Ticker

6/recent/ticker-posts

Alkunut A Sallar Asuba

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Yaya Matsayin Alƙunutu Da ake Karantawa Asallar Asubahi? Shin Wajibi ne Sai Mutum ya yi Ko Liman Yana ɗaukewa mamu?

AL-ƘUNUT A SALLAR ASUBA

𝐀𝐌𝐒𝐀

Alƙunuti sunnah ne na addu'a da ake yi awani bigire kebantacce na tsayuwa wanda aka shar'anta asallar wutiri bayan dagowa daka

ruku'u a bisa zance ingantacce cikin zantukan Malamai.

Ana yin Alƙunutu idan wata masifa ko bala'i ya aukawa Musulmai sai su dunga addu'a bayan dagowa daka ruku'u akowacce raka'ar karshe ta sallar farillah guda biyar, Har Allah ya yaye musu wannan bala'i daya auka musu yadauke musu shi. Duba littafin (Tas-heehi du'aa'i na Shaik Bakar Abu Zaid shafi na 460)

Amma yin Alƙunutu ko da yaushe Asallar asuba bai inganta daka Annabi sallallahu Alaihi wasallam ya keɓance sallar asuba yana alƙunuti a cikinta ko da yaushe ba, Abin da yatabbata daka gareshi shi ne yana yin Alƙunutu idan wata masifa tasauka, ya yi alƙunutu asallar asuba dasauran salloli yana yi wa ZAKWAAN DA USAYYAH mummunar addu'a saboda kashe mahaddata Alƙur'ani dasu kai wadanda Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) yaturasu zuwa garesu dansu sanarda da su addinin musulunci, yatabbata ya yi ƙunuti asallar asuba yana rokawa raunana daka cikin muminai dabasu samu damar yin hijiraba saboda rauninsu Allah yakubutar da su daka Abokan gabarsu, bai dawwama akan hakan ba, halifofi shiryayyu suka tafi akan haka abayansa, Abin da yake alheri ga limamai shi ne sutakaita dayin Alƙunutu asallar asuba dama sauran salloli sai dai idan wata masiface ta aukawa musulumi, anan yahalatta aita Alƙunuti har Allah yayewa Musulmi wannan masifar. Kamar yanda hadisinda Asha-bul Sunan suka ruwaito banda Abu dauda daka Abu malik Al'Ashja'iy Allah ya kara masa yarda. Albani ya Ingantashi a cikin Irwa'u (435)

Mafificiyar shiriya ita ce shiriyar manzan Allah

sallallahu Alaihi wasallam. fatawa lajnatul da'imah (7/47)

Sannan ba a iyakance wata addu'a damutum

zai yi A'alƙunuti na wata masifa da ta samu Musulmai ba, liman zai yi addu'a wacce tadace dahalin da ake ciki da kuma masifar kamar yanda aka ruwaito Annabi sallallahu Alaihi wasallam ya tsinewa wasu kabilun dasuka bijirewa sahabbansa suka kashesu, da kuma rokawa raunana da suke makkah Allah yakubutar dasu. Amma Akwai wasu sigogi da'aka ruwaito Annabi sallallahu Alaihi wasallam da shabbansa sun yi a addu'ar ƙunuti a cikin sallah kamar yanda baihaiƙi yaruwaito (2/210) Albani ya ingantashi a cikin Irwa'u (2/170).

Yahalatta kayi alƙunuti da addu'a takashin kanka kamar yanda Imamun Nawawi yabayyana a cikin Almajmu'u dinsa (3/497).

