Khadija Lawan Daura (2023). Sanadi. Ɗaukar Jinka (Labaran Da Suka Samu Nasara A Gasar Gajerun Labarai Ta Arc. Ahmed Musa Dangiwa, 2022). Kangiwa Multimedia and Communication Company LTD
SANADI
Na
Khadija Lawan Daura
Daka mata dukan da aka yi ne ya farkar da ita
daga baccinta. “Sannu Zainab, kin sani ba bacci ba ne a gabanmu ba, ko baki ji
abin da Oga Bala ya ce ba? Lallai-lallai tara na
safe ta yi mana a filin jirgi, don Allah ta shi ki shirya.” Tsaki Zainab ta ja
ta miƙe tana sosa idanuwanta. cikin muryar jin bacci ta ce, “Saddiƙa ki na
da matsala, kin san me nake a cikin mafarkin nan kuwa?” A yatsine Saddiƙan ta kalleta. “Ban sani ba.” Ta faɗa da
gatse.
“Hmmm, ina tunanin akwai gagarumar nasara a wannan
tafiyar tamu, tabbas burina yana gab da cika Saddiƙa, mafarki na yi na ci nasara sanye cikin kakin soja
yayin da sauran sojijin da suke ƙasa da ni suke mini
biyayya, abin mamakin ma Yusuf ne ɗaure cikin ankwa, babu abinda suke jira sai umarnina na
ya za a yi da maciyi amana? Harbesa za su yi ko kuma uƙuba za su gana masa.” Bata bari ta kai ƙarshe ba ta zauna tare da kai hannunta
kan kafaɗunta.
“Zainab, ki kwantar da hankalinki ɗaukan fansa ba abu
ne da yake kara zube ba, abu ne mai buƙatar nazari sannan
da aiki tuƙuru, kamar yanda na faɗa miki hanyar
safarar kayan harka ce kaɗai zata sa ki cimma burinki, wallahi idan yau aka ce
aljihunki a cike yake da sulalla to tabbas za ki juya kowa ki taka kowa ki yi
abin da ranki ya ke so ciki har da ɗaukar fansar abin da Yusuf ya yi miki.” Cike
da gamsuwa da kuma jin daɗi Zainab ta saki murmushi.
“Zan iya yin komai akan hakan, saboda Yusuf ya kashe mini rayuwa, ya azabtar da
ruhina ya kuma wulakanta mutumcina, ya hana jama’a ganin ƙimata a cikin idanuwansu…..”
Hawaye
ya ciko mata ido. “Ni fa wannan sakarcin naki ne bana so.” Saddiƙa ta faɗa
tana bata rai. “Ke har yanzu baki bar kuka ba, izuwa yanzu ko darom ɗin hawaye ne a cikin idanuwanki ya ci ace sun
kafe, Yusuf ɗin me? Ai yanzu kin fi ƙarfin zubarwa da wannan mahaukacin
hawaye.”Ƙwafa
Zainab ta yi. “Ban
taɓa
baki labarina cikakke ba ne, na faɗa
miki wani, wasu kuma na boye saboda ni kaɗai
nasan su na kuma sha alwashin babu mai jin su har sai na cimma gaci……..”
Katseta ta yi. “Kin ga ta shi don Allah ki shirya mu tafi
ba a bori da sanyin jiki, yau ne fa rana ta farko da zamu fara harkan nan, kuma
ayau ɗin aka tabbatar mana da cewa tsallakewarmu tamkar raba mu
da baƙin talaucin da ya yi mana rumfa ne.” Da sauri Zainab ta tashi ta fita tana mita
akan abin da take fama da shi.
“Wallahi shi ne na farko da zan fara azabtarwa fiye da yanda ya azabce ni, sai
na wulaƙanta rayuwarsa na ɗaiɗaita
farin cikinsa.” Tana mitar ta shirya. Cikin kulawa Saddiƙa ta miko mata wasu ƙwayoyi
guda tara.
“Oga
ya ce musha wannan guda uku, saboda yau zamu fara kada rashin gaskiya ya sa mu
zama shege a rabon gado.” Dariya ta yi duk da zuciyarta na yi mata wasu muggan
saƙe-saƙen,
tunaninta akan gagarumin aikin tsallaka ƙasa
jikinsu cike da kayan maye. “Hmmmm,
wai kina nufin shan wannan zai ƙara
mana kuzarin riƙe
tsoro da fargaba?” Taɓe
baki Saddiƙa ta yi. “Haka dai oga ya ce mini wai
fatauci sai da gagarumin shiri, ciki sai ka yi ƙoƙarin
fatauce duk wata hanya da zata sa aga wata alama a tare da kai.” Ajiyar zuciya ta yi tare da
kallon Saddiƙa cikin saddaƙarwa.
“Kina
ganin za mu yi nasara kuwa? Karfa garin neman gira mu
rasa ido.” Dariyar ƙarfin
hali ta yi. “E,
to, amma ina da tabbacin za mu
nemi girar ba tare da mun rasa ido ba, a cikin matan da ya yi mana kwatance
babu wacca bata haye ba, wai ma banda abinki wanne mahaluƙi ne
ya isa ya gano inda kayan suke a jikinmu?” Dariya suka yi dukkansu. “Kuma fa
haka ne, ni kaina sanin hakan ke karfafa mini gwiwa Saddiƙa.”
Bata zaci haka ba sam, ba tasan abun babba ba ne sai da
ta tsinci kanta cikin filin jirgi wanda zuwanta wajan shi ne na farko a tarihin
rayuwarta, kallo ɗaya zaka yi mata ka fahimci gazawarta da tsoron da ya
hanata sukuni. “Saddiƙa na shiga uku!” Ita kanta Saddiƙan a cikin yanayin
take don kar ta sagarwa da Zainab ɗin gwiwa ta ce, “Wai kin sha ƙwayar nan kuwa?” Goge gumin goshinta ta yi
wanda take jin zubar wasu cikin jikinta tamkar an bude famfo. “Na sha mana ko
ba a gabanki na sha ba, ni dai da-na-sani ma ban
sha ba don babu abin da
ya ƙara
min. Kalli wa’yancan ‘yansandan ji fa yanda suke zare ido kamar su ci babu.”
Hankalin Saddiƙa ya tashi. “Ni kaina Zainab abun ya fara
damuna babban baƙin
cikina ko an kama mu ba mu isa mun ce Oga ba, ni kam ban san abin yi ba an ya ba za mu koma wajan Oga ba?”
Da
mamaki Zainab ta kalle ta. “Kin manta sharaɗin
kenan? Tun farko me ya ce mana.” Bakin Saddika na rawa ta ce, “Ce wa ya yi
dawowarka tamkar mutuwarka ne, idan mun dawo ma babu wanda zai taimaka ya raba
mu da kayan mayen nan, Innalillahi.” Daidai lokacin da layi ya iso kansu.
Cikinsu ya ɗuri ruwa hankalinsu ya yi mummunan ta
shi. Kwatsam ba zato su ka
ga wani kakkauran ɗansanda
ya tsura musu ido yana kallonsu cike da nazari. “Shi kenan ta faru ta ƙare Saddiƙa.”
Zainab
ta faɗa
hankalinta a tashe. Wani kuka ne ya taho mata wanda ta kasa tsayar da shi.
Wanda ke gaban Saddika ne ya isa kusa da ‘yansanda da suke bincike tana kallon ɗansandan da ya kara masa na’ura nan da nan ta
hau ƙarar da ke nuna akwai wani abu ajikinsa
wanda ba a so. Da sauri ta ja baya tana kallonsu cikin rawar jiki ɗansandan
da ke kallonta tun ɗazu ya ƙura mata ido yana son gano gaskiyar da
take ƙoƙarin
ɓoyewa
da sauri ya yo kanta hakan ya hautsina mata hankali ta kwasa aguje tana ihun
akawo mata ɗauki wallahi saka ta aka yi.
Ƙura masa ido ta yi tana kallonsa. Wai
shin ina burinta yake? Kakkausar muryarsa ta doki kunnanta. Ta ji abin da yake tambayarta sai dai amsar sa tamkar
neman allura ne a cikin ruwa. Wai tambayarta yake waya ƙunsa musu kayan maye a cikinsu? Sake daka mata tsawan ya yi wacca
sai da ta razana don
da sauri ta ɗago kai tana kallonsa a firgice. “Don
Allah ku kashe ni na huta! Wannan rayuwar ta ishe ni na gaji da ita! Allah ya
isa Yusuf! Duk kai ne sanadiyyar jefa rayuwata cikin masifa gashi a ƙarshe ka zamar min ajalina!”
Zafin
marin da ɗansandan ya yi mata ne ya sa ta dawo
hayyacinta. Ta kalli ɗansandan, taga wani irin
kallo da yake mata wanda ta kasa tantance na menene? Tsawar da ya kuma yi mata
ce tasa ta cure kanta cikin cinyoyinta. Ta yarda a kasheta ta huta amma ba za ta taɓa
magana ba. Rashin maganarta ya fusata ɗansandan
ya fice tare da aiko mata wa su ‘yansanda biyu mata suna zuwa suka rufeta da
duka. Tun tana ihu har ta kai bata iya wa saboda muryarta ta dushe.
Da-na-sanin
fallasa kanta a filin jirgi ya ziyarceta. Sai da suka yi mata lilis sannan suka
barta kwance cikin mugun yanayi, Ta kasa ko motsi sai idonta kawai take juyawa
hakan ya bata damar ƙura
wa bangon ɗakin ido tana tuna rayuwarta.
Ita
kaɗai
mahaifiyarta ta haifa ta rasu, ta tashi wajan kishiyar mahaifiyarta wacca ta yi
mata riƙon sakainar kashi. Rayuwarta abar sha’awa a wajan mutane don tana
yinta ne a sanyaye bata cika shiga jama’a ba
duk da tana sana’ar ƙunshi, sai dai bata samun mutane da yawa
don ba a barinta yi, a haka take rayuwarta wacca take ganin tamkar akan ƙaya take don girmanta ya sa Inna
kishiyar mamanta ɗora
mata duk wani aikin wahala ko na ƙarfi
ita ke yinsa da karatunta kawai ta tsira saboda babanta ya dage akan yana son
ya ilimantar da ‘ya’yansa, a haka
ta gama secondary ta samu sakamako mai kyau, babansu ya ba ta damar cigaba da
karatu. Yusuf ya shigo rayuwarta ne kwatsam duk yanda ta so yakice shi abun ya
faskara don Yusuf saurayi ne mai matuƙar
surutu da son saka mutane a nishaɗi,
bata san ya a ka yi ba sai tsintar kanta cikin tsananin
soyayyarsa don har gidansu ya tura iyayansa aka tsayar da maganar aure kan yana
kammala karatu sai aure saboda shi a lokacin yana aji uku ita kuma tana aji ɗaya
gab da shiga aji na biyu.
Soyayyarsu mai tsabta suke yi, don sosai Yusuf ya sake a
gidansu saboda daƙin zaure aka ba su inda suke hirarsu
a nan, sau tari suna tsaka da hira idan aka yi abin dariya sai ya kai hannu
cinyarta tun tana ɓata rai da nuna masa bata so, sai ya nemi afuwarta da
cewar ya saba hira da abokanansa ne ya manta, ta amshi uzirinsa don tasan shi
mutum ne mai hira da abokai. Da haka ya fara zarcewa har yana kai hannu duk
inda ya ga dama da ta nuna ranta ya ɓaci sai ya nuna na shi ya fi nata ɓacin saboda tana ƙoƙarin mayar da shi ɗan iska wani zubin
har tafiyarsa yake ya barta a nan sai ta nemo shi ta ba shi hakuri saboda tana
son shi, har ta kai yana yanda ya so bata isa ta yi magana ba saboda kada ransa
ya ɓaci ya tafi ya barta. Abinda yake yi mata yana ci mata
tuwo a ƙwarya amma ya ta iya, son shi take
kamar ta cire ranta ta ba shi sau tari idan ya yi yanda ya so da ita sai dai ta
shiga ɗaki ta yi ta rusa kukan baƙin cikin abun, babban takaicinta yanda ta zama kamar wata
raƙumi da akala wato sai yanda yaga dama da ita, har takai
ta kawo ma kiranta yake wasu keɓaɓɓun waje ta je ta same shi, ba kuma isa ta ƙi zuwa ba, hakan da yake mata ko alama baya gudunta don
wata soyayya yake nuna mata kamar babu wata mace a duniya sai ita, sau tari ya kan
faɗa mata yana kallon mata ne tamkar yan’uwansa maza don
idanuwansa da ita kaɗai suke kallo a mace don ita ta mallaki dukkan abin da
yake nema a wajan mace. Yana yawan faɗa mata akanta babu abin da ba zai
iya yi ba, kuma zai iya komai don ya mallaketa don haka ta kwantar da
hankalinta ta saki jiki ita ce mace ɗaya tilo da ta sarƙafe masa zuciya
kuma ita ce kawai yake kallo ta dace da zama uwar ‘ya’yansa. Waɗannan
kalamai nasa sun taɓa mata zuciya kwarai kuma
sun yi tasirin da ta mayar da kanta tamkar mallakinsa.
A
haka suka kwashe shekara ɗaya tare suna gudanar da
wannan rayuwar wadda ta
zame mata matsala,
kwatsam wata ƙawarta
ta kawo mata katin ɗaurin aurensa. Tun daga
ranar lafiyarta ta yi mata hijira kira babu wanda bata yi masa ba ya ƙi biyo sahu duk inda yake kiranta ta je
nemansa babu shi babu alamarsa ga tsananin rashin lafiyar da ke addabarta, mahaifinta da kan shi yake rarrashinta
akan ta haƙura da shi tunda ba
shi kaɗai
ba ne namiji tana da manema ta barshi ta fauwalawa Allah tabbas ubangiji zai
karɓi
addu’arta.
Tun
tana ƙunci da baƙin
ciki akan hakan har ta kai yanzu ta lafiyarta take. Ta je kemis tasha magani kala-kala amma sauƙi babu a haka mahaifinta ya gaji ya kaita babbar asibiti
gwaji, aka tabbatar masa da tana da cikin wata biyu. Da
kyar Baba ya tambayeta cikin
waye, Cikin kuka ta sanar da shi.
Ya rufe ta da wani irin duka, duk abin da ya ɗauko maka mata yake
da kyar aka kwaceta, sai da Inna taga bata motsi ta yi kururuwar akawo mata ɗauki, yana gama
dukan ya yanke jiki ya faɗi. Labarin cikin Zainab har makaranta, ‘yan unguwa kuwa suka samu
abin yi yara da manya na tururuwar zuwa ganinta. Baba kam ya shiga tashin
hankali mara misaltuwa
don cikin fitar hayyacin yake jerawa Zainab munanan maganganu marasa daɗi.
Irin kalaman mahaifinta ya fi komai ɗaga
mata hankali.
Shi
Yusuf da ya ji labarin ya yi tsalle ya dire ya ce sharri take yi masa su je can
su nemi uban da ya yi wa ‘yarsu ciki. Abu ta kai
har da ‘yansanda sai da ya ji matsi ya
amsa. Ko da suka dawo gida hawaye baba ya yi ta yi har da furta mata kalmar ina
ma ban haife ki ba Zainab. Wannan maganar ta shi ce tasa ta yanke shawarar
barin duniyar don ta huta. Yana fita sallar la’asar ta fito da gudu ta zunduma
kanta a rijiyar gidan.
An
yi nasarar fitar da ita sai dai cikin nata ya fice duk da baƙar wuyar da tasha a asibiti hakan bai sa
babanta tausaya mata ba, ita kaɗai ta san ciwon maganganun
da babanta ke yi wanda take ganin Inna ce take ƙara
zuga shi. Inna na sane take aikenta waje duk da bata da lafiya duk ta fita, haka mutanen unguwar za su rakata da idanuwa
suna nunata har ta dawo. Ta rame ta jeme. Ita kam tuni kome na duniya ya fita kanta, babban abinda ke ci
mata tuwo a ƙwarya
wata ƙara take ji a kunnanta da kuma rashin
bacci don yanda taga dare haka take ganin rana sai bayan sallar asuba baccin ke
surarta shi ma tana farawa Inna ke tashinta da faɗan
tsiya akan ta tashi ta gyara gida.
Baba
lamarinsa sai ta’zzara yake faɗan yau dabam da na gobe,
haka faɗan
Inna yaƙi tsayawa, tsegumin mutane da rashin
bacci da wannan ƙarar
ya taru ya cukurkuɗe mata rayuwa ba shiri ta
yanke hukuncin tattarawa ta bar gidansu ba tare da sanin kowa ba, ta tafi can
Kaduna wajan ƙanwar
mahaifiyarta, zuwanta gidan ta amshe ta don dama tun tana yarinya suka so
amsarta baban ya ƙi
duk kuma suna da labarin abin da
ya faru da ita.
Ƙanwar mamanta da take kiranta da Anty ita ta yi ta tausar
ta tana kwantar mata da hankali a haka har ta saki jiki uwa-uba unguwar babu
wanda ke yi mata kallon tara saura biyu, matsala ɗaya mijin Anty
talaka ne don da kyar ake iya cin abinci sau ɗaya a gidan, ganin
zata shiga mummunan yanayi yasa ta dawo da sana’arta ta ƙunshi cikin hukuncin Allah ta samu karɓuwa.
A sanadin ƙunshi ta haɗu da Saddika wacce
kowa a unguwar yake yi wa kallon ‘yar bariki ta su ta zo ɗaya sosai don duk
Saddika ta zauna tana bata labarin irin wahalhalun da ta sha wanda ciki har da
rashin bacci cikin mamaki Zainab ta katse ta “Kina nufin kema kina fama da
wannan lalurar?” Cikin mamakin ita ma Saddika ta amshe da “Sosai ma kuwa Zainab
don kin ganni nan aurena biyu a ‘yan ƙananan shekaruna
dukkan mazajen nan babu na arziƙi dole ce ta sani
zawarci, tsangwama da kuma ƙunci ne yasa na
kamu da cutar baƙin ciki har na daina barci da na je
naga likita ta ce mini ya zama dole na daina tunani na kuma daina damuwa idan
ba haka ba kuwa tabbas cutar zata iya haihuwa ta zame min babba da zan iya rasa
hankalina.
Bayan na dawo gida
hankalina ya tashi dole na nema wa kaina mafita yanzu ai labarin rashin barci
ya zama tarihi a rayuwata Zainab, don ko yanzu na so yin barci zan yi abina.” Cikin
jin daɗi
Zainab ta ce, “Na ji daɗi wataƙila nima warakata ta zo.” Cikin hikima
da hilata ta ware mata zare da abawa ta so yin gardama, Saddika ta yaudareta da
cewar wai babu mai sani kuma ai su dole ce ta sa ba wai don sun so ba.
Alaƙarsu ta yi ƙauri sosai don sanadiyyar Saddika, Zainab ta san
mutane, gidan
Anty kullum cike yake da mutane masu zuwa
lalle.
“Ina
son baki shawara ƙawata.”
Zainab ta kalleta. “Ke fa yanzu kin zama hajiya manyan yara na zuwa wajanki
lalle mai zai hana ki jefi tsuntsu biyu da
tarko ɗaya?
Ma’ana da wannan gantalin da muke zuwa siyan kayan harka ki saro mana kawai a
wajan su Muntari ki rinƙa sayarwa ko ya kika gani?”
