Citation: Muhammad ADAMU da Ahmed Sulaiman BAFFA da Usman Ibrahim KAOJE (2024). Turken Tauhidi A Wasu Waƙoƙin Husaini Jikan Boka. Yobe Journal of Language, Literature and Culture (YOJOLLAC), Vol. 12, Number 1. Department of African Languages and Linguistics, Yobe State University, Damaturu, Nigeria. ISSN 2449-0660
TURKEN
TAUHIDI A WASU WAƘOƘIN HUSAINI JIKAN BOKA
By
Muhammad
ADAMU
Da
Ahmed
Sulaiman BAFFA
Da
Usman
Ibrahim KAOJE
Tsakure
Wannan
takarda ce mai taken ‚Turken Tauhidi A Waƙoƙin Hussaini Jikan Boka‛. Hussaini Jikan Boka fitaccen mawaƙi ne da ya shara ga basira
da yake ƙulla zaren tunaninsa wajen
sako saƙonni masu muhimmanci a
cikin waƙoƙinsa. Tauhidi babban batu
a cikin rayuwar Musulmi wannan ya sa yawancin mawaƙan baka sukan yi amfani da
shi wajen jan hankalin da tunasarwa ga jama’a. Saboda haka, wannan takarda
tana ɗauke da bayani kan tauhidi
da rabe-rabensa, da kuma fito da misalan kalmomin tauhidi a cikin waƙoƙin wannan mawaƙi Hussaini Jikan Boka.
Daga ƙarshe hakan ya nuna irin
taka rawar da addinin Musulunci ya yi wajen kawo Allah kusa da al’umma ta sanin
tauhidi, mawaƙi Hussaini Jikan Boka ya
yi amfani da wannan dabara cikin wasu ɗiyan waƙoƙinsa.
1.0 Gabatarwa
Tauhidi
shi ne kaɗaita Allah Ta’ala da bauta tare da amincewa
da dukkan abin da ya jingina wa kansa na sunaye da siffofi da ayyuka. Tauhidi
ne abu na farko da ke tabbatar da kasancewar mutum Musulmi. Kaɗaita Allah
(tauhidi)
shi ne ginshiƙi na farko mai ƙarfi da addinin Musulunci yake kansa. Don a
kaɗaita shi (Allah) ne ya aiko Annabawa da manzanni masu yawa daga
zamanin Annabi Adamu (AS) zuwa Annabi Muhammadu (S A W). Bayan tauhidi sai
sauran ayyukan ibada kamar Sallah da Azumi da Zakkah da Hajji da sauran
al’amurran zamantakewa, (Umar Aliyu Bunza: 2014).
Al’ummar
Hausawa mutane ne waɗanda suka kasance Musulmi,
kuma masu riƙo da tauhidi cikin kowane
lamari nasu. Wannan ya sa kowane abu ya faru mai kyau ko maras kyau, Bahaushe
yakan danganta kasancewar abin daga Allah (S W T). Husaini Jikan Boka
yana ɗaya daga cikin mawaƙan Hausa wanda ke da cikakken tasirin
musulunci cikin rayuwarsa. Wannan tasirin ya kasance wani muhimmin abu har
cikin waƙoƙinsa. Kasancewar tauhidi ginshiƙi ne babba cikin rayuwar Musulmi, ya sa
Husaini jikan Boka yake tsarma tauhidi waƙoƙinsa, musamman yayin buɗe wasu daga cikin waƙoƙin. Yana yin haka ne saboda wani lokaci ya yi
wa al’umma wa’azi da faɗakarwa. Wani lokaci kuma
saboda tasirin Musulunci da ƙarfin
imaninsa ga kasancewar Allah mai iko ne kan komai da kowa, kuma mai aikata abin
da ya so, da kuma kasancewar Allah abin dogara da neman biyan buƙata da kuma kariya. Manufar wannan takarda
ita ce nazari tare da sharhin tauhidi da ke ƙunshe cikin wasu mabuɗan waƙoƙin
Husaini Jikan Boka na Hausa.
1.1 Ma’anar
Tauhidi
Masana
lamuran addinin Musulunci sun dubi matsayin tauhidi a Musulunci a kuma a bin da
ya ƙunsa suka fito da ma’anoni
daban-daban gwargwadon fahimtarssu. Ga kaɗan daga cikinsu.
