Ahmad Muhammad Adam (2023). Kaddarata. Ɗaukar Jinka (Labaran Da Suka Samu Nasara A Gasar Gajerun Labarai Ta Arc. Ahmed Musa Dangiwa, 2022). Kangiwa Multimedia and Communication Company LTD
ƘADDARATA
Na
Ahmad Muhammad Adam
Kuka ta ke mai taɓa rai har shiɗewa ta ke ƙoƙarin yi, ta share hawaye ta ce,”
Haba Abban Sajida, shaye-shaye ba na ka bane, kana da ‘ya’ya fa, amma ka...”Cikin
zafin rai ya ɗauke ta da mari, cikin maye ya ce,”Ba zan de na ba, ki
fita daga lamura na na faɗa miki, in ba haka ba wallahi ni ne ajalin ki”. Yasa
ƙafa ya fice da ga ɗakin
ba tare da sake sauraron ta ba.
Salima
mace mai haƙuri, inda sabo ta
saba da halin Musa, yadda
ya maida shaye-shaye abokin rayuwa, ba dare ba rana, duk da cewa yanzu da ɗan
sauƙi tunda ko ya ya ne yana fita yin buga
bugarshi, Wata rana in an samu kuɗin a
kawo a aci da haƙuri,
watarana kuwa abin da ya samo ko gida bai kawo shi, sai dai ya ƙarar da shi a can wurin shaye-shayenshi.
Tabbas
da mahaifiyar Salima
na raye abubuwa za suyi mata sauƙi,
ta san ko ta koma wurin mahaifinta, iya bala’in da matar mahaifin na ta ke da
shi ba zai bari a taimaka mata ba, amma kuma dole ta je dan kuwa tun jiya basu
ci komai ba, yau ma haka Musa ya fita bai bar mata komai ba sai dan karan duka
da ya naɗa
mata.
Haka
ta nufi gidan su ci ke da fargabar abin da zai je ya zo,da sallama ta fa ɗa
cikin gidan, ba ta ƙarasa
sallamar ba, su kayi iɗo huɗu da
matar babanta, kai tsaye ta fara faɗin “To
‘yar jaraba, yaushe garin ya waye har kin biyo duhun asuba, to maza ja tsummar
rayuwarki ki ban wuri, muma yau haka muka tashi malam naira tamanin ya ban ya
ce na yi haƙuri da shi kuma...”.
Cikin ladabi Salima ta ce, “Baba Attine ina kwana” ta juya kanta can da yatsine
ta ce” lafiya” Yadda baba Attine ta yi ne ya sa Salima cewa, “dama wucewa zan yi
nace bari nazo mu gaisa”.Tana gama faɗin
hakan fita ta yi zuciyar ta kamar ta haɗiyi
ruwan dalma.
Fitowa
tayi ba tare da sanin inda za ta je ba, zuciyar ta kuwa tunani ta ke, da ace
mijin ta ya zama kamar kowane nagartaccen namiji, da bata tsinci kanta cikin
wannan yana yin mara daɗi ba, da ya maida hankali
sosai a sana’ar shi,da komai yazo mata da sauƙi.Ita
ba kanta ta ke dubawa ba, illa yaran ta guda biyu, shin wacce kalar rayuwa za
suyi, dukkan tarbiya tana tabbatuwa ne a inda uba ya jajirce a gidansa, ya
sauke dukkan haƙƙoƙin da Allah ya ɗora
masa, ya tsaya, tsayuwa irin ta daka dan ganin mutuncinsa dana iyalansa basu
tagayyara ba, to amma ita bata da zaɓi
tunda haka shi ne ƙaddararta,
kuma tana fatan Allah ya dube ta ya kawo mata mafita.
Ba ta
yi aune ba, wata mota ta shawo kwana kamar zata kifar da ita, matuƙin motar ya fito a sukwane cikin fushi
ya kwaɗa
mata mari, ya ce, “Ke wacce irin mara hankali ce, Hon biyar na miki amma kin ƙi kaucewa.
Wani
da ke kusa da shi yace, “ Tunanin ta na banza da wofi mana, ƙila ma cikin maye take” Salima bata saurare
su ba ta wuce, tana faɗin sanadin shaye-shaye ne ya
sani cikin wannan ƙaddarar.
Gida
ta nufa, tun da ba abin da ya fi dacewa da ita illa ta koma gidan. Ahmad ƙaramin ɗanta
ta gani a kwance, yunwa sosai ya ke ji, ta rungume shi tana faɗin, “
Allah ya na tare da masu haƙuri,
kuma baya tauyewa masu kyautatawa” Sallama taji ɗan
maƙotansu ya ce “wai umman mu ce ta ce na
kawowa Ahmad abinci” Da sauri Salima ta fito daga ɗaki
ta karɓi
abincin tana godiya, a yadda taga yawan abincin tasan bawai Ahmad ake nufin
bawa ba, ta ƙara godewa Allah san
nan suka ci abincin suka ƙoshi,
a ranta tace an gama da wannan sai kuma wani.
Ana
magriba Musa ya shigo da baƙar
ledar dake hannunsa, taliya ce guda ɗaya
dame ɗanɗano,
ya faɗa
cikin nutsuwa. “Salima ayi haƙuri
da wannan”. Murmushi tayi tace “ ba komai Allah ya ƙara
buɗi”.
Ta tashi ta nufi inda mangal ya ke, dama da sauran gawayin shekaran jiya, ta dafa musu taliya ta kawo musu.
Yana
fara cin abincin ta ce, “Kai miji na ne, kuma
so da ƙauna ya sa
na aure ka, ban da
uwa. Kuma kasan halin baba
Attine, ka duba yanayina da na yaran nan ka daina shaye-shaye, ba abin da zai anfanar dakai a duniya da kuma lahira,
illolin da shaye-shaye ke haifar wa sun fi
dukkanin yadda mai tunani zai yi,
kana cutar da cikin jikin ka, duk wanda ke kusa da kai yana cutuwa, ga zubewar mutunci, abin haushin masu safarar miyagun ƙwayoyin nan sun killace na su iyalan
saboda sun san illar abin, shin me yasa zaka sayi abin da zai juya ma ƙwaƙwalwa da kanka?
Duk
wanda ka ganshi ya na hauka, Allah ne ya jarabce shi kuma in san samun sane da
dangin sa to Allah ya bashi lafiya, to
dan me kai zaka sayi haukan da kanka, wace rib ce a cikin shaye-shaye, miji na ne kai, ina sanka ina san ka dubi rayuwar yaran mu a
nan gaba kuma ka...” kuka
ya ƙwace mata, jikin shi ya yi sanyi ya kuma
mata alkawarim bazai kara shan komai ba.
Sati
ɗaya, kullum ya na fita buga bugar sa. Ranar wata alhamis ya dawo gidan cikin maye, Sajida ta
tafi da gudu tana oyoyo baba, cikin maye ya kalli ‘yar ta sa ya ce “Ni ki ke
zagi?” Ya
ɗauke
ta da mari ya hankaɗata gefen tsohuwar rijiyar
gidan nasu, ji kake dam ta faɗa. Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un Salima
ta ringa faɗa tun kan ta fito daga ɗaki, shi kuwa gogan
naka bai ma san meya aikata ba, dan haka ɗaki ya shiga yana fadin ”ke uwar ki
bata koya miki girmama manya ba”
Da matuƙar tashin hankali
ta fita tana kiran a taimaka mata, matasan da ke zaune a gaban gidan su suka
taso aka shiga har Allah ubangi ya ba su nasarar fito da Sajida daga rijiyar, da
sauri Salima ta matso kusa tana faɗin ku bani ‘ya ta. Saurayin da ke kusa da ita yace, ”ai
sai dai ki yi haƙuri wannan kam Allah ya ɗauki abar sa, addu’a
kawai take buƙata” jiri ne ya ɗauke ta, ta tafi
kamar zata faɗi amma ta dake, ta ci gaba da kiran sunan Allah tun da
tasan ba abin da ya gagare shi.
Bayan minti ashirin Musa ya farka daga baccin da yake tun
bayan da ya rusa gidansa da hannusa, ya ɗan dawo hayyacin sa kaɗan a lokacin da ake
ƙoƙarin yiwa Sajida sutura, wani
rarraba idanu yake kamar an kwashewa karya ‘ya’ya. Ya zo kusa da gawar da yinƙurin yin magana amma Salima tayi saurin tare shi tare da
cewa cikin kuka ”kayi haƙuri abban Sajida
haka Allah yaso, kullum ina kiyayewa kar tayi wasa kusa da rijiyar ashe
ajalinta ne a ciki”. Musa yana ɗan
tuna wani abu da ya
faru amma ya basar ya kuma turɓune fuska da kiran Allah ya
mata rahama.
“Kai
ku duba min kamar yarinyar man motsi take” wata mata ta faɗa, tuni kukan da Salima take ya dauke tamkar
ruwan sama, tabbas motsin take, kenan da
ranta?” ya kamata kuyi gaggawar kaita asibiti dan
ceto rayiwar ta”.
Salima ta tashi a zabure kamar wacce kunama ta
harba, ta nufi inda take, suka nufi asibitin dake kusa da su.
Nurse
ɗin
dake duty ta wani kalleta a yatsine tace “je can kisai kati” Salima ta ɗan
noƙe” magana
ake miki, in baki da shi kuma ki ɗauki
‘yarki ki ban
wuri, l have alot to do” lailai Salima tana ganin masifa yau, kuma ba wanda ya janyo mata ita sai mijinta a
sanadin shaye-shayen da ba zai
mai rana ba har
abada.
Ta
kalli nurse ɗin sannan ta nufi wurin siyan katin
bakin ta yana ƙara kiran sunan
Allah. Layi ta bi har aka zo
kanta, ”baiwar Allah ina kuɗinki me ye
kuma sunan mara lafiyar”? Me karɓar
kuɗin
kati ta tambaya.Tace sunan ta Sajida Musa” okay
ban kuɗin”
ta faɗa
tana rubuta suna. Salima
tayi narai-narai da ido kawai taji daga bayan ta ance, ”ah ba kece wacce ‘yarki
ta fa ɗa rijiya ba? da saurin tace nice tana kuma ƙoƙarin gaida shi, ya amsa mata sannan
ya biya kuɗin katin da sauran dukkan abin da ake buƙata a asibitin, tun da ya fahimci ba ta da kuɗi.
Lailai
Alhaji Garba yana taimakawa mutane sosai. Da da irin su da yawa da al’umma ba su
sha wuya ba,” maƙoci me rana kenan” Salima ta faɗa tana murmushi
bayan da ta ga dukkan abin da likitoci ke buƙata an samu, dan haka ta godewa Allah.
Sati
ɗaya
su kai a asibiti aka sallame su, Musa bai wani basu kulawar da ta dace ba. Haka kuma, bai ɓata wa Salima rai ba, saboda tasan
halin mijin nata, a dan haka suna dawowa ba ta ko zauna ba sai da ta shiga
gidan Alhaji Garba tayi masa godiya yadda ya temaki rayuwar ‘yarta. Ta yi sa’a yana nan ya kuma ce ba komai, za ta
tafi yace in zata iya wanke-wanke ta ringa yi musu. Matar shi tace ba komai dama meyi musu
wanke-wanken ta yi
tafiya, yace a ringa biyan ta
duk wata, sannan a ringa ba su abinci daga cikin wanda ake rabawa na sadaka. Rabon
da Salima tayi farin ciki irin na wannan ranar ta manta, ta yi
godiya sosai, su kai sallama ta nufi gida cikin farin ciki da
godiya ga Allah.
“Wannan
baccin asarar ya isa haka, ace
yaro matashi wanda ya mallaki hankalin kansa ba zai
sallar asuba a jam’i ba sai ƙarfe
takwas, a tashe sa yaƙi
tashi. Bari ki ga ruwan wankin nan zan kwara masa
ja’iri”, ai kuwa ruwan ta kwara masa, firgigit ya tashi yana kiran dala dubu
biyar kenan,” Allah yasa riyad ne ,malan tashi kai salla” ta faɗa fuskantar ta bako
annuri, wayyo mama wayyo, wallahi wani mafarki nake mai shegen daɗi, wai sarkin Makka
yaban dala dubu uku, ya ƙara min biyu suka
zama biyar, ina ƙoƙarin karɓa kika tasheni.
‘’Wayyo da ma gaske ne wallahi da saina...” gwaf ta gwaɓe masa baki tare da
cewa sallah nace kayi ba zancen banza da wofi ba. Bakin
nashi ya rike bai ƙara
magana ba ya nufi ban ɗaki
yayi alwala yayi salla.
“Mama
ina abinci, yinwa na tashi da ita ‘yar gaske, ji
nake kamar ana min screenshot a ciki” maman ta turo mai ƙwanon waina da ƙuli tare da faɗin
meye kuma sigarishot? Abdul
dariya kawai yayi yana faɗin ba zaki gane ba mama, zan miki bayani bari ciki na ya ɗauka.
Kwana ukku kenan bata sa idan ta a nashi ba, tana zaune
da farar safiya ya shigo ta gaida shi ya kuma amsa yana murmushi, tare da faɗin da fatan kin
tashi lafiya ya jikin Sajida ina kuma Ahmad? “Da sauƙi,duk bacci suke”ta fa ɗa tana kokarin
tashi tsaye, tayi masa nuni daya zauna, ya kuwa zauna.
Sauran abincin da suka ci ta ɗakko masa ya karɓa yana faɗin Allah ya jiƙan baba, ta ji daɗin addu’ar da yayiwa mahaifiyarta,
gefen gadon ta zauna kanta ƙasa” baban Sajida
ina sanka ina ma biyayya, me yasa bazaka dena ta’ammali da miyagun ƙwayoyi ba? Me yasa ba za ka inganta rayuwar ka kamar kowa ba? Ka kalla
har kusan salwantar da rayuwar ‘yarmu
kayi a sanadin shaye-shaye amma na rufa ma asiri duk duniya ba wanda ya ji, duk
dan ka gane gaskiya”
Tana
ɗaga
kai ta kalle shi idan sa sun fara ƙwalla, tausayin sa duk ya kamata dan haka tayi
saurin rufe maganar da wannan
abokan naka dole ka yanke alaƙar
ka da su, dan
suma na fahimci suna taka muhimmiyar rawa wajen ganin baka dena shaye-shaye ba, yanzu kamun alƙawarin
ba zaka ƙara
ba kaji abin ƙauna ta” ta faɗa
tare da murmushi. ”ba zan ƙara
ba insha Allah” ya ɗan yi gyara zama yace, ”kin san
yanzu babbar matsala ta rashin sana’a, wannan
zaman mara tushe ya fara isa ta, jiya
fa me abincin bayan layi Ƙaura
ya gaggaurawa mari ya karɓe bokitin alalalen ya kawo
muka ci, ai Allah ba zai
kama niba ko? Tunda bani na sato ba” ya faɗa
yana ƙaryar da kai,
murmushi ta ƙara yi tare da
tanbayar sa ”kayi sallar asuba yau? Ya ɗan
kalli sama wai shifa a dole tunani yake
yace ”nayi mana tun jiya ma” ta fahimta.
Ruwan alwalar ta ɗebo masa tare da shinfiɗa abin salla tace, ”yi
maza kayi salla sahibi na ina da labari mai daɗi” da sauri ya
tashi yai alwala ya yi salla a ranta tana faɗin ai salla tana
hana saɓawa Allah.
Abdul ya shiga gida yana ɗan cin magani, ɗakin mama ya nufa
ya same ta tana ɗan rintsawa, ya kalle ta yace “mamana ta kaina tashi
burin ki ya kusa cika” ta bude ido kaɗan, ga dukkan alamu ta fara nisa a
baccin ”mama magana nazo miki da ita mai matuƙar muhimmanci da daraja da ɗaukaka da cikar
burin ki dama nawa” ta tashi zaune tana fadin “to audu ina jinka. Allah
yasa ba shashancin naka ne ya tashi ba” ya kalli maman
da shagwaɓa yana faɗin
ni fa ba suna na Audu ba. Mama da ɗan
fushi a fuskar ta tace” ka tasheni daga bacci, ka
faɗi
meya kawo ka ko kaban wuri” Ya gyara zama yace”duk duniya ba wanda zai iya
fahimta ta sai ke, dan haka nazo wurin ki danki dube ni kuma ki
kalli yadda abubuwan suke
wakana a rayuwar yau da gobe Kuma ki duba irin...”
Ta katse shi da faɗin” ka faɗi abin da ya kawo
ka kawai” ya ƙara gyara zama yace”Mama kinsan ƴar gidan Alhaji Sammani tare mu kai B.U.K da ita, to mun
gama daidaitawa auranta zan yi” da sauri ta zaburo”au me kace!!! “ya
kalle ta yace auren ta zan yi
dan haka waccan sauran gonar da baba ya bari ta ƙauye
kawai a saida ita.
Kuma fa wataƙila baban nata yai min manager a gidan mansa na ‘yan kaba kuma dam... Ji kake kau!!! ta kaure shi da wani farin mari tare da cewa Allah
yasa ba shaye-shayen zamanin nan ka fara ba, kodai
kasha giyar wake ne kafin kazo nan, mst
ina ga ciwon hauka ne ya fara kama ka, dole na yanko ma kati a dawanau” ai bai ko ƙara
sauraron taba fuuu ya fice yana fadin yanzu me degree za’a mara?
Musa
kam yanzu sai masha Allah, salla yake sosai har a jam’i. Tabbas ya fara nutsuwa, wannan abokan ya watsar da su, komai
ya fara yiwa Salima daɗi, adan haka ne da taje gidan Alhaji Garba ta
tanbayi matar tasa inda wani gurbi da za ayi wa
mijin ta, ai kuwa tayi sa’a Alh Garba
ya bashi mukullin mota dan ya ringa ɗaukar
abincin da ake rabawa mabuƙata.
A ƙaramin lokaci ya canza, farin sa har ya
fara dawowa, shi kanshi yayi mamakin
hakan.
Yau
wata biyu kenan yana zaune yaro ya shigo wai ana kiran Daguji, ya
san ba wanda zai kira shi da wannan sunan sai su
Ƙaura,
haka yasa ƙafa yabi yaran” Daguji ina ka shiga ne kwana biyu bana ganin ka a eka, akwai
fa sababbin eyane ya kamata mu muje mu sheƙe su fa” Musa kam kallo yabi Ƙaura
da shi tare da tanbayar sa katin ɗaurin
auran waye a hannun sa? Yace “ci dagahi ne zaiyi aure wannan lahadin”ya faɗa
yana ɗan
wani juyayi.
Musa yace”zan zo, karfe nawa za a ɗaura” ya kalle shi
sheƙeƙe yace “yo wama ya sani, kasan
gudawa nayi a makaranta, ka karanta mana, kai na wuce zanje wurin Abba taye
yanzu” ya faɗa yana ƙoƙarin tsallaka kwatar dake ƙofar gidan, ai kuwa ji kake facal ya fancala ciki, Musa
ya zaburo yana faɗin “duk jikin naka ne ba kwari sannu kaji tashi” Yasa
hannu da niyyar ya ɗago shi, to shima dai jikin ba wani kwari ya gama ba, ji
kake facal shima ya bishi, suka fara iyo kamar wasu kifaye.
Yau
lahadi, Musa yayi wanka ya tafi ɗaurin
aure, bayan gama ɗaurin
auran ne suka koma bayan gari dan suyi murnar auran abokin na su. Ba kalar kayen mayen da ba su haɗa ba, ko a ina suke
samu oho, ko Gwamnati ta san ana shigo da irin wannan baƙar annobar, ko akwai matakan da gwamnatin ke ɗauka? ko meye ribar
masu safarar ta? Iya kuɗi ne, kuma ba ta yadda za suyi albarka tunda ana sa
matasa cikin wani hali ba tare da la’akari da cewa matasa sune ci gaban al’umma
ba.
Musa yace musu ba zai sha ba, ƙaura yace ”kai dalla ware yauhe ka zama haka, iya yau dai
ai ka henye koma meye, abokin mu zamu taya murnar higewa daga ciki fa” da haka
dai Musa ya ɗora daga inda ya tsaya.
Yau
kwana hudu kenan bai dawo gida ba wai ana can ana shagalin biki, kowa ya faɗa
masa cewa ana farin ciki da shan kayan maye, ai
nisantar su shi ne
ke tabbatar da farin ciki da nutsuwa. Abin
takaicin ma duk kusan matasa ne a wurin bikin, ko
taya al’umma za ta
ci gaba a yayin da matasan cikin ta ke shaye-shaye? Dole fa akwai matsala,ba al’ummar
da zata ci gaba matuƙar
matasan cikin ta basu san inda yake musu ciwo ba.
A
bige ya shigo gidan anyi biki an gama ya iske Salima bata nan, ya nufi ɗaki
yana zuwa ya tadda Sajida kwance tana bacci abinta, ya kalle ta sosai sannan yace,”gaskiya Salima baki da hankali, yanzu na tafi yau kusan wata shida bana nan
amma ba oyoyo? Ina san ki Salima nayi
kewar ki sosai dan haka dole ki bani haƙƙi na na
aure yau kuma yanzu” afka mata yayi, yarinyar da ba ta fi shekara uku ba ,tun
tana ihu da motsi har ta dena, ya lalata mata rayuwa duk a dalilin shaye-shaye
gashi ya jefa rayuwar ‘yarsa a cikin yanayin da yai sanadiyyar mutuwar ta,
lailai wannan ba ƙaramar musiba bace wacce maganin ta
sai dai Allah kawai.
Sallamar da Sadeeq ɗan maƙociyar yayi ne ya sa shi dagowa da fushi yana faɗin kai ƙaura nace ka dena shiga rayuwa ta amma kaƙi, shi ne ka biyo ni har gida har ɗakin matata? “Nayi
sallama fa, dama cewa akai na ɗakko
Sajida ina ta tashi daga bacci” ya faɗa
yana kallon Musa. Tuni
gogan naka ya finciko shi ya haɗa kansa da bangon ɗakin ,take jini ya
fara zuba, wuƙar dake ajiye a cikin kwando ya ɗakko ya fara caka
masa, bai ko motsa ba rai yayi halinsa.
Salima ta ji shiru dan haka ta biyo taga yadda akai aka
haihu a ragaya, ai kuwa tana zuwa ta iske abin da ya ɗugunzuma mata
hankali, ta fice tana faman ihun neman ceto, tuni jikin ta ya kasa ɗaukar ta, ta faɗi ƙasa sumammiya, mutane suka kawo ɗauki inda suka
cafke wanda ake zargi zuwa ofishin ‘yan sanda dan a tabbatar da laifin sa kuma
ai masa hukumci da irin abin da ya aikata, ko hakan zai iya zamowa izina ga
sauran mutane masu hali irin nasa.
Alhaji Garba ya kaɗu sosai da abin ya faru dan haka
yaga baiga ta zama ba dole ya haɗa kan al’umma dan a magance dukkan matsalar data taso a
cikin al’umma, dan haka kai tsaye gidan Alhaji Sammani ya nufa, sun tattauna
sosai akan matsalolin. Bayan kwana ukku suka haɗa
duk matasan dake cikin unguwar tasu. Alhaji Garba yayi gyara murya sannan yace.
“Ya ku jama’ar wannan yanki namu me albarka, ku sani
gwamnati nada ayyuka da yawa a gaban ta, a dan haka ba zamu bar mata komai ba, dole
mu haɗa ƙarfi da ƙarfe mu tallafi yankin mu, amma ku sani hannu ɗaya baya ɗaukar jinka. Ni kaɗai ba zan iya ba,
Alhaji Sammani ba zai iya ba, dole sai mun haɗu ni da ku, matasan
wannan yankin namu mai albarka, ku sani dole zaman banza ba sana’a ba zai taɓa haifar mana da ɗa me ido ba, ku
kama sana’a ku bar shaye-shaye, ku kalli yadda ɗan uwan mu wanda ya
taso a cikin mu yadda sanadiyyar shaye-shaye ya dakusar da rayuwar sa, ya
tsayar da dukkan burikan sa, ya rasa matar sa ,tun da yanzu kuna gani bayan da
aka yanke masa hukumcin ɗaurin rai da rai a gidan ajiya da gyaran hali, a ta dole
aka raba auran sa da matar sa.
In har za kusha kayen maye tofa ku sani wallahi ba inda
rayuwa za ta kai ku sai tashar wulaƙanci da tozarci
kuma daga ƙarshe kuyi dana sani wanda Hausawa
sukace ƙeya ce. Duk ƙanƙantar sana’a kuyi
ku dai dogara da kanku a sannu a hankali Allah zai buɗa muku,amma indai
kuka riƙe hannu kuna jiran sai gwamnati ta
baku aiki to zaku zauna kullum gafara sa amma bakuga ƙaho ba,domin kamar yadda na faɗa muku gwamnati
nada ayyuka da yawa a gaban ta.
Dan haka dani da Alhaji sammani ga Alhaji Umar zamu bawa
duk matashin da yake san yin sana’a dan ya dogara da kansa jari, domin rashin
aikin yi na jefa da yawa daga cikin matasa harkar shaye-shaye ko fataucin kayan
mayen idan abin yai tsamari”
Yau wata huɗu da kwana goma kenan, unguwar tasu harta dawo hayyacin
ta,sace-sacen da ake na waya ko haurawa gidan mutane an dena, balle kuma
shaye-shaye da yake ƙoƙarin zama tarihi a yankin gaba ɗaya,matasa maza da
mata sun kama sana’a,yaran da iyayen su basu da ƙarfi ana ɗaukar ɗawainiyar karatun su daidai gwargwado.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.