Da
wannan ta zama dila a harkar, sun raina mutanen unguwar don da sana’ar ƙunshi ta fake take siyar da kayan maye
ga mata, ta yi ƙaurin
suna ga abokanan harka don sosai take ciniki. Dalilin sana’ar ta zama ita ce take faɗa a
ji a gidan don ita ke ciyar da su. Musamman Saddika ta haɗata
da manyan mata da ‘ya’yan masu kuɗi
wanda suke shaye-shaye. Ita kam ta zama hajiyar kanta ta manta da wani ƙuncin sai dai har gobe baƙin cikin Yusuf ya ƙi
barinta tana yawan binciken halin da yake ciki. Mahaifinta sai da ta kwashe
shekara ya neme ta duk da hakan cewa ya yi ta zauna a can shi bai son ganinta. Babban burinta shi
ne ta ji yau rayuwar Yusuf ta lalace don duk ta tuna shi a ranta sai ta jefe shi da baƙar addu’ar Allah ya yi kaca-kaca da
rayuwarsa. Babban burinta shi ne ta zama babbar hajiya ko ta halin ƙaƙa ba
don komai ba sai don ta ɗaiɗaita
rayuwarsa. Cikin hakan Saddika ta kawo mata shawarar ta samo musu hanyar
safarar kayan maye.
Azabar dukan da aka ka yi wa cikinta ne ya dawo da ita
daga dogon tunanin da take yi, Cikin jin azaba da murƙususun take jin masifar wacca ta shigo wai ashe
tambayarta take yi ta ƙi bata amsa hakan ya tunzirata dukan
nata, tana cikin shafa cikin don ji ta yi tamkar an fasa mata shi saboda azabar
zafi cikin jin zafi ta sake jin wani dukan hakan ya tunzirata yin ƙara tare da sumewa don bata ƙara sanin me ya faru ba.
An yi nasarar yi mata aiki ita da Saddika don tun a filin
jirgi bata san a wanne irin hali Saddikan take ciki ba, an cire kayan mayan da
Oga ya sa musu an kuma tallatasu a duniya duk yanda aka so su yi magana sun ƙi duk da cewa an raba su da kayan mayen sai dai gargaɗin oga na bibiyasu
don ya tabbatar musu da cewa tona masa asiri tamkar ƙarewar zuri’arsu ne a doron duniya wai sai ya sa an kashe
dukkan iyayensu da ƙannansu da danginsu, a yanda suke ji
ƙwara su su mutu da su yi sanadiyyar mutuwar danginsu
saboda Oga ya faɗa musu shi ba ƙaramin mutum ba ne
yana da rassa kala-kala a duniya sannan kafin ka shiga harkar sai an sanka an
san iyayanka da adireshinka, da shi zai fara yi maka barazana.
Tambayoyi
da azaba babu wanda ba ta
sha ba ta ƙi magana don asalima
bata san cikakken sunan Ogan ba, sannan bata san inane gidansa ba don duk haɗuwar
da za su yi a otel suke haɗuwa. Sau tari idan ‘yansanda
suka shigo, abin da
suke tambayarta dabam da amsar da take ba su, su da kansu suka fuskanci lallai
akwai matsala.
Ta ƙurawa likitan da ke tambayarta ido tana
kallonsa tamkar Yusuf don fuskarsa take gani. Cikin zubar hawaye ta ce, “Ka ci
riba ko Yusuf? Menene babban laifin da na yi maka? .” Ta tashi cikin wani irin
kwarin gwiwa ta shaƙo
shi da kyar ‘yansandan dake gadinta suka kwace shi, tuburan ta haukace musu
tana ihun a bata shi ta kashe shi.
Bata
san ya aka yi ba, sai farkawa ta yi ta ga likita a kusa da ita tana jera mata
sannu. “Likita na sani an yi mini aiki an cire mini kayan mayen amma bayan nan
ina jin surutai a kunnuwana sannan ina ganin maƙiyina
Yusuf na ƙoƙarin sake cutar da rayuwata, kuma ina
ganin wasu mutane a kusa da ni suna kallona don jiya ma wata tsohuwa a cikinsu
ta ce mini wai zata taimaka mini.” Ta ƙarasa
maganar cikin jin jiki. Gyaɗa kanta likitar ta yi. “Kada
ki damu Zainab nima abin da
ya kawo ni kenan na yi miki wasu tambayoyi wanda nake son ki amsa mini su don
su za su taimaka mini wajan gano ainahin abin da
ke damunki.” Girgiza kai Zainab ta yi cike da gamsuwa.
“Tun
yaushe kika fara jin surutan?”
“Tun
da aka kama ni ne don a ranar
ma sai da na ji muryar wani yaro yana faɗa
mini wai na gudu.” “A da can baya kafin a kamaki kin taɓa
jin makamancin haka? Ko ki ji surutu ko ƙarar
wani abu a kunnanki?” Cikin sauri Zainab ta ɗaga
kai. “E, lokacin da bana bacci na kan ji kamar ƙarar
ƙarafa
a cikin kunnena.” “Kin taɓa lalurar rashin bacci
kenan?” Cikin tabbatarwa ta ce, “Sosai ma kuwa don na jima bana barci,” “Ya aka
yi kika samu lafiya, ma’ana magani kika sha kika dawo yin barcin?” Hawaye ya
sauko mata. “Na sha kayan maye ne.” Tsura mata ido likitar ta yi, “Bayan kin
sha kayan mayen baki ƙara
jin wannan ƙarar
da kike yawan ji ba?” “Ina ji. Likita don Allah me ke damuna.”
Ajiyar
zuciya likitar ta yi. “Kina fama da severe depression. (cutar baƙin ciki).” Kuka ta fashe da shi.”Ba dole
na kamu da cutar baƙin
ciki ba likita kin san wahalar da na sha a rayuwata kuwa?” Girgiza mata kai
likitar ta yi. “Amma kuma ke da kanki kika yi sanadiyyar hauhawar cutar zuwa
matsayin da zaki rasa hankalinki gaba ɗaya.”
Mamakin Zainab ne ya hanata kukan sai kallon likita da ta yi. “Ni kuma likita
ta yaya?” “Ta dalilin shan kayan maye da kika
yi, a tunaninki wannan kayan mayen sauƙi ya baki, to shi ɗin
ne sanadin rasa hankalinki.
Depression yana ɗaya daga cikin cutukan da muke kira
da sunan non communicable diseases wato cutukan da ba a ɗaukarsu a wajan
kowa sannan su waɗannan cutukan babu wanda ya san causes dinsu ma’ana abin da
ke kawo su sai dai wasu dalilan kan saka su hauhawa a jikin ɗan adam wanda drugs
abuse wato shaye-shaye na ɗaya daga cikin abin da ke hauhawar da cutukan, su kaisu
kan babban matakin da ba a so, lokacin da ƙunci yasa kika kamu da cutar maimakon ki zo asibiti a
dora ki akan anti depression drugs, maganin cutar sai kika gwammace shan
maganin maye don yaye miki rashin barci kinga ƙilu ce ta ja miki bau, amma kada ki damu in sha Allahu
idan aka ɗoraki akan magani kuma kika kiyaye tabbas zaki warke.” Kuka
ta fashe da shi da ƙarfi.
“Shi
kenan yanzu haka zan ƙare
a rayuwata! Haka zan dauwama! Wallahi Saddika kin cuce ni da ace ban sha kayan
mayen nan ba ban kuma yarda da safararsu ba tabbas da yanzu ina nan da
hankalina, wayyo wannan rayuwa!” Kanta ta fara bugawa jikin bango tana sambatu.
“Na tashi a tutar babu kenan? Bayan taɓin
hankali ga hukuma na jirana don shukar abinda na girba! Tabbas ba zan wahalta
ba ni kaɗai
zan fallasa Oga idan ya so a yi mutuwar kasko! Zan kuma faɗawa ‘yansanda
abin da ya ce akan dangina!”
Ta
fallasa sirrinsa don ta sanar da su komai babu abin da ta sani akansa illa tana da wani hoto a
wayarta da ta ɗauki selfie (hoton kai da kai) cikin
kuskure ya fito a ciki shi ma hoton ta ɗauka
ne saboda kayatuwar otel ɗin da suka je wajansa, in da
suka keɓe
shi da ainahin wanda ya kawo su wajan a nan
ta ɗaga
wayar ta yi hoton.
Da
wannan kaɗai ‘yansanda suka yi nasarar kama shi.
Ita kam Zainab sai hamdala don tuni suka ajiyeta asibitin masu taɓin
hankali, da kyar ta samu labarin wai Saddika ta rasu bayan an yi musu aikin
cire kayan maye mutuwarta ta girgizata ta kuma ƙara
shiga taitayinta.
Ƙarshe!
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.