Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Wanda Ya Kashe Kansa Bayan Ya Aikata Luwadi

HUKUNCIN WANDA YA KASHE KANSA BAYAN YA AIKATA LUWAƊI

TAMBAYA TA 3231

Assalamualaikum malan Ina yini

Malam na ce idan mutum ya aikata luwaɗi sannan ba a yi masa hukunci ba sai ya kashe kansa

Me hukunci sa?

AMSA

Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Wanda ya aikata haka tabbas ya aikata manyan laifuka guda uku wadanda ukubar da ke cikin kowannensu mai girma ce.

Laifin farko shi ne aikata luwaɗi. A cikin Alƙur'ani Allah ya ba mu labarin cewa shi dai luwaɗi laifi ne mummuna wanda babu wanda ya taɓa aikatashi a cikin halittu baki ɗaya sai mutanen Annabi Luut (alaihis salam). Harma a cikin Suratul Anbiya Allah ya ce "HAKIKA SU MUTANEN BANZA NE FASIKAI".

Daga ƙarshe kuma Allah ya fadi irin hallakar da ta samesu tun daga nan duniya. An kifar da su da garin nasu, an yi musu ruwan duwatsun garwashin wutar jahannama.

Shi ya sa ma Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce "ALLAH YA TSINE WA DUK WANDA YAKE AIKATA IRIN AIKIN MUTANEN ANNABI LUUT (ya fada ya maimaita har sau uku). Imamu Ahmad ne ya riwaitoshi).

Sayyiduna Abubakr da Sayyiduna Aliy bn Abee Talib da Sayyiduna Khalid bn Waleed da Sayyiduna Abdullahi bn Zubair sun ce wajibi ne haddin ɗan luwaɗi ya fi na mazinaci tsanani.

Kasancewar ba a yi masa haddi ba, wannan ba zai zama dalilin da zaije ya kashe kansa ba. Domin hakika kisan da ya yi wa kansa ba zai rage komai cikin azabar da Allah zai masa ba. Hasali ma ya Ƙara aikata wani zunubin ne mafi muni daga wancan. Domin banda shirka babu wani zunubin da ya kai kisan kai girma a wajen Allah.

A cikin Hadirhin Abu Huraira wanda Imamul Bukhara da Muslim suka riwaito, Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce:

"Duk wanda ya gangarar da kansa daga kan wani dutse (Ko abu mai tudu) Kuma ya kashe kansa, to hakanan zai rika jefo kansa zuwa cikin wutar jahannama har abada, kuma shi abin dawwamarwa ne a cikinta har abada.

"Wanda kuma yasha wata guba (poison) har ya kashe kansa, to wannan gubar za ta kasance a hannunsa zai ci gaba da kurbarta a cikin wutar jahannama har abada, kuma shi abun dawwamarwa ne a cikinta".

"Wanda ya kashe kansa da wani karfe (kamar wuka ko takobi ko bindiga) To wannan makamin zai kasance ahannunsa zai ci gaba da chakawa (ko yankawa ko harbawa) a cikinsa har abada a cikin wutar jahannama kuma shi abun dawwamarwa ne a cikinta"

 (Sahihul Bukhariy hadithi na 5442 da Sahihu Muslim hadithi na 109).

Hakika babban dalilin da zai kaishi ga jashe kansa ba zai wuce fidda tsammani daga samun rahamar Allah ba. Kuma shi ma wannan babban laifi ne.

Sayyiduna Abdullahi bn Abbas (radhiyal-Lahu anhuma) ya ce "Wani mutum ya tambayi Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) cewa: "Ya Rasulallahi mene ne kaba'ira? "

Sai ya ce "YIN SHIRKA DA ALLAH DA FITAR DA TSAMMANI DAGA RAHAMAR ALLAH..."

Amma fa duk da haka bai kafirta ba. Musulmi ne shi don haka ya halatta sauran Musulmai su yi masa wanka su sallaceshi, kuma ya halatta ka yi masa addu'ar samun gafara da afuwar Ubangiji.

WALLAHU A'ALAM.

ƘARIN BAYANI

Tambaya:

Mene ne hukuncin wanda ya kashe kansa bayan ya aikata laifin luwaɗi?

Amsa:

Wa Alaikumus Salaam wa Rahmatullahi wa Barakatuhu.

Wanda ya aikata wannan aiki, tabbas ya aikata manyan laifuka guda uku, dukkaninsu manya ne a wajen Allah. Laifi na farko shi ne aikata luwaɗi, wanda Allah Ya bayyana a Alkur’ani a matsayin mummunan zunubi wanda babu wanda ya taɓa aikatawa a cikin halittu sai mutanen Annabi Lût (alaihis salam). Allah Ya ce:

القرآن الكريم – سورة الأنبياء: 74-75

وَأَهْلَ لُوطٍ إِذْ قَالُوا لَهُ أَخْرِجْ قَوْمَكَ هَـٰذِهِ فِجْرَةٌ إِنَّهُمْ أُنَاسٌ يَسْعَوْنَ فِي الشَّهْوَةِ… فَجَعَلْنَا الَّذِينَ آمَنُوا وَالَّذِينَ هَاجَرُوا فِي أَرْضِ الْبَرَارِي … وَأَهْلَكَ أُمَّهُمْ فَجَعَلْنَاهُمْ غُثَاءً

Kuma mutanen Lût, sa’ad da suka ce masa: Fitar da mutanen ka! Lallai waɗannan mutane ne masu zunubi, suna aikata abin banza… Sai Mu tsira da waɗanda suka yi Imani da waɗanda suka hijira, sai Mu halaka mutanen su, Mun mayar da su garwashin ruwaya.” (Surah Al-Anbiyaa: 74-75)

Annabi ya ce:

Allah Ya tsine wa duk wanda yake aikata irin aikin mutanen Annabi Lût.” (Riwayar Imam Ahmad)

Laifi na biyu shi ne kashe kai, wanda babban zunubi ne a Musulunci. Annabi ya bayyana:

حديث – صحيح البخاري: 5442; صحيح مسلم: 109

Duk wanda ya gangarar da kansa daga wani dutse ko wani abu mai tudu, zai rika jefo kansa cikin wutar Jahannama. Duk wanda ya sha guba har ya kashe kansa, zai rika riƙe gubar a hannunsa a wutar Jahannama. Duk wanda ya kashe kansa da wani ƙarfe (kamar wuka, takobi, ko bindiga), wannan makamin zai kasance a hannunsa yana chakawa a cikinsa a wuta.”

Wannan ya nuna cewa kashe kai babban zunubi ne, kuma yana kara zunubi ga wanda ya riga ya aikata babban zunubi kamar luwaɗi.

Dalilin da yasa mutum zai iya kaiwa ga wannan kisan kai shi ne fidda tsammani daga rahamar Allah, wanda shi ne babban zunubi a Musulunci. Sayyiduna Abdullah ibn Abbas (radhiyallahu anhuma) ya ruwaito cewa wani mutum ya tambayi Manzon Allah :

Ya Rasulullah, menene kabairi (manyan zunubai)?”

Annabi ya ce:

Shirka da Allah, da fitar da tsammani daga rahamar Allah.”

Ko da yake mutum ya aikata wannan laifi, muddin ya mutu cikin imani, har yanzu musulmi ne, kuma ya halatta sauran Musulmai su yi masa wanka, su yi sallarsa, su yi addu’a ga Allah ya gafarta masa. Wannan yana nuna cewa duk da girman zunubi, Allah Mai Rahama yana da iko ya gafarta wa bayinsa.

Wallahu A’lam.

 ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments