𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Aslamu alekum dafatan malam ya yini lpy da shi da iyalansa da almajiransa da sauran masoyansa ameen.
Tambaya ta ita ce:
cikin wannan watan da muke ciki na mai wani abu yafaru a garin Maradi aynahin
cikin ƙasar mu ta Niger. Wai wasu dalibai ne yan boko mace da
namiji suka haɗa kansu Aure suka
saka rana za a ɗaura musu auren bayan
iyayensu basu sani ba, basuda labari. Amma lalle an ce yarinyar taringa haudawa
saman status dinta foton gayyata ga mutane. Da ranar ta zo sai kuma aka yi katari
malaminda zai basu darasi bai zoba sai shi namijin yahiddo jaka biyu acewarsa
kuɗin saki ne yabiya sai
ita kuma tamaidomar jaka daya. Sai sauran daliban abokaninsu suka ringa ihu
suna cewa bizou bizou bizou. Kurum sai ga wani daga cikin malaman makarantar
yana wucewa sai yaji hayaniyar tayi yawa kurum sai ya leƙo ya ga abin da yake
faruwa Sai yakamasu ya kaisu gurin shugaban makarantar. Aka kira iyayensu aka
sheda musu aikinda yaransu sukayi sai baban yarinyar ya ce bai yadda ba da
wannan auren dan baida labari kuma shi baisan kome ba aka yi. Shi ne aka ce wai
akwai auren su daram duk da cewa babu waliyayye daga kowane bangare na namiji
ko na mace. Duba da cewa yarinya ce ƙarama batakai shekaru
ishirin ba kuma ba ta taba yin aure ba balantana a ce bazawara ce ta san ciwon
kanta. Akan haka ne muke neman ƙarin bayani akan wannan lamari. Allah
ya ƙaramawa
Malam tsawon kwana masu albarka ya kuma jiƙan iyayen Malam da
rahama ameen
SUN ƊAURA AURE BA TARE DA
SANIN IYAYENSU BA
𝐀𝐌𝐒𝐀❗
Wa'alaikumussalam.
Aure baya zama Aure
Tsakanin mace da Namiji Har sai da Abubuwa guda Huɗu.
1. Na farko Shi ne ya
zama Akwai Sigar Aure a Tsakanin Waliyyan Waɗannan Ma'auratan. Ma'ana Waliyyin Namiji ya
ce Ina Nemawa Ɗana ko Kanina Ko Jikana ko Abokina Wane Auren Ɗiyarka Wance ko
Kanwarki Wance Ko Mahaifiyarka Wance. Domin Da zai iya yi wa Mahaifiyarsa
Alwalanci. Kamar Yadda Anas ɗan Malik ya yi wa Mahaifiyar sa Ummu Sulaimin Alwalanci a
Lokacin da Abu Dalhatal Ansariy ya zo Aurenta. Sannan shi Alwalalin wannan
Macen ya ce Na Baka. Sai Alwalin Wannan Namijin Ko Wakilin wannan Namijin ya ce
Na Karɓa Masa.
2. Abu Na Biyu Kuma Shi
ne Alwalanci. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya ce MACE BA TA AURAR DA
MACE, SANNAN MACE BA TA AURAR DA KANTA. Sabida haka Ke nan. Wajibi ne a sami
wanda zai Aurar da ita, Kuma Wajibi ne ya Wannan da zai Aurar da ita ɗin ya zama Namiji.
Mutumin da ya fi kowa Chanchanta wajen Aurar da ita, Yi mata Alwalanci. shi ne
Mahaifinta. Idan babu Mahaifi. Sai a Sami wani daga Cikin Dangin Mahaifinta Ya
Aurar da Ita. Idan babu daga dangin Mahaifin ta, sai a sami wani daga dangin
Mahaifiyar ta. Idan babu dangin Uwa sai Shugaba Kamar Sarki ko Hakimi ko Dakaci
ko Bulama ko Mai Unguwa ya yi Mata Alwalanci.
3. Aure Baya Yiwuwa
sai da Sadaki. Wajibi ne ya zama an san sadakin wannan Matar tin kafin A zo
Maganar Ɗaura Wannan Auren. Sannan Waliyyanta za a dankawa Wannann
Sadakin Ba Ita ba. Daga baya ne kuma za su ba ta kayanta. Amma mace ba ta karɓa sadaki da hannunta.
Ko da Kuma ta karɓa da hannunta. za ta
kawowa Waliyyanta su gani su sanya Masa Albarka. Sai Kuma ita wannan ba ta Nemi
Albarkar iyayenta akan Wannann sadakin Nata ba. Hatta a Auren Nata ma ba ta Nemi
Iyayenta su Sanya Mata Albarka ba.
4. Wajibi ne a sami
Shedun da za su Bayar da Shaidar Cewar a Gabansu Aka Ɗaura wannan Auren,
kuma duk Wani Sharadi na Wannan Auren an cika Shi. Sannan Ne za su Ba da
Shaida. Wajibi ne Waɗannan Shaidun Akalla
Su Zama Kamar Mutum Ukku, da za su tabbatar da Dauruwar Wannan Aure. Idan babu
Shedu Aure bai yiwu ba. Sannan ya zama Wajibi Waɗannan Shedun su zama Masu Hankali,
Adalai. Ba dalibai 'yan Secondary ba.
Sabida haka ke nan.
Ta Kowanne Fuska wannan Auren bai yiwu ba. Domin bai Cika Duk wani Sharadi na
Aure ba ko guda ɗaya ma bai cika ba.
Wannan Wasan yara ne. In banda ma Rashin Tarbiyya. Ta yaya Mace Budurwa za ta
Aurar da kanta ga wani Namiji. Ba tare da sanin Iyayenta ba. Allah ya gyara
mana wannan zamanin da Muke Cikinsa.
Allah Shi ne Masani.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.