Dan samun karin bayani za ka iya yin wacce aka ruwaito sannan kakara dataka duba (ƙiyamu ramazhan na shaik Albani (31)

Hadisai da'aka ruwaito akan alƙunuti da kuma

ingantaccen zance na malamai shi ne ana yinsa bayan dagowa daka ruku'u idan kayi kafin tafiya ruku'u babu komai kana da zabin idan kagama karatun sallah kayishi kafin tafiya ruku'u sannan za ka iya yin ruku'u idan kadago saikayi alƙunutin. Kamar yanda shaik Usaimeen yabayyana a cikin Sharhin Mumti'i Ala zhadul mustaƙni'i ( 4/64)

Dan haka yin Alƙunuti asallah baya kan mamu,

liman ne ke haƙƙin yinsa, shi mamu zaidunga Ameen ne lokacinda liman yake addu'ar

Alƙunutin.

Alƙunuti wanda muka tashi mukaga ana yi akasar nan kowacce sallar asuba da kuma siga daya dasunan mazhabar malikiyyah bidi'ane bai tabbata daka Annabi sallallahu Alaihi wasallam ba.

Asalin Alƙunutu asallar asuba malamai sun yi saɓani akansa akwai wadanda suke ganin shar'antuwarsa kamar malikiyyah da shafi'iyyah, akwai wadanda ba sa ganin shar'antuwarsa kamar Hanafiyyah da Hanabila.

Ibnu ƙudama rahimahullah a cikin Almugni ( 1/449) Yace: Ba sunnah ba ne alƙunutu asallar asuba ko watanta daka cikin salloli, inba wutiriba, haka Assauri ya ce da Abu hanifa, haka aka ruwaito daka ibnu Abbas, da Abdullahi Ɗan Umar da Ibnu mas'ud da Abul dar-daa'i.

Malik da Abi laila da hasan bin salih da shafi'i sukace: Sunnah ne yin alƙunutu asallar asuba adukkanin zamunnah domin Anas yace: ( Manzon Allah sallallahu Alaihi wasallam baigushe ba yana alƙunutu asallar asuba har ya bar duniya) Imamu Ahmad a cikin Musnad ɗinsa.

Umar ya kasance yana Alƙunutu agaban sahabbai da wasunsu. Da Abin da aka ruwaito Annabi Sallallahu Alaihi wasallam ya yi alƙunutu tsawon wata guda akan wasu larabawa rayayyu sannan yadena. Muslim.

Abu huraira yaruwaito irin wannan hadisin daka Annabi Sallallahu Alaihi wasallam, ( Annabi Sallallahu Alaihi wasallam ya kasance baya alƙunutu asallar asuba sai dai idan zai yi wa wasu mutane addu'a ta alkhairi, kozai musu addu'a mummuna.)

Alƙunutun Umar ya kasance lokacin saukar musibu domin mafiya yawan ruwayoyi sunzo akan baya alƙunutu, jama'a da yawa sunruwaito haka daka gareshi, wannan yake nuna baya alƙunutu sai a lokacin saukar musiba. Mausu'ah fiƙ-hiyyah ( 34/58).

Tare dacewa magana mairinjaye ita ce: Baya halatta yin alƙuntu asallar asuba ko da yaushe sai dai idan masifa tasauka, Sai dai babu laifi dankayi sallah abayan wanda yake alƙunutun asallar asuba ɗin, dayin Ameen a addur'asa.

Shaikul Islam ibnu taimiyyah rahimahullah yace: Idan mamu yabi limamin dayake alƙunutu asallar asuba ko sallar wutiri zai yi ƙunuti tare da shi, yana alƙunutunne kafin ruku'u ko bayan ruku'u. idan baya alƙunuti ba zai yi ba.

Koda liman yana ganin Mustahabbancin wani abu, mamu kuma baya ganin hakan sai ya barshi dan samun haduwar kai da hadewa yakyauta, Maj-mu'u fatawa (22/ 268).

Dan haka dai lazimtar yin alƙunutu ko da yaushe asallar asuba ba sunnah ba ne, sai dai idan wata matsala ta tunkaro Musulmi ko wani bala'i sai aita alƙunutu harsai Allah yakau da wannan matsalar.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Tambaya Da Amsa a bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group za ku iya bi ta Links ɗin mu...


ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments