Ticker

6/recent/ticker-posts

Wanda Bai Ji Bari Ba…

Nana Aicha Hamissou (2023). Wanda Bai Ji Bari Ba…. Ɗaukar Jinka (Labaran Da Suka Samu Nasara A Gasar Gajerun Labarai Ta Arc. Ahmed Musa Dangiwa, 2022). Kangiwa Multimedia and Communication Company LTD

WANDA BAI JI BARI BA...

Na

Nana Aicha Hamissou

Tun daren jiya da na yi tozali da taliya gidan Hajiya Marka, yawuna yake tsinkewa, harshena ya kwaɗaitu da ɗanɗana ta, sai dai kash! Tsabar rowarta sai dawowa gida na yi ina haɗiyar yawu, duk yadda nake muradin ta. Ladar wankin da na shafe awanni ina yi, sai ƙarshen wata za a ba ni ballatana na sayo taliyar da kuɗin. Ga shi ba ni da ko sisi, ko wata kadarar da zan bayar a musanya mini da taliya. Mamaki! Kwalli a kunne. Ni da taliya ba ta sha mini kai ba, nake haɗa yawu a kanta, lallai da walakin gishiri a ruwa.

Kawar da mamakina na yi ta hanyar yafa gyalena ina ficewa daga ɗaki, a falo na tarar da Habib yana latsa waya. Kallo guda na yi masa na kawar da kai haɗe da ficewa, ba tare da na amsa tambayar da yake yi mini ba akan inda zan tafi. Haushinsa ya cika mini zuciya, da a ce ya tashi tsaye ya nemi na kansa har ni Maryam Alhaji Mansur taliya za ta gagara?

Kaina na ji yana sara mini tamkar zai fashe, na dafe shi ina tunanin rashin shan haɗin da na saba yi ne ya haifar mini shi, wanda matsalar kuɗi ce ta yi mini shamaki ga muradin nawa.

Ina kaiwa daidai shagon Ɗan-Sala na ja gefe ina jiran mutane su ragu, kafin na je masa da kokon barata kamar yadda na saba. Bayan ya ba ni bashin sirof, na shanye shi tas tun a hanya. Sannan na yi gaba zuwa gidan Alhaji Na-Hantsi, ɗayan gidan da nake musu wanki, ko zan samu wani abu cikin albashina.

Ban san me ya sake faruwa ba, sai tsintar kaina na yi a gadon asibiti, hannuna da ƙarin ruwa. Ko ranar da iyayena suka rasu ban yi irin kukan da na yi yau ba, sakamakon abin da ya yi silar tsintar kaina a asibiti da aka sanar da ni. Watau shigata falon gidan santsi ya kwashe ni na zube sai jini aka ga yana bin ƙafafuwana, dalilin da ya sa aka kawo ni asibiti. A nan aka tabbatar da ɓarin ciki na yi sakamakon faɗuwar. Silar shan kayan maye na yi asarar gudan jinina wanda na shafe shekaru ina nema, wanda nake tunanin zai yi mini addu’a bayan ƙasa ta rufe idona.

Na same shi a lokacin da na yanke tsammani, sai dai rashin sani ya fi dare duhu. Ban san ina da juna biyu ba, ban san yaya aka yi na kasa ganewa ba. Sai yanzu da lokaci ya ƙure mini ƙwaƙwalwata take tuno mini ƙwaɗayin taliyar da nake yi yana da alaƙa da cikin. Ban taɓa nadamar auren Habib ba sai yau, ban taɓa jin tsanar shi ba kamar yau. Shi ne silar jefa ni cikin ƙaddararriyar rayuwa wacce ko maƙiyina ba na yi wa fatan irinta. Abin da ya fi damu na a halin yanzu shi ne zubewar cikina, yaya zan yi ya dawo? Ba zai yiyu ba jirgin ƙasa saman gajimare, hannun agogo ba zai taɓa dawowa baya ba. Wanda ya tuna bara, bai ji daɗin bana ba, na yarda da azancin nan saboda ko kaɗan ba ni son tuna rayuwata ta baya, sakamakon irin gatan da na taso cikinsa amma ƙaddararren auren Habib ya sauya mini rayuwa daga haske zuwa duhu. Silarsa na aikata babban zunubin da ba zan iya yafe wa kaina ba. Shafa cikina na yi ina fashewa da kuka, hawaye suna ambaliya daga ƙoramar idanuwana suna gangarowa saman kuncina. Radaɗi da zugin da jikina yake mini, ba su kai kwatar zafin da nake ji a zuciyata ba sa’ilin da nake tuna rayuwata, daga lokacin da ƙaddara ta haɗa ni inuwa guda da Habib a matsayin ma’aurata.

Kamar yadda na samu labari, Habib da kuɗin gadon wajen mahaifinsa ya aure ni, aka sha biki na kece-raini. Yana tunanin bayan aure zai samu aikin ofis. Sai dai aiki ya ce ɗauke ni inda ka ajiye ni, duk inda yake tunanin zai samu aiki ya je amma magana ɗaya ce ɗan wuta ya ga kafiri. Maimakon ya fara sana’ar hannu sai ya yi kunnen uwar-shegu da zancen sana’a. Ba shi da wata magana sai tunanin aikin ofis saboda yana da kyakyawan sakamako.

Abin da ya kasa ganewa akwai waɗanda suka zarta shi kyakkyawan sakamako, suna kasuwanci ko aikin ƙarfi, ba su yi kwance sai an kashe an ba su ba balle takaici ya kashe su. Kullum sai ya fita nema ko zai dace amma tamkar an aiki loma kewayar moƙoshi. Kasancewar ina aikina sai ya zamana ni ce na ci gaba da jan ragamar gidanmu bayan kuɗin hannunsa da garar aure sun ƙare.

Ina da shekara biyu da aure iyayena suka samu hatsarin mota suka rasu. Bayan an ba ni gadona gabaɗaya na damƙa masa, burina ya fara juya su ko kukanmu zai ƙare. Don albashina ba wani isar mu yake yi ba, don ma ban haihu ba har a lokacin, da abin sai ya yi mana yawa. Tiryan-tiryan na yi masa bayanin abin da nake so a yi da dukiyar, watau sayar da kayan masarufi da kayan miya. Na yi masa bayanin sanaa ce wacce ko ba mu yi ciniki ba, muna iya ɗauka ciki mu ciyar da kanmu. Ballatana mai sana’ar kayan miya rana ba za ta taɓa fitowa ta faɗi ba tare ya yi ciniki ba.

Yini guda cur ya kwashe a waje, ina tunanin yana can kasuwa yana sayayyar sai dai me zai faru? Dila guda ta kaya ya shigo da ita irin su shaddodi; yadi; kayan ado na maza da sauran su. Mamaki ya hana ni magana har ya gama buɗe kayan, ido ne nawa ba tare da na ce uffan ba. Don ba haka na so ba, ra’ayina sana’ar kayan masarufi amma ya ɓige da saɓanin ra’ayin nawa.

Cikin wani irin yanayi nake tuhumarsa akan me ya sa zai yi hakan? Waɗannan kayan ba su da wani ciniki na a-zo-a-gani a zamanin da muke ciki, me ya sa ya ƙi amfani da shawarata akan sayo kayan masarufi kamar yadda na yi masa bayani? Wani ƙululun bakinciki ya samu matsuguni a maadanar sirrina sakamakon amsar da ya ba ni wacce ta shayar da ni gubar mamaki. Wai kayan jiki ne ya sayo masu kyau da tsada, idan ya ɗinka su yana zuwa neman aiki ba zai sha wahalar samu ba.

Za a yi tunanin ɗan wani ne shi, da ma an fi hana ‘ya’yan talakawa aiki. Saura kaɗan na zube ƙasa lokacin da yake sanar da ni bahagon hangensa. Ko kaɗan bai kula da yanayin fuskata ba, ya nuna mini sabuwar waya ƙirar iPhone, yana sanar da ni idan ana ganin sa da ita zai samu aiki, saboda tsadar wayar kuma ba kowa ya san ta ba. Ban gama shan mamaki ba sai da ya sake nuna mini makullin mota, yana faɗa mini su ne abin da sayo da kuɗin, ya san zuwa wannan lokacin babu wata ma’aikata da za a gan sa da mota a hana shi aiki.

Tsabar takaici ban kalle shi ba na shige ɗaki ina mamakin rayuwarsa, mutum har mutum amma ya ɗauki burin duniya ya ɗora shi ga aikin ofis? Aikin da in har kana da ƙwaƙwaran sanaar da za ka tsaya da kafafuwanka ta fiye maka shi, kodayake ya riga da ya kurumce sai fatan Ubangiji Ya taro shi. Dayake ya yi mugun ba ni haushi ko kuɗin da ya kashe ban tambaye shi ba, shi ɗin ma bai ce mini komai ba sai faman kiɗansa da rawarsa yake yi.

Haka ya fara fita da sabbin kaya da takardun karatu a hannu. Nan nake jira na ji ya samu aiki amma tsit kamar Malam ya ci shirwa. A haka aka kuma kwashe wasu shekaru lokacin sabbin kayan da yake tunƙaho yana da su sun fara tsufa, kuma ya daina fita a-kai-a-kai neman aiki, hatta motar ba kullum yake fita da ita ba saboda ba ruwa zai tayar da ita ba. Dukiyar gadona miliyoyin kuɗi ta lalace cikin lokaci ƙanƙane. Abu biyu kaɗai na fita da su gidan da muke ciki wanda na ci gadonsa sai firij da na saya ina sayar da zobo.

Watarana na tashi ba kuɗi sosai a hannuna, sakamakon kwana biyu ba mu samun wuta ba, ban samu na yi zobo ba, ga kuma wata ya yi nisa. Kuɗin motar tafiya aiki kaɗai nake da, na yi latti ballatana na tafi a ƙafa idan na dawo na hau mota. Babu yadda na iya na tafi a mota, a hanyar dawowata ban ankara ba sai na ji an yi sama-sama da ni an zube ƙasa, mai mashin ya kaɗe ni. Babu tsoron Allah haka ya ɓace wa ganina, a galabaice aka samu wasu suka tafi asibiti da ni. Bayan gwaje-gwaje aka tabbatar na karye a ƙafa sai an mini ɗori. Tashin hankali! Wanda ba a sa masa rana! Haka Habib ya shiga fafutukar neman inda zai samu kuɗi, mahaifiyarsa ba ta da shi, ita ma ta kanta take yi. Shi ne babba kuma bai nema ba balle ya amfane su. A haka na wuni ba a yi mini aiki ba, azaba ta addabe ni. Ni kuma dangina ban neme su ba bayan na samu gadona bare na nemi taimakonsu. Sai washegari ya samo kuɗi aka yi mini aiki. Ban tambaye shi inda ya samo ba don a lokacin burina na samu waraka.

Haka muka ci gaba da jinya a asibiti, har aka sallamo mu. Washegarin ranar da aka sallamo mu tun da safe ina kwance nake jin hayaniya, cikin matuƙar tsoro na ji yara suna ihun yansanda sun tafi da Habib. Tashin hankali! Faɗa da maigari ranar salla! Ina zan sa kaina? Duk iya tunanina amma ban hasaso abin da zai sa a kama shi ba. Haka na wuni na kwana cikin ƙunci, da ƙunar zuciya ina tunanin mijina. Ban sake tozali da shi ba sai bayan kwana biyu, shi ɗin ma tare da ‘yansanda ne ya shigo. Kai tsaye ɗakinsa ya wuce, bai jima ciki ba suka kuma tafiya ba tare da sun ce mini ci kanki ba.

