
manazarta da malamai da ɗalibai tuwo a ƙwarya dangane da koyo da koyarwa da
kuma nazartar Hausa. A bisa haka ne aka gudanar da wanann yunƙuri na koyar da
muhimman ƙa’idojin rubutun Hausa a cikin bidiyoyi. An yi ƙoƙarin gabatar da
bayanan dalla-dalla ta yadda masu kallo za su fahimta kai tsaye. Haka kuma, an
yi ƙoƙarin samar da wadatattun misalai domin ƙara sauƙaƙa fahimta ga masu
kallo.
Darussa
ƘA’IDOJIN RABA RUBUTU
Waɗannan
su ne dokokin rubutun Hausa waɗanda
a duk lokacin da aka ci karo da su, to za a raba rubutu ne, wato ba za a haɗe kalmomin ba. Haɗa rubutu a ire-iren wuraren
kuskure ne, ko da kuwa an ji cewa tamkar kalma ɗaya
ake furtawa. Danna NAN domin duba bayanai game da ƙa'idojin rabe rubutu.
1. Ƙa'idojin Rubutun Hausa 001: Gabatarwa
2. Ƙa'idojin Rubutun Hausa 002: Aikatau Mai
Gaɓa Ɗaya
3. Ƙa'idojin Rubutun Hausa 003: Gutsurarren
Aikatau/Ɗaurarren
Aikatau
4. Ƙa'idojin Rubutun Hausa 004: Aikatau Da
Wakilin Suna Karɓau/Sha-Wuya
5. Ƙa'idojin Rubutun Hausa 005: Kalmomin
Dirka
6. Ƙa'idojin Rubutun Hausa 006: Doguwar
Mallaka
7. Ƙa'idojin Rubutun Hausa 007: “wa” a Matsayin Wakilin Suna
8. Ƙa'idojin Rubutun Hausa 008: Lamirin
Lokaci Kafin “a”
9. Ƙa'idojin Rubutun Hausa 009: Kalmomin
Jaddadawa/Ƙarfafawa
10. Ƙa'idojin Rubutun Hausa
010: “a kan” a Matsayin Manuni Ko
Ishara
11. Ƙa'idojin Rubutun Hausa
011: Kalmomi Masu Zaman Kansu
12. Ƙa'idojin Rubutun Hausa
012: Lamirin Lokaci Kafin Wakilin Suna
13. Ƙa'idojin Rubutun Hausa
013: Mahaɗi “da”
14. Ƙa'idojin Rubutun Hausa
014: “ba” a Muhallin Korewa
15. Ƙa'idojin Rubutun Hausa
015: “a” Da Aikatau
ƘA’IDOJIN HAƊA RUBUTU
Waɗannan
su ne ƙa’idojin rubutun Hausa waɗanda a duk lokacin da aka
ci karo da su, to za a haɗe
rubutu ne, wato ba za a rabe kalmomin ba. Rabe rubutu a ire-iren wuraren
kuskure ne, ko da kuwa an ji kamar kalmomi mabambanta ake furtawa. Danna NAN domin duba bayanai game da ƙa'idojin haɗe rubutu.
16. Ƙa'idojin Rubutun Hausa
016: Gajeruwar Mallaka
17. Ƙa'idojin Rubutun Hausa
017: Sababben Lokaci (Lokacin Sabo)
18. Ƙa'idojin Rubutun Hausa
018: Wakilin Suna Kafin Lamirin Lokaci
19. Ƙa'idojin Rubutun Hausa
019: “a” Gabanin Lamirin Lokaci
20. Ƙa'idojin Rubutun Hausa
020: Kalmomin Nuni Ko Ishara
21. Ƙa'idojin Rubutun Hausa
021: Kalmomin Tambaya (Tambayau)
22. Ƙa'idojin Rubutun Hausa
022: Kalmomin Jam’I
(Jam’u)
23. Ƙa'idojin Rubutun Hausa
023: “a” Gabanin Lamirin Lokaci
24. Ƙa'idojin Rubutun Hausa
024: “wa” a Matsayin Ɗafa-Ƙeya
25. Ƙa'idojin Rubutun Hausa
025: Kalmomin Jam’u Da
Wakilin Suna
26. Ƙa'idojin Rubutun Hausa
026: “ma” Gabanin Wakilin Suna
27. Ƙa'idojin Rubutun Hausa
027: Wasu Ƙa’idoji Masu Ruɗarwa
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.