Citation: Abdullahi Haruna IMAM (2025). Wasu Kyawawan Ɗabi’un Hausawa: A Cikin Waƙoƙin Malam Gambo Hawaja Jos. Yobe Journal of Language, Literature and Culture (YOJOLLAC), Vol. 13, Number 1. Department of African Languages and Linguistics, Yobe State University, Damaturu, Nigeria. ISSN 2449-0660
WASU KYAWAWAN ƊABI’UN HAUSAWA: A CIKIN WAƘOƘIN MALAM GAMBO HAWAJA JOS
NA
ABDULLAHI HARUNA IMAM
Tsakure
Manufar wannan Muƙala ita ce ta fito da wasu kyawawan ɗabi’u na Hausawa da aka san su da su. Waɗannan halaye duk wanda ya yi mu’amala da Hausawa zai tabbatar da su. Daga cikin ɗabi’un da Bahaushe ya yi fice a kansu akwai gaskiya, da amana da
zumunta da kyauta. Duk da sauyin zamani da ya shigo cikin al’adun Hausawa, har
yau sun riƙe wannan halaye ba su saki ba. Za a bi sawun waƙoƙin Malam Gambo a tsakuro misalai. A lokacin da ake yunƙurin tattaro bayanai an yi
amfani da ayyukan magabata musamman
waɗanda suka yi rubutu da ke
da alaƙa ta kusa da wannan
bincike. An nemo baitocin da ya yi maganar gaskiya da amana, da zumunta a yi misali da su. An yi amfani da ra’in nason adabi a al’ada
wanda yake yin bayanin alaƙar adabi da al’ada
saboda suna da kusanci duk da cewa ana samun wasu ‘yan bambance-bambance da ake
samu wanda bai yi illa ga kowane ɓangare ba. A ƙarshe aikin ya gano cewa Gambo ya fito da waɗannan kyawawan ɗabi’u na Hausawa da suka
haɗa da gaskiya, da amana, da zumunta da sauransu,
domin saura su yi koyi da su.
1.0 Gabatarwa
Ɗaya daga cikin kyawawan al’adun Hausawa shi ne a sami mutum yana
da halaye nagartattu. Daga ciki akwai riƙo da gaskiya, duk mai riƙe da gaski yana da babban matsayi a cikin al’umma. Bugu da ƙari za a ga cewa kowa yana sha’awar ya yi koyi da halayensa. Sai
kma amana, wadda a yau ta yi ƙaranci ga al’ummar
Hausawa. A zamanin da duk in da Bahaushe yake yana kasance wa amintacce, kamar
yadda su ma sun amince sun yarda ko da kuwa ga maƙwabtansa ne. shi ma ya
yarda da cawa ba zai ci amanar mutane ba. Sai kuma zumunta, Bahaushe yana
girmama zumunta tsakaninsa da ‘yan’uwansa a duk yadda yake ba tare da nuna
fifiko ba. Haka kuma kyauta ɗaya ce daga cikin
kyawawan halaye da Hausawa suka gada. Tun kafin zuwan Musulunci ƙasar Hausa, idan mutum ya zama marowaci sai mutane su guje masa
har ya rasa abokan hulɗa. Da musulunci ya zo ƙasar Hausa aka san Hausawa da waɗannan halaye, shi ya sa
Larabawa da Turawa suka ji daɗin yin mu’amala da su. Wannan muƙala ta leƙa waɗannan halaye na Hausawa
kamar yadda aka ji Malam Gambo ya ambace su a cikin waƙoƙinsa. Bayan nan an yi sharhin baitocin da ya
ambaci waɗannan kyawawan ɗabi’u na Hausawa.
1.1 Hanyoyin Tattara Bayanai
An tattauna da wasu masana fannin al’adun
Hausawa, da iyalan Malam Gambo Hawaja a Jos da Takai mahaifarsa, da Haɗejiya inda ya zauna. Lokacin yin wannan binciken, an duba ayyukan
magabata daban-daban waɗanda aka yi a Jami’o’i da cibiyoyin ilimi. Kuma
an duba wasu litttafai masu alaƙa da aikin.
1.2 Ra’in Bincike
Wannan bincike ya ɗauki Ra’i (Gusau ya kira shi da mazahaba) wato, mazahabar NASON
ADABI A AL’ADA. An bi sawun Gusau (2015, sh49) an ɗauki bayaninsa a kan wannan mazahaba, “Mazahabar nason adabi a
al’adun al’umma tana ƙoƙarin daidaita hikima ta
isar da ma’ana ko ƙaramin saƙo ko harshen magana da
ayyuka na gyaran rayuwar al’umma ta yau da kullum. Haka kuma mazahabar tana bin
sawun yadda al’umma take ƙoƙarin bayyana abin da ya
shafe ta.”
Asalin wannan mazahaba ta faro ne ta kallon
yadda hikima da sauran dabaru na fusahar baka da suka danganci abubuwan da
al’umma take gudanarwa. Wannan ra’i yana da shugabanni, irin su: William Bascom
(1912-1981) wanda shi ne ya fara assasa mazahabar a nahiyar Afrika ta yamma,
Wasu daga cikin mabiya wannan mazahaba bayan Boscom (1912-1981) sun haɗa da: Roɓert Gorges da Macheal Owen Jones da Danial
Crowley da Alan Dundes da sauransu.