Ban sake tozali da shi ba sai da yamma, a nan yake sanar mini kuɗin da aka yi mini aikin asibiti ne ya ranta. Mutumin ne ya kai sa ofishin ‘yansanda, yanzu motarsa aka sayar a wulakance aka biya shi kuɗinsa. Na yi kuka sosai cikin tausaya wa mijina, da kuma taurin kai irin nasa. Sauran kuɗin da suka rage na motar na ba shi shawarar me zai hana ya saro kayan miya ko cikin gida mu riƙa sayarwa? Amma dayake har a lokacin bai saduda ba sai ya shafa wa idonsa toka ya ƙi ɗaukar maganata, a cewarsa ba zai iya sana’ar nan ba. Babbar damuwata albashina ya tsaya tun da ba aikin gwamnati ba ne, balle na ci gaba da ɗauka har zuwa lokacin da zan ji sauki. A haka muka dawo da rayuwa yau daɗi gobe godiyar Ubangiji, watarana mu ci watarana sai mu yi kwana biyu ba mu ci ba. Ga shi ina jinyar ɗori ya kamata a kula da ni amma ban samun wata kulawa ta a-zo-a-gani ba, don daga kwance nake haɗa zobo shi kuma ya saka a firij.

Bayan shafe watanni kwance na koma ma’aikatar da nake aiki suka ba ni haƙuri sun samu madadina, ba zai yiyu a bar wuri ba kowa ba, saboda kamfanin aika kuɗaɗe ne na gari-gari da ƙasa-ƙasa. A hanyar dawowa saura kaɗan a kaɗe ni saboda tsabar rashin nutsuwa. Sai ga ni da kuka a hanya kamar wacce aka yi wa mutuwa. Da na iso gida kuka na fashe wa Habib da shi akan lallai sai ya fara sana’a amma haka ya kalallame ni da romon baka da kalamansa na yaudara, wai na ci gaba da yi masa addu’a wataran sai labari, yana ji a jikinsa zai samu aiki. Babu yadda na iya na zuba wa sarautar Allah ido. Babu iyayena balle na kai musu kokon barata su taimake ni, sauran dangina kuwa ban kula da su ba bayan na samu gadona balle na tunkare su. Ga shi mu biyu ne a wajen iyayenmu, yayata tana ƙasar waje ita da mijinta. Ko labarinta na daina samu tun da ba waya a hannuna.

Tun daga wannan ranar abubuwan da suka haskaka rayuwata suka fara gushewa, wani duhu ya fara mamaye ta. Babu yadda ban yi da Habib ba akan ya sayar da iPhone ɗinsa, amma ya ƙi. Sai dai mu kwana da yunwa ina ji ina gani ga kadarar da za mu iya sayarwa amma Habib ya ce bai san zancen ba. Ai kuwa olsa ta kayar da shi har da zaman asibiti na kwana biyu.

Muna can asibitin aka shigo aka sace mana firij ɗin da muke taƙama da ita, wanda shi kaɗai ya yi mini sauran da zan bugi ƙirji in ce ina da shi. Allah da ikonSa wani yana rabon zakka ya biya mana kuɗin asibiti. Muka dawo gida aka ɗora daga inda aka tsaya. Yunwa ta riga da zame mana jiki. Ganin zan cuci kaina, da raina da lafiyata na fara aikatau. Idan na yi shara da wanke-wanke a ba ni abinci na zo gida da shi, tamkar mayunwatan zaki haka muka dawo, nakan sha mamaki da tunanin wai ni ce Maryam nake aikatau? Silar auren mai dogon buri? Kasancewar abincin da suke ba ni ba ya isar mu sai na koma neman wankau.

Na samu wankin sai dai ba nan gizo ke saƙa ba, ban iya aikin wahala ba don ko a gidanmu ba na wanki, gidan aure ne na fara yi. Idan na yi wanki sai na sha wahala, ga rashin sabo ga kuma wulakanci da nake sha a wurin masu gida. Ba na mancewa watarana na yi wa yaran gidan wanki, ina tsaka da guga sai ga budurwar gidan ta watso mini kayan a ka tana masifa akan lallai sai na biya ta leshinta, don tsabar na raina ta dauɗa kawai na jiƙa mata a kaya ga shi leshinta daga ƙasar waje aka sayo mata shi. Inda take shiga ba nan take fita ba. Ban iya ba ta amsa ba sai kallon ta nake yi zuciyata tana bugawa da ƙarfi, ƙwaƙwalwata tana faman tariyo mini rayuwata ta baya.

Ni Maryam ake yi wa cin mutumci don ina aiki ƙarƙashin inuwar wasu. Tsabar na cika da mamaki ina kallon ta har na ƙone musu kaya ba tare da na kula ba sai ƙauri da muka ji yana tashi. Sababi! In ji Arawa! Nan wata rigima ta ƙara sarƙewa sai da na ƙwammace kiɗa da karatu, wulakanci dami-dami, cin mutumci ba wanda ban sha ba. Babban tashin hankalina gabaɗaya kuɗin aikina na wata suka ce za su fanshi kuɗin kayansu da na ƙone, sannan kafin na baro gidan sai da na sake wanke leshin yarinyar ina wankin ina kuka mai cin rai. Zuciyata sai tafarfasa take yi, na san a lokacin da za a auna ni babu abin da zai hana sakamakon gwajin nuna hawan jini, tsabar damuwa da ta lulluɓe ma’adanar sirrina.

A hanyar komawa gida nake bayyana wa Maraliya mai aikin gidan, rashin sabo ne ya sa nake shan wahala. Ta ba ni shawarar na sayi magani na riƙa sha, zan yi ta aiki ba tare da na gaji ba kamar jaka. Babu ɓata lokaci na fara amfani da ƙwayoyi, sai ga shi wanki komai yawansa nakan yi shi ba tare da na gaji ba. Tun ina shan ƙwayoyi har na fara taamalli da sirof waɗanda suke sanya maye, ban damu ba ko kaɗan saboda ina samun kuɗi, gwanjon sutura sannan ina ci ina koshi.

Na ci gaba da wankau ba kama hannun yaro, sai dai matuƙar ban sha magani ba za a samu gagarumar matsala. Saboda zuwa lokacin ya riga da zame mini jiki. Idan ba ni da kuɗi nakan je amsar bashi wurin mai sayarwa.

Wataran bayan farkawa daga barci na tsinci kaina a farfajiyar gidan aikina, jikina ciwo tamkar an ɗora mini duwatsu saman sa, kayan jikina duk sun yi baje-baje da ƙasa. Na rasa me ya same ni don haka sai na miƙe a tsorace da nufin shiga falon gidan, kafin na isa maigadi ya ƙwala mini kira. Ina zuwa yake sanar da ni kar na kuskura na shiga ciki, idan ina son lafiyar jikina, dukan da zan sha sai ya fi wanda suka yi mini da farko. Kallon mamaki nake yi masa tamkar shashasha, ganin irin kallon da nake masa ne ya sanar da ni abin da ya faru. Amai na kila saman kujeru ga shi suna da manyan baƙi, dalilin da ya sa suka yi mini dukan kawo-wuƙa. Hawaye ne suka ci gaba da ambaliya daga idanuwana, zuciyata ta fara raɗaɗi da zafi kamar za ta ƙone. Sai a lokacin ƙwaƙwalwata ta fara tariyo mini baya.

