Ticker

6/recent/ticker-posts

Wata Hudu Mijina Bai Sadu Da Ni Ba

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Salam malam, Dan Allah mene ne hukuncin wannan auren? Mutum ne sai ya yi wata shida ko huɗu bai sadu da matarsa ba, kuma lafiyarsa kalau, kuma da chan ba Hakka yake ba sai da ya yi sabon aure. na ji Mutanen suna cewa ba aure a tsakanin mu har sai ya kuma ba ni sadaki, sannan inna yi jini uku sannan zan zama matarsa?

WATA HUƊU MIJINA BAI SADU DA NI BA

𝐀𝐌𝐒𝐀

WA ALAIKUMUS SALAM WA RAHMATULLAH.

Kina nan amatsayin matarsa tun da bai yi niyyar yi miki ILA'I ba. Amma in dai haka tana faruwa to ya zalunceki. Ita saduwar Aure hakki ne wanda dukkan ma'aurata suke da shi akan junansu. Kuma duk wanda yaki ba ma dayan hakkinsa zai afka cikin laifi da kuma fushin Ubangiji. Ba daidai ba ne don mutum ya yi sabon aure shi ke nan sai ya rika wulakanta uwargidan yana tauye mata hakkinta. Allah yana cewa:

وَلَنْ تَسْتَطِيْعُوْۤا اَنْ تَعْدِلُوْا بَيْنَ النِّسَاۤءِ وَلَوْ حَرَصْتُمْ فَلَا تَمِيْلُوْا كُلَّ الْمَيْلِ فَتَذَرُوْهَا كَالْمُعَلَّقَةِۗوَاِنْ تُصْلِحُوْا وَتَتَّقُوْا فَاِنَّ اللّٰهَ كَانَ غَفُوْرًا رَّحِيْمًا

"BA za ku TAƁA YIN (HAKIKANIN) ADALCI A TSAKANIN MATA BA. ko da KUN YI KWADAYIN YIN HAKAN. AMMA KADA KU KARKATA GABA DAYAN KARKACEWA (GEFEN WATA) BALANTANA KU BAR WACCEN KAMAR WATA WACCE AKA RATAYA MUKU" [Suratul Nisai 4:129]

Kunga anan Ubangiji ya fimu sanin kanmu. shi ya sa ya ce bazamu taɓa yin hakikanin adalci ba. ana nufin cikakken adalci wajen soyayyar da take zuciya, ko Kulawa wajen kwanciyar aure da sauransu.

To amma Allah ya ce mana kar mu karkata wajen mace guda. Domin kuwa a cikin hadisi Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ba mu labarin cewa masu aikata irin wannan za su tashi a ranar Alkiyamah suna tafiya karkace. gefensu guda ya shanye.

Nisan wata huɗu shi ne mafi nisan kwanakin da bai kamata Namiji ya haura su ba tare da ya kusanci matarsa ba. Duk wanda ya haura haka ba tare da wani dalili wanda shari'a ta yarda da shi ba, to hakika ya zama azzalumi. Shi kuwa Azzalumi bashi da daraja a wajen Allah. Allah shi kiyayemu.

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...

 ƘARIN BAYANI

TSAWON WATANNI 4 MIJINA BAI SADU DA NI BA

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum malam, don Allah ina so in fahimci hukuncin wannan auren: Mijina bai sadu da ni ba tsawon wata huɗu, lafiyarsa kalau, kuma ba wani uzuri ne ya hana shi ba sai ya yi sabon aure. Wasu mutane suna cewa ba aure a tsakanina da shi har sai ya biya ni sadaki, sannan in yi jini uku, sannan zan zama matarsa. Menene hukuncin wannan a cikin addinin Musulunci?

𝐀𝐌𝐒𝐀

Wa Alaikumus Salam wa Rahmatullahi.

A cikin shari’ar Musulunci, saduwa a cikin aure hakki ne na kowa tsakanin miji da mata. Wannan hakki ya haɗa da kwanciyar hankali, soyayya, da kusantar juna domin kare aure daga duk wani rashin jituwa ko damuwa. Idan mijin bai sadu da matarsa tsawon wata huɗu ba, musamman ba tare da wani uzuri na shari’a ba, wannan ya zama zalunci a kan matarsa, domin yana tauye mata wani haƙki da Allah ya halatta mata a cikin aure.

Allah ya ce a cikin Alƙur’ani:

وَلَنْ تَسْتَطِيْعُوا أَنْ تَعْدِلُوا بَيْنَ النِّسَاءِ وَلَوْ حَرَصْتُمْ فَلَا تَمِيلُوا كُلَّ الْمَيْلِ فَتَذَرُوهَا كَالْمُعَلَّقَةِ وَإِن تُصْلِحُوا وَتَتَّقُوا فَإِنَّ اللَّهَ كَانَ غَفُورًا رَّحِيمًا

"Ba za ku taɓa yin cikakken adalci tsakanin matanku ba, ko da kuwa kun yi ƙoƙari. Kada ku karkata gaba ɗaya ga mace ɗaya ku bar ɗayan kamar an rataya. Amma idan kun yi gyara ku kiyaye, to, hakika Allah Mai gafara ne Mai jin ƙai."

(Suratun Nisa’i: 4:129)

Ayar ta nuna cewa cikakken adalci a aure yana da alaƙa da kulawa da mata, musamman wajen kusanci, soyayya, da kwanciyar aure. Rashin yin hakan, musamman yayin da babu wani dalili na shari’a, yana sanya mijin cikin zalunci da rashin daraja a wurin Allah.

Manzon Allah ya nuna a cikin hadisi cewa waɗanda suka karkata wajen aure ba tare da yin adalci ba, za su tashi a ranar Alkiyamah sun karkace a gefensu, wato rashin adalci yana ɗaukar hukunci mai tsanani.

Game da lokacin da bai kamata a wuce: Mafi tsawon lokacin da mijin zai iya tsayawa ba tare da kusantar matarsa ba shi ne wata huɗu idan lafiyarsa kalau. Wato duk wanda ya wuce wannan lokaci ba tare da uzuri mai halatta ba, yana cikin azzalumi, kuma azzalumi bashi da daraja a wurin Allah.

A game da wasu ƙurakurai kamar cewa: “Ba aure a tsakanina da shi sai ya biya sadaki, sannan in yi jini uku…” – wannan magana ba ta da tushe a shari’ar Musulunci, domin aure ya faru da sadaki da yiwuwar cikawa lokacin aure. Rashin kusantar aure ba ya janyowa sharuɗɗan musamman kamar yin jini uku.

Hukunci a takaice:

• Miji yana da hakkin kusantar matarsa a aure.

• Rashin yin hakan ba tare da uzuri na shari’a ba yana zama zalunci.

• Wata huɗu shine mafi tsawo da ya kamata mijin ya wuce ba tare da kusantar matarsa ba.

• Duk wanda ya wuce wannan lokaci ba tare da dalili ba, ya shiga cikin azzalumi a wurin Allah.

Allah shi ne mafi sani.

Zauren Fatawoyi Bisa Alƙur’ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin fadakarwa.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments