TAMBAYA TA 3091
Assalamu alaikum
barka da warhaka Malam da fatan malam yana cikin koshin lafiya.
Tambayana shi ne mene ne matsayin wanda ya kashe kansa?
A ranan tashin kiyama
shin zai dauwama ne a cikin wutan jahannama ne ko akwai wa'adin fitarsa?.
AMSA
Wa alaikumus salam wa
rahmatullahi wa barakatuhu.
Hakika kisan kai ko
kuma mutum ya kashe kansa, babban laifi ne a addinin Musulunci. Kuma Allah mai
girma da ɗaukaka ya haramta wa
bayinsa yin haka. Allah ya ce "KADA KU KASHE KAWUNANKU, HAKIKA ALLAH
TABBAS MAI JIN ƘAI NE GAREKU".
"WANDA DUK YA
AIKATA WANNAN DOMIN KETARE IYAKA DA KUMA ZALUNCI, DA SANNU ZAMU SHIGAR DA SHI
WUTA, KUMA YIN HAKAN YA KASANCE ABU NE MAI SAUKI GA ALLAH".
A cikin hadisai da
dama, Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya yi bayanin cewa duk wanda ya
kashe kansa ta wata hanya, to zai dawwama a wutar jahannama ana azabtar da shi
da wannan abin da ya kashe kansa din.
Misali akwai hadisin
Sayyiduna Abu Hurairah (radhiyallahu anhu) wanda Manzon Allah (Sallallahu
Alaihi Wasallam) ya ce:
"Duk wanda ya
fado da kansa daga saman wani tsauni kuma ya kashe kansa, to hakanan zai
kasance yana jefo da kansa awutar jahannama har abada.
Duk wanda yasha guba
ya kashe kansa, to hakanan zai dawwama a wutar jahannama yana kwankwadar guba.
Wanda ya kashe kansa
da wani Ƙarfe, to zai rike wannan Ƙarfen nasa a hannunsa
yana chakawa a cikinsa a cikin wutar jahannama.
Sannan akwai wata
ruwayar itama ta Bukhariy da Muslim din ce, daga Sayyiduna Thabitu bn Dhahhak,
(radhiyallahu anhu) ya ce Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce:
"DUK WANDA YA
KASHE KANSA DA WANI ABU, TO za a AZABTAR DA SHI DA WANNAN ABUN A RANAR ALƘIYAMAH".
Sai dai Malamai sun
yi saɓani game da shin
wanda ya kashe kansa, zai dawwama ne a wutar jahannama ko kuwa akwai ranar
fitarsa?
Mafiya rinjaye sun ce
kalmar "KHALIDAN MUKHALLADAN" da ta zo a cikin hadisan ba wai tana
nufin dawwama ne har abada ba. A'a tana nufin dai za a yi musu azaba mai tsawo
ne. Amma akwai ranar fitarsu.
Sun kafa hujjah da
cewa ai laifin kashe kai ba shirka ba ne. Kuma shirka ne kaɗai laifin da Allah ya
ce ba zai gafarta wa wanda ya mutu yana yinsa ba. Amma duk wani laifi komai
girmansa Allah yana iya yafewa wanda ya aikatashi.
Sannan sun ce kalmar
"KHALIDAN" din nan ba ta zo a cikin riwayar Imamul Bukhariy ba. A
cikin riwayar Muslim ne kawai tazo. Kuma Bukhariy yana gaba da Muslim. Don haka
malaman hadisi suke ganin cewar kalmar nan ba ta inganta ba.
Wasu malaman kuma
suka ce an ambaci dawwama ne a cikin maganar domin a tsoratar da mutane kada su
aikata laifin.
Amma dai abin da
Maluman Ahlus Sunnah sukayi ittifaki ko ijma'i akansa shi ne duk wanda ya mutu
bisa imani, to ba zai dawwama awuta ba. Komai girman laifin da ya mutu yana yi,
in dai ba shirka ba ne, to akwai ranar fitarsa daga wuta.
WALLAHU A'ALAM.
ƘARIN BAYANI
Tambaya:
Wanda ya kashe kansa, shin zai
dawwama ne a wutar Jahannama ko kuwa akwai wa’adin fitarsa?
Amsa:
Wa Alaikumus Salaam wa
Rahmatullahi wa Barakatuhu.
Hakika kisan kai, ko kuma kashe
kansa da gangan, babban zunubi ne a Musulunci. Allah Mai girma da ɗaukaka Ya haramta wa
bayinsa yin haka, Ya ce:
القرآن الكريم – سورة النساء: 29
وَلَا تَقْتُلُوا أَنفُسَكُمْ إِنَّ اللَّهَ
كَانَ بِكُمْ رَحِيمًا
“Kada ku
kashe kanku; lalle Allah Mai jin ƙai ne gareku.” (Surah An-Nisaa’:
29)
Manzon Allah ﷺ ya bayyana a cikin
hadisai cewa duk wanda ya kashe kansa ta wata hanya, zai fuskanci azaba daga
Allah saboda wannan laifi. Misali:
حديث – صحيح البخاري و صحيح مسلم
Abu Hurairah (radhiyallahu anhu)
ya ruwaito cewa Annabi ﷺ
ya ce:
“Duk wanda ya
fado daga wani wuri ya kashe kansa, zai dawwama a wutar Jahannama yana jefo da
kansa. Duk wanda ya sha guba ya kashe kansa, zai dawwama a wuta yana kwankwadar
guba. Duk wanda ya kashe kansa da wani ƙarfe, zai riƙe wannan ƙarfen
a hannunsa yana chakawa a cikinsa a wutar Jahannama.”
“Whoever
kills himself with something, he will be punished with it on the Day of
Resurrection.” (Sahih Muslim, Thabit bn Dhahhak, r.a.)
Wasu malamai sun yi saɓani akan ko wannan azaba za
ta dawwama har abada ko kuwa akwai wa’adin fitarsa daga wuta.
Ra’ayin mafi rinjaye:
Kalmar “خَالِدًا”
(Khalidan – dawwama) da ta bayyana a cikin wasu hadisai ba lallai ta nufin har
abada ba ce. Ana fassara ta ne a matsayin azaba mai tsanani da tsawo, amma
Allah Mai Rahama yana iya gafarta wa wanda ya yi wannan zunubi idan ba ya cikin
shirka.
Dalilin wannan ra’ayi:
1. Laifin kashe kai ba shirka ba
ne, shirka shi kadai ne laifi da Allah Ya bayyana cewa ba zai gafarta wa wanda
ya mutu a ciki ba. Duk wani laifi da mutum ya aikata, Allah yana iya gafarta wa
wanda ya mutu bisa imani.
2. Riwayar da ta ambaci
“Khalidan” ba ta zo a cikin Sahih Bukhari ba, sai a riwayar Muslim, kuma
Bukhariy ya fi Muslim a matsayin ingancin riwaya. Wannan ya sa wasu malaman
hadisai ke ganin cewa kalmar ba ta da tabbacin nuna dawwama har abada.
3. Wasu kuma sun ce an ambaci
wannan hukunci ne don tsoratar da mutane daga aikata wannan babban zunubi.
Ittifaqin Ahlus Sunnah:
Duk wanda ya mutu cikin imani, ba
zai dawwama a wutar Jahannama ba, komai girman zunubinsa. Idan laifin da ya
aikata ba shirka ba ne, akwai wa’adin fitarsa daga wuta.
Wallahu A’lam.
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.