Ticker

6/recent/ticker-posts

Abin Da Yake Kai Ga Kashe Mutum

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Mene ne yake kai ga a kashe Musulmi ko Wanda ba Musulmi ba a Shari’a?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam.

Inna Lillahi wa inna Ilaihi Raji’una, Lallai rai a gurin Allah tana da daraja kuma Allah ya haramta kashe ta:

وَمَنْ يَقْتُلْ مُؤْمِنًا مُتَعَمِّدًا فَجَزَاؤُهُ جَهَنَّمُ خَالِدًا فِيهَا وَغَضِبَ اللَّهُ عَلَيْهِ وَلَعَنَهُ وَأَعَدَّ لَهُ عَذَابًا عَظِيمًا

Kuma wanda ya kashe mumini da gangar, to sakamakonsa Wutar Jahannama ce, yana mai dawwama a cikinta, kuma Allaah ya yi fushi da shi, kuma ya la’ance shi, kuma ya yi masa tattalin azaba mai girma. (Surah An-Nisaa’: 93).

Hadisi ya inganta daga Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam Ya ce duk wanda ya taimaka wajen kashe wata rai, to ba zai ji kanshin Aljanna ba ko ba zai samu rahamar Allah ba.

Hakika halin kunchi da muke ciki a duniyar na je riya ta yau, baya rasa nasaba da kisan rayukan da ba su ji ba, ba su gani ba. Allah ya shiryemu.

Rayuwar Musulmi da na wanda ba Musulmi ba, duk rayuka ne masu alfarma a waje Allah SWT. Kuma Allah ya hana kashe ko wace irin rai ne ba tare da hakki ba. A musulunci hukuma kaɗai takeda hurumin kissa idan hukunci ya tabbata cewa mutum ya yi ɗaya daga abubuwa masu yawa, ga kaɗan daga cikin wanda nassi ya zo da su:

1. Idan mutum ya kashe wani kisan ganganci, to shi ma Shari’ah za ta kashe shi.

2. Idan mutum ya ba da haɗin kai ko goyon baya ko ya taimaka wajen kashe wani, kuma Shari’ah ta zartar masa da hukuncin kisa.

3. Ma-auraci kuma ma-zinacin da Shari’ah ta yanke masa hunkun kisa.

4. Riddajen Musulmin da Sari’ah ta yanke masa hukuncin ridda.

5. Ɗan fashin da shariah ta zartar masa da hukuncin kisa.

6. Ɗan taaddan da ke kashe mutane da makami, bindiga, ko bam, ko kwaya da sauran muyagun yanyoyin taaddancin da Shariah ta bayyana.

7. Mai Luwaɗi da wanda ake yin luwaɗin da shi.

8. Mutumin da ya hana zakka.

9. Mutumin da ya bar Sallah.

10. Mutumin da ya yi tawaye ga shugaban da al’umma suka yi wa Mubaya’ah.

11. Mutumin da ya jakoranci tawaye ga shugaba.

12. Idan aka yi wa mutane biyu Mubaya’ah, to akashe danyansu idan suka ki dai-daitawa.

13. Mutumin da ya raba kan al’umma.

14. Mutumin da yake fasadi kuma yana yaɗa shi abayan kasa.

A ƙarshe, dukkan abin da hukuma ta yanke hukuncin kisa akai, to ya zamo dalili na kashe mutumin da ya taka wannan hukunci. Allah shi ne mafi sani.

Ya Allah! Ka taimaki shugabanni da hukumomi wajen tsare rayukan al’umma da dukiyar su. Amin.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...

ƘARIN BAYANI

Mene ne yake kai ga kashe mutum a Shari’a, ko Musulmi ne ko wanda ba Musulmi ba?

Amsa:

Alhamdulillahi, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu, Annabi Muhammad . Rayuwa ce daga cikin manyan ni’imomin Allah kuma tana da daraja sosai. Allah Ya bayyana a cikin Alkur’ani cewa kashe rai ba tare da hujja ba haramun ne, kuma yana ɗauke da hukunci mai tsanani:

القرآن الكريم – سورة النساء: 93

وَمَنْ يَقْتُلْ مُؤْمِنًا مُتَعَمِّدًا فَجَزَاؤُهُ جَهَنَّمُ خَالِدًا فِيهَا وَغَضِبَ اللَّهُ عَلَيْهِ وَلَعَنَهُ وَأَعَدَّ لَهُ عَذَابًا عَظِيمًا
“Kuma wanda ya kashe mumini da ganganci, to sakamakonsa Wutar Jahannama ce, yana mai dawwama a cikinta, kuma Allah ya yi fushi da shi, ya la’ance shi, kuma Ya tanadar masa azaba mai girma.” (Surah An-Nisaa’: 93)

Hadisi daga Annabi Muhammad ya ƙara tabbatar da girman wannan haramci:

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ ﷺ: "مَنْ يَقْتُلُ نَفْسًا فَلَا يَجِدُ رَائِحَةَ الْجَنَّةِ وَلَا يَرْحَمُهُ اللَّهُ"

“Duk wanda ya taimaka wajen kashe rai ba tare da hujja ba, ba zai ji kamshin Aljanna ba, kuma Allah ba zai yi masa rahama ba.” (Sahih Bukhari da Muslim)

A Musulunci, rayuwar kowa – Musulmi ko wanda ba Musulmi ba – tana da daraja. Allah Ya haramta kashe kowa ba tare da hujja ba. Hukuncin kisa a Shari’a yana faruwa ne kawai lokacin da hujjoji suka tabbatar da cewa mutum ya aikata wani laifi da nassoshi suka bayyana:

  1. Kisan ganganci: Idan mutum ya kashe wani da gangan, Shari’a na ba da izinin hukuncin kisa.
  2. Taimako wajen kisa: Duk wanda ya bada goyon baya ko ya taimaka wajen kashe mutum.
  3. Laifuka masu nasaba da zina ko rashin biyayya: Misali, maza da mata masu yin zina da hukuncin kisa, ko wanda ya yi ridda (taɓarɓarewar addini).
  4. Ta’addanci: Ɗan ta’addan da ke kashe mutane da makami, bam, ko kwayoyi.
  5. Fasadi a ƙasa: Mutanen da ke yada fitina, hana zakka, barin sallah, ko raba kan al’umma.

Wannan tsarin hukunci yana nuna cewa Shari’a ba ta yarda da kashe rai ba tare da adalci ba, kuma duk wanda aka yanke masa hukuncin kisa bisa Shari’a, wannan ne kawai dalilin da zai sa a kashe shi.

Daga karshe, muna roƙon Allah:

“Ya Allah! Ka taimaki shugabanni da hukumomi wajen kare rayukan al’umma da dukiyarsu, Ka tsare mu daga zalunci da rashin adalci. Amin.”

Rayuwar ɗan Adam babban amanar Allah ce. Duk wani yunkuri na kashe mutum ba bisa ka’ida ba babban zunubi ne kuma yana kai mutum zuwa fushin Allah da azaba mai girma.

 ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments