Citation: Asma’u SULEIMAN (2025). Sana’ar Adon (Feren) Ƙwarya A al’adar Hausawa. Yobe Journal of Language, Literature and Culture (YOJOLLAC), Vol. 13, Number 1. Department of African Languages and Linguistics, Yobe State University, Damaturu, Nigeria. ISSN 2449-0660
SANA’AR ADON
(FEREN) ƘWARYA
A AL’ADAR HAUSAWA
NA
ASMA’U SULEIMAN
Tsakure
Sana’ar ƙorai dadaɗɗiyar sana’a ce wadda ta
samo asali tun kaka da kakanni, tana da matuƙar muhimmanci ga rayuwarmu
ta yau da kullum saboda tana samar da muhimman abubuwa waɗanda suke da matuƙar amfani ga rayuwar
tafiyar da gidaje. Sana’ar tana daga cikin sana’o’in gargajiya na Hausawa, sai
dai da tafiya ta yi tafiya an sami ‘yan sauye-sauye da suka shige ta saboda ci
gaba da aka samu sabili da cuɗanya da Hausawa suka yi da
wasu ɓaƙin al’umma. An aza aikin a bisa ra’in Adana Al’adu da Ci
Gaban Al’umma (Cultural Sustainability Theory), wadda Gusau 2015; 55 ya kira
sunan makarantar da “Mazhabar Adana A’ladu”. Ra’in ya bayyana cewa lalle idan
al’umma na son samun ci gaba da bunƙasa to dole ne ta
kyautata hanyoyin da za ta rinƙa adana al’adunta domin
kada su salwanta.
1.0 Gabatarwa
Sana’a ita ce ƙashin bayan ko wace al’umma, abu ce mai matuƙar muhimmanci domin ita ce tafarkin da ɗan’adam ke ɗauka ya bi don samun abin masarufin biyan buƙatunsa na rayuwa. Sana’oin Hausawa na gargajiya sun daɗe ana yin su a doron ƙasa, kuma suna da matuƙar muhimmanci a rayuwar al’umma, ba ma Hausawa kaɗai ba. Hakan ya sa suke da babban matsayi kuma suke taka
muhimmiyar rawa a al’adun al’ummu daban-dabam, saboda ta hanyar aiwatar da su
ne Bahaushe ke biya wa kansa buƙatun da suka taso masa na yau da kullum, haka
kuma ta hanyar sarrafa albarkatun ƙasa ne ɗan’adam yake samun damar mallakar abubuwa na kansa. Sana’ar Ƙore tsohuwar sana’a ce wadda ta daɗe ana yin ta, ta samo
asali ne daga sana’ar noma saboda “duma” wanda shi ne ƙashin bayan sana’ar, manoma ke shuka shi. A taƙaice, wannan rubutu ya tattaro bayanai ne a kan sana’ar ƙorai, an yi bayani a kan asalin sana’ar da kayayyakin da ake
amfani da su wajen aiwatar da sana’ar da yadda ake aiwatar da ita da kayayyakin
amfani da ake samarwa daga sana’ar, sai kuma daga ƙarshe ‘yan sauye-sauye da suka shigi sana’ar a wannan zamani.
2.1 Ma’anar Sana’a
C.N.H.N, (2006:387) an bayyana ma’anar sana’a da
aikin da mutum yake yi don samun abinci, misali manoni sana’arsa noma, wanzami
kuwa aski ne sana’arsa.
Tukur, (1989:1) “Sana’a wata aba ce wadda mutum
yake yi yau da kullum da nufin samun abin masarufi domin gudanar da harkokin
rayuwarsa na yau da kullum, kuma hanya ce ta sarrafa albarkatun ƙasa da sauran ni’imomin da Allah ya yi wa ɗan’ adam kamar amfanin gona da dabbobi da tsirrai da sauransu don
samun abin masarufi. Haka nan ta shafi harkar kasuwanci, wannan shi ya sa
ake ɗaukar sana’o’i da babban matsayi a rayuwar
kowace al’umma domin kuwa akasari su ne suke zama ƙashin bayan kowace al’umma”.
Yahaya, (1992:48) da Auta (2006: 195) Sana’a a
wurin Bahaushe ta ƙunshi duk wani abin da mutun yake yi yau da
kullum domin samun abin da zai rinƙa biyan bukatunsa. Haka
nan sana’a na nufin sarrafa wani abu ta hanyar amfani da ƙarfi ko wata dabara da Allah ya hore wa ɗan ‘adam domin ya sayar ya sami riba. Kuma ta danganci tono
albarkatun ƙasa da sarrafa su ta amfani da hanyoyin kimiyya
da fasaha da ni’imomin da ke tattare da ɗan’adam.
2.1.1 Rabe-raben Sana’a
Dangane da rabe-raben sana’a kuwa za a iya kasa
ta zuwa gida biyu, wato akwai sana’o’in gargajiya akwai na zamani. Sana’o’in
gargajiya su ne waɗanda muka gada tun iyaye da kakanni irin
su ƙira da jima da wanzanci da noma da sauransu.
Sana’o’in zamani kuwa baƙi ne waɗanda Bahaushe ya haye
su, irin waɗannan sana’o’in akasarinsu Hausawa sun same su
ne ta hanyar cakuɗuwa da baƙin ƙabilu, da suka same su, sai suka koya har suka iya. Misalan irin
waɗannan sana’o’i sun haɗa da sana’ar walda da sana’ar yankan farce da sana’ar wankin
takalma da sauransu.
2.2 Ma’anar Ƙwarya
C.N.H.N (2006:293) an bayyana ƙwarya da mazubi da ake samu bayan an fafa duma.
A wurin Prince Christian (1968) kuwa, “Ƙwarya na samuwa ne daga duma wanda ke fitowa ya girma, idan
ya ƙosa sai a cire shi a gyara, a mai da shi ƙwarya da dangoginta”.
Newman, (1972:147) ya bayyana ƙwarya da “wata abu ce da ake amfani da ita don ajiye ruwa ko wani
abu, cin abinci da yin kwalliya. Ya ƙara da cewa “ƙwarya guga ce da ake jan ruwa”.
A taƙaice dai, ƙwarya abin amfani ce da ake samarwa daga duma tana da faɗi, da buɗaɗɗen baki zagayayye mai
sigar da’ira, tana da ƙaramin gindin zama wanda hakan ya sa ake tanadin
abin da za a ajiye ta bisa wanda ake ce ma tarde. Ƙwarya tana da siffa irin ta akushi kuma tana kama da kwatarniya ko
kaskon suya. Ƙwarya abu ce da ake amfani da ita tun zamani mai
tsawo da ya wuce, don yin ayyuka na yau da kullum.
3.1 Asalin Sana’ar Ƙorai
Sana’ar ƙorai tsohuwar sana’a ce,
ta samo asali tun iyaye da kakanni, daga sana’ar noma saboda duma tsiro ne
wanda ake shukawa, kuma tun lokacin da Ɗan adam ya gane hikimar
noma yake shuka duma. Amma a lokacin da, kafin a gane hikimar sarrafa shi ya
zama ma’aikaci, ana dafa shi a ci tun kafin ya riƙa ya yi ƙwari, ana kiran shi “duman kulubutu”. Daga baya sai suka lura cewa
ashe wannan duman da suke dafawa suna ci idan ya bushe yana yin ƙwari, saboda haka sai suka fara fafa shi suna kankare cikinsa
domin amfani da shi, musamman wajen cin abinci da ajiye-ajiye. A hankali, a
hankali basira ta daɗa ƙaruwa har suka rinƙa yi masa ado iri daban-dabam a jikinsa kuma suka gane dabarar yin
ado da su a muhallansu.
3.2 Kayayyakin da ake Amfani da su Wajen Aiwatar
da Sana’ar Ƙorai
Akwai wasu kayayyaki na musamman da ake amfani
da su wajen aiwatar da sana’ar ƙorai, daga cikinsu
akwai:
3.2.1. Duma
Duma wadda ita ce kanwa uwar gami idan babu ita,
babu sana’ar. Ana shuka shi a gonaki da fadamu ko a cikin gidaje, akasari ana
shuka shi a ƙarshen damina a cire shi lokacin bazara bayan
ya ƙosa, ya sha rana ya bushe, daga ‘ya’yan duma ne
ake samar da ƙwarya da sauran danginta. Abin lura a nan shi ne
akwai duma iri daban-dabam kamar duman gidauniya da duman ƙoƙo da duman masaki, amma dukansu ana kiransu da
duman ƙwarya domin banbancinsu bai wuce na girma ko
sifa ba. (Malam Badamasi Sa’idu 2025A).
3.2.2 Majaujawa
Majaujawa tana ɗaya daga cikin muhimman kayayyaki a sana’ar ƙorai, wuƙa ce doguwa mai kaifi sosai, akasari duk
geffanta na da kaifi, amma ana samun wadda gefenta ɗaya ne kaɗai ke da kaifi. A da can, kafin sauyawar zamani
da ita ake amfani a fafe duma, amma yanzu mafi yawan masu sana’ar suna amfani
da sankiso.
3.2.3 Sankiso
Sankiso na ɗaya daga cikin kayayyaki
na zamani da bahaushe yake amfani da shi wajen aiwatar da sana’ar ƙorai, zarto ne yana kama da zarton yankan ƙarfe, sai dai shi ƙarami ne yana da haƙora a gefe ɗaya kaɗai. Ana amfani da shi a
fafe ƙwarya.
3.2.4. Mahuri
Mahuri lanƙwasassar wuƙa ce wadda ke da ƙotar ice, tana da kaifi
a duk geffanta biyu, ba ta da tsawo sosai kuma tana da ƙota daga tsakiyar ƙarfen. Wuƙar tana kama da lauje, ana amfani da ita a katse cikin ƙwarya a fitar da dussa da ‘ya’yan dake ciki. Irin su shantu da
zunguru da kurtu kuwa, waɗanda hannu ba ya iya shiga cikin su, sai a yi
amfani dogon ice mai ƙwari a katse ciki.
3.2.5. Gizago
Gizago ɗan ƙaramin ma’aikaci ne, yana da siffar magirbi. Masu sana’ar ƙorai na amfani da shi su cire hancin duma kafin a fafa shi saboda
idan ya ƙosa sosai hancinsa na yin tauri ƙwarai, shi ya sa ake tanadar gizago.
3.2.6. Magogi
Ana amfani da shi a goge cikin ƙwarya don ta yi santsi, masu sana’ar kan sami gwangwani su huhhuda
shi domin goge ƙwaryar. Amma a da ana amfani da soso ko soshiyar
dawa. A yanzu kuma ana anfani da samfefa.
3.2.7. Zarton Fere Ƙwarya
Wannan yana kama da zarton kafintoci na zamani,
yana da haƙora a duk geffansa biyu. Ana amfani da shi wajen
yanka duma da yin alama ko sheda na irin zane ko kwalliyar da ake so a yi
wa ƙwarya a jikinta ko shantu da sauran
nau’ukan ƙoran da ake kwalliya da su a muhalli.
3.2.8. Wuƙar Zanen Ƙwarya
Wuƙa ce ‘yar gajera
mai ƙotar itace, ƙarfen wuƙar ba ya da faɗi kamar na wuƙa, kuma gefe ɗaya kawai ke da kaifi. Wuƙa ce wadda ake yi
wa ƙwarya zane da ita da tusa alamomin da aka yi da
zarton fere ƙwarya.
