Citation: Musa Muhammed CHIROMARI, Hauwa MU’AZURI & Tijjani Muhammad BELLO (2025). Tasirin Waƙoƙin Baka Wajen Bayyana Tarihin Sarakunan Ƙasar HausaYobe Journal of Language, Literature and Culture (YOJOLLAC), Vol. 13, Number 1. Department of African Languages and Linguistics, Yobe State University, Damaturu, Nigeria. ISSN 2449-0660

TASIRIN WAƘOƘIN BAKA WAJEN BAYYANA TARIHIN SARAKUNAN ƘASAR HAUSA

NA

MUSA MUHAMMED CHIROMARI

HAUWA MU’AZURI

TIJJANI MUHAMMAD BELLO

Tsakure

Wannan bincike ya duba muhimmiyar rawa da waƙoƙin gargajiya suke takawa wajen bayyanawa da adana tarihin sarakunan gargajiya a ƙasar Hausa. Makaɗan gargajiya sun kasance masu riƙe da tarihin mulki, nasaba, jarumtaka, da canje-canjen da suka faru a zamanin sarakuna daban-daban, ta hanyar amfani da waƙoƙi masu ɗauke da hikima, yabon halaye da ayyuka, da kuma adabin baka na musamman. Sannan binciken bi-bayani ne domin ya fayyace yadda waɗannan waƙoƙi ke zama tushe mai amfani ga masu binciken tarihi, musamman a matsayin madogara ta tarihi da al’ada. Haka zalika, binciken ya bayyana ƙalubalen da ke barazana ga wanzuwar wannan harka kamar rashin adanawa ta hanyar zamani, tasirin zamani da fasaha, da kuma raguwa ko ɓacewar sana’ar waƙa. A ƙarshe, an bayar da shawarwari da matakan da ya kamata a ɗauka domin kare wannan gado na ilimi da al’ada ga ƙarni masu zuwa.

1.0 Gabatarwa

A cikin al’ummar Hausawa, waƙa ba wai nishaɗi kawai take nufi ba, illa ma ana ɗaukar ta a matsayin wata hanya mai muhimmanci ta sadarwa da watsa ilimi. Sannan Gusau (2023, shf. ɗiɓ), ya bayyana waƙa da cewa, "wani zance ne shiryayye cikin hikima da azanci da yake zuwa gaba-gaba bisa ka'idojin tsari da daidaitawa a rere cikin sautin murya da amsa-amon kari da kida da amshi Ɗaya daga cikin muhimman fannoni da waka ta taka rawa shi ne ɓangaren adanawa da wanzuwar tarihi, musamman tarihin sarakunan gargajiya. Wannan takara na ɗauke da bayani da kuma misalai daga cikin wasu waƙoƙin baka kan yada mawaƙan ke bayyana tarihin sarakuna da kuma irin ƙalubalai da waƙoƙin gargajiya ke fuskanta a ƙasar Hausa sanadiyar ci gaban zamani da kuma hanyoyin da za a bi wajen magance su

2.0 Bitar Ayyukan a Suka Gabatas

Masana irinsu: Furniss (1996) da Usman (1998) da Abba da Zulyadaini (2000) da Yakubu (2002) da Gusau (2003) da Ahmad (2005) da kuma Muhammed (2011) da Gusau (2023) dawasu masana da dama sun tofa albarkacin bakinsu dangane da tarihin waƙar baka da ƙasar Hausa da ma irin sarakunan ƙasar Hausa. ashe kenan waƙar baka magana ce mai ayyananniyar manufa da ake ajiyewa a ka a kuma rera dab aka bisa wani daidaitaccen tsari.

2.1 Takaitaccen Tarihin Maƙadan Baka a Ƙasar Hausa

2.1.1 Asalin Maƙada

Maƙada a al’ummar Hausa sun samo asali tun zamanin daular gargajiya, inda ake da tsarin sarauta da fadar sarki, wanda ya ƙunshi manyan masu fada a ji, da masu raye-raye da kuma mawaƙa. Maƙadan gargajiya sun kasance ƙungiya ta musamman da ke da hurumin rerawa a lokuta na musamman, musamman a fadar sarki, don yabon sarauta, tuna jarumta, da kuma wanzar da tarihi (Furniss, 1996).

A wasu lokuta, maƙada suna da alaƙa da rukuni ko gandu na masu fasaha, inda sana’ar waka ke bin tsari da ladabi. A Misira da Sudan, masana sun danganta hakan da irin tsarin daular gargajiya inda masu waƙa ke zama kamar 'yan jaridana wancan zamani suna rera waƙa bisa abubuwan da suka faru a zamansu (Usman, 1998).

2.2.2 Matsayinsu a Cikin Al’umma

Maƙadan gargajiya suna da matuƙar daraja a cikin al’ummar Hausa, musamman a daular gargajiya. Ana ɗaukar su a matsayin rumbun tarihi da masu ba da labari. Sannan waƙoƙin suna da tasiri sosai wajen gina tunanin jama’a game da shugabanni da tarihi. Haka kuma, suna taka rawa wajen ƙarfafa gwiwar sarki, ko kuma su zamo masu nasiha da tunatarwa ta hanyar waƙa.

Misali, a cikin gidan sarautana Kano ko Zazzau, ba a fara wani taron sarauta ko yanka sallah ba tare da waƙoƙin maƙada ba. Waƙoƙin nan suna ƙarfafa tsarin sarauta da ɗaukaka sarki tare da Ambato ayyukansa da tarihi (Ahmad, 2005). Wani lokaci ma, makaɗa suna amfani da waƙa wajen fallasa miyagun halaye da kuma faɗakar da al’umma.

2.2.3 Hanyoyin da Suka Gaji Sana’arsu

Sana’ar waƙa yawanci ana gadonta ne ta hanyar iyali. Wannan yana nufin cewa yaro zai taso yana koyo daga mahaifinsa ko wani na kusa da shi da ke sana’ar waƙa. Haka kuma, akwai matakai na horo da koyar da dabarun waƙa, kamar:

· Fara rera baitin yara,

· Koyon Karin magana,

· Koyon yadda ake zaƙulo tarihi daga labarai,

· Da kuma ƙwarewa wajen rera waƙa cikin girmamawa da fasaha.

Misali, a cikin iyalanmawaƙi a ƙasar Hausa ana samun iyalai da ake danganta su da waƙoƙin fada kamar Ɗankwairo da Natambaɗa da Aliyu Dandawo da sauransu da kumaNa-Gari a Kano, ko Iyalin Gogo a Katsina, sun shahara wajen rera waƙoƙin sarauta da suka shafi tarihin sarakuna (Yakubu, 2002).

Wasu kuma sun fara ne a matsayin ‘yan kallo ko masu wasa a wajen bikin sarauta, amma daga bisani suka samu horo, har suka zamo manyan maƙada.

3.0 Rawar da Waƙoƙin Makaɗan Gargajiya ke Takawa Wajen Adanawa da Watsa Tarihin Sarakunan Hausa

Waƙoƙin makaɗan gargajiya na ɗaya daga cikin muhimman hanyoyi na adanawa da watsa tarihin sarakunan Hausa. Makaɗa ba kawai masu nishaɗi ba ne, su masu tarihin baka ne waɗanda ke rayar da abubuwan da suka faru a zamanin sarakuna daban-daban, ta hanyar waƙoƙin yabo, faɗakarwa, da tunatarwa, ta hanyoyi jamar haka:

3.1 Bayyana Nasaba da Salsalar Sarauta

Waƙoƙin makaɗa suna bayani dalla-dalla kan nasaba da salsalar sarakuna, daga wanda suka gāje su, har zuwa tarihin zuriyarsu. Wannan yana taimakawa wajen tabbatar da ingancin mallakar sarauta da asalin ikon mulki. Misali, a cikin waƙar da makaɗan fada ke rerawa a Daura ko Kano, ana Ambato sunayen sarakuna daga tushe, tare da alaƙantasu da shahararrun kakanninsu kamar Bayajidda, wanda ya kafa daular Hausa (Furniss, 1996).

Jagora :Ko can asalin sarauta Daura,

:Tun Kai’ana tun Lamarudu,

:Tung a Magajiya Daurama,

:Har Umarun Bagadaza da Mulka,

:Da Abdu tsohon sarki.

Y?Amshi :Kwana lafiya mai Daura,

:Jikan Abdu gwauron giwa.

(Mamman Shata. Waƙar Sarkin Daura M. Bashar)

Jagora :Ado san Kano ɗan Abdu,

:Jikan Shehu baban Shehu,

:Mai birnin Kano har daji.

(Mamman Shata. Waƙar Sarkin Kano Ado Bayero)

Waɗannan gunduwowin waƙa suna da muhimmanci ƙwarai wajen tabbatar da salsalar sarauta da kuma nasabar sarakuna r tare wanzuwar tarihin sarauta da sarkunan.

3.2 Bayyana Jarumtaka da Ayyukan Sarakuna

Waƙoƙin makaɗa suna rerawa masu ɗauke da jarumtar sarakuna, nasarorinsu a yaƙe-yaƙe, da abubuwan da suka yi wa jama’a. Wannan yana taimakawa al’umma su fahimci irin gudunmawar da Sarki ya bayar a zamaninsa. Waƙoƙin suna bayyana yadda a wasu lokutan sarakuna sukan fuskanci ƙalubalen mulki tare da kawo zaman lafiya da ci gaba (Ahmad, 2005).

Jagora :Mai nasara bai ɗau wargi ba,

:Toya matsafa uban Alkali,

Haɗeja ba a zuwanki da yaƙi,

:kwaj je Haɗeja inda faɗa ne,

:Mu mun san ajali na far mai.

Alh. Mohd Sarkin Tabshin Katsina. Waƙar Sarkin Haɗeja Haruna)

Jagora :Usman mujaddadi ya kawo addini,

:Cikin ƙasag ga shi,

Y?Amshi :Yah hore mu, muka gane hwarilla,

:Sannan mustahabi.

:Sai Musulmai ka ƙwarewa

:Sai albarka ka komawa.

(Abdu Inna Bakura. Waƙar Sarkin Musulmi Abubakar na III)

 

Jagora :Tanƙwafau na Mujaddadi Shehu

Y/Amshi :Ba a jam aka tsoro.

 (Idi Ɗangiwa Zuru. Waƙar Sarkin Zazzau Alh. Shehu Idris)

Waɗannan gunduwowi da ke sama suna nuni da jarunta da kuma halayen sarakunan ƙasar Hausa. sun kuma ƙara tabbatar da rawar da raƙar da mawaƙan baka suke takawa wajen adana tarihin sarakuna da kuma masarautu.

3.3 Yabo da Kwatanta Halayen Sarakuna

Makaɗa suna amfani da kalaman yabo da kwatanta kyawawan halaye na sarakuna kamar adalci, sadaukarwa, hikima da gaskiya. Wannan yakan zama kamar tsarin nuni ga jamaa cewa sarki mai waɗannan halaye ne ya dace da mulki. Waƙoƙin sukan kwatanta sarki da dodanni, zakuna, ko rowan sama don nuna ƙarfin halinsa.

Jagora :Abdullahi shugaban Dabo,

:Imamuddina Dabon Kanoi,

Y/Amshi :Allah dais hi kyauta maka

Jagora :Dattijo mai halin karama

Y/Amshi :Allah dais hi kyauta maka

Jagora :In an yi batun sarakuna gabas,

:In an faɗi Dabo to ina wani.

(Salisu Jankiɗi. Waƙar Sarkin Kano Abdullahi Bayero)

Jagora :Mun taho Zazzau,

Y/Amshi :Ta yi kyau inda sabon sarki,

:Aminu amincinka nak kai ka ka zama sarki.

(Sarkin Tbshin Katsina Alh Mohd. Waƙar Sarkin Zazzau Aminu Mohd)

A waɗannan misalai ma an ga yadda mawaƙan suke yabon sarakuna kan wasu halayensu na kirki. Haka ya nuna yadda ake amfani da waƙa wajen ƙarfafa shugabanci na gari da bayyana bambancin halayen sarakuna.

3.4 Bayyana Canje-canjen Tarihi a Zamaninsu

Waƙoƙin makaɗa na dauke da labarai kan canje-canjen tarihi da suka faru a zamanin sarakuna, kamar zuwan Turawa, juyin siyasa, ƙaddamar da wasu manyan ayyuka, da sauye-sauyen al’adu. Misali, akwai waƙoƙi da suka bayyana lokacin da Turawa suka karɓi iko a Kano da yadda hakan ya shafi sarautar gargajiya (Usman, 1998).

Jagora :Baba baya ga zamanin, zamunna,

:Baicin zamani na Bature,

:Dubi na yamma baban Shehu,

:Yi nan gabas har teku,

:Mamman mulkinka ne ɗan Umaru,

:Baya ga zamanin Turawa.

Y/Amshi :Kwana lafiya mai Daura,

:Jikan Abdu gwauron giwa.

(Mamman Shata. Waƙar Sarkin Daura M. Bashar)

Wannan gunduwa na nuni ƙarara kan asalin ƙasar Daura da sauyin da zamani ya kawo dangane da wanzuwar mulki a ƙasar Daura da kuma irin sauye-sauyen da zamani ya kawo tun kafin zuwan wasu al’ummu ƙaƙsar Hausa.

4.0 Rawar da Waƙoƙin Makaɗan Gargajiya ke Takawa Wajen Bayyana Nasaba da Jaruntakar Sarakunan Hausa

Waƙoƙin makaɗan gargajiya suna taka muhimmiyar rawa wajen wanzar da tarihin sarakuna, musamman ta hanyar yabobayyana nasabajarumtaka, da kuma canje-canje a zamanin mulkinsu. Wannan waƙa ba wai kawai nishaɗi ba ce, illa ma kuwa babban madogara ce ta tarihin al’umma da ke da matuƙar amfani ga masana tarihi da masu adabin baka.

4.1 Bayyana Nasaba da Salsalar Sarauta

Makaɗan gargajiya suna amfani da waƙa wajen bayyana asalin zuriyar sarki, gado da dangantakar mulki daga kaka zuwa jika. Wannan yana taimakawa mutane su gane asalinsu da kuma halaccin sarautar sarki. Misali:

Jagora :Idrisu ya dawo..

Y?Amshi :Ku;;um ana buga mai tambura.

Jagora :Yunusa ya dawo..

Y?Amshi :Ku;;um ana buga mai tambura.

Jagora :Sambo ya dawo..

Y?Amshi :Ku;;um ana buga mai tambura.

Jagora :Jafaru ya dawo..

Y?Amshi :Ku;;um ana buga mai tambura.

Jagora :Kwasau ya dawo..

Y?Amshi :Ku;;um ana buga mai tambura.

Jagora :Aminu ya dawo..

Y?Amshi :Ku;;um ana buga mai tambura.

Jagora :Ga Sidi ya dawo..

Y?Amshi :Ku;;um ana buga mai tambura.

 ………………………..

(Alh. Sa’idu Maidaji Sabon Birni. Waƙar Sarkin Zazzau Shehu Idris)

Wannan gunduwa tana nuni da yadda mawaƙa suke ƙarfafa halaccin sarauta da tushe na mulki ga sarakunan da suke mulki a zamaninsu. Ta hanyar danganta su da kakanninsu da suka mulki a wannan masarauta..

4.2 Bayyana Jarumtaka da Ayyukan Sarakuna

Waɗannan waƙoƙin na ɗauke da bayani kan jarumtar sarakuna a yaƙe-yaƙe, haɓaka kasuwanci, gyaran birane da shimfiɗa zaman lafiya. Misalai:

Jagora :Mijin maza labarinka ya fi zancen rago,

:Ka ji labarin gwani yau ka zo ka iske shin a Abdu,

:Tuwon salla ne maganin mai zari na Abdu..

Y?Amshi :Wandara makaye,

: ‘Yan maza na tsoron karo da shi.

 (Musa Daɓalo Waƙar Sarkin Kano Alu)

Jagora :Daura nik kai in ishe sarki.

Y?Amshi :Mamman Bashar mai hana ƙaeya,

:Dattijo bai son wargi

:Daura ni kai in ishe sarki.

(Alh. Sani Aliyu Ɗandawo. Waƙar Sarkin Daura M. Bashar)

Jagora :Ya wuce raini,

Y?Amshi :Ba a yi mai shi,

:Amadu jikan Garrba sadauki.

 (Musa Ɗanƙwairo. Waƙar Ahmadu Bello Sardauna)

Jagora :Ina mazan suke..

Y?Amshi :Sarkin Gobir ina mazan suke duk sun ƙare.

 (Alh. Sa’idu Maidaji Sabon Birni. Waƙar Sarkin Gobir Muhammadu Bawa)

Waɗannan gunduwowin waƙa suna ɗauke da nuna halaye da jaruntakar sarakunan ƙasar Hausa. Wannan yana tabbatar da cewa sarakuna ba kawai suna zaune ba ne, suna aiki tukuru don kare al’ummarsu da ciyar da al’umma gaba.

4.3 Yabo da Kwatanta Halayen Sarakuna

Waƙoƙi sukan bayyana kirki, adalci, cikar hali da kima da sarki ke da shi. Wannan yana ƙarfafa shugabanni su zama abin koyi, kuma yana ɗaukaka martabar sarauta. Misalai:

Jagora :Sardauna ya yi yayin shi ya wuce

:Shina shuka hairi ƙasa-ƙasa,

Y?Amshi :Ko ya wuce ga madadi nai,

:Muhammadu Bashar ba ya da wargi.

(Alh. Sani Aliyu Ɗandawo. Waƙar Sarkin Daura M. Bashar)

Wannan yana bayyana yadda makaɗa ke amfani da waƙa wajen kwatanta halin sarakuna inda ya kwatanta sarkin Daura Muhammad Bashar da Sardauna domin ya nuna suna halin ƙwarai, ta hanyar yabon nagartattun sarakuna.

4.4 Bayyana Canje-Canjen Tarihi a Zamaninsu

Waƙoƙin baka na ɗauje da canje-canje kan al’amura da suka faru a lokacin zuwan Turawa, sauyin dokoki, ko sababbin tsare-tsaren mulki. Misali:

Jagora :Katsinawa Barebari, Mallawa

:Bakin ɗiyan sarautar Zazzau,

Y?Amshi :uk mai jiran gado,

:Ba zakara yau ƙasag ga in bayanka

 (Musa Ɗanƙwairo. Waƙar Turakin Zazzau Mohd Aminu)

Jagora :Zamanin Mamman na Abashe,

Y?Amshi :Babba da yaro maza da mara,,

:Wajen ilimi duk mun ƙaru.

Jagora :Ga makarantu an yi fiyayyu,

Y?Amshi :Ga siniya firamare na nan,

:Forobishal sakandare na nan.

:Ga makarantun mata na nan

Jagora :Iliminmu yau ya kai ga Kwaleji,

 (Andulrahaman Sarkin Kotson Kano.Waƙar Sarkin Kano Muhammadu Sunusi)

Wannan na nuni da yadda makaɗa ke riƙo da tarihin mulki da zamani da harshe mai sauƙin fahimta. Tare da nuna sauyi da zamani kan haifar a masaurautu.

5.0 Muhimmancin Waƙoƙin Makaɗan Gargajiya Ga Binciken Tarihi

Waƙoƙin makaɗan gargajiya suna da matuƙar muhimmanci a fagen binciken tarihi, musamman a ƙasashe irin naAfirka da ke da dogon tarihin baka. A ƙasar Hausa, makaɗa da waƙokinsu na taka rawa wajen adana tarihi, bayyana abubuwan da suka faru a baya, da kuma samar da mahimman bayanai ga masana tarihi da manazarta ilimi.

5.1 Amfaninsu Ga Masana Tarihi

Waƙoƙin makaɗa na zama tushe mai ƙarfi ga masu binciken tarihi domin suna ƙunshe da bayanai masu mahimmanci da ba a samu a cikin litattafan tarihi. Waƙoƙin suna bayani kan:

a. Tarihin sarauta da nasabar sarakuna.

b. Yaƙe-yaƙe da jarumtar shugabanni.

c. Canje-canjen zamantakewa da siyasa a lokuta daban-daban.

Misali:
Wakar da Mamman Shata ya rera kan Muhammadu Dikko na Katsina tana 
ɗauke da tarihin nadinsa, manufofinsa, da hulɗarsa da Turawan mulkin mallaka:

"Dikko ya taso da hankalin Turawa,
Ya sa Katsina ta samu aski da wanka."

(Mamman Shata. Wa
ƙar Sarkin Katsina Dikko)

Wannan waƙa na bayyana halayen sarki da rawar da ya taka a lokacin mulkin mallaka abin da ke taimakawa mai bincike gane tsarin mulki da sauye-sauyen zamantakewa a lokacin.

5.2 Tasirin Waƙoƙin A IliminTarihi

Waƙoƙin gargajiya sun ba da gudunmawa ta hanyoyi da dama kamar haka:

· Ƙarfafa tarihin baka wanda ke ƙara yawan madogarar bayanai ga bincike.

· Bayar da hangen jama’a dangane da wani shugaba ko wani al’amari – wanda ke sa a ga tarihi daga idon talakawa da mawaƙa.

· Ƙara fahimtar al’adu da addini a zamanin da aka rera wakar.

Misali:
A cikin wa
ƙar Sarkin Gobir, makaɗin ya bayyana yadda sarki ke tafiyar da sha’anin mulki da kuma alaƙa da malamai:

"Gobe Gobirawa za su tuna da Sarki,
Mai kunya da adalci ga malamai."

(Ahmad, 2005)

Wannan na nuni da dangantakar sarauta da addini – wani muhimmin ɓangare na tarihin Hausawa.

6.0 Ƙalubale da Matsalolin Da Ke Fuskantar Waƙoƙin Maƙadan Gargajiya

Duk da muhimmancin waƙoƙin makaɗan gargajiya na adanawa da yaɗa tarihin Hausawa, musamman tarihin sarakuna, suna fuskantar ƙalubale da matsaloli da ke barazana ga ɗorewarsu da tasirinsu a cikina l'umma. Waɗannan matsaloli sun samo asali ne daga canje-canjen zamani, rashin kulawa daga gwamnati da al’umma, da kuma raguwar sha’awar matasa ga ayyukan adabin gargajiya.

6.1 Rashin Adanawa Ta Zamani

Yayin da duniya ke ci gaba da dogaro da fasahar zamani wajen adana ilimi da tarihi, waƙoƙin makaɗa da dama sun rasa tushe saboda rashin adana su ta hanyar zamani kamar:

1 Rikodin na sauti (audio recordings)

2 Rubuce-rubuce cikin litattafai ko dijital (digital)

3 Bidiyo na rayayyun waƙoƙi

Misali:
Wasu daga cikin wa
ƙƙin da aka rera shekaru aru-aru ba a iya samunsu a yau saboda ba a rikoda suba, kuma mawaƙan da suka rera su sun riga mu gidan gaskiya (Furniss, 1996).

6.2 Tasirin Sauyin Zamani da Fasaha

Sauyin al’adu da shigowar salon waƙa ta zamani (hip-hop, pop, da sauransu) ya sa matasa da dama sun daina sha’awar sauraren waƙoƙin gargajiya. Hakan ya haifar da:

· Raguwar masu sauraro da mabiya.