Tabbas sun sanar da ni za su yi baƙi, na kama wa mai aikinsu sharar falo, ni kuma lokacin na sha haɗin da na saba. Da wannan na fara sharar falon kaina yana juyawa ban sake sanin abin da ya faru ba sai da na tsinci kaina a farfajiya. Hawaye na goge ina yi wa maigadi godiya sannan na bar gidan. Bayan kwana biyu na koma gidan ko sun huce amma sai na iske har sun samu wata mai wankin, na buƙaci kuɗina suka hana ni wai sun biya an wanke musu kujerun da na ɓata. Lallai na tabbatar matar gidan ba ta da kirki, da tana da shi ba za ta biye wa yaranta su tafka mini rashin mutumci ba. Haka na dawo gida ina jin zafi a zuciyata. A lokacin muka sake komawa ‘yar gidan jiya, gudun yunwa ta sake hallaka ni na sayar da gadona, na kwaso kayan abinci.

Har zuwa wannan lokacin Habib bai saduda ba, ba shi da wani aiki face ya kwanta ya yi wanka ya kai wayarsa wajen caji. Don wutar ma mun jima ba mu da ita, rashin kuɗi ya sa aka yanke mana ita da daɗewa.

Tuni na yi wuri na ajiye Habib, babbar damuwata ita ce na samu haihuwa. Na samu wanda zai rarrashe ni idan ina cikin damuwa, wanda zai mini nasiha, saboda Habib bai taɓa damuwa da halin da nake ciki ba, duk da yana da masaniya akan komai. Babbar damuwarsa aikin ofis wanda har lokacin bai yanke tsammani ba.

Bayan wani lokaci, abincinmu ya ƙare na sake shiga damuwa, ga yunwa ga kuma rashin kuɗin kayan maye. Matuƙar ban sha haɗina ba kaina zai kama ciwo kamar zai tarwatse. Aladole na sake neman aiki, na samu gidan Hajiya Asabe. Kafin wata ya mutu nakan saci kuɗinta don lokacin na kai maƙura game da shaye-shaye.

Abin yana damu na amma ba yadda zan yi, don ita kaɗai ce mafita a gare ni. Ranar da ta yi tozali da ni a ofishin ‘yansanda na kwana, an gana mini azaba, sosai aka sauya mini kamanni kamar ba Maryam ba, sai da suka zubar mini da haƙora biyu na gaba. Duk yadda Habib zai yi, ya yi an ƙi fitar da ni, don babban sharri suka ɗora mini, wai sarƙar gwal na sata. Babu yadda Habib ya iya ya sayar da wayarsa da katifarmu, ya biya kuɗin da suka gindaya aka sallamo ni muka dawo gida, na kama jinyar jikina.

Ban daddara na kuma komawa neman aiki ido rufe, saboda na kai maƙura game da shan haɗina, ba zan iya bari ba, ban jin akwai abin da zai hana ni sha. Lokaci guda na samu wankau gida biyu. Gidan Hajiya Marka da gidan Alhaji Na-Hantsi. Bayan ƙarewar wata na karɓi albashina da ɗan nauyi, sai na ajiye su saboda buƙata. Na duba zan ɗan tsakura don sayen haɗina, kuɗi suka ce ɗauke ni inda kika ajiye mu. Sai ganin Habib na yi da waya, shakka babu su ne ya ɗauka, babu tausayi ko jinƙai. Kallon sa kawai na yi don na rasa abin da zan ce masa.

Hajiya Marka mace ce mai rowar tsiya, ba a cin abin hannunta, wani lokacin albashina har sai na tambaya da kaina. Yinin jiya a can na shafe sa ina wanki. Ina kallo tana girki, har ta sanya ni duba mata tukunya a lokacin da ta yi baƙuwa. Sai faman haɗa yawu nake yi ina son ci, haka ta sauke suka ci ita da baƙuwarta ba ta zuba mini ba.

Sai ma ƙoƙarin kora ta daga falon ta yi tana faɗa mini gobe na zo da wuri na ƙarasa sauran wankin. Haka na dawo gida ina haɗa yawu, har na kwana ina tunanin taliyar. Dalilin da ya sa na fita neman kuɗin saya na mayar da yawuna, wannan ƙaddarar ta afka mini.

Runtse idanuwana na yi zuciyata na ci gaba da tafarfasa. Ina jin yadda Habib yake yi mini sannu amma ko kallo bai ishe ni ba. Ba ni da burin da ya wuce ya sawwake mini, ko da zan ƙare rayuwata ni kaɗai. Aurensa babu abin da ya tsinana mini sai tarin nadama da da-na-sani. Likita ta shigo tana yi mini bayanin irin rashin lafiyar da na kamu da ita, hatta mahaifata ta samu matsala, na kuma kamu da rashin lafiya mai tsanani silar shaye-shaye, sannan jinina ya yi ƙololuwar hawa. Don haka ya rage nawa, idan zan ci gaba da yi matsalata ce.

Da wannan na roki alfarmar ta ba ni sallama, amma ta hana ni a cewarta sai na ƙara samun sauƙi. Tana barin ɗakin ita da Habib na cika bujena da iska na bar asibitin. Ban jima da zuwa gida ba sai ga Habib. Babu ɓata lokaci na fara sauke masa rashin mutumci kwando-kwando, na umarci ya sawwake mini, ya bar mini gidana idan kuwa ya ƙi hukuma ce za ta raba ni da shi.

Ban taɓa ganin shi cikin tashin hankali ba kamar yau. Kuka wi-wi yake akan na gafarta masa, kowacce irin sana’a nake so ya amince zai yi. Tamkar gunki haka na zama, don idan mutumin da ke yi wa hoto magana ya amsa, ni ma na amsa masa. Tuban Habib tuban muzuru ne da ɗan-tsaƙo a baki. Na ci gaba da masifa ina faɗin duk inda yayata take a faɗin duniyar nan zan neme ta, ta taimaka mini ya sake ni ko a kama shi. Kuka ya ci gaba da rera mini kamar sabuwar amarya, ni kam ko sauraren sa ban yi ba, sai ma ɗaki na shige ina sake jaddada masa awa uku kacal na ba shi ya sawwake mini.

Da yake ba isasshiyar lafiya ce da ni ba, ina nan ina wasikar jaki barci ya sace ni. Ina farkawa kai tsaye falo na dawo na yi masa tsaye a ka ina sake jadadda masa bukatata. Sam ban lura da ledojin da suke zube a falo ba sai da ya nuna mini su yana sanar da ni kayan miya ne ya saro, wayar hannunsa ya sayar, da kuma sauran suturunsa kusan rabi ya yi gwanjon su ya saro kayan miya. Ko kaɗan bai birge ni ba, don ya jima da ɓata rawarsa da tsalle. Sake matsa masa na yi amma bai bi ta kaina ba sai ficewa ya yi da kayan daga falon, yana kaiwa ƙofar gida.

Kewar yayata ta cika mini zuciya, sosai nake buƙatar ta a kusa da ni. Burina na yi tozali da ita, domin ta share mini hawayena. Na shafe kwanaki ina nazarin yadda zan neme ta, wata dabara ta faɗo mini na ari wayar maƙwafciyarmu na neme ta a fesbuk, Allah da ikonSa na same ta. Cikin kuka nake zayyane mata abubuwan da suka faru da ni. Ba a ɗauki lokaci mai tsayi ba ta aiko mini da kuɗi na tafi asibiti aka duba lafiyata, tare da saka mini haƙora. Kuma ta ba ni jari na kama sanaa.

Rayuwarmu da Habib ta dawo ba yabo ba fallasa. Idan na tuna yadda na biye masa muka nakasa dukiyata, ina jin haushi sosai a raina. Kodayake mun ga ishara da aya ƙarara, don sanaar da ya ƙi yi da dukiya mai yawa, ita ce yake yi da kuɗi ƙalilan. Lallai Wanda Bai Ji Bari Ba, Zai Ji Hoho!

Ɗaukar Jinka

Post a Comment

0 Comments