Citation: Nasir Abdullahi USMAN (2025). Yarfe A Wasu Waƙoƙin Yabo Na Haruna Aliyu Ningi. Yobe Journal of Language, Literature and Culture (YOJOLLAC), Vol. 13, Number 1. Department of African Languages and Linguistics, Yobe State University, Damaturu, Nigeria. ISSN 2449-0660
YARFE A WASU WAƘOƘIN YABO NA HARUNA ALIYU NINGI
NA
NASIR ABDULLAHI USMAN
Tsakure
Wannan takarda mai take:
Yarfe A Wasu Waƙoƙin Yabo Na Haruna Aliyu
Ningi an shirya ta ne domin nazarin yadda mawaƙa suke amfani da abubuwa na
yarfe a zamantakewar irin yau da kullum duba da yadda suka mayar da yarfe in
babu shi to babu waƙar ballantana ma waƙar yabo duk ba za ta yiwu
ba, ko kuma za ta zama kamar miya ba gishiri ma’ana ba za ta yi armashi
ba. Manufar
wannan bincike ita ce yin nazarin yarfe a cikin waƙoƙin yabo na zamantakewar rayuwa a cikin waƙoƙin Haruna Aliyu Ningi. Takardar ta mayar da
hankali ne ga waƙoƙinsa na zamantakewar
rayuwa, domin ganin yadda yarfe ya ginu a cikinsu. An yi amfani da ra’in
Awon baka wanda aka ɗora binciken a kansa,
wanda a ƙarshe takardar ta gano cewa yarfe abu ne da ya ginu a cikin
waƙoƙin yabo na Haruna Aliyu
Ningi. tun lokaci mai tsawo kuma har yanzu ana amfani da shi.
1.1 Shimfiɗa
Nazari a kan ayyukan adabi da suka haɗa da waƙoƙi da wasannin kwaikwayo
da kuma rubutattun zube ba sabon abu ne a fagen nazarin Hausa ba, musamman idan
aka yi la’akari da irin gudummawar da masana da manazarta suka bayar wajen fito
da muhimman abubuwan da suka ƙunsa. Masana da
manazarta irin su Mashi (1986) da Birniwa (1987) da Funtua (2003) da Ɗangulbi (2003) da Ɗan’illela (2010) da Sani (2012) da Adamu (2019) da Adamu
(2021) sun yi waɗannan nazarce-nazarce ne ta la'akari da yadda
adibai suka baje kolin basirarsu kan al'amuran ayyukansu na adabi. Yawancin nazarce-nazarce da ayyukan da aka gudanar
sun shafi nazarin zubi da tsari da salo da turke ko jigo ne, yayin da
aikin Yahaya (2016) ya yi nazarin bijirewa a waƙoƙin siyasa da Yusuf (2018) wanda ya yi nazarin tarihin jam'iyyar
PDP a cikin rubutattun waƙoƙin siyasa.
Dangane da batun samuwa da bunƙasar siyasar zamantakewar rayuwa ko siyasar jam’iyya kuwa, za a
iya alaƙanta shi da cuɗanyar da aka samu
tsakanin Turawa da al’ummar ƙasar Hausa. Birniwa, (1987, sh 27-28) ya bayyana cewa tun a wuraren shekarun
1930-1940 ne aka fara jin ƙamshin samuwar ƙungiyoyin siyasa a Arewacin Nijeriya. An samu ɓullar ƙungiyoyi da dama duk da cewa ba su fito
fili ƙarara a karon farko sun kira kansu da jam’iyyun
siyasa ba, amma dai sun samar da cibiyoyin da sukan riƙa haɗuwa lokaci-lokaci domin tattauna al’amuran
siyasa. Su kuwa Dudley (1968, sh 78-79) da Idris (2016, sh 51) suna da ra’ayin cewa, an fara samun ɓullar ƙungiyoyi ne a tsakankanin shekarar 1943. Ƙungiyoyin da aka samar wannan lokacin sun haɗa da; Ƙungiyar Inganta Rayuwar Mutanen Bauchi (Bauchi General Improɓement Union) wadda Sa’adu Zungur ya kafa a 1943, da Ƙungiyar Tattaunawa ta Mutanen Bauchi Discussions Circle) a 1944, da Ƙungiyar Zumunta ta Sakkwato (Youth Social Circle) a 1945, da Ƙungiyar Matasa ta Kano
(Kano Youth Association) a 1948 da Ƙungiyar Matasan Zariya
(Zaria Youth Association) ita ma a 1948 da sauransu. Waɗannan ƙungiyoyi da ma wasu duk an kafa su ne a
tsakankanin 1943 zuwa 1948, waɗanda su ne suka narke suka zama jam’iyyar (Northern Poeple Congress) a shekarar 1951. Daga baya, sai wasu mutane suka ɓalle, suka kafa jam’iyyar (Northern Element Progressiɓe Union). Waɗannan jam’iyyun da aka samu, wato Northern Element Progressiɓe Union da Northern Poeple Congress, su ne suka kasance manyan jam’iyyun siyasa guda biyu masu
hamayya da juna a ƙasar Hausa.