· Ƙarancin girmamawa ga mawaƙan gargajiya.

· Sauya salo da ƙunshewar saƙon tarihi cikin waƙoƙi.

6.3 Raguwa ko Ɓacewar Sana’ar Makaɗa

Yayin da masu kaɗe-laɗe ke mutuwa, ba a samun masu ci gaba da sana’ar. Dalilan sun haɗa da:

· Rashin riba a harkar makaɗa.

· Rashin ɗaukar sana’ar a matsayin aikin yi na gaskiya.

· Rashin tallafi daga gwamnati ko hukumomi.

6.4 Watsuwar Maƙada

A sakamakon rikice-rikicen tsaro da ƙaura daga ƙauyuka zuwa birane, wasu daga cikin mawaƙan da ke ɗauke da waƙoƙin tarihi sun ɓace ko kuma sun bar sana’ar. Wannan yana rage yawan masu laɗe- kaɗe da kuma lalata dangantakar da makaɗa ke da ita da fadar sarauta.

6.5 Rashin Ƙarfafa Harshe da Al’ada

Tare da ƙarancin amfani da harshen Hausa a wasu matakan ilimi da watsa labarai, waƙoƙin da aka rera da salo na harshen gargajiya sun fi wahalar fahimta ga matasa da ba sa jin Hausa da kyau.

Misali:
Matashi a makaranta da ke amfani da Turanci a koyarwa zai fi sha’awar wa
ƙa da aka yi da Turanci fiye da wacce aka yi da tsantsar Hausa ta gargajiya.

7.0 Matakan Da Za a Ɗauka Don Kare Waƙoƙin Gargajiya

Domin tabbatar da ɗorewar waƙoƙin gargajiya da kumat asirinsu a fage na adana tarihin sarakunan Hausa, akwai buƙatar ɗaukan matakai na gaggawa da ts are-tsare na dogon lokaci. Wannan yana da muhimmanci don kare al'adun mu daga ɓacewa a sakamakon sauye-sauyen zamani da rashin kulawa. A nan za mu tattauna wasu daga cikin muhimman matakai da za a iya ɗauka:

7.1 Gina Cibiyoyin Adana Tarihi kan Adabin Baka

Ƙirƙirar cibiyoyi na adana ayyukan adabin baka (oral archiɓes) a manyan jami’o’i da cibiyoyin nazarin harshe da al’ada zai taimaka matuƙa. Wadannan cibiyoyi za su tattara, riko da, da adana waƙoƙin ta hanyoyin zamani kamar:

7.2 Ƙarfafa Bincike da Rubuce-Rubuce

Masana ilimi, dalibai, da marubuta su kasance masu gudanar da bincike kan waƙoƙin da rawar da suke takawa a tarihin Hausa. Akwai bukatar:

· Rubuta digiri (BA, MA, PhD) a kan mawaƙa da waƙoƙinsu

· Fitar da kundin rubuce-rubuce na mawaƙa

· Buga littattafai da mujallu a kan adabin makaɗa

7.3 Amfani da Fasahar ZamaniWajen Watsa Waƙoƙin

Fasahar zamani na iya taimakawa wajen yaɗa waƙoƙin gargajiya zuwa duniya baki ɗaya. Hanyoyin sun haɗa da:

· Ƙirƙirar tashoshin YouTube da podcasts na waƙoƙin baka

· Ƙirƙirar manhajojin waya (apps) na karanta ko sauraron waƙoƙin mawaƙa

· Tura waƙoƙin zuwa bankunan bayanai na UNESCO ko Spotify

Misali:
Wataman haja a waya da ke 
ɗauke da waƙoƙinAlhaji Mamman Shata za ta ba da dammar matasa su san tarihin Hausa ta hanyar sauraro.

7.4 Shirya Gasar Makɗa da Horaswa Ga Matasa

Gwamnati da ƙungiyoyi na al’adu su shirya gasar mawaƙa da tarurrukan horaswa don jan hankalin matasa. A cikin irin wannan tsari:

· Za a ƙarfafa matasa su koyi waƙoƙin gargajiya

· Za a ba da lada da kyaututtuka ga gwanaye

· Za a kafa kwamitocin kula da mawaƙa a matakin ƙasa da jihohi

7.5 Ƙarfafa Hulɗar Makaɗa da MasanaTarihi

Masu kaɗe-kaɗe su riƙa hulɗa kai tsaye da masana tarihi, domin su tabbatar da sahihancin bayanan tarihi da suke fitarwa. Wannan zai taimaka wajen:

· Kyakkyawan ingancin waƙoƙi da bayani

· Rikodin waƙoƙin da aka tantance

· Rubuce da fassara waƙoƙin zuwa harsunan duniya

8.0 Kammalawa

Wannan bincike ya bayyana yadda waƙoƙin gargajiya ke taka muhimmiyar rawa wajen adana da wanzar da tarihin sarakunan Hausa. An fahimci cewa makaɗan ba wai masu nishaɗantarwa kaɗai ba ne, har ma su ne masu rike da nauyin tarihin al’umma da sarautar gargajiya ta hanyar waƙa. A cikin waƙoƙinsu, suna bayyana asalinsu, nasabar sarauta, jarumtaka, halaye, da kuma sauye-sauyen da suka faru a zamanin mulkin sarakuna daban-daban. Irin waɗannan waƙoƙi na taimakawa wajen fahimtar tsarin mulki da zamantakewa na Hausawa tun kafin zuwan Turawa da bayan haka. Binciken ya kuma nuna yadda waƙoƙin ke taimakawa ga masu binciken tarihi, musamman wajen samar da sahihan bayanai da ke ginuwa a kan ƙwarewa da shaida kai tsaye. Amma duk da wannan muhimmanci, waƙoƙin suna fuskantar barazanar ɓacewa saboda rashin adanawa da sauye-sauyen zamani da fasaha.


 

Manazarta

Abba, M. da Zulyadaini, B. (2000) Nazari Kan Waƙar Baka Ta Hausa: Gaskiya Corporation Ltd.

Ahmad, I. (2005). The Role of Oral Poetry in the Preserɓation of Hausa History. Zaria: Ahmadu Bello University Press.

Dangana, A. A. (1991). Maƙadan Hausa da GudummawarsugaTarihi da Al’adu. Kaduna: ABU Press.

Furniss, G. (1996). Poetry, Prose and Culture in Hausa. Edinburgh: Edinburgh University Press.

Gusau, S. M. (2023). Jagoran Nazarin Waƙar Baka. Kano: WTPress: printing & Publishing Ltd.

Gusau, S. M. (2007). Diwanin Waƙoƙin Baka. Kano: Century Reseach Publishing.

Gusau, S. M. (2008). “Waƙoƙin Baka na Ƙasar Hausa: Yanaye-Yanayensu da Sigoginsu. Kaduna: Benchmark Publishers Limited.

Ibrahim, M. A. (2011). GudunmawarMaƙadaWajen Adana Tarihin Hausa. Kano: Murtala Muhammad Library Press.

Paden, J. N. (1973). Religion and Political Culture in Kano. University of California Press.

Usman, Y. B. (1998). The Transformation of Katsina: 1400–1883. Zaria: Gaskiya Corporation.

Yahaya, I. Y. Sani, M. A. Z. Gusau, S. M. ‘Yar’aduwa, T. M. (2007). Darrusan Hausa don manyan makarantun sakadare 2. Ibadan:University Press limited.

Yakubu, M. (2002). Oral Traditions in Northern Nigeria: A Study of Hausa Praise Poetry. Kano: Bayero University Press.

Yusuf, B. (2010). Adabin Baka a Matsayin Makamin Ilimi da Al’ada. Kano: Benchmark Publishers.

 Yobe Journal of Language, Literature and Culture (YOJOLLAC)