3.3.9. Jansara
Duk jikinsa ƙarfe ne amma wasu na yi
masa ƙotar itace don su ji daɗin riƙewa. Ƙarami ne, kuma yana kama
da gatari daga bakinsa, daga sama kuma an lanƙwasa shi kamar makaɗin ganga. Ana amfani da shi a wasa zarton da ake fere ƙwarya idan ya dakushe.
3.2.10. Bidar Zanen Wuta
Bidar zanen wuta wani ƙarfe ne ɗan siriri mai tsawo, wanda ake yi wa ƙota saboda zafi. Ana saka ta cikin wuta, idan ta yi zafi sai a rinƙa nanawa a jikin ƙwarya don yi mata ado. A
yanzu kuma saboda zamananci ana amfani da ɗan bida na wutar
lantarki (sondering iron)
3.2.11. Farar Ƙasa
Ana shafa Farar ƙasa a jikin ƙwarya don ta ƙara haske, garura da
tawada kuma ana shafa su a jikin ƙwarya da dangoginta a yi
mata ado. A yanzu har fenti ana shafawa ƙore domin ya fi daɗewa a jikin ƙoren.
3.2.12. Ragaya
Masu sana’ar ƙorai suna tanadar
ragaya. Ana saƙa ta da igiyar kaba ko zaren lilo. Ana amfani da
ita don ɗauko duma daga gona zuwa gida kuma da ita ake
kwasar ƙorai masu yawa domin kai wa kasuwa cikin sauƙi.
3.3 Yadda Ake Aiwatar da Sana’ar Ƙorai
Aikin sana’ar ƙorai ɗan dangana ne, wato sana’a ce ta mai haƙuri, saboda mai yin ta kullum buɗu-buɗu yake da ƙura, ga kanta a hannu saboda riƙon ƙarafa iri daban-dabam. Akwai matakai huɗu da ake bi wajen aiwatar da wannan sana’ar waɗanda suka haɗa da fafewa sai ƙanƙarewa sai gogewa daga ƙarshe kuma zana ado.
Mataki na farko shi ne fafewa. Idan mutum ya
sami duma wanda ya bushe sai ya sa majaujawa ko sankiso ya fafe shi, da farko
za a cire hancin da gizago sannan a fafa daga tsakiyar hancin duman har a
zagayo amma sai an bi a hankali don kada duman ya tsage ko ya karkace.
Idan buta ce ko zunguru kawunansu kawai ake
yankewa, kurtun tawada kuma huda shi ake yi da wuta maimakon fafewa.
Mataki na biyu shi ne kankarewa. Maimakon
kankara wasu kan zuba wa duman ruwa su bar shi har sai dussar da ‘ya’yan ciki
sun cire, wasu kuma suna sa mahuri su kankare cikin. Shantu da gyanɗama da zunguru da kurtu kuwa waɗanda hannu ba ya shiga
cikinsu sai a yi amfani da siririn ƙarfe ko itace a kankare
cikinsu.
Mataki na uku shi ne gogewa, bayan an kankare
cikin ƙwarya sai gogewa. Ana amfani da gwangwani wanda
aka huhhuda da ƙusa ko soshiyar dawa ko soso a yi ta goge ƙwaryar har sai ta yi tsantsi. Shantu da zunguru da buta kuwa ana
goge bakinsu ne kawai don su daidaita.
Mataki na huɗu shi ne zane idan ana
buƙata. Ire-iren adon da ake yi sun haɗa da adon fira da adon
wuta da kuma na shafe. Akasari kusan ko wace ƙwarya ko wadda ba za a yi mata zane ba, ana shafa mata farar ƙasa ga zagayen bakinta. Idan adon fira za a yi, ana sa zarton
firar ƙwarya a yi alamar irin zanen da ake buƙata, sannan a bi alamomin da aka yi da wuƙar zanen ƙwarya, a kankare su har su fito da zanen ƙuru-ƙuru. Zanen wuta kuwa, sai ƙarfen da za a yi zanen ya yi ja-jawur sannan a ɗauko a zana abin da ake buƙata a jikin ƙwaryar. Adon Shafe kuwa ana yin shi da garura, ko tawada ko
farar ƙasa, ana amfani da gashin kaza ko toton kara a
yi shafen, yawanci an fi yi ma kayan ƙawa ko kwalliya ta adon
shafe.
3.4 Ire-iren Kayayyakin da Sana’ar Ƙorai ke Samarwa
3.4.1 Ƙwarya
Ƙwarya ma’aikaci ne da ake amfani da ita domin wanke hatsi ko
shinkafa da rege su a raba su da ƙasa da tsakuwa, akwai
wadda ake amfani da ita a yi wa jarirai wanka (masaki), akwai wadda ake amfani
a yi wankan magani da ita, haka kuma akwai ƙarama wadda ake amfani
da ita a sha rubutu da magani, sannan kuma akwai ƙwaryar da ake yin awon hatsi.
3.4.2 Ludayi
Ludayi na daga cikin abubuwan da ake samarwa
daga dangin ƙorai saboda ana samar da shi daga duma, yana da
mariƙi da maɗebi kuma yana kama
da ƙoshiya, sai dai ya fi ta zurfi. Akwai luduwa iri
biyu, ludayin tsama, wanda ake kira gwagwa da ludayin shan koko da fura da
kunu, kuma dukansu akwai manya akwai ƙanana. Shi ludayin tsama
ana huhhuda cikinsa ta amfani da wuta da bidar zanen wuta, ana amfani da shi
wajen tsame ɗan wake da kalwa.
3.4.3 Gora
Daga gora ana samar da abubuwa muhimmai da suka
haɗa da:
1. Buta wadda ake amfani da ita wajen yin alwalla.
2. Goran duma wanda ya kasu zuwa iri biyu kamar haka; Gyandaro, yana
da tsawo da babban ciki, ana amfani da shi wajen kaɗa nono da kuma shantali, wuyansa na da tsawo amma cikinsa ba ya da
girma sosai. Matafiya na amfani da shi su zuba ruwa idan za su yi tafiya.
3.4.4. Goran Su
Shi ma ana samar da shi daga duma, ta hanyar yin
‘yar ƙaramar ƙofa daga saman duma. Ana
amfani da shi wajen kamun kifi.
3.4.5 Shantu
Shantu dogo ne kuma ba ya da kauri sosai, ana
fafe sama da ƙasan shi, a yi masa kwalliya ya yi gwanin kyau.
Yana ɗaya daga cikin kayan kiɗan Hausawa, mata na amfani da shi wajen yin kaɗa da waƙa.
3.4.6 Talle
Yana kama da ƙwarya, ana fafe duman
daga sama wajen hancin don samar da shi. Masu kiɗan gwauraye ke amfani da
shi musamman lokacin azumi.
3.4.7 Kurtu
Kurtu ya kasu kashi biyu, akwai kurtun tawada da
kurtun maɗi (kurtun gyartaye). Kurtun tawada ƙarami ne bai kai rabin ƙoƙo ba kuma yana kama da kwallo, ana yi masa ‘yar ƙaramar huda daga sama wadda ba ta fi girman yatsa ba ana amfani da
shi wajen ajiye tawada. Kurtun maɗi kuwa yana da ɗan girma, a sifa yana kama da talle, ana amfani da shi wajen ajiye
maɗi da kabar da gyartaye ke ɗinke ƙorai da sauransu idan sun tsage.
3.4.8 Duman Kiɗa
Ana yin shi da duman ƙwarya babba, yana kama da talle da dundufa wanda ake samarwa daga
itace. Hausawa na amfani da duma su yi kiɗa lokacin bukukuwa da
wasu shagulgula.
3.4.9 Zunguru
Zunguru ma asalinsa daga duma ne, yana da kauri
fiye da shantu kuma dogo ne, sai dai tsawonsa ba ya wuce daga tafin hannu zuwa
gwiwa, mata na amfani da shi su yi ƙunshi.
3.4.10 Mara
Mara wadda ake samarwa daga ɓallin duma (sakaina). Akwai babba da ƙarama kuma tana kama da tafin hannu, ana amfani da ita wajen
kwashe tuwo da sauran abinci.
3.4.11 Ranwa
Ranwa ana yin ta daga ɗan kan goran da aka fafe, ɗan kan da aka cire shi
ake gyarawa a yi ranwa. Yara, akasari maza ke yin wasa da ranwa.
3.4.12 Fuska
Ana yin Fuska daga sakaina, sai a yi mata ƙofofi daidai saitin idanu, baki da hanci yadda za a samu iska da
yin magana idan an ɗaurata. Ana amfani da ita lokacin tashe, kafin a
fara amfani da bula ko zargina da akan shafa a wannan zamani.
3.5. Muhimmancin Sana’ar Ƙorai
Sana’ar ƙorai tana da matuƙar muhimmanci ga rayuwarmu saboda tana:
1. Samar da aikin yi ga masu sana’ar da masu sarin kayan da ake
samarwa daga sana’ar domin su sayar.
2. Samar da sana’ar gyartai, wato masu ɗinke duk wani abin da aka samu ta hanyar sarrafa duma.
3. Samar da kayayyakin amfani irin su ƙwarya da masaki da ludayi da ƙoƙo da mara da ludayin tsama da buta da gora da ‘yar kwalfa da
zunguru da sauransu.
4. Samar da kayayyakin kiɗi domin samun nishaɗi irin su molo da kuntugi da shantu da garaya da talle da ƙoroso da ƙwarya da sauransu.
5. Sun kasance abubuwan ado da kwalliyar muhalli ko wuraren shaƙatawa, da fadar Sarakunan ƙasashen Hausawa. Ana
amfani da ƙwarya da ƙoƙo da ludayi da kurtu a yi kwalliya a kakkafa a su a bangon ɗaki. Idan ludduna ne kuma, ba a fafe su sai a huɗa mariƙin daidai inda za a saka zare a rataye shi a
saman rufin ɗaki, ya yi ta reto gwanin ban sha’awa.
6. Amfani da fasassun ƙorai a samar da marar
kwashe tuwo da fuska, wadda masu tashe na Machukule ke amfani da ita, Tayoyi da
ake saka ma motocin wasa na yara da ranwa wadda yara ke wasa.
7. Sana’ar ta zamo taska ta adana al’adun Hausawa na gargajiya.
3.6. Tasirin Sauye-sauyen Zamani a Kan
Sana’ar Ƙorai
1. Wasu kayayyakin aiwatar da sana’ar na zamani sun canji na
gargajiya. Misali an daina amfani da majaujawa idan za a fafe duma, an koma
amfani da sankiso wanda zamani ya kawo.
2. A da, ana amfani da Soso da Soshiyar Dawa don a goge cikin kwarya
amma a yanzu an koma amfani da gwangwani wanda aka huhhuda ko soson ƙarfe.
3. A gargajiyance ana amfani da wuƙa a yi alama ko sheda na
irin zanen da za a yi wa ƙwarya kwalliya amma yanzu ana amfani da Zarton
firar kwarya wasu kuma suna yin alama da fensiri ko biro.
4. Amfani da kayayyakin amfani na duma irin su ƙwarya da ludayi da buta da sauransu ya yi rauni a yanzu, an koma
ga amfani da kayayyakin roba waɗanda aka sarrafa a zamanance. Hakan ya haifar da
samuwar kamfanonin da ke samar da su.
5. Raguwar amfani da kayayyaki dangin duma ya haifar da raguwar yawan
masu sana’ar.
4.0 Kammalawa
Sana’ar ƙore, sana’a ce wadda aka ɗaɗe ana yi kuma tana da matuƙar muhimmanci da babban matsayi ga rayuwar al’ummar Hausawa. Sana’ar ta taimaka wa ɗan adam wajen biya wa kansa buƙatun da suka taso masa, bugu da ƙari sana’ar ta taimaka wajen raya da adana al’adun gargajiya da samar da abubuwan amfani na yau da kullun a cikin gidaje. Abin lura a nan shi ne waɗansu daga cikin sauye-sauyen da aka samu cikin sana’ar sun kawo ci gaba wasu kuma sun taimaka wajen durƙusar da ita. Misali kayayyakin da ake aiwatar da sana’ar da zamani ya kawo sun taimaka wajen saurin yin aiki, sai dai kuma yanzu yawanci duk kayayyakin da ake samarwa ta sana’ar ƙore an yi masu kishiya, misali akwai kamfanoni yanzu waɗanda ke samar da kayayyaki da ake yin ayyuka da su, waɗanda suka maye gurbin ƙorai, irin su buta da bokiti na roba da farantai na cin abinci da manya da ƙananan robobi na ayyukan gida. Rage amfani da kayayyakin da sana’ar ke samarwa ta sa an samu babban giɓi a wannan sana’ar mai matuƙar muhimmanci ga rayuwa da al’adun Hausawa a wannan zamani.
Manazarta
Abdullahi, M. (2020). Feƙe da Adon Ƙwarya a Garin Gummi. www.amsoshi.com.
Alhassan, H. da Wasu (1982). Zaman
Hausawa. Islamic Bureau.
Ado, A. (2019). Ra'o’in Bincike kan
Al'adun Hausawa. Goɓernment Printing Press Nigeria.
Auta, A. L (2006). Tattalin Arzikin Al'umma:
Nazarin Sana'o'i da Kasuwancin Hausawa. Algaita Journal of Current Research
in Hausa Studies, No 4 Vol 1. Jami'ar Bayero.
Asma'u Suleiman (2021). Tasirin Zuwan Turawa kan
Sana'din Hausawa na Gargajiya. Federal University Dutsin-ma Journal of Hausa
Studies. Vol. 1 Number 1. Dutsin-ma Federal University.
C.N.H.N (2006). Ƙamusun Hausa.
Jami’ar Bayero.
Ɗangulbi, A.R. (2020). Nazarin Sana'ar Aruguma (ƙwarya). www.amsoshi.com.
Ɗan'iya, M.A. (2006). Tasirin Kimiyya da Ƙere-ƙeren Zamani a kan Sana'o'in Hausa na Gargajiya. Kabs Print Serɓices.
Hassan A (1988). Matsayin Sanadin Hausawa na
Gargajiya wajen Bunƙasa Tattalin Arzikin Nijeriya. Takardar da aka
gabatar a taron ƙara wa juna ilimi. Jami'ar Bayero.
Louis, E.J- (1974). Decoratiɓe Art of Africa. Colin St. James Palace.
Madauci, l. (1968). Hausa Customs.
Northern Nigerian Publishing Company.
Newman, TR. (1972). Contemporary African
Art Craft. George Union Limited.
Prince, C. (1968). Made in West African
Studies. London Press.
Sa'idu, S. da Wasu. (2004). Sana'ar Ƙorai. ƊKundin binciken da aka gabatar don samun Diploma
ta Ƙasa a Katsinaɗ. Hassan Usman Katsina
Polytechnic.
Tukur, A (1990). Sanadin Gargajiya (HS 204)
Laccar Aji Kano: Jami'ar Bayero.
Yahya, l. Y. da Wasu (1992) Darussan
Hausa don Makarantun Sakandare na 2. University Press, Nigeria.
Waɗanda Aka Tattauna da su:
Tattaunawa ta Musamman da Malam Badamasi Sa'idu,
Kasuwar 'yar laraba. 20/01/2005.
Malam Iro Sani Kasuwar 'yar Kutungu, Katsina
12/03/2005.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.