Da aka duba sai aka ga cewa binciken da ake yi
ya dace da wannan ra’in domin yana da alaƙa da ke ƙulla tsakanin adabi da al’ada, yadda za a kalli gundarin adabin a
fito da al’ada a cikinsa.
1.3 Taƙaitattacen Tarihin Malam Gambo Hawaja Jos
Magabata da suka yi bincike a kan tarihin Malam
Gambo Hawaja sun daidaita a kan garin da aka haife shi. An haifi Gambo Hawaja a
cikin garin Takai a ƙaramar hukumar Takai, ta Jahar Kano Kimanin
Kilomita 82 daga birnin kano a unguwar Tungulun bakin kasawa. Abdulƙadir (2008, sh251) kuma ya ce an haife shi ne a Sumailan jahar
Kano. An samu saɓanin shekarar haihuwarsa, kamar yadda magabata
suka rattaba. Birniwa ya ce an haifi Malam Gambo a shekarar (1914) Birniwa
(1987, sh176). Haka Abdulƙadir shi ma ya ce an haife shi a shekarar (1914)
Shi kuma Imam (2019, sh26) ya samu nasa a wurin iyalansa da wajen wasu abokansa
cewa an haife shi a shekarar (1919). Wannan ya yi daidai da wanda Dagaceri
(1990, sh9) ya ruwaito. Sunan mahaifinsa Malam Abubakar, bafilatani ne.
Mahaifiyarsa kuma Malama Asma’u ‘yar ƙibilar kanuri ce
(Babarbariya). An yi ittifaƙi a kan asalin sunansa shi ne Salisu. Haka kuma
Gambo Bahaushe ne, saboda in da ya taso cikin Hausawa ne, Hausar ita ce harshen
mutanen garin Takai. Mahaifinsa yana yi musu Magana da fillanci shi da sauran
‘ya’yan gidansu mahaifiyarsu tana yara musu harshen Kanuri, wanna dalili ne ya
sanya Gambo Hawaja ya ƙware da waɗannan harsuna guda uku,
wato Fillanci da Hausa da Barbarci. Kuma ya yi sa’a aikin Turawa ya kai shi
garuruwan Nguru da Barno da Adamawa da Kamaru ya ƙara gogewa sosai da harsunan mahaifansa.
Lokacin da Gambo Hawaja ya kai kimanin ɗan shekara 15 a duniya, a cewar Imam (2019, sh27) haziƙancinsa ya bayyana a fili, duk abin da zai yi a cikin ‘yan uwansa
sai ya yi musu zarra. Idan kuma a cikin tsararrakinsa ne sai ya zama zakara
saboda ƙaƙƙarfa ne ga wayo da iya
shugabanci a cikin tsararrakinsa. Na farko dai ba shi da tsoro, kuma bai barin
takwana idan ya lura akwai ɓurɓushin zalunci a cikin al’amarin. (1)
Kamar yadda al’adar Hausawa take, kowane yaro in
ya taso, akan yi ƙoƙari a kai shi wajen
malami don neman ilimi na Alƙur’ani mai girma, ko a garinsu ko a wani gari na
daban. Shi ma Malam (1) Akwai wata rijiyar kwakware (Kankare) mai suna
“Tungulun” a ƙofar gidansu wadda suke ɗiban ruwa a cikinta. Sannan akwai wani mutum mai yin dako da
jakai, kullum ya zo sai ya tura jakunansa su shanye wa mutane ruwa. Rannan wani
wansa ya tara ruwa a cikin ɗan akwakun da ake yi na
kankare, sai ya ga wannan mutum ya sako jakai. Daga nesa sai Gambo ya ce da
wannan wan nasa karya bar shi ya hana shi, shi kuwa yayan nasa ya koma gefe,
saboda ya ga abin yafi ƙarfinsa. Da Gambo ya zo, sai ya kore jakunan
mutumin. Ya sake koro su don su shanye wannan ruwa, Gambo ya hana su sha, har
dai mutumin nan ya haƙura ya kora jakunansa ya ƙara gaba yana mamakin tsaurin ido na Gambo Hawaja. Amma sai ya ce
“Lallai in yaron nan ya girma za a ji shi a duniya.”
Gambo Hawaja ya sami wannan gatan, inda
mahaifinsa ya kai shi wajen wani malami a nan garin
Takai mai suna Malam Muhammadu wanda yake
unguwar Tungulun, kafin ya kai shi a wurinsa ya fara karatusa a gaban
mahaifinsa.
Bayan nan ya yi karatun littattafai na Fiƙihu tun daga ƙawa’idi da Ahalari da littattafai na addini a
garin Haɗejiya. Wannan karatu ya taimaka masa wajen jin
harshen Larabci. Bugu da ƙari, Gambo
Hawaja ya yi karatun yaƙi da jahilci, shi ma a garin Haɗejiya. Wannan karatun yaƙi da jahilci ya taimaka masa ya iya karatu da rubutu na Hausa da
Ingilishi, har ma yakan yi sadarwa da In
Ya samu sunansa na Gambo saboda an haife shi
bayan tagwaye (‘yan biyu). Wato yayunsa Hassan da Hussaina. Amma sunansa na
yanka shi ne Salisu. Hawaja kuwa ya samu sunan ne a garin Hadejiya, a lokacin
yana hayar kekuna. Sai N. A. (Natiɓe Authority) ta Hadijiya
ta kafa dokar hana hawa keke sannan kuma a ja wani, Kamar yadda aka san al’adar
masu haya. Shi Gambo sai ya hau
ɗaya yana jan ɗaya, in mutane suka haɗu da shi, sai su riƙa yi masa kirari suna
cewa “Hawa-ja” shi kuma sai ya ce “Sauka lafiya da ikon Allah” Hukuma suka kama
shi suka hukunta shi, amma bai fasa ba, har suka hakura suka kyale shi. Shi
kuma ya zame masa al’ada duk inda zai je sai ya
hau keke ɗaya yana jan ɗaya. A nan ya samu sunansa na ‘Gambo Hawaja’.
Gambo ya taso a lokacin mulkin Turawa, bayan sun
cinye ƙasar Hausa. Hausawa sun firgita da
mulkinsu. A lokacin akwai Turawan kiwon lafiya,
waɗanda in suka je gari kamen marasa lafiya suke yi
su yi musu magani kyauta. Amma duk da haka tsoronsu ake ji sosai (kamar yadda
aka karanta a wasan kwaikwayon nan mai suna Wasan Marafa). Da Turawan kiwon
lafiya suka shiga garin Takai, sai mutane suka gudu kowa ya ɓuya, sai wanda aka ritsa da shi. Shi kuwa Gambo Hawaja sai ya
tsaya yana kallon yadda suke bai wa majinyata magani suna warkewa. A wannan
lokaci kuwa mahaifiyarsa tana fama da ciwon ido har ba ta gani ta makance, sai
ya je wajen su Turawa ya yi mata cune aka zo aka kamata, aka tafi da ita
Asibiti, suka yi mata magani ta warke. Daga bisani ya gaya mata shi ne ya yi
mata cune, ta yi ta sanya masa albarka.
A cikin tawagar Turawan nan akwai wani baƙar fata Bahaushe mai suna Malam Shitu mutumin Lafiyar Barebari.
Shi ya jawo Gambo kusa da shi yana aikensa da ’yan wasu aikace-aikace. Haka
kuma in akwai wanda bai jin Hausa sai Fillanci ko Barbarci, sai Gambo ya
fassara masa. Da suka gama da Takai za su wuce zuwa garin Zuga sai ya bi su.
Daga nan ya zama ma’aikacinsu suka tafi da shi.
Bayan Gambo ya rabu da Turawa masu ba da magani,
sai ya koma garin Haɗejiya ya zauna. A nan ya yi arziƙi, ya shahara. An san Gambo da rashin tsoro, ga shi ƙaƙƙarfa ga wayo da wayewa da farin jinin matasa, ga
fasahar iya magana da sauran mu’amalar jama’a. Wasu mutane da yawa sun ɗauka Gambo Hawaja Bahaɗeje ne, saboda shaharar
da ya yi aka san shi sosai a garin da kewaye, ya zama kamar haifaffen garin ne,
ba wanda bai san shi ba.
Da Gambo ya koma Haɗejiya sai ya duƙufa da neman ilimi na littattafai da na zamani,
saboda aikin da ya yi da Turawa, sai ya gane rayuwa tilas ne sai an yi cikakken
ilmi za ta daidaita. Allah ya ba shi sa’a ya samu waɗannan fannoni guda biyu daidai gwargwado. Gambo yakan yi magana da
Larabci da kuma Turanci. Yana ba da fatawa a kan wata matsala ta fikihu. Saboda
irin baiwar da Allah ya ba shi, har Sarkin Hadejiya na wannan zamanin ya so ya
mayar da Gambo ya zama Bafadensa. Amma ina! Abin bai yiwu Sarki daɗi ba, sai dai yakan je fada lokaci-lokaci ya gaida Sarki da sauran
muƙarrabansa. Haka ba ta hana shi in ya ga an yi hukuncin da bai dace
ba, ya yi magana ko a gaban Sarkin ne bai jin tsoron faɗa. Hadejiya ta zama tamkar Takai a wajensa. Duk kwarabniyar gari
da shi ake yi, hakan tasa ya zama ɗan cikin gida a gidan
Galadiman Hadejiya.
Wata rana Gambo ya je Malam-Madori yana dawowa,
sai maciji ya sare shi. Sai Allah ya kawo wani maharbi, ya taimake shi da
magani. Kuma sai ya lura da ganyen da ya ciro ya dandaka ya jika masa, nan take
da ya sha ya yi amai. Daga nan ne ya sami laƙaninsa na maganin maciji
da shawara, wanda har yau ana ba da shi a gidansa na Jos.
Zamansa a Haɗejiya ya buɗe masa ƙofofi na fahimtar rayuwar duniya da kyakkyawar
mu’amala da shige-da-fice na neman abin duniya. Sai Gambo ya fara tunanin
ya ƙaura ya bar Haɗejiya tun da dai ba
mahaifarsa ba ce, kuma kullum yana samun saɓani da masu gari a kan
haraji da lasisin hayar keke da sauransu. Duk da yake Gambo yana tunanin barin
garin Haɗejiya, bai sa a ransa zai koma Takai mahaifarsa
ba. Sai ya fara tunanin komawa Kano don ci gaba da kasuwancinsa na sai da kayan
koli. Kuma haka aka yi ya bar Haɗejiya ya koma Kano ya
zauna a Fage da ƙofar Ɗan’agundi, bai daɗe sosai ba, sai ya bar Kano ya ƙara gaba.
Ko da Gambo ya bar Haɗejiya yana da jarinsa a aljihunsa, saboda haka duk inda ya dosa ba
sai ya sha wahalar neman jari ba, sai dai ya ɗora daga inda ya tsaya. Da ya yi zaman Kano ɗan kaɗan ya ga bai gane ba yana son ya sake canza
gari, sai ya doshi Legas. A can ma shekara ɗaya ya yi ya bar ta.
Kafin ya bar Legas sai ya tuna da garin Jos wanda ya taɓa zuwa tun yana aiki da Turawa a ƙarƙashin uban gidansa Malam Shitu mutum Lafiyar
Barebari. In zai raka shi zuwa ganin gida ta Jos suke bi, tun a wannan lokacin
Jos ta zama ɗaya daga cikin garin da yake so ya zauna. Ba
tare da wata-wata ba daga Legas, sai Gambo ya nufo Jos da niyyar nema. Amma sai
da ya je wurin mahaifansa suka yarje masa sannan ya tafi.
Da ya isa Jos ya sauka a layin Adebayo, kusa da
gidan Alkali Abubakar, saboda a Jos a wannan lokacin babu layi da yake
tara ɗaliban ilimi daga ko’ina a Nijeriya kamar layin.
Gambo ya zaɓi ya zauna a wannan layin ne don ya ɗora a kan saninsa da yake da shi. Haka kuwa aka yi ya ci gaba
da ƙara zurfafa iliminsa na fiƙihu da sauransu. Yana nan a Jos sai ya sake shawara ya koma Lafiya
da zama wurin mai gidansa Malam Shitu wanda a lokacin ya yi ritaya daga aiki ya
koma gida. Daga can Lafiya ne yake zuwa Legas kasuwancin goro, ya sayo ya kawo
Lafiya da Jos. Daga ƙarshe ya koma Jos gabaɗaya da zama.
Wannan karon da ya koma Jos sai ya zauna a layin
Majema ƙarshen layin Sarki cikin garin Jos. Da yake
yana ƙulle da jarinsa, sai ya fara tunanin me zai yi
na sana’a, sai ya yanke shawara ba zai zaɓi sana’a ba haka kawai
da wuri, har sai ya jaraba sana’o’i daban-daban, kar ya kama sana-ar da ba ta
dace da shi ba.
Kaɗan daga cikin sana’o’in
da Malam Gambo ya yi a garin Haɗejiya da Kano da Legas da Lafiya da Jos. Da ya
bar aikin Turawa ya koma Haɗejiya da zama, sai ya kama sana’ar hayar keke,
ya yi noma, ya yi sana’ar sai da bulawus. Da ya koma legas ya yi sana’ar sayar
da goro. A jos kuma ya yi tuƙi, da kuza da sai da baƙin mai, da goro, da ba da hayar kujeru da rumfa don yin maulidi,
da kakkafa gidajen sai da man fetur a Jos da Kaduna da Gwambe da Bauci da
Azare. Wannan shi ne sirrin samun kuɗin Malam Gambo Hawaja
Jos. A cikin garin jos ya yi auren fari ya haifi ‘ya’ya Goma Sha Biyar (15) ya
mallaki gida Goma (10) da Motoci na haya da na hawa. Saboda yawan kyautarsa sai
da ya kai kowa ya san shi. Ga shi da raha, da iya magana, ga tsayawa a kan
ra’ayinsa baya canzawa. Kuma mutum ne mai yawan ibada da son ‘yan uwansa da
sauran halaye nagartattu.
Nagartansa ta shi a sahun manyan garin Jos
masu ƙima da daraja. Hatta waɗanda ba Hausawa bas una bas hi girman da ba sa baiwa manyansu.
Wannan daraja da Allah ya ba shi sai ta sanya wa Sarkin Jos hasada ya ɗauki Gambo a matsayin barazana ga sarautarsa.
Ya zama ɗaya daga cikin manyan
garin Jos, masu faɗa a ji. (3) Bai taɓa yin wata jam’iyya ba
daga NEPU sai PRP. Duk arziƙin da Allah yake bai wa bawa na ilimi da dukiya
da ‘ya’ya ya bai wa Malam Gambo Hawaja. Duk wanda suka yi bincike a kansa sun
yi ittifaƙi a kan shekarar da ya rasu, wato (1985) a
gidansa dake Unguwar Dilimi a garin Jos.
2.1 Ɗabi’un Hausawa a Bakin
Gambo Hawaja Jos.
Mawaƙa su ne suke adana
al’aun al’umma har na baya su zo su tarar da su har su yi alfahari su, ko
su ƙara taskace su. Waƙoƙin Malam Gambo cike suke da al’adun Hausawa kyawawa. A nan za
a ɗauki wasu domin a buga maisali da su
2.1.1 Gaskiya
Wannan kalmar ta gaskiya Bahaushiya ce ba ta aro
ba ce, kuma jinsin mace ce. Sannan suna ne, aikatau ɗinta shi ne gaskata ko gaskiyarsa da sauransu. Wato gaskiya tana
nufin tsayawa a kan maganar da babu ƙarya. ko kuma aikata
wani abu a kan daidai.
Duk lokacin da aka danganta mutum da gaskiya to,
Hausawa suna ba shi daraja, yana zama abin so ga kowa, saboda yana da abinda
mutane da yawa ba su da shi. Mafi yawan mutanen da suke da gaskiya za a same su
da sauran kyawawan halaye na riƙon amana da zumunta da kyauta. Malamai sun faɗi ma’anar gaskiya. cewa “gaskiya wata ɗabi’a ce mai wuyar yi, don kuwa ba duka mutane za a samu suna da
gaskiya ba, gaskiya tana da wuyar faɗa musamman in ta faɗo tsakanin waɗanda ake jin nauyi, ko kuma na gaba da mutum,
amma duk da haka ita ce take nuna cewa mutum na ƙwarai ne, wanda ba za a yi shakkar yin wata hulɗa da shi ba, da sauransu.” Muhammad (2020, sh182)
Tun asalin Hausawa mutane ne masu gaskiya, idan
mutum ya zama maras gaskiya zai zama koma baya a cikin mutane. Babu mai yarda
da shi. Ga abin da Malam Gambo ya ce:
21-In
mutum na da hankali,
Ya ga
dattijo kamili,
Na ta ruɗu a dandali,
Tabbata
ba shi hankali,
A’a ko ba
shi gaskiya.
(Waƙar Zalumai Kun Shiga
Uku)
A wannan baitin Malam ya nuna girman gaskiya,
kowace irin siffa ta kamala ce ta bayyana ga mutum matuƙar ba shi da gaskiya sai ka gan shi yana yin abin da bai kamata
ba. Ya nuna ga mutum dattijo wanda ya kamata a same shi da kamala, rashin
gaskiya ya sa shi yin ruɗu a dandali. Kalmar “ruɗu” daga ruɗewa tana nufin rashin hankali, Gambo ya nuna
rashin gaskiya ne ya sa wannan tsoho yin haka. Ta la’akari da abin da Malam ya
faɗa gaskiya tana da ƙima a wurin Hausawa. Bunza (2009, sh103) ya ruwaito karin maganar
Hausawa da suke cewa “gaskiya sunanta gaskiya.” Haka kuma akwai wasu karin
maganar da ke nuna darajar gaskiya a wurin Bahaushe, Mai gaskiya yana tare da
Allah, akwai kuma gaskiyar mutum jarinsa, da gaskiya dokin ƙarfe, da saransu.
Malam Gambo ya nuna gaskiya tana da wani
irin ƙarfi mai girma, ya ce duk wanda ya riƙe gaskiya ya fi ƙarfin mai bindiga da bom
da igwa.
13-Mun ɗau makamai sun fi bom har bindiga,
Kun san
su ko mu faɗe su su ne gaskiya.
14-Igwa
da bom bai magani in ta zaka,
Wa ke da
ikon dankwafewar gaskiya.
(Waƙar ‘Yan Sawaba)
Waɗannan baitoci sun ƙara fito mana da matsayin gaskiya a wajen al’ummar Hausawa kamar
yadda Malam Gambo ya kawo. A nan ya nuna babu wani ƙarfi da ya zarce na gaskiya, idan mutum ya riƙi gaskiya ya fi ƙarfin duk wani mai ƙarfi kowane ne shi in dai Ɗan’adam ne. waɗannan baitoci suna nuna yadda Bahaushe yake kallon gaskiya.
2.1.2 Amana
Kalmar amana ararriya ce daga Larabci. Yadda
ma’anarta take a Larabci ta yi daidai da yadda take a Hausa. Mutum ya kauda kai
a kan abin da ba nasa ba. In kuma ajiya ce aka ba shi ba zai taɓa ba komai tsanani, duk ranar da ka zo karɓa za a sami komai babu cin gara ba na zago. Ƙamusun Hausa (2006, sh15) ya ba da ma’anar amana da cewa: “Ba mutm
ajiyar kaya ko wani abu yadda zai adana shi kamar nasa ba tare da wani abu ya
salwanta, ko wani abu ya same shi ba.”
Amana tana ɗaya daga cikin
kyawawan ɗabi’u na Hausawa. Idan mutum ya kasance mai
tsantseni da kama kai, da kau da kai a kan abin da ba nasa ba, wannan mutum
yana da amana. Idan mutum ba shi da amana al’umma ba ta son yin hulɗa da shi, saboda tsoron kar ya ci musu amana. A cikin jama’a akwai
waɗanda suka yi fice a kan riƙon amana, haka kuma akwai waɗanda suka yi suna da
rashin riƙon amana. Game da waɗanda ba su da riƙon amana ga abin da Malam Gambo ya ce:
66-Jama’a
haɗin nan ko kaɗan bai zaunu ba,
Tamfar a
dama kunu idan a sa miya.
67-Ko kau
a ba kura amanar tinkiya,
Jama’a ya
biri zai yi gadin gurjiya.
(Waƙar ‘Yan Sawaba)
Yana faɗa mana cewa tsakanin
amana da rashinta akwai rata da yawa, kamar yadda ya kwatanta da cewa haɗin sam bai yi daidai ba, kamar a dama kunu a zuba masa miya, ko
kuma a ba kura amanar tsaron tinkiya ko a ba biri tsaron gurjiya. An san cewa
wannan amana ba za ta tsaru ba, to haka wasu mutane suke wajen rashin riƙon amana. A yau in aka kwatanta maganarsa da riƙon amanar mutanen yau waɗanda za su hau mizani su
haye ba su da yawa, tamkar a bai wa kura amanar tsaron tinkiya ne.
A wata waƙar siyasa da ya yi yana
sukar ‘yan jam’iyyar NPC, wadda yake adawa da ita yana cewa:
108-Yau
duk mutan NPC in ka ƙididdige,
Maciya
amana sai barorin dukiya.
(Waƙar ‘Yan Sawaba)
A nan, ya nuna ‘ya’yan waccen jamiyyar da yake
adawa da su maciya amana ne masu yin barance saboda dukiya. Duk lokacin da
Bahaushe ya kwatanta mutum da rashin riƙon amana ya ƙasƙantar da shi, ya mayar da shi maras ƙima. Kishiyar haka kuma idan aka danganta mutum da mai amana an
samar masa da daraja da ƙima a idon mutane. A waƙar waiwaye adon tafiya, ya yi ƙarin haske yana cewa:
132-Bar
ganin yau caca jere,
Ba su son
juna da gare,
Ba amana
inda kare,
Ɗan’uwa daidai da bare,
Ga faɗa ga shirga sata.
(Waƙar Waiwaye Adon Tafiya)
A nan ma Malam ya ƙara nuna illar rashin amana da ke faruwa, ya buga misali ne da
‘yan caca, inda ya nuna saboda rashin amana ba sa son junansu ko da an gan su
tare. Ya ce a wurin su ɗan’uwa daidai yake da bare.
2.1.3 Zumunta
Kalmar zumunta tana nufin ƙarfafa dangantaka da ‘yan’uwa na jini. Asalin Kalmar Bahaushiya
ce, ba baƙuwa ba ce. Kuma suna ne, aikatau ɗinta ita ce zumunci. Madauci da wasu (1968, sh 25-28) sun kawo
jerin mutum talatin waɗanda ya kamata a yi zumunci da su a matsayin su
na ‘yan’uwa makusanta a tsarin al’adun Hausawa. Ga wasu kaɗan kamar haka:
Akwai kaka: mahaifin uba, ko uwa. Sai uba:
mahaifin ɗa/’ya. Sai uwa: mahaifiyar ɗa/’ya, da sauran dangi makusanta ga mutum. Sauran a koma ga
Madauci (1968)
Waɗannan dangi su aka fi
sani da yin zumunta a tsakanin junansu. Amma ba iyakarsu ke nan ba, za a iya
samun wasu na daban su riƙe zumunci suna yi kuma ya tafi daidai da wanda
ake yi da ‘yan’uwa. Malam Gambo ya kawo matsayin zumunci a wurare daban-daban.
Wani wurin gargaɗi yake yi ga waɗanda suke wasa da
zumunta ba sa riƙe shi da kyau suna sakin zumunci. Ga misali:
76-Inuwar
giginya ban ga amfaninta ba,
Sai dai
na nesa ka shanta nata ya sha wuya.
(Waƙar ‘Yan Sawaba)
Idan Allah ya fifita wani ya fi ‘yan’uwansa
samun abin duniya, amma ba ya taimakonsu, sai dai ya taimaki bare, sai a yi
wannan karin magana “Inuwar giginya na kusa da ita ba ya shanta sai na nesa”
wato ‘yan’uwa da danginsa ba sa cin moriyarsa sai wasu na daban.
Malam Gambo ya kawo wani misali a waƙarsa ta Neman Kuɗi yana ƙara tabbatar da abin da
ya faɗa kamar haka:
92-Kuɗi shi yakan sa zumunta ta watse,
Ana kashe
juna a neman kuɗi.
(Waƙar Neman Kuɗi)
Duk da ƙarfin da zumunta take da
shi a tsakanin ‘yan’uwa amma kuɗi sai ya watsa wannan zumuncin, har ya kai ga an
rasa rai. Malam ya nuna zumunci zai iya kawo ƙarshen zumuntar ‘yan’uwa saboda kuɗi.
2.1.4 Kyauta
Kyauta wata kyakkyawar ɗabi’a ce ta Bahaushe, wadda ya tashi ya samu magabata suna yinta.
“Kyauta ita ce ka bai wa wani mutuum alheri ko hasafi na kuɗi ko tufafi ko abinci ko dabba.” Muhammad (2020,
sh173) Haka kuma kyauta ita ce, “Bai wa mutum wani abu ba don ra’ayi ba tare da
ya yi wa mutuum wani aiki ba.” Bahaushe ya ɗauki ɗabi’ar kyauta da muhimmanci, mutane suna girmama mai halin kyauta.
Bugu da ƙari kyauta tana ƙarfafa danƙon zumunci a tsakanin ‘yan’uwa na jini. Kyauta
kan ƙara wa babba girma. Da kyauta ne sarakai suke
iya mallakar talakawansu, rashin yin kyauta ga talakawa yakan haifar da tawayen
talakawa. Idan mutuum yana da dukiya sai ya kasance ba ya kyauta ga mabuƙata, sai ka same shi yana da baƙin jini ba mai sha’awar
ya raɓe shi sai mai kwaɗayin gaske. Ga misali
daga waƙoƙin Malam Gambo Hawaja
Jos.
201-Sai
da samu kan yi baiwa.
202-Kan
ana son kyautatawa.
203-Arziƙi mai tara barwa.
(Waƙar Ɗebe Kewa)
Waɗannan baitoci guda uku
Malam Gambo ya kawo wasu sunayen da ake kiran kyauta da su, wato “baiwa” da
“kyautatawa.” Za a iya kiran kyauta da baiwa ba sai an ce kyauta ba. Ko kuma a
ce kyautatawa da nufin kyauta. Sai dai ya nuna komi son mutum ya yi kyauta sai
da samu, in ba a da shi ba za a ga kyauta ba. Ya nuna duk yadda mutum yake son
ya kyautata ba zai iya ba. A baitin ƙarshe ya yi wa kyauta
kirari da ya ce, “arziƙi mai tara barwa yana nufin tara bayi.”
3.1 Sakamakon Bincike
A wannan bincike an samu sakamako mai nuna wasu
kyawawan al’adun Hausawa da ɗabi’u da kowa yake so ya
yi koyi da su. Daga ciki akwai gaskiya. An fahimci duk mutumin da yake da
gaskiya a cikin al’umma zai samu karɓuwa. Bayan gaskiya sai
riƙon amana. A yau in an samu mutum yana da amana zai zama kowa yana
son shi, kuma yana ƙaunar a danganta shi da mai amana. Da wuya a
samu wanda yake ƙin sa.
Akwai kuma zumunta wadda take faruwa a tsakanin
‘yan’uwa na jini, duk da cewa akan samu waɗanda ba ‘yan’uwa na jini
ba su riƙe yin zumunci a tsakanin su.
4.1 Kammalawa
Wannan muƙala ta tattauna a kan
wasu halaye da ɗabi’un Hausawa masu nuna kyakkyawar mu’amala da
ake son kowa ya koya ya aikata a cikin rayuwarsa ta yau da kullum. Kamar yadda
Gambo Hawaja ya bijiro da su. Haka kuma maƙalar ta fito da baitocin
da suke ɗauke da saƙonni. An kuma yi ƙoƙarin yin sharhin waɗannan baitoci. Haka kuma muƙalar ta taɓo kyawawan halayen Hausawa guda huɗu ne kawai, hakan ba
yana nuna iyakar kyawawan halayen Hausawa ba ke nan, akwai wasu da yawa waɗanda ba a ambace su ba. Misali akwai kunya da kara da yawan
gaisuwa da sakin fuska da raha da kaiwa dangi ziyara da biyayya, da neman
ilimi, da jarumta, da ƙoƙarin dogaro da kai da
yin biyayya ga iyaye da yin biyayya ga mahukunta da makamantansu.
MANAZARTA
Aminu, A. (2009). Jirwayen Musulunci a Waƙoƙin Gambo Mai Waƙar Ɓarayi. Bitar Tsarin Baƙin Al adun Larabawa A
Ma’aunin Al’adar a kan Makaɗi a Mahangar Manazarta. Sakkwato: Sashen Nazarin
Harsuanan Nijeriya Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Birniwa, H. A. (1987). A Conserɓatism and Dissent: A Comparatiɓe Study of NPC/NPN and NEPU/PRP Hausa Political Ɓerse from Circa 1946-1984. Ph.D Thesis, Sokoto: Department of
Nigerian Languages, Sokoto: University of Sokoto.
Bunza, A. M. (2006). Gadon Feɗe Al’ada. Lagos.
TIWAL Nigerian PLC
CNHN (1981). Rayuwar Hausawa. Cibiyar
Nazarin Harsunan Nijeriya. Kano: Jami’ar Bayaro.
CNHN (2006). Ƙamusun Hausa. Kano:
Jami’ar Bayero
Dagaceri, M. K. (1990). Malam Gambo Hawaja da Waƙoƙinsa. Takardar Neman Digirin Farko. Kano: Bayaro
University
Garba, C. Y (1991). Sana’o’in Gargajiya
a Ƙasar Hausa (sana’a Bahaushiya). Kaduna: Spectrum books Limited.
Gobir, Y.A. (2019) Tsofaffin Al’adun Hausawa A
Cikin Waƙoƙin Narambaɗa. Maƙalar Da Aka Gabatar A Taron Ƙarawa Juna Sani Na Ƙasa-Ƙasa Da A Aka Yi A Kano: Jami’ar Bayaro.
Gusau, S.M. (2010). Al’adun Hausawa
a Ƙasar Hausa. A Cikin Littafin Al’adun
Hausawa da Fulani. Department of Hausa Federal Collage 0f Education
Katsina. Kaduna: Printers and Publishers. El-Abbas Printers and Media
Gusau, S.M. da Sani, M.A.Z da Birniwa, H.A. da
Mukhtar; I. da Adamu, S. da Abdulƙadir, Ɗ. (2011). Gyara kayanka: Tasirin Al’adun Hausawa Ga Ci gaban Ƙasa. Kano: Studies in Hausa Language Literature and
Culture. The Siɗth Hausa Intarnational Conference. Centre for
The Study Of Nigerian Languages Bayaro University (EDITORS) Lawan Ɗanladi Yalwa, da Abdu Yahaya Bichi da Sammani Sani.
Gusau, S.M. (2011). Tsokaci Kan Al’adun
Hausawa. Harsunan Nijeriya Vol.ɗɗiii Special Edition,
Centre for The Study of Nigerian Languages Kano: Bayero University.
Gusau, S.M. (2015). Mazahabobin Ra’i da
Tarke a Adabi da Al’ada na Hausa. Kano: Century Research and
Publishing Limited.
Hauwa, S. L. (2014). Tarbiyya a Mahangar
Bai Ɗaya. Nazarin Waƙar Tarbiyya Ginshiƙi Na Zaman Bisa Lafiya. Ta Malam Adamu Salihsu. Maƙalar da aka gabatar a taron ƙasa da ƙasa na farko a kan nazarin Hausa a ƙarni na ishirin da ɗaya. Sashen Koyar da
Harsunan Nijeria. Kano: Jami’ar Bayaro.
Ibrahim, M.S. (1982). Dangantakar Addinin
Musulunci da Al’adun Gargajiya Na Hausawa. Kundin Digiri na M.A. a Sashen Koyar
da Harsunan Nijeriya. Kano: Jami’ar Bayaro.
Imam, A.H. (2019). Rayuwa Da Waƙoƙin Malam Gambo Hawaja Jos. Kundin Digiri Na Biyu
M.A. Hausa Studies. Sashen Nazarin Harsunan Nijerya, Sakkwato: Jami’ar
Usmanu Ɗanfodiyo.
Madabo, M. H. (1979). Ciniki Da Sana’o’i
a Ƙasar Hausa. Ibadan: Thomas Nelson Limited
Maiyama, U.H. (2010). Dangantakar Adabi da
Al’adu Nazarin Dabarun Sata a Waƙoƙin Muhammad Gambo Fagada. Ɗunɗaye Journal of Academic eɗcellence Sokoto: Department of Nigerian Languages
Usmanu Ɗanfodiyo University VOL: N0 3
Ma’azu, A. (2014). Na zaune Bai Ga Gari Ba:
Tsokaci Kan Tafiye – tafiye A Al’adar Hausawa. In Harshe Journal of
African Languages. Department of African Languages and Culture. Zaria:
Ahmadu Bello University.
Magaji, A. (2002). Wasu Al’adun Hausawa
Yanaye-yanayensu A Ƙasar Katsina. Kundin Digiri Na uku. Sashen
Nazarin Harsuna Nijerya. Kano: Jami’ar Bayaro.
Muhammad, L. (1990). Mu Fara Karatu,
littafi na 3. Zaria: Longman Nigerian Limited. Publication Bereau.
Muhammad, M.S. (2020). Bahaushiyar
Al’ada. Kano: Bayaro University Press.
Nuhu, A. (2016) Kyawawan Al’adu da Ɗabi’u A Matsayin Hanyar Samar Da ingantacciyar Al’umma. Waiwaye
Daga Wasu Waƙoƙin Hausa Na Zamani”.
Sakkwato: Maƙalar da aka gabatar a taron ƙarawa juna sani na ƙasa kan rawar da harshe
da adabi da suke bayarwa wajen ci gaban haɗin kai da samar da tsaro
a Nijeria wanda Tsangayar Fasaha. Sakkwato: Jami’ar Usmanu Danfodiyo.
Sani U.B. (2003). Jirwayen Al’adun Hausawa Cikin
Ayyukan Masu Jihadi (Tsokaci Cikin Ayyukan Mujaddadi Ɗanfodiya) Kundin Digirin (M.A) Sokoto: Jami’ar Usman Ɗanfodiyo.
Umar, M.B. (1978). Dangantakar Adabin
Baka da Al’adun Gargajiya Na Hausawa. Zaria: Publication Center of
Nigeria.
Yahaya, I.Y da wasu (2007) Darussan
Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire Littafi Na Biyu. Ibadan:
University Press.
Yola, M.M. (2013). Tarihin Dalilin Aure da
Tasirinsa a Rayuwar Hausawa. Study in Hausa Language, Literature and
Culture. The 1st National Conference Center for The
Study of Nigeria Languages, Kano: Bayero University (Eds) Lawal Ɗanladi Yalwa da Sa’idu Muhammad Gusau da Haruna Abdullahi
Birniwa da Mukhtar Yusuf Abdulƙadir da Isa Yusuf Chamo.
Zarruƙ, R.M. (1978).
Dangantakar Hausa da Larabci.Studies In Hausa Language Literiture and
Culture. The first Hausa International Confrence. Kano: Bayaro
University.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.