Bayan kafuwar jam’iyyun siyasa na farko, an riƙa samun musayar yawu daga magoya bayan jamiyyun biyu, inda aka
samu rubuce-rubuce cikin jaridu da wasiƙu da jawaban siyasa waɗanda suke ƙunshe da al’amuran siyasa da suka faru a wancan
lokacin. Irin waɗannan abubuwa sun ci gaba da gudana har zuwa
wannan jamhuriya da ake ciki, wato jamhuriya ta huɗu, inda ayyukan adabi suka riƙa nuna hoton yadda
al’amura da suka riƙa gudana waɗanda suka shafi waƙoƙin yabo.
Duk da cewa masana da manazarta sun bayar da
gagarumar gudummawa da suka cancanci yabo, amma ba a samu wani aiki na nazarin ilimi da hannu
ya kai kansa wanda aka yi nazarin yarfe daga cikin waƙoƙin yabo na Haruna Aliyu ba. Wannan ne ya sa aka
ga dacewar tattauna wannan batu a wannan takarda domin ganin yadda yake da kuma yadda ake
gudanar da shi a har kokin yau da kullum.
2.1 Bayani A Kan Muhimman Kalmomin Bincike
2.1.1 Ma’anar Yarfe
Kalmar Yarfe Bahaushiyar kalma ce, kuma kalma ce ta fannu aka
aro domin a yi amfani da ita a kan waƙoƙin yabo, tana ajin suna ne mai ɗauke da jinsin namiji.
Kalmomin Ƙage da Ƙazafi suna da makusantan
ma’anoni da juna ko ma a ce ma’anarsu guda, sai dai kowacce da asalinta,
kuma ana iya amfani da wata a maimakon wata. Kalmar tana nufin a ce mutum ya yi
abin da bai ji ba, bai gani ba ko kuma a ƙulla masa sharri (CNHN,
2006 sh 273). Ƙazafi kuwa kalma ce da
take da asali daga Larabci wato ‘Ƙazaf, wadda Hausawa suka
ara suka yi mata Karin -i a ƙarshenta ta koma Ƙazafi. Ma’anar kalmar a Hausa da Larabci duk abu guda take nufi.
Kalmar Ƙazafi suna ne mai ɗauke da jinsin namiji, kalmar tana nufin laƙa wa mutum laifi ko yi masa sharri da (CNHN, 2006 sh 279).
Ƙamusun CNHN (2006, sh 479-480) ya bai wa kalmar yarfe ma’anoni guda biyar
kamar haka:
i.Maka ko daka
ii.Watsa
iii.Ƙaga
iv.Aika da, musamman na zagi
v.Amfani da hannu don share wani abu.
Daga cikin waɗannan ma’anonin, ma’ana
ta biyu da ta uku ne suke da alaƙa kai tsaye da wannan
takardar, domin a ƙarƙashin ma’ana ta biyu an
ba da misali da ‘na watsa masa taɓo’ kuma duk abin da aka watsa masa taɓo to an bata wannan abin, domin zai nuna alamomi a wurare da dama
a jikinsa. Ita ma ma’ana ta uku daga cikin ma’anonin an ba da misali ƙarƙashinta kamar haka: ‘Sun ƙaga masa laifi’. Ke nan kalmar yarfe tana nufin ƙaga wa wani mutum wani laifi kamar yadda aka bayyana ta a sama.
Idan aka ƙaga wa wani mutum wani laifi wanda bai ji ba, bai
gani ba yakan zubar masa da ƙima ko ya rage
masa ƙima a idon mutane. Idan magoya bayansa ne sai a
samu wasu su dawo daga rakiyarsa.
Don haka, kalmar tana nufin a sanya wani baƙon abu a jikin wani ta yadda zai iya yin ɗigo-ɗigo a jikinsa har ya fito a gani. Alal misali,
kamar a samu farar tufa a yarfa mata manja ko wani baƙin mai wanda zai zama an ɓata wannan tufar.
Manufar yarfe a nan ita ce ɓatawa, kamar yadda aka yarfa wa wannan farar tufar wasu launuka
don a ɓata ta.
Kalmomi biyu na farko wato ‘yarfe’ da ‘ƙazafi’ dukkansu kalmomi ne da ake amfani da ma’anarsu a cikin
harkokin yau da kullum, kuma in aka yi amfani da su suna iya dacewa da ko wa
aka jefa da su. Za kuma a iya cewa an yi wa wane yarfe, ko an yi wa wane ƙazafi. A cikin waƙoƙin yabo ko waɗanda ba na yabo ba, za a iya faɗa an yi wa mutum yarfe ko ƙazafi, ma’ana an yi mishi ɓatanci ko an yi sharri. Ke nan, daga bayanan da suka gabata za a
fahimci cewa, kowane yarfe ko ƙazafi duk abu ɗaya ne wato sharri ne, kuma ɓatanci ne, da ake yi wa wani a cikin waƙoƙi na zamantakewar rayuwa ciki har da na yabo, domin a daƙushe shi kuma a ɓata shi a idon mutane, ta hanyar ɗora masa wani abu da bai ji ba bai gani ba. A taƙaice dai, kalmar yarfe bisa fahimtar mai nazari a wannan binciken
tana nufin faɗin wani abu da bai tabbata ba, tare da danganta
shi kan wani mutum.
2.1.2 Ma’anar Waƙa
Masana da manazarta adabi da dama sun bayyana
ra’ayoyinsu tare da bayar da fahimtar su dangane da ma’anar waƙar Hausa. Daga cikin su akwai:
Ɗangambo, (1982), “Waƙa wani furuci ne wato
lafazi ko saƙo cikin azanci da ake aiwatarwa ta hanyar rerawa
da daidaita kalmomi cikin wani tsari ko ƙa’ida da kuma yin amfani
da dabaru ko salon armashi”.
Umar, (1980, sh 3) “Waƙa tana zuwa ne a sigar
gunduwoyin zantuka waɗanda ake kira baitoci ko ɗiyoyi kuma ake rerawa da
wani irin sautin murya na musamman”.
Shi kuwa Yahaya, (1976). “Waƙa magana ce ta fasaha a cure wuri ɗaya a cikin tsari na musamman”
Yahya, (1984). “Waƙa maganar hikima ce da
ake rerawa ba faɗa kurum ba wadda ke da wani saƙo da ke ƙunshe cikin wasu kalmomi zaɓaɓɓu, tsararru kuma zaunannu”.
Waƙa ita ce maƙerar mawaƙi. A nan ne yake narka kalmomi ya fito da saƙonsa zuwa ga al’umma. A nan ne kuma yake narka su ya yi maganganun
hikima, hikima ta harshe ko ta hanyar rayuwa. Waƙa magana ce ta tsakanin
zukata ko bayan cewa tunani ma yana naƙalta. Abin nufi a nan
ita waƙa takan yi tsari ne kai tsaye kan zuciya fiye da
sauran nau’o’in magana. (Yahya, 2016, sh 26).
A fayyace ana iya cewa waƙa magana ce da aka zayyana ba wadda aka sako kara-zube ba. Magana
ce wadda aka aza bisa sanannu ko ayyanannun ƙa’idoji waɗanda ke daidaita furuci da sauti, su kuma tilasta zaɓar kalmomi domin dacewar ma’ana da furuci. Ta haka ne maganar take
zuwa babu karo da juna ta furuci ko kalmomi ta fuskar daidaiton tsawon gaɓoɓi, saɓanin magana ta yau da
kullum. (Yahya 2016, sh 27) Waƙa wasu zantuka ne da ke ɗauke da saƙo mai nusarwa tare da nishaɗi cikin hikima.
2.1.3 Ma’anar Yabo
Wannan kalma ta yabo abu
ne da kowane mutum ke ƙaunar ya samu ko ya ji alaƙanta shi da ita a cikin
harkokin rayuwarsa ta yau da kullum, sannan kuma bai son akasinta a ma’amalarsa
irin ta yau da gobe, Kalmar yabo tana ƙara wa mutum ƙwarin guiwa da karsashi
a rayuwarsa. CNHN (2006) ya bayyana yabo kamar haka ‘faɗar duk wata kalma mai daɗi ga wani mutum da ya
aikata wani kyakkyawan abu. Misali (i) saboda ya yi masu (ii) ambaton sunayen
Annabi da yi masa addu’a, kamar irin na Ishiriniya da Diwani.
3.1 Ra’in Bincike
An ɗora wannan aiki ne a kan
Ra’in Awon Baka (Oral Formulaic Theory). Wannan ra’i an ƙirƙire shi ne a ƙasar Sabiya, wato
Philips Ɓiscy (1767-1834) ne
ya ƙirƙiro shi, kuma shi ne ya yaɗa ra’in a ƙasar Sabiya har zuwa wasu
sassa na Turai da Amurka. Wannan mazhaba ta sami bunƙasa ne tun a farkon ƙarni na ashirin (1920-1935)
a lokacin da masana na Turai suke nazarin dogayen waƙoƙi, musamman irin ayyukan
Milman Parry da ɗalibansa Albert Lord. Amma fitaccen wanda ya ɗabbaƙa wannan mazhaba shi ne
John Miles Foley, tare da taimakon wani mutumin Sabiya wato Francis Peabody
suka bunƙasa ta. Daga bisani kuma
Albert Lord ya yi ƙoƙarin ɗora wannan mazhaba a kan tsofaffin waƙoƙi na Turawa tare da fito da
bambance-bambance da ke cikin waƙoƙin.
An ɗora wannan aiki a kan ra’in
Awon Baka saboda la’akari da aka yi cewa, abubuwan da aka kula da su a kan
wannan ra’i sun haɗa da layukan ɗan waƙa da ƙulli da ƙari, ta nazarin waƙar baka Bahaushiya (ta
hanyar duba hawa da sauka da saukar sauka da amsa-amo kari da amfani da sassan
adabin baka da sauran su) kamar yadda Gusau (2015) ya yi nuni. Ire-iren ayyukan
da waɗannan masana na cikin gida
suka aiwatar mai nasaba da wannan ra’i sun haɗa da: Abdulƙadir (1975) da Bichi (1975)
da Ibrahim (1983) da Gusau (1983 da 1988 da 2014).
Wannan Ra’i yana ganin cewa
waƙoƙi rumbu ne na hikimomi,
wanda ake amfani da su yau da gobe kuma ya bayyana irin al’amuran da
suke faruwa cikin hikima tare da danganta su cikin magana, daga ƙarshe suke rikiɗewa su koma ɗiya na waƙa. Wannan mazhaba tana da
manufofi kamar haka:
· Nazarin azancin magana na baka kamar karin
magana da adon harshe.
· Duba aikin adabi musamman adabin baka
· Fito da hanyoyin nazarin awon baka na waƙoƙi, domin gane irin hanyar
da aka bi wajen irin awon baka da aka ɗora waƙa a kai.
· Ƙoƙarin faɗaɗa fahimta da nuna burgewa dangane da yadda
ake gudanar da waƙoƙin baka.
· Neman bayanin tarihin mawaƙin da zamaninsa.
· Nazarin dokokin al’umma ta hanyar adabin baka
kamar camfe-camfe da sauran su.
· Adana labarun gargajiya a ka ta hanyar naƙalta da adanawa a ka ba
tare da rubutu ba.
· Tattara tatsuniyoyi da waƙa daga wata al’umma zuwa
wata.
· Lalubo yadda yanayin waƙoƙi suke a bakunan mutane.
(http://en wikipedia.org/wiki/maɗist literary criticism).
Duba da waɗannan manufofi na wannan
mazhaba ta Awon baka, ya sa wannan bincike ya dace a ɗora shi bisa wannan mazhaba
ta awon baka, musamman ganin cewa wannan aiki ya yi duba ne a kan wasu waƙoƙin yabo na baka na Haruna
Aliyu Ningi.
4.1 Taƙaitaccen Tarihin Haruna
Aliyu Ningi.
An haifi Haruna Aliyu Ningi
ne a ranar talata ashirin da biyu ga watan Nuwamba alif ɗari tara da saba’in da
bakwai (22-11-1977) a garin Ningi. Sunan mahaifinsa Abdullahi amma yana amfani
da sunan kakansa Aliyu saboda tunawa da kakan da kuma irin addu’o’in da ya yi
wa iyayensu da kuma dangin su.
Bayan ya samu kimanin
shekaru biyar ne, sai aka sashi a makarantar firamare a shekarar alif ɗari tara da tamani da biyu
(1982), makarantar firamare
ta Rumbu inda ya shekara biyu 1982-1984. Daga nan ne sai ya wuce makarantar
firamare ta Garɗo daga (1984-1985), kuma
(1985-1986) ya koma makarantar firamaren Ziɗaga dukansu a garin Ningi. A wannan shekarar ya
tafi sakandare dake Burra daga 1986-1988. Bayan ya ƙara zama a gida na kimanin
shekaru huɗu, a shekarar 1992 ya koma aji
hudu a babban sakandare ta Dagauda a karamar hukumar Dambam ta Jihar Bauchi
inda ya kammala makarantar a shekarar 1993.
A shekarar 1994 ya tafi
makarantar kimiyya da fasaha da ke Ƙauran Namoda a inda ya samu Diploma a kan
harkokin kuɗi (financial studies) a
shekarar 1996, Ya zauna a gida na
shekara ɗaya, kuma wannan shekarar
ana cikin siyasar UNCP da DPN, kuma a wannan shekarar ya rubuta waƙa ta siyasa. Wannan ko ya faru ne a sanadiyyar
murɗiya ko maguɗi wanda aka yi ma ɗan takarar su a ƙarƙashin jam’iyyar DPN, wanda
shi ne Ɗanlami Garba Bara’u. Mawaƙin ya yi wannan waƙa ba kai ba gindi, domin ya
ce ko suna bai sa mata ba balle ƙafiya. Kuma bai ajiye ta ba, Saboda haka a yanzu ta ɓace. Daga baya sai ya lura
akwai hannun gwamnati a wannan murɗiya da aka yi, saboda haka sai ya rabu da
siyasar Bauchi ya koma Kano, a nan sai ya fara yi wa UNCP waƙa da kuma shugabanta Alhaji
Shehu Shanono.
Haruna Aliyu Ningi ya sake rubuta waƙa a lokacin siyasar PDP.
Dalilin da ya sa ya yi wa PDP waƙa kuwa shi ne ya karanci jama’arta kaf ‘yan
siyasa ne. Waƙar da ya fara rubuta ma PDP
ita ce “Iyata Sarauniya”. Inda ya yaba wa jam’iyyar da ‘ya’yanta tare da kuɗa da washi’. Daga nan sai ya zarce da rubuta
wa mutane waƙoƙin yabo masu armashi da
kama zukata.
A halin yanzu Haruna Aliyu
Ningi ya sauke farali wato aikin hajji, kuma ya yi auren fari a ranar a 23 ga
watan Augusta 2003. Sannan Allah ya albarkace shi
da ɗa namiji a ranar 26 ga
watan Yuli 2005, inda aka sa wa yaron Umar Faruk, sanan matarsa Fatima.
Dangane da karatun allo
kuwa Haruna Aliyu ya yi na ɗan ƙanƙanin lokaci ne, wanda bai
wuce wata uku ba, sai kuma wanda ya yi a makarantar firamare daga aji ɗaya zuwa uku.
5.1 Yarfe A Wasu Waƙoƙin Yabo Haruna Aliyu Ningi
Haruna Aliyu Ningi fasihin mawaƙi ne wanda ya shahara a fagen rera waƙoƙin Hausa, musamman ma waƙoƙin yabo da kuma waɗanda ba na yabo ba. Mutane da yawa a ƙasan nan sun sami ɗaukaka da sanuwa ta dalilin waƙoƙi da ya yi masu, saboda yadda ya riƙa ɗabbaƙa manufofinsu ta hanyar yabo a idon mutane har
suka amince suka karɓe su. Kasancewarsa gwani a fagen waƙoƙin ya sabbaba masa iya yin yarfe yayin da yake
rera waƙa. Alal misali, a waƙarsa ta ‘Ba Za Mu Ɗau Coge Ba’ wanda ya yi
wa Faruƙ Adamu Jigawa, inda ya yi wa wani yarfe a
cikin waƙar kamar haka:
A Jigawa an takura an kai mu bango bana,
An mai da
kaf al’ummammu kamar dashen zogala,
A rashin
sani mun ɓata da hannunmu mun ɗau rina,
Ba za mu sake zuwa Kogi da ɗan kurme ba. Usman (2011).
Wannan ɗan waƙar, mawaƙin ya yi yarfe da kalmar rina, wato wani ɗan ƙwaro baƙi mai fiffike wanda ya
fi zama a kan bishiya wanda yake harbin mutumin da ya hau bishiyar da gidansa yake kanta kuma ya kusanci
gidan. To babu shakka sai dai ya ji saukar harbi, kuma da
ya yi harbin, zai ɗauke ƙarinsa ya tafi da shi.
Kuma ya sake yin yarfe inda ya ce, ba za su sake zuwa
kogi da ɗan kurme ba. Wannan kalma ta kurme ma’anarta shi ne yin nutso can ƙasan ruwa a daɗe ana tafiya ana kamo kifi
wanda masunci yake yi, wato nutsa ƙasan ruwa a kogi a daɗe ana kama kifi ba tare
da ɗagowa sama ba shi ne kurme, kuma ba duk masunci ne yake yi ba saboda yana
da haɗari. Kalmomin rina da kurme duk
yarfe ne.
Kullum a
yawo yake tamkar Karen Barbara,
Ba za ya zauna ba ne ko za mu ɗau kokara,
Don dai
da amsar faɗawa Jigawa ko mun jira,
Sai tafka
sata yake bai gane mun farga ba.
A wannan ɗan waƙan na sama kuwa, ya yi masa yarfe da cewa kullum bai tsaya wa ya
sauke nauyin da ke kansa, wato haƙƙin mutane da ya yi alƙawarin zai iya, sai yawon yake ta yi kamar karen
Barbara. Ma’ana a nan shi ne, karan Barbara kare ne wanda ba na kowa ba kuma ba shi
da wani tsayayyen waje da ake samunsa, shi duk inda ya ga matan karnuka bin su
kawai zai kama yi. Sannan ga tafka sata kamar ɓera. Ma’ana a nan shi ne duk abin da ya gani wanda hannunsa ya kai gare shi ko
ya ƙyalla ido ya gani to zai ɗauke. Waɗannan kalmomi guda biyu duk yarfe ne.
Mawaƙi Haruna Aliyu Ningi ya
yi wa Bola Ahmad Tinibu yarfe a cikin waƙarsa, inda ya ayyana shi
da:
Baba Hamed Bola Tinibu Lagos ya take?
Ba ni da tambayar in ji ya jama’ar Lagos suke,
Shi ba ya sani ba sabo in ka ƙi ya take,
Cinnaka yake baka san na gida a ɗangaren yarbawa. Usman
(2011).
A cikin wannan ɗan waƙar ya yi amfani da kalmar cinnaka, wato
wani ɗan ƙwaro ne baƙi ɗan ƙarami mai fitowa daga
cikin rami a ƙasa lokacin damina. Yana da fuffuke da yake tashi sama ya maƙe wa mutum cikin tufa ya yi ta cizonsa, in ma a ƙasa ne haka zai yi wa duk wanda ya maƙale masa a jikin tufafi. Saboda haka Bahaushe ke masa kirari da
cinnaka ba ka san na gida ba, kowa cizo yake, matuƙar dai ka raɓe shi, to babu shakka sai ya cije ka. A wajen
Bahaushe da zarar aka ce wannan mutum ai cinnaka ne, to abin da ke zuwa a ransa
shi ne wannan mutum azzalumi ne ko maƙetaci. Duk kalmomin biyu
na yarfe ne.
A waƙar ‘Dokin Ƙarfe’ ma, ya yi yarfe ga wani mutum kamar yadda ya faɗa a ɗan waƙar da yake tafe:
Wakilinmu
na ɗazu mun ga illa,
Muna kai
shi ya fara sunce dala,
Ya mance alai la da ƙila,
Ya kwanta
a hakin mu ya ɓace yai mana laya. Hussaini (2009).
Mawaƙin ya yi yarfe da
kalmar sunce dala, kalmar kuɗi ne irin na ƙasar Amurka wanda aka fi yin hada-hadar hulɗar cinikayya a duniya, saboda haka wani mutum sai ya riƙa kwashe wa yana sawa a aljihunsa.
A ɗan waƙar ‘Ƙalubale’ da ke tafe Mawaƙi Haruna Aliyu Ningi nan ma ya yi yarfe a cikinta inda yake cewa:
Kan ‘yanci da tararradin wai a yi gardama,
Idan za ka shigo gidanmu sai ka yi sallama,
Muna shuka fara wa’yansu na shuka baƙar rama,
Macutan nan Baba kaf suke kashe Nijeriya. Yusuf,
(2018).
A cikin wannan ɗan waƙar mawaƙin sojoji ya yi wa yarfe
inda ya kira wasu mutane da Macuta kuma ya ce su ne
suke ɓata ƙasar, cuta tilo
macuta jam’i saboda kullum idan suka
tashi shigowa ƙasarmu ba sa sallama sai dai a wayi gari
da su ko’ina kurum, kuna so ko baku so, oho dai, wannan dai ku ta shafa su ba
ruwansu.
A wannan ɗan waƙar ‘Iyata Sarauniya’ ya
yi wa rundunar sojojin ƙasarmu yarfe domin al’umma su ƙara tsanarsu tare
da ƙyamatarsu ta
hanyar ƙanga masu wasu batutuwa
kamar haka:
Kai ina Abba Haruna
Ningi Rimin mabuƙata,
Wa’yanda muke so a
kauda mulkin matsiyata,
Suna iƙirarin yasu-yasu za su
wadata,
Da yardarm Allah ƙasarmu mu za mu riƙeta. Yusuf (2018).
A nan ma ya yi
yarfe a ɗiyan wannan waƙar ga mulkin sojoji inda ya kira shi da mulkin
matsiyata sannan kuma ya yi masu yarfe da cewa suna iƙirarin yasu-yasu za su
wadata, ma’ana su kaɗai ne kawai za su amfana da wannan mulki da
suke yi, sauran al’umar ƙasa kuwa ba za su amfana da wannan mulkin
nasu ba. Mulkin sojoji mulki ne na danniya wanda jama’ar ƙasa ba su da ‘yancin faɗin albarkacin bakin su game da yadda suke
jagorantar su.
Ai na san jama’ar ƙasarmu yau sun yi tunanai,
Da al’ummomin ƙasarmu duk an mana rauni
A yau mun
gama shawarar mu ɗauko mai mana Danni,
Ta fishe
mu ga dukka jalli-jogon matsiyata. Usman (2011).
A ɗan wannan waƙar mai suna ‘Abar So A Zukata’ ya yi yarfe ga wasu mutane da cewa
al’ummomin ƙasa sun wahala sun sha wuya saboda irin rauni da
suka yi masu, wannan kalma ta rauni tana nufin lahani ko ciwo don haka tun wuri
bari su rabu da waɗannan batutuwa, yarfe ne.
Haruna Aliyu Ningi ya yi wa wani yarfe a cikin
waƙar Hazo rufe rana a wannan ɗan waƙar inda yake cewa:
Ga gwanje
a cikin Arewa wanda yake ƙyamar mutane,
Bai taɓa jaddada ƙa’ida ba duk lamarinsa a yaudara ne,
Ya yi ada kuma ya matsanta wai ya daɗa koma ta yane,
Yau da
Zidani ƙwallo take yi ba da Agentina ba Baba. Usman
(2011).
A wannan ɗan waƙa mawaƙin ya yi masa yarfe da cewa shi mutum ne wanda
yake ƙyamar mutane, a nan ana nufi bai son mutane. Haka kuma ya sake cewa bai taɓa jaddada ƙa’ida ba, sannan kuma duk lamarinsa yaudara ne,
wato ba gaskiya, saboda ba a gane inda aka sa gaba. Ke nan duk kalmomin biyu
yarfe ne.
Mawaƙi Haruna Aliyu Ningi ya
yi wa wani shugaba yarfe a cikin waƙarsa, inda yake cewa:
Zan fara
batun mantau ya mance Jiharsa cikin yaƙi,
Rikici
suka huhhura dubbab jama’a aka yayyanke,
Bai kai
masu diyya ba bai damu ba su aka faffarke,
Inda a
tazarce ne da kun ga shirin rikici babba. Hussaini (2009).
Mawaƙi Haruna Aliyu Ningi ya yi yarfe a waƙar ‘Ba Mu Yarda Ba’ ga wani jagoran al’umma inda yake cewa ya mance Jiharsa cikin yaƙi, yaƙi shi ne faɗa tare da kashe rai, da ɓarnar dukiya. Sannan kuma har ila yau ya sake yarfe da cewa rikici suka
huhhura dubban jama’a aka yayyanke waɗannan batutuwa yarfe ne.
6.1 Sakamakon Bincike
Daga bayanan da aka kawo a sama, an fahimci cewa
waƙoƙin yabo na Haruna Aliyu Ningi suna cike da wasu
al’amura waɗanda suka zama tamkar gishiri a cikin miya. Daga
cikin waɗannan abubuwa kuwa akwai yarfe, wanda Haruna
Aliyu Ningi yake yin amfani da shi a zahiri da kuma tsarin wanda yin hakan ba
daidai ba ne. Domin a wasu lokuta yakan taɓa mutuncin wani kai
tsaye cikin abin da bai ji ba bai gani ba sannan ma babu tabbas ko ma ba
gaskiya ba ne, sai dai ya zama hanyar jawo ra’ayin al’umma ne da su ƙara jin daɗin waƙoƙin yabo na Haruna Aliyu Ningi.
Binciken ya gano cewa, yarfe ba sabon abu ba ne
a cikin waƙoƙin yabo na Haruna Aliyu
Ningi, wato daɗaɗɗan abu ne, kuma yana amfani
da shi ne domin cim ma wani
burinsa a waƙoƙinsa na yabo da yake yi
wa mutane. Kuma har yanzu yana ci gaba da amfani da shi a waƙoƙin nasa kamar yadda wasu mawaƙan da suka gabace shi suke
amfani da shi.
Wani abu kuma da binciken
ya gano shi ne, yarfe yana taimaka wa mawaƙi wajen samun nasara a
cikin waƙoƙinsa na yabo, musamman
Haruna Aliyu Ningi, domin faranta ran wanda ya yi wa waƙar, ya kuma baƙanta ran wanda aka yi wa
yarfen.
7.1 Naɗewa
Wannan maƙala ta tattauna a kan yadda
Haruna Aliyu Ningi ya riƙa amfani da yarfe a cikin waƙoƙinsa na yabo. Tun da farko a cikin gabatarwa an kawo taƙaitaccen tarihinsa da kuma waƙoƙinsa na yabo. Daga nan
sai aka kawo ma’anar yarfe da waƙa da yabo domin haska
inda sunan takardar ta dosa. Daga bisani sai aka tsunduma cikin nazarin yarfe a
cikin waƙoƙin yabo na Haruna Aliyu
Ningi tare da kawo
misalai daga cikin waƙoƙin. A ƙarshe, binciken ya gano cewa waƙoƙin yabo na Haruna Aliyu Ningi mafi yawa suna ɗauke da yarfe, wanda ya samo asali tun farkon fara waƙoƙinsa, kuma ba abin mamaki ba ne idan aka ga ya ci gaba da amfani da
shi a waƙoƙinsa na yau da gobe, a
matsayin wata hanya ta faranta waɗanda yake yi wa waƙoƙin yabo.
Manazarta
Adamu, M. (2019). Kawatanci
Tsakanin Rubutattun Waƙoƙin Siyasar Jumhuriya Ta Uku Da na Jumhuriya Ta Huɗu A Nijeriya. Jami’ar Umaru
Musa ‘Yar’adua.
Adamu, A. I. (2021).
Dabarun Jawo Hankali AWasu Waƙoƙin Siyasa A Jihohin Kano da Katsina da
Zamfara Daga 2007 Zuwa 2018. ƊKundin digiri na ukuɗ sashen koyar da harsunan Nijeriya. Jami’ar Bayero.
Bichi, A.Y. (1975). Waƙoƙin Aure a Ƙasar Hausa (Hausa
Wedding Song). Cikin Yahaya, I.Y. Bello, G, Bichi, A.Y,
Dresel L., Sa’id, B. Harsunan Najeriya Vol. 41-45.
Birniwa, H. A. (1987). Conserɓatism and Dissent: A Comparatiɓe Study of NPC/NPN and
NEPU/PRP Hausa Political Ɓerse from Circa 1946 To 1983, Ɗkundin digiri
na ukuɗ, sashen harsunan Nijeriya. Jami’ar Usmanu
Danfodiyo.
CNHN. (2006). Kamusun Hausa na Jamiar
Bayero. Ahmadu Bello University Press.
Ɗan’illela, A. (2010). Rubutattun Waƙoƙin Siyasa: Nazari A Kan Jihohin Sakkwato Da Kebbi da Kuma Zamfara. ƊKundin digiri na biyuɗ sashen harsunan
Nijeriya. Jami’ar Usmanu Danfodiyo.
Ɗangambo, A. (1984). Rabe-raben Adabin Hausa da Mahimmancisa ga Ryuwar
Hausawa. Triumph Comfany.
Ɗangambo, A. (1975). The Role of
an Oral Singer in Hausa/Fulani Society: A case study of Mamman Shata. ƊKundin digiri na ukuɗ. jami’ar Indina.
Ɗangambo A. (2007) Daurayar
Gadon Fiɗe Waƙa (sabon tsari).
K.D.G. Publishers.
Ɗangulbi, A. R. (2003). Siyasa A Nijeriya: Gudunmawar Marubuta Waƙoƙin Siyasa Na Hausa ga Kafa Dimokuraɗiyya a Jumhuriya ta Hudu Zango na Farko. ƊKundin digiri na biyuɗ sashen harsunan Nijeriya.
Jami’ar Usmanu Danfodiyo.
Dudley, B. J. (1968). Parties and
Politics in Northern Nigeria. Frank Cass and C Ltd.
Funtua, A. I. (2003). Waƙoƙin siyasa na Hausa a Jumhuriya ta uku: yanaye-yanayensu da
sigoginsu, Ɗkundin digiri na biyu, sashen harsunan Nijeriya.
Jami’ar Bayero.
Gusau,
S. M. (2003). Jagoran Nazarin Waƙar Baka.
Benchmark Publishers.
Gusau, S. M.
(2008). Waƙoƙin Baka a Ƙasar Hausa:
Yanaye-yanayensu da Sigoginsu. Benchmark Publishers.
Gusau, G. U.
(2014). Al’ada da Ɗabi’un Mawaƙan Hausa, Zauren
Waƙa Journal. Jami’ar Usman Ɗanfodio.
Gusau, S. M. (2015). Mashabobin
Ra’i da Tarke da Al’ada na Hausa. Kano: Center Research and Publishers.
Gusau, S. M.
(1983). Waƙoƙin Noma na Baka:
Yanaye-yanayensu da jigoginsu musamman a Sakkwato, Ɗkudin digiri na biyuɗ sashen koyar da
harsunan Nigeria. Jami’ar Bayero.
Gusau, S. M. (1988)
‘‘Waƙoƙin Makaɗan Fada: Sigoginsu da
Yanaye- Yanayensu, Ɗkundin digiri na ukuɗ sashen koyar da
harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.
Hussaini, B. (2009). Haruna
Aliyu Ningi Da Waƙoƙinsa. Amana Pulishers.
Ibrahim, M. S. (1983). Kowa
Ya Sha Kiɗa. Longman Nigeria.
Idris, Y. (2016). Bijirewa A Waƙoƙin Siyasa: Bincike Kan Wakokin 1903-2015, Ɗkundin digiri na biyuɗ sashen harsuna da al’adun Afirka. Jami’ar Ahmadu Bello.
Mashi, M. B. (1986). Waƙoƙin Baka na Siyasa, Dalilansu da Sababinsu ga
Rayuwar Hausawa, Ɗkundin digiri na biyuɗ Jami’ar Bayero.
Mustapha, O. (2015, Satumba 4). Yarfen
Siyasa Ce A Ce Muna Gaba Da Buhari –Ali Wakil. An samo daga https://aminiya.ng/yarfen-
siyasa-ce-a-ce-muna-gaba-da-buhari-ali-wakili/
Umar, M. B. (1980). Nazarin Waƙoƙin Hausa. Publications Centre.
Usman, N. A. (2011). Tarken Waƙoƙin Adawar Siyasa na Haruna Aliyu Ningi, Ɗkundin digiri na biyuɗ. Jami’ar Ahmadu Bello.
Sani, M. M. (2012). Tunanin Siyasa a Waƙoƙin Malam Hassan Nakutama, Ɗkundin digiri na biyuɗ. Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Yahaya, A. B. (1984). Matsayin Waƙoƙin Baka a Cikin Adabin Hausa. Maƙala Wadda Ya Gabatar A
Makon Hausa. Kwalejin Horar da Malamai Mata ta Larabci.
Yahaya, I. Y. (2016). Hausa a Rubuce:
Tarihin Rubuce-Rubuce Cikin Hausa. NNPC
Yusuf, J. (2018). Tarihin Jam’iyyar PDP a Bakin
Marubuta Waƙa, Ɗkundin digiri na biyuɗ. Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.