Ticker

6/recent/ticker-posts

Kwatancin Shugabanci A Wasu Sana’o’in Hausawa Jiya Da Yau

Citation: Nasir Usman NASIR, Professor Balarabe ZULYADAINI & Dr. Jamilu ABDULLAHI (2025). Kwatancin Shugabanci A Wasu Sana’o’in Hausawa Jiya Da Yau. Yobe Journal of Language, Literature and Culture (YOJOLLAC), Vol. 13, Number 1. Department of African Languages and Linguistics, Yobe State University, Damaturu, Nigeria. ISSN 2449-0660

KWATANCIN SHUGABANCI A WASU SANA’O’IN HAUSAWA JIYA DA YAU

NA

NASIR USMAN NASIR

PROFESSOR BALARABE ZULYADAINI

DR. JAMILU ABDULLAHI

Tsakure

Wannan takarda ta yi duba ne a kan kamanci da bambance-bambancen da ke tsakanin tsarin shugabanci a wasu sana’o’in Hausawa a gargajiyance da zamanance. Muhimmancin da shugabanci yake da shi ya sa kusan dukkan al’amuran da Hausawa suke gudanarwa, kama tun daga zamantakewa har ya gangaro kan sana’o’i, sai an tarar akwai shugabanci a ciki. Yayin gudanar da wannan bincike, an tattauna da masu ruwa da tsaki kama daga kan shugabanni da waɗanda ake jagoranta domin su rabe mana zare da abawa a kan yadda tsarin shugabancin yake a jiya da yau. Baya ga nan, an gudanar da karance-karancen muƙalu da kundayen bincike da kuma bugaggun litattafai. Bincike ya yi amfani da ra’in Shugabancin Sauyi (Transformational Leadership Theory) wanda James Macgregor Burns ya assasa a shekarar 1978. A ƙarshe, takardar ta gano cewa akwai kamanceceniya da kuma bambance-bambance daidai gwargwado.

Fitilun Kalmomi: Kwatanci, Shugabanci, Sana’a, Hausawa

1.0 Gabatarwa   

Shugabanci yana nufin jagorantar al’umma ta fuskar mulki ko madafan iko bayan mabiya sun tabbatar da cewa ga wanda suke so ya jagorance su. Shugaba shi ne mutumin da yake fara bin doka da oda, daga nan sai ya tabbatar da cewa kowa ya bi ita wannan dokar kamar yadda aka tsara. Al’ummar Hausawa ba a bar su a baya ba kan wannan tafarki na tsarin shugabanci. Wannan ya yi daidai da karin maganar nan ta Bahaushe da yake cewa, “Bin na gaba, bin Allah”. Wannan ya nuna ke nan tsarin shugabanci ba sabon abu ba ne a wurin Bahaushe. Asali ma, tsarin shugabanci ya samo tushe ne bisa dalilin tsaro da kyautata zamantakewar jama’a. Haka, shi Bahaushe mutum ne wanda yake tafiyar da harkokinsa na shugabanci tun daga gida. Misali, yanayin zaman iyali da yake yi irin na gandu, inda ake samun kakanni da iyaye da ‘ya’ya tare da matansu a gida ɗaya, za a tarar akwai shugabanci. Za a iya cewa tsarin shugabanci ya shiga jini da tsoka na Bahaushe, musamman idan aka lura da yadda yake tafiyar da abubuwansa tare da shawarwarin na gaba da shi. Idan aka koma ɓangaren sana’o’in Hausawa kamar Farauta da Noma da Ƙira da Fawa da Wanzanci da makamantansu, za a tarar da cewa ba haka nan suke kara-zube ba. Su ma suna da tsari na shugabanci ba don komai ba, sai don a gudu tare a tsira tare. Waɗannan masu jagorancin suna tafiyar da ayyukansu kasancewar suna samun haɗin kai da taimakon juna da samun kyakkyawar fahimta a tsakaninsu, musamman masu sana’a iri ɗaya. Irin wannan tunani, ya yi matuƙar tasiri a zukatan Hausawa waɗanda suke gudanar da wasu ayyukansu na samun taro da sisi domin dogaro da kai.

Idan kiɗa ya sauya, to, ya zama wajibi rawa ma ta sauya. A yau sai ga shi an wayi gari fasalin shugabanci a sana’o’in Hausawa yana neman ya sauya sakamakon cuɗanyar al’ummar Hausawa da wani tunani na daban, musamman tasirin siyasar zamani. A sakamakon wannan cuɗanya da siyasar zamani, al’ummar Hausawa sun ƙaru da wata dabara musamman a wannnan ɓangare na tsarin shugabanci, yayin da ta wata fuskar ana iya cewa tsarin shugabancin asali ya samu koma-baya a kan yadda yake tun fil’azal. A wannan lokaci da muke ciki, salon yadda ake tafiyar da shugabanci a wasu sana’o’in Hausawa ya sauya ya koma irin tsari na siyasa, inda za a tarar a kowacce sana’a akwai Shugaba (Chairman or President) da Mataimakinsa da Sakatare da Ma’aji da dai sauran muƙamai waɗanda ba haka suke a gargajiyance ba. Wannan ya sa aka ga ya dace a rabe zare da abawa kan yadda tsarin shugabancin yake a jiya da yau, tare da nuna bambance-bambance da kuma kamanceceniyar da ke tsakaninsu ta hanyar fito da su fili a ga yadda suke a kuma fahimce su.

2.1 Ma’anar Shugabanci

Masana da dama sun tofa albarkacin bakinsu gwargwadon fahimtarsu a kan shugabanci. Daga cikinsu akwai:

Alhassan da wasu (1982, sh 66) suna ganin, “Shugabanci shi ne yi wa mutane jagora da jan ragama a harkokinsu na zaman tare”.

C.N.H.N (2006, sh 415) ya bayyana shugabanci da cewa, “Yana nufin jan ragamar jama’a ko wata ƙungiya, wato daidai da jagoranci”.

Sallau (2010, sh 7) yana da ra’ayin cewa, “Shugabanci yana nufin yi wa al’umma jagora a halin zamantakewarsu na yau da kullum”.

Bunza (2014,sh3) ya kawo ma’anar shugabanci guda uku kamar haka: “Shugabanci shi ne jagorar jama’a wanda suka aminta da shi wajen jiɓantar al’amuransu na siyasa, zamantakewa da addini”. Ya ƙara da cewa, “Shugabanci shi ne tafiyar da al’amuran jama’a bisa ga yardarsu da amincewarsa ga dokokin da suka yi imani da su”. A ƙarshe ya ce, “Shugabanci shi ne wakiltar mutane ga abin da suka miƙa wuya gare shi bisa ga tafarkin da zai ciyar da su gaba ga manufofinsu da daidaita tunaninsu”.

Baba da wasu (2024, sh214) sun ce; “Shugabanci wani muhimmin aiki ne da shugaba kan yi domin yi wa jama’a adalci da zame musu garkuwa da yi musu hidima cikin dukkannin sha’aninsu na rayuwa”.

A ra’ayin mai bincike kuwa, shugabanci shi ne jagorantar al’umma ta fuskar mulki ko madafan iko bayan mabiya sun tabbatar da cewa ga wanda suke so ya jagorance su ko ya wakilce su domin samun ci gaba mai amfani.

3.1 Ma’anar Sana’a

Masana daban-daban kan al’ada sun kawo ra’ayoyinsu a game da ma’anar sana’a, irin su, Ibrahim (1981) da Yahaya da wasu (1992) da Lawan (2019) da Nuhu (2020) sun raja’a a kan cewa sana’a, “Tsari ne na hikima da ake sarrafa albarkatun ƙasa da sauran ni’imomin da Allah ya yi wa ɗan’adam domin samar da muhimman abubuwan buƙata da rarraba su ga jama’a masu buƙata.

Sana’a ita ce, “Wani tafarkin rayuwa da mutum kan ɗauka ya bi shi domin samun abin biyan buƙatunsa na yau da gobe” (Auta, 2006, sh.195).

A wani ra’ayin, sana’a na nufin, “Aikin da mutum yake yi don samun abinci” (CNHN, 2006, sh. 387).

A ra’ayin Yakasai (2020, sh. 118) yana ganin, “Sana’a hanya ce ta neman ɗan abin dogaro da kai, kuma shi Bahaushe a al’adance ko kaɗan bai amince da mutum ya zama cima-kwance ko ɗan zaman-kashe-wando ba.”

Duba da waɗannan ma’anoni da aka ji daga bakin masana, tunanin mai bincike ya fahimci ba komai ake nufi da sana’a ba, sai duk wata hanya da ɗan’adam yake amfani da ita domin ya samu abin kashewa da nufin ya rufawa kansa da iyalansa da ‘yan’uwansa asiri.

3.2 Mafarin Sarauta ko Shugabanci a Wurin Hausawa

An samu ra’ayoyin masana daban-daban dangane da asali ko mafarin sarauta a ƙasar Hausa. Akwai wasu yankin masana da ke ganin cewa sarauta ta samo asali ne daga jagorancin wurin bauta. Mafi yawa waɗanda suka yi jagoranci sukan kasance su ne shugabanni a wurin bauta. Misali a wurin bautar Tsumburbura wanda aka yi a kan dutsen Dala da ke Kano, a ƙarƙashin jagorancin Barbushe. Barbushe ne ke hawa kan dutsen Dala, ya je bukkar Tsumburbura sannan ya gangaro ana masa kirari, sannan ya faɗa wa mutane abin da zai faru a wannan shekara. Baya ga nan, a wajen bautar ‘Madara’, wanda aka gudanar a dutsen Kufaina da madarkaci a Zazzau, shugaban wannan bauta shi ne kamar sarki. Idan aka koma Katsina a wajen bautar Doguwa, da Durbi ta Kusheyi, a can ma shugaban bautar shi ne kamar sarki. Ƙasar Gobir su ma sun yi bautar ‘Inna’, shugaban shi ne tamkar sarki. Akwai waɗanda suke da ra’ayin cewa, sarauta ta samo asali ne daga sana’a. Duk wani wanda ya shahara a sana’arsa ko wajen wata harka wadda ta shafi sana’a, shi ne shugaba ko sarki. Masu wannan ra’ayi suna ganin daga wajen sarakunan sana’o’i aka samo asalin sarauta. Wasu kuwa suna ganin jarumta ita ce asalin sarauta. Masu wannan ra’ayi sun kafa hujja ne da cewa,duk wanda ya gagara a fagen farauta ko yaƙi, sai a naɗa shi mai dawa, ko sarkin dawa da sarkin baka. Wanda ya zama jarumi shi ma ana masa sarauta. Kamar a Katsina masu takarar sarauta kan yi kokuwa a tsakaninsu. Duk wanda aka kayar zai yanke kansa, sannan ya zama sarki (Sa’adu, 2020, sh12).

Sarauta a ƙasar Hausa na da wasu tsare-tsare, duk da yake ba a rasa ɗan saɓani ko bambance-bambance kaɗan dangane da yadda ake kiransu a wasu yankuna. Ga yadda tsarin sarauta take a ƙasar Hausa kamar haka; Sarki da Waziri da Galadima da Madaki da Chiroma da Yarima da Barde ko Jarma ko Magayaƙi da Sarkin Malamai ko Ɗan Masani ko Magajin Malam da sauransu. Haka kuma akwai bayi da barorin Sarki da suka haɗa da Shantali da Wawan Sarki da Shamaki da Zagi da makamantansu.

Duba da waɗannan bayanai da suka gabata, ake hasashen shugabanci a sana’o’in Hausawa shi ma ya bi sahun yadda ake gudanar da shugabanci a ƙasar Hausa. Shi kuma Sarki ko Uban Gari a matsayinsa na shugaba, kuma duk wani ɗan garin a ƙarƙashinsa yake. Hakan ya sa ya yi ruwa ya yi tsaki (Sarki) ya shiga sha’anin naɗa shugabanni a kusan dukkannin sana’o’in Hausawa na gargajiya.

4.1 Bambance-Bambance da ke Tsakanin Shugabanci a Wasu Sana’o’in Hausawa Jiya da Yau

Al’ummar Hausawa suna gudanar da sana’o’insu da tsari na shugabanci tun fil’azal kafin zamani ya yi tasiri a kan wannan tsari nasu. Kodayake, duk ko da zamani ya yi tasiri a kan tsarin shugabancinsu na gargajiya hakan bai sa sun yi watsi da yadda suke gudanar da shugabncinsu a sana’o’insu na asali ba. Sai dai wasu sun rungume su duka biyu suna gudanar da su a lokaci guda. Amma duk da haka, akwai wasu ‘yan bambance-bambance da ke tsakanin shugabanci a sana’o’in Hausawa na gargajiya da na zamani. An fasalta bambance-bambancen ta fuskoki mabambanta da suka haɗa da bambanci ta fuskar tsarin shugabanci da bambanci ta fuskar mai naɗa shugaba da bambanci ta fuskar matakan zama shugaba da bambanci ta fuskar adadin muƙamai da bambanci ta fuskar sunayen muƙamai da ayyukansu, da bambanci ta fuskar wa’adi da kuma bambanci ta fuskar dangantaka da Sarakunan Ƙasa da Hukumomin Gwamnati (Hira da sarkin askan Wudil, kuma shugaban ƙungiyar masu sana’o’in Hausawa na gargajiya, Sadiku Magaji).

4.1.1 Bambanci Ta Fuskar Tsarin Shugabanci

Tsarin shugabancin sana’o’in Hausawa a gargajiyace, yana tafiya daidai da yadda ake gudanar da jagoranci a ƙasar Hausa a wancan lokaci, in da ake tarar da sarki a matsayin jigon da ke gudanar da mulki a ƙasarsa. Su ma masu gudanar da sana’o’i irin wannan tsarin suka kwaikwaya domin ganin sun samar da tsarin shugabanci a sana’o’insu. Wannan ya sa suka bi tsarin sarautun Hausawa a matsayin su ne shugabanni a sana’o’insu, wato masu jan ragamar jagorantar masu sana’a iri ɗaya. Daga cikin waɗannan shugabanni akwai Sarki da Waziri da Madaki da sauransu. A ɗaya ɓangaren kuwa, duba da cewa an samu siyasar zamani ta yi matuƙar tasiri a kusan dukkannin al’amuran rayuwa ta yau da kullum, ciki har da tsarin shugabanci a sana’o’in Hausawa na zamani, wannan ya sa a yau aka koma amfani da tsarin siyasa inda ake samun ‘Chairman ko President’ a matsayin shugaba da sauran muƙamai da suka haɗa da Sakatare da P.R.O da Ma’aji da makamantansu.

4.1.2 Bambanci Ta Fuskar Mai Naɗa Shugaba

Bisa ga tsari, Uban Gari ko Hakimi ko kuma Sarki shi yake da alhakin naɗa shugabanni a sana’o’in Hausawa a gargajiyance. Ba haka kawai sarki yake naɗa sarkin wata sana’a ba, sai an tabbatar da ya cika wasu sharuɗɗa na zama shugaba, ciki har da tabbatar da cewa ɗan gado ne. A taƙaice dai kamar yadda aka faɗi a sama, Sarki ko Hakimi ko kuma Uban Gari shi yake da alhakin naɗa sarkin kowacce sana’a da ta yi fice a ƙasar Hausa. Saɓanin yadda abin yake a yanzu, lokacin da ‘ya’yan ƙungiya da kansu suke gudanar da zaɓensu a tsakaninsu tare da sa idon hukuma domin tabbatar da an gudanar da zaɓen cikin aminci.

4.1.3 Bambanci Ta Fuskar Matakan Zama Shugaba

Kafin ka zama shugaba ko sarki a wata sana’a a yadda fasalin shugabanci a sana’o’in Hausawa yake a gargajiyance, galibi sai an tabbatar da wasu matakai kamar haka:

i.Abu na farko sai ya kasance gadon sarautar ya yi daga iyaye da kakanni

ii.Sai ya zama shahararre a sha’anin sana’ar da yake gudanarwa

iii.Ya kasance ya san asirai a abin da ya shafi sana’arsa. Misali, sarkin ruwa ya kasance buwayayye ne a sha’anin ruwa, sarkin aska ya kasance ya san asirrai na magunguna da dai sauran sana’o’in Hausawa.

iv.Ya zama mai ladabi da biyayya ne ga Sarkin gari ko Uban gari ko kuma Hakimi.

Idan aka koma kan shugabanci a sana’o’in Hausawa na zamani kuwa, za a tarar abin ya sha bamban. Domin kuwa a nasu tsarin zaɓe ake gudanarwa bayan masu son kujerar sun nuna sha’awarsu. Kowane ɗan takara zai bayyana manufofinsa, su kuma waɗanda za a jagoranta sai su yi nazari su zaɓi wanda suke ganin ya fi dacewa da ya jagorance su. Ana iya naɗa wanda jama’a suke so a matsayin shugabansu, musamman idan aka fahimci cewa zaɓen zai iya haddasa ruɗani da rashin kwanciyar hankali. Matakan da ake bi kafin mutum ya tsaya takara bai wuce abubuwa kamar haka ba:

i.Ƙayyade adadin wasu ‘yan shekaru a cikin ƙungiya kafin yin takara

ii.Tabbatar da wanda zai yi takara yana da ilimin boko, musamman kujerar Shugaba da Sakatare da Ma’aji.

iii.Wanda ba shi da tabo na mummunar abu.

4.1.4 Bambanci Ta Fuskar Adadin Muƙamai

A gargajiyance, galibi shugaba ɗaya Sarkin gari yake naɗawa a matsayin Sarkin wata sana’a ko masana’anta a tsarin shugabancin sana’o’in Hausawa. Kodayake, Gummi (2018) ya nuna cewa a ƙasar Kabi akwai wasu sarautun ruwa da sarkin gari ke naɗawa saboda muhimmancin muƙaman. Misali, Homa da Magajin Ɗankanawa da Maƙawashe da sauransu. Sai dai shi wannan Sarkin yana da damar ya naɗa waɗanda zai yi aiki tare da su domin su taimaka masa wajen ganin ya sauke nauyin da aka ɗora masa. Ke nan, a tsarin shugabancin sana’o’in gargajiya matsayin da aka sani guda ɗaya ne wato ‘Sarki’, kuma kowace sana’a da nata. Yayin da a gefe guda, adadin muƙaman da ake da su a tsarin shugabancin sana’o’in Hausawa a yau sun kai a ƙalla guda shida da suka haɗa da Shugaba (Chairman ko President) da Mataimakin Shugaba (Ɓice Chairman) da Magatakarda (Sakatare) da Mai Hulɗa da Jama’a (P.R.O) da Ma’aji (Treasurer) da kuma Jami’i Mai Kula da Walwalar Jama’a (Welfare).

4.1.5 Bambanci Ta Fuskar Sunayen Muƙamai da Ayyukansu

Akwai bambance-bambance da ake samu ta fuskar sunayen muƙamai a tsarin shugabancin sana’o’in Hausawa na jiya da yau. Misali, shugabanci a sana’o’in Hausawa a gargajiyance Sarki kaɗai aka sani, wani lokaci akan naɗa waziri. waɗanna muƙamai Uban gari ko Hakimi ko Sarkin gari ne yake naɗa su. Amma shi wannan sarki da ka naɗa yana da damar ya naɗa masu taya shi gudanar da ayyukansa. Sukan rarraba muƙamai da dama, wasu sukan zama daga cikin ‘ya’yan sarki wasu kuma daga waje. Baya ga nan, kowace kujera tana da aikin da ya keɓanta a kanta. Hakan shi ne yake ba su damar gudanar da ayyukansu cikin sauƙi ba tare da wata damuwa ko matsala ta kunno ba. Waɗannan muƙamai sun haɗa da Sarki da Waziri da Yarima da Chiroma da Madaki da Wawan sarki da Zagi da Muƙaddas da makamantansu. Ga yadda fasalin ayyukansu yake kamar haka:

i.Sarki: Sarki shi ne shugaba a gari gaba ɗaya ko a wani abu na musamman da aka ware kamar wata sana’a, kuma mai ƙarfin sawa a yi ko a bari. Misali a ɓangaren sana’o’in Hausawa ana da sarkin fawa da mai dawa ko sarkin dawa ko mai baka. Haka, akwai sarkin ruwa da sarkin ƙira da sarkin aska da dai sauransu. Sarki ne ke da ikon naɗa duk wani muƙami da kansa. Bayan haka shi yake karɓarwa mai rauni hakkinsa.

ii.Waziri: Waziri shi ne mataimaki ga sarki, shi yake gudanar da ayyukan da suka rataya a wuyan sarki musamman idan baya gari ko wani abu ya shige masa gaba. Su ma sarakunan sana’o’in Hausawa suna naɗa Waziri a matsayin mataimakinsu, yakan wakilce su a wurare da dama musamman idan sarki ba ya nan.

iii.Yarima: Yarima sarauta ce da ake yi wa ɗan sarki, sannan ana alaƙanta wannan sarauta da jin daɗi, shi ya sa akan ce a bi yarima a sha kiɗa, ko a bi yarima a sha miya. Sarakunan sana’o’in Hausa kan naɗa ‘ya’yansu da wannan suna ‘Yarima’.

iv.Chiroma: Chiroma kuwa sarauta ce da ake yi wa ‘ya’yan sarki. Sarautar Chiroma tamkar na Yarima take a wurin Sarakunan sana’o’in Hausawa. Suna ne da suke kiran ɗansu da shi. Shi ne yake bin bayan Yarima.

v.Madaki: Wata muhimiyar sarauta ce a Kano, a wasu wurarern ana kiranta da Barde ko Jarmai ko Gummi ko Uban dawaki ko Ƙaura ko Goje ko Kacalla ko Kaigama ko Kagu. Aikinsa shi ne jagorancin mayaƙa lokacin yaƙi. Shugabannin sana’o’in Hausawa suna naɗa irin wannan muƙami a tsarin shugabancinsu. Wasu daga cikin sarakunan sana’o’in Hausawa kan naɗa irin waɗannan muƙami musamman Sarkin Dawa da Sarkin Aska.

vi.Shamaki: Wannan shi ne ke kula da sarki wajen abubuwan da suka shafi harkokin gida.

vii.Zagi: Zagi shi yake yi wa sarki zagi, watau ya wuce gaba duk inda sarki za shi. Wasu Sarakunan sana’o’in Hausawa suna naɗa wannan muƙami domin su na wuce musu gaba a duk inda zasu je. Misali Sarkin Aska da Sarkin Fawa suna naɗa wannan muƙami.

viii.Wawan Sarki: Wawan sarki shi yake bai wa sarki dariya, ko kuma ya sanya shi cikin nishaɗi da kuma ɗebe masa kewa, musamman idan yana cikin ɓacin rai. A nan, kusan dukkan sarakunan sana’o’in Hausawa na da wannan muƙami, domin mai wannan matsayi a kodayaushe tare yake da sarki yana ba shu nishaɗi.

ɗaya ɓangaren kuwa, sunayen muƙaman da ake da su a tsarin shugabancin sana’o’in Hausawa na zamani ya bambanta da na gargajiya. Baya ga nan, ayyukansu ya bambanta da na takwarorinsu na gargajiya. Waɗannan muƙamai mafi yawanci zaɓensu ake yi ba shugaban ba ne yake ɗora su kamar na tsarin gargajiya. Ire-iren muƙaman sun haɗa da Shugaba (Chairman/President) da Mataimakin shugaba (Ɓice Chairman ko ɓice President) da Magatakarda (Secretary) da Mai Hulɗa da Jama’a (Public Relation Oficcer (P.R.O) da Ma’aji (Treaturer) da Mai Kula da Walwalar Jama’a (Welfare Officer) da makamantansu. Ga yadda ayyukan nasu yake kamar haka:

i.Shugaba (Chairman): Shugaba shi ne jagora ko ja gaba wanda ya ɗauki nauyin jan ragamar jama’a ko wata ƙungiya. Wannan shugaba shi ke jagorantar ƙungiyar kasuwancinsu a wajen kasuwar. Haka, shi ne wanda yake kwantar da duk wata matsala da za ta taso. Haka kuma shi ke jagorantar duk wani taro da za a yi na ƙungiyarsu da dai sauransu.

ii. Mataimakin Shugaba (Ɓice chairman): Mataimakin Shugaba kamar Shugaba yake. Shi ne yake wakiltar shugaba idan ba ya nan, a wasu lokutan shi ne yake jagorantar tarurrukan cikin gida tare da warware wasu matsalolin da suka taso.

iii. Magatakarda (Secretary): Sakatare shi ne mutumin da yake rubuta abubuwan da aka tattauna a wajen taro. Misali a ofishin gudanar da harkokin mulki musamman na hukuma ko siyasa ko wata ƙungiya. A taƙaice, sakatare shi ke kula da shirya taro da kuma rubuta abubuwan da aka tattauna domin ajiye tarihi.

iv.Ma’aji (Treasurer): Ma’aji shi ne mutumin da yake kula da asusu ko kuɗin ƙungiya da wasu kadarori da ƙungiya ta mallaka.

v. Mai Hulɗa Da Jama’a (P.R.O): Mai hulɗa da jama’a (P.R.O) shi ne mutumin da yake sauraren duk wasu matsalolin da suka shafi al’ummar da ake jagoranta, shi kuma zai isar da saƙon al’umma ga shugabansu. Haka kuma, idan wain abu sabo ya taso shugaba zai sanar wa mai hulɗa da jama’a (P.R.O) domin ya isar wa al’umar da suke jagoranta.

vi.Mai Lura Da Shige Da Ficen Ma’aikata Da Kuɗaɗe Da Kadarori (Auditor): Wannan shi ne wanda yake gudanar da aikinsa kan shugabannin ƙungiya, musamman kan yadda ake fitar da kuɗi da yadda ake kashe su tare da tabbatar da kadarorin ƙungiya ba su taɓu daga wurin shugabannin ba.

vii.Walwala da jindaɗin jama’a (Welfare): Wannan ya shafi kula ko lura da jama’a yayin da aka zo wani taro ta hanyar ba su wasu abubuwa da za su saka su jin daɗi da annushuwa, kamar ba su ruwa da lemo da makamantansu. Yana kuma kula da wurin kwanan baƙi waɗanda aka gayyata don gudanar da wani taro. Haka zalika, idan ƙungiya (‘yan ƙungiya) suka tafi wani wuri, shi ne zai sama musu masauƙi mai kyau. Mai kula da wannan sashe ana kiransa da mai kula da walwala ko jin daɗin jama’a.

viii.Shugaban Masu Tsaro (Chief security): Wannan kuwa shi ne wanda yake kula da masana’anta da kadarorin masana’antu ko shaguna. Mai wannan aiki ana kiransa da babban mai kula da harkokin tsaro. Ƙarƙashinsa akwai masu taya shi aiki wanda su suke gadin wannan masana’antu domin gudun sata daga ɓata-gari.

4.1.6 Bambanci Ta Fuskar Wa’adi

Ba a iyakance wa’adin shugabannin a sana’o’in Hausawa a gargajiyace har sai Shugaban ya mutu ko ya yi wa Sarki ko Hakimi ko Uban Gari wani gagarumin laifi ba, ko kuma da kansa ya nuna rashin sha’awar ci gaba da shugabanci. A gefe guda, shugabanci a sana’o’in Hausawa na zamani kuma akwai wa’adin da aka ɗibar wa shugabanni tun daga lokacin da aka gudanar da zaɓe ko aka naɗa su. Mafi yawanci wa’adin da ake ɗibar wa shugabanni ba ya wuce shekara huɗu ko ma ƙasa da haka. Da zarar wa’adin ya cika za a sake gudanar da wani sabon zaɓe ko kuma a naɗa sababbin shugabannin da za su cigaba da jagorantar masana’antar ko kuma ƙungiyar.

4.1.7 Bambanci Ta Fuskar Dangantaka da Sarakunan Ƙasa da Hukumomin Gwamnati

Kafin a samu wayewar siyasar zamani a ƙasar Hausa, tsarin shugabancinsu yana tafiya ne bisa tsari na sarauta. Wannan ya sa shugabannin sana’o’in Hausawa na gargajiya suka fi alaƙa ko dangantaka da Sarki ko Uban Gari. Duba da cewa Sarki ko Uban gari a matsayinsa na Shugaba, kuma duk wani ɗangari a ƙarƙashinsa yake. Hakan ya sa ya yi ruwa ya (Sarki) yi tsaki ya shiga sha’anin naɗa shugabanni a kusan dukkannin sana’o’in Hausawa na gargajiya. Haka kuma, shi ne yake da ikon sauke duk wani shugaba na wata sana’a idan aka tabbatar ba ya gudanar da mulkinsa yadda ya kamata ko aka same shi da laifin raina masarauta. Kuma su waɗannan shugabanni wurin Sarkin gari suke kai kukansu idan wata matsala ta taso. Ashe ke nan, wannan ya nuna ɓaro-ɓaro ba ƙaramar dangantaka ba ce ke tsakanin shugabannin sana’o’in Hausawa na jiya da sarautun ƙasar Hausa. A taƙaice tsarin shugabancin sana’o’in gargajiya ba su da wata dangantaka ta kai-tsaye da gwamnati sai dai da sarakuna ko masarautu.

A gefe guda kuwa, tsarin shugabanci a sana’o’in Hausawa a yau ba shi da wata dangantaka ta kai-tsaye da masarautu. Sun fi dangantaka da hukumomin gwamnati, domin kuwa kafin su kafa ƙungiya ma sai sun yi rajista da hukumar gwamnati. Sannan duk wani motsinsu gwamnati tana sani (Hira da shugaban masu sana’ar Arkomi, Alhaji Husaini).

4.2 Kamancin Tsarin Shugabanci a Wasu Sana’o’in Hausawa Jiya da Yau

Ko shakka babu, akwai kamanceceniya a tsarin shugabanci a sana’o’in Hausawa jiya da yau. Ana iya karkasa kamancin ta ɓangarori kamar haka:

4.2.1 Kamanci ta Fuskar Manufa

Tsarin shugabancin a sana’o’in Hausawa na jiya da yau ana iya cewa manufarsu ɗaya ce. domin kuwa alaƙa ko dangantakar da ke tsakaninsu bai wuce a ce dukansu jagorantar al’umma masu sana’a iri ɗaya ne suke yi ba. Haka kuma, manufofinsu duka ɗaya ne wato su kasance masu murya ɗaya da samar wa kansu haɗin kai da taimakon juna wanda hakan zai sa masu faɗa aji ko masu madafun iko su waiwaye su domin a samar musu abubuwan da suke buƙata a inda suke gudanar da sana’o’insu da ma sauran al’umma baki ɗaya. Misali, wayar da kan mutane kan muhimmancin sana’o’insu da ma koyar da irin waɗannan sana’o’i ga masu buƙata.

4.2.2 Kamanci ta Fuskar Matsalolin Shugabanci ko Ƙungiyoyin Masana’antu

Sha’anin shugabanci a sana’o’in Hausawa a jiya da yau, suna da kamanci ta ɓangaren matsaloli ko ƙalubale. Wasu matsalolin sun shafi al’umma kai tsaye, yayin da wasu waɗanda ake jagoranta abin ya shafa (Hira da sarkin dako da shugaban ‘yan dakon garin Wudil da ke Jihar Kano, Malam Ibrahim da Alhaji Ɗahiru). Irin waɗannan matsalolin kuwa sun haɗa da;

i.Makwaɗaitan shugabanni. Shugabanci abu ne da yake shiga zukatan jama’a. Wannan ya sa ake samun masu son su ga su ma sun zama shugabanni. Hakan na kawo wa masana’antu da ƙungiyoyi cikas wajen tafiyar da harkokinsu na yau da kullum.

ii.Shigowar gwamnati cikin sha’anin shugabanci a sana’o’in Hausawa jiya da yau. A wasu lokutan, gwamnati tana yin shisshigi ko kutse a sha’anin shugabanni, wanda hakan yana kawo taɓarɓarewar mulki da sauran abubuwan da suka shafi cigaban al`umma a ɓangaren sana’o’insu.

iii. Raina shugabanni ko ƙin bin umarninsu daga wasu waɗanda suka shahara a harkokin kasuwanci waɗanda ‘yan ƙungiya ne.

iv.Matsalar adawa da zagon-ƙasa daga wasu mambobi. Kasancewar tsari ne da ya shafi shugabanci, dole ne a samu waɗanda ba sa goyon bayan wasu shugabanni. Wannan abu zai sa a rinƙa yi musu zagon-ƙasa domin su ɓata su a idon sauran mambobin ta yadda za a ga kasawarsu.

v.Siyasar zamani da bambancin ra’ayin siyasa na ‘yan ƙungiya. Ana samun saɓanin ra’ayi tsakanin shugabannin ƙungiya da mambobinta ta siyasar jiha ko ta ƙasa. Wasu shugabannin suna so mambobinsu su zaɓi wani ɗan siyasar da su kuma mambobin ba sa son wanda aka nuna musu. Misali, shugabannin ko ƙungiyoyin masana’antu na iya goyon bayan jam’iyyar APC, wasu mambobi kuma su nuna PDP suke so ko NNPP. Wannan yana haifar da matsala.

vi.Hassada, wato nuna ƙyashi. Ana samun hassada sosai musamman daga waɗanda ake jagoranta ko ‘ya’yan ƙungiya da suke yi wa shugabanninsu.

Idan aka dubi waɗannan bayanai da aka zayyano a sama, za a tarar da cewa da tsarin shugabanci a sana’o’in Hausawa na gargajiya da na zamani duka suna fuskantar irin waɗannan matsaloli, don haka suna da kamanci ta wannan ɓangare.

4.2.3 Kamanci ta Fuskar Tawayen Shugabanni ko Ƙungiyoyin Masana’antu

Tawaye na nufin zanga-zanga ta fito na fito da nuna rashin yarda da burin ta’addanci domin ramuwar gayya ko bore ga wanda ba a so ko zanga-zangar tabbatar da wanda ake so (Bunza, 2006:21). Akan samu irin wannan tawayen a tsarin shugabanci kasancewar abu ne da ake jagorantar wasu. A nan za a fasalta tawayen shugabanni ko ƙungiyoyi kashi biyu kamar haka:

4.2.3.1 Tawayen Waɗanda Ake Jagoranta ko ‘Ya’yan Ƙungiya

Tawayen waɗanda ake jagoranta ko ‘ya’yan ƙungiya shi ne tawayen da ake samu a cikin gida ko rikicin cikin gida tsakanin waɗanda ake joranta ko ‘ya’yan ƙungiya da masu jagoranci ko shugabannin ƙungiya. Irin wannan tawaye yana faruwa sakamakon mulkin kama-karya da shugabanni ke yi na rashin sauke nauyin da ke kansu ga waɗanda suke jagoranta. Wannan abu yana haifar da tawaye inda ‘ya’yanta kan nuna fushi ta hanyar zanga-zanga na nuna rashin goyon bayan waɗannan shugabanni. An taɓa samun irin wannan tawayen a Kasuwar Famsenta da ke Kano. Kasuwa ce ta matasa, ko da yaushe cikin rikici da warware matsala ake. Aka wayi gari ‘ya’yan ƙungiya suna zargin Shugaba da zaluntar su ta hanyar haɗa baki da ‘yansanda da hukumar Kasuwa, maimakon ya taimake su a matsayinsa na shugabansu. Wannan mataki nasa ya jefa su cikin mummunan hali. Suka yi ta zargin wannan Shugaba a kan yana haɗa baki da ‘yansanda idan aka kama wani ɗan ƙungiyarsu da laifi ta hanyar sanar da ‘yan sanda cewa, ai wane yana da kuɗi saboda haka a tatse shi sosai. Ko da ɗan Kasuwa yana da gaskiya, wani lokaci sai jami’an tsaro su ba shi rashin gaskiya. ‘Yan kasuwa sun zargi cewa bayan an warware rikicin ko matsalar, ‘yansanda suna ba Shugaban ƙungiyar wani kaso daga abin da aka samu a hannunsa. Tafiya da ta yi nisa, ‘ya’yan ƙungiya suka gano abin da shugabansu ke musu. Wannan ya sa suka shiga zanga-zangar son a tsige shi. Zanga-zangar ce ta sa aka tsige shugaban ƙungiyar da sauran maƙarrabansa a shekarar 2014. Hukuma ta naɗa kantomomin da suka ci gaba da riƙƙungiyar. (Hira da shugabannin ƙungiyar kasuwar Famsanta, Hamza Abubakar da Jamilu Bala).

4.2.3.2 Tawayen Shugabanni ko Ƙungiya ga Gwamnati

Wannan ya shafi tawayen da shugabannin ko ƙungiyoyin masana’antu ke yi wa gwamnati sakamakon rashin jituwa ko gamsuwa kan yadda gwamnati ke yi musu kutse kan wasu sha’anoninsu na sana’a’o’i ko rashin cika musu alƙawarurruka. Misali, muhimman abubuwa biyu su ne ke haifar da tawayen shugabanni masana’antu ga gwamnati. Waɗannan kuma su ne:

i.Haraji

Haraji na nufin kuɗin ƙasa da mutane ke biyan hukuma. Haraji na ɗaya daga cikin abin da ke haifar da tawaye ga hukuma. Shugabannin masana’antu ko Ƙungiya kan biya haraji ga hukumomi gwargwadon abin da aka nema daga gare su. Ko da yake kafin a daidaita yadda masana’antu za su biya kuɗin haraji, gwamnati kan yi wa shugabanni ko ƙungiya alƙawura kan wasu abubuwa kamar tallafi ko jari da kula da masana’antu ta hanyar tsaftace ta da kuma samar da tsaro. A wasu lokutan, gwamnati ba ta cika waɗannan alƙawura da ta ɗauka. A ƙarshe, sai shugabanni ko ƙungiya ta shiga bore ko yajin aiki na ƙin sayar da wasu nau’o’in kayayyakin da suke sayarwa musamman waɗanda al’umma ke buƙata. Hakan ya fi faruwa ne idan an yi niyyar ƙara kuɗin haraji. Al’umma kan shiga wani yanayi sakamakon wannan yajin aiki. Wannan abu yakan fusata al’umma har su fara rubuce-rubuce a shafukan sadarwa da shigowar ‘yan jaridu kan lamarin. A ƙarshe ba zai yi wa gwamnati daɗi ba, dole ta sasanta da waɗannan shugabanni ko ƙungiya a cigaba da gudanar da harkoki kamar yadda aka saba. Irin wannan abu ya so ya faru a kasuwar famsenta, sai dai bai yi tasiri ba. An so a ƙara musu haraji amma an samu kyakkyawar fahimta tsakanin ƙungiyar ‘yan kasuwar da hukuma.

ii.Sauya Fasalin Masana’antu

Al’umma ita take yi wa kanta wurin da za ta gudanar da sana’o’inta, a nan ne suke gudanar da hada-hadarsu. Daga baya idan gwamnati ta fahimci wannan wuri ya samu karɓuwa a wurin jama’a, sai ta yi tunanin shigowa ciki domin tallafa musu ta hanyar nuna musu za a sauya fasalin wurin ko kuma inda aka gina ta bai cancanta ba. Irin wannan abu yana sa masu masana’atar su tunzura har ta kai ga zanga-zanga.

5.0 Kammalawa

Kamar yadda bayanai suka gabata, wannan aiki ya yi duba ne kan kamanci da bambancin da ke tsakanin tsarin shugabanci a sana’o’in Hausawa jiya da yau, inda takardar ta rabe mana zare da abawa a kan yadda abin yake dalla-dalla. Haƙiƙa ruwa na ƙasa sai ga wanda bai tona ba. Wannan nazari ya tabbatar mana da cewa, shugabanci abu ne da yake tafiya da rayuwa. Rashin tafiyar da shugabanci a rayuwar ɗan’adam abu ne da ba zai haifar da ɗa mai ido ba. Muhimmancin da shugabanci yake da shi ya sa kusan dukkan al’amuran da Hausawa suke gudanarwa, kama tun daga zamantakewa har ya gangaro kan sana’o’i, sai an tarar akwai shugabanci a ciki. Haka nan kuma, idan aka kwatanta tsarin harkokin shugabanci a sana’o’in Hausawa jiya da yau, za a gane cewa akwai kamanceceniya da kuma bambance-bambance daidai gwargwado.

Manazarta

Alhassan H, da Musa, U.I (1982). Zaman Hausawa. Lagos: Academy Press Limited

Auta, A.L. (2006). “Tattalin arzikin Al’umma: Nazarin Sana’o’i Da Kasuwancin Hausawa”. A Cikin Algaita Journal of Current Research in Hausa Studies No. 4, Vol 1. Kano: Benchmark Publishers Limited.

Baba, I. da Ɗanjuma, S.A. da Madaki, B. (2024). “Nazarin Turakun Siffofin Miyagun Shuwagabanni a Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALAN Waƙa)”, a cikin MBORMI Journal of Language, Literature and Culture, Vol1, No 1, pp 210-224. Sashen Harsunan da Kimiyya. Kashere: Jami’ar Tarayya.

Bunza, A.M. (2006). Gadon Feɗe Al’ada. Gusau:Tiwal Press Limited

Bunza, A.M. (2014). “Shugabancinmu da Cigabanmu: A Tsarin Ƙasarmu”. Takardar da Aka Gabatar a Taron Ƙara wa Juna Sani na ‘Yan’uwa Musulmi Ƙarƙashin Jama’atul Muslim, Jagorancin Malam Muhammadu Bello Ɗan Malam, a Makarantar Nana Asma’u Ranar Alhamis 2 ga Watan Junairu, 2014 da Ƙarfe 8 na Yamma.

Bass, Bernard M. (2008). The Bass Handbook of Leadership: Theory, Research and Managerial Application, 4th edn. (New York: The free Press).

Burns, J.M. (1978). Leadership. New York. Harper & Row

C.N.H.N. (2006). Ƙamusun Hausa. Kano: Jami’ar Bayero.

Gummi, M. F. (2018). “Tsarin Shugabanci a Sana’ar Sarkanci”, cikin Malumfashi, I.A.M., Yakasai,S.A., Abdullahi, I.S.S. (eds) The Hausa People, Language and History. Past, Present, and Future. Pp.435-448 ISBN: 978-978-956-169-8.

Ibrahim, M.S. (1981). “Tattalin Arzikin Hausawa Na Gargajiya”. Takardar da Aka Gabatar a Taron Ƙara wa Juna Sani, Sashen Harsunan Nijeriya. Kano: Bayero University.

Lawal, N. (2019). “Nazarin Saye a Tunanin Bahaushe Jiya da Yau”. Kundin Digiri na Uku, Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya. Kano: Jami’ar Bayero.

Nuhu, A. (2020). “Zamani Abokin Tafiya: Wasu Al’adun Maguzawan Katsina a Ƙarni na 21”. Kundin Digiri na Uku, Sashen Harsunan Nijeriya. Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.

Sa’adu, M.M. (2020). Bahaushiyar Al’ada. Kano: Bayero University Press.

Sallau, B.A. (2010). Wanzanci Da Muhimmancinsa Ga Rayuwar Hausawa. Kaduna: Najiu Professional Printers.

Yakasai, S.Y. (2020). Jagoran Ilimin Warwarar Harshe. Sokoto: Amal Printing Press.

Yahaya, I.Y. da wasu (1992). Darussan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire. Ibadan: Ride Printing Company Limited.

Jerin sunayen waɗanda aka yi hira da su:

SUNA

UNGUWA

SHEKARUN HAIHUWA

SANA’A

MATSAYI

WURIN DA AKA YI HIRA

RANAR DA AKA YI HIRA

Sadiku Magaji

Sabuwar Unguwa

55

Wanzami

Sarkin Askar Wudil/Chairman na ƙungiyar masu sana’o’in gargajiya

Gidansa da ke garin Wudil

2024

Amadu Tundurmi

Jambulo

60

Farauta

Babban Shagon El-Smart Kantin Ƙwari

2024

Alhaji Bashir Abdullahi

Goron dutse

39

Su

Sarkin Ruwa

Gidansa

2024

Malam Garba Musa

Haɗeja Road, Kano

43

Su

Sarkin Kogi

Rumfarsa

2024

Hamza Abubakar

Sabuwar gandu

35

Gyaran Waya

Sakatare

Shagonsa da ke Famsanta

2025

Jamilu Bala

Gama

39

Sana’ar Waya

Chairman

Shagonsa da ke Famsanta

2025

Malam Ibrahim

Sheka

65

Dako

Sarkin Dakon Wudil

Cikin Kasuwar Wudil

2025

Alhaji Ɗahiru

Waliri layin Tsangaya

42

Dako

Chairman

Cikin Kasuwa

2025

Husaini Adamu

Dawanau

38

Arkomi

Chairman

A teburinsa da ke kasuwar Dawanau

2025

 Yobe Journal of Language, Literature and Culture (YOJOLLAC)

Post a Comment

0 Comments