A
cewar Wazirin Kano (1980:8): Tauhidi shi ne tabbatar da samuwar zati, ƙaduri, mai siffofin kamala, tsarkakakke daga
kowace irin tawaya da kowace irin naƙasa
wanda bai yi kama da komai ba, kuma babu wani abu da ya yi kama da shi ta
kowace fuska da kowane hali.
A taƙaice idan aka yi la’akari da wannan ma’ana a
iya cewa, tauhidi shi ne
tabbatar da samuwar Allah Maɗaukakin sarki mai kowa mai
komai tare da bauta masa shi kaɗai ba tare da tarayya da
komai ba a cikin kowane nau’a na bauta masa ba, da kuma sakankancewa ga samun
sakamako ga yi masa bauta da kuma azaba ga yi masa tarayya a bauta.
1.2 Rabe-Raben
Tauhidi A Musulunci
Tauhidi
ya mamaye dukkan rayuwar Musulmi wanda hasali ma shi ne ƙofar da ake shiga addinin Musulunci daga gare
ta. Wasu malaman Musulunci kamar Asimina (1980) ya karkasa tauhidi zuwa gida
uku kamar haka:
a. Tauhidur-Rububiyyat
(Kaɗaita Allah da ayyuka) wanda shi ne tauidin kaɗaita Allah da ayyuka misali halitta, da azirtawa da rayawa da kashewa da juyar
da al’amurra da kawar da cuta da makamancin waɗannan.
b. Tauhidi-uluhiyyat (kaɗaita Allah da bauta) shi
ne na kaɗita Allah da bauta misali, addu’a da yanka da alwashi da neman
taimako da neman tsari da wanin waɗannan. Wannan nau’i na
tauhidi shi ne wannan da kafurai suka yi musun shi, kuma jayayya ta kasance a
cikin shi take tsakanin manzanni da al’ummunsu tun daga Nuhu amincin Allah ya
tabbata a gare shi har zuwa ga Annabi Muhammadu sallallahu alaihi wasallam.
c. Tauhidi-Asma’u was-sifft. (kaɗaita Allah da sunaye da
siffofi) wannan ana nufin miƙa
wuya (Imani) ga dukkan abin da ya tisgo (ya zo) a cikin Alƙur’ani mai girma da hadisai ingantattu na
daga sunayen Allah da da siffofinsa waɗannan da ya siffanta kansa
da su, ko manzonsa ya siffanta shi da su a kan haƙiƙan (tabbaci). Waɗannan su ne muhimman kasha-kashen tauhidi da malaman Musulumci
suka bayyana.
1.3 Taƙaitaccen Tarihin Hussaini
Jikan Boka
An
haifi Hussaini Jikan Boka a ƙauyen
Madugu na Ƙaramar Hukumar Misau ta
jihar Bauchi a shekarar 1946. Sunan mahaifinsa malam Muhammadu Ɗan Jimeta da mahaifiyarsa Malama Aishatu.
Asalin mahaifinsa mutumin ƙauyen
Daya Kudu maso Yamma da Potiskum da ke Ƙaramar Hukumar Fika a jihar Yobe. Ita kuma mahaifiyarsa ’yar ƙauyen Gadama ce a Ƙaramar Hukumara Misau, jihar Bauchi. Hussaini
Jikan Boka ya samu wannan laƙabi
na Jikan Boka ne ta wajen kakarsa ta wajen ubansa, wadda ta kasance Boka ce.
An kai Hussaini
Jikan Boka makarantar Allo (Al’ƙur’ani)
a garin Kuli wurin Malam Idi lokacin yana ɗan shekara tara. Bayan
wasu ’yan shekaru ya koma ƙauyensu.
Bayan dawowarsa gida, a wannan lokacin ne ya ga abokinsa mai suna Tintin yana
kaɗa kumbi, wannan ya ba shi sha’awa. Dalilin haka ya sa shi haɗa nasa. Cikin wasu watanni ya fara zuwa wasu ƙauyuka yana waƙa. Waƙarsa ta farko ita ce da ya
yi da harshen Karekarenci mai taken ’Tansuku Ma Kwarabai, ma’ana ‘A Gaya Masa
Ba Ta Nan Ba’, waƙa ce ta soyayya.
Husaini Jikan
Boka ya samu karɓuwa da shahara a wajen
jama’a musamman ma masu kuɗi da ‘yan siyasa a
dukkannin Arewacin Nijeriya da Nijar. Daga cikin mutanen da Jikan Boka ya yi wa
waƙa akwai tsohon gwamnan
Borno Alhaji Muhammadu Goni da Waziri Ibrahim tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa
da Sanata Ahmad Aruwa da Tsoho Abdullahi Zariya da Lawandi Tabako Zariya da
Hashimun Tukur Sakkwato da Shata Katsina da sauransu da yawa.
Haka nan yana
da alaƙa da mawaƙan Hausa kamar su: Alhaji Mamman Shata da
Haruna Uji da Ɗanmaraya Jos da sauransu.
Daga bisani Hussaini Jikan Boka ya bar sana’arsa ta waƙa ya koma gida Potiskum da zama, dama a nan
iyalansa suke da zama. Ya rasu a shekara ta 2007, yana da shekaru 61. Ya ya bar
‘ya’ya shida, biyar daga ciki mata, ɗaya namiji. Allah ya
jikansa ya gafarta masa, amin.
2.0 Ma’anar Turke
Gusau (2000:369), cewa ya yi‚ “Kalmar turke a
lugga a taƙaice tana nufin
wurin ɗaure dabba ko maɗaurin dabba ko tauye dabba ko mutum ko wani abu waje ɗaya ta yadda ba zai ɗaga ya tafi ba. Turke
a ƙa’idar masu nazarin waƙar baka na nufin saƙon da waƙa
take ɗauke da shi”. Ɗangambo (2007:14), ya ce‚ abin da ake nufi da
jigo shi ne saƙo, ko manufa, ko abin da
waƙa ta ƙunsa, wato abin da take magana a kai’.
Abba da
Zulyadaini (2000: 45) sun ce a bisa ga ma’ana, Kalmar Jigo na nufin‚ Saƙon da mawaƙi yake so ya isar cikin waƙarsa
ga jama’a.
Yahaya
(2001:17) ya ce: “Isar da saƙo a cikin waƙa yana nufin mai sauraro ya fahimci jigon waƙar, ya kuma samu tasiri a cikin halayyarsa
daga kalmomin da aka yi amfani da su cikin waƙar”.
Don haka turke
yana nufin saƙo ko manufa da mawaƙi ke son isarwa ga mai sauraro, kuma shi
babban maƙasudi na yin waƙa. Galibi mawaƙa kan tsara waƙoƙinsu bisa abubuwan da suka shafi rayuwar
al’umma na yau da kullum da suka haɗa da; addininsu, da
yanayin zamantakewarsu a gidajensu, da sauran al’amuransu na rayuwa. Husaini
Jikan Boka ya yi waƙoƙi da dama, kuma bisa manufofi daban-daban
daga ciki akwai kaɗaita Allah, wato tauhidi.
Jikan Boka ya
yi amfani da waƙoƙinsa wajen nusar da al’umma da karantar da
tafarkin muhimmi na addininsu, inda ya bayyana hanyoyin kaɗaita Allah a waƙoƙin nasa ta fuskoki guda uku da ake da su a
Musulunci, wato tauhidi rububiyyah da tauhidin uluhiyya da na asma’u wassifa.
Kmar yadda wannan takarda ta kawo bayaninsu dalla-dalla.
2.1 Tauhidur-rububiyya
(Kaɗaita Allah da ayyukansa)
Wannan shi ne
tauhidin kaɗaita Allah da ayyukansa, misali halitta da
azurtawa da rayawa da kashewa da jujjuya al’amurra da kawar da cuta da
makamancin waɗannan.
Tauhidin
rububiyyi ya bayyana cikin waƙar
‘Yakuba Direba’ kamar haka:
Jagora: Ya Tabaraka ya Allah.
: Sarki Jalla buwayi,
: In ban da Allah sarki,
: Ba wanda zai ba ka,
: Yau ya ba ka gobe ya ƙara ma.
A wannan ɗan waƙa Jikan Boka ya yi wa
Allah kirari ta hanyar ambaton sunayensa, inda ya ambaci kalmar ‚Tabaraka‛
wadda take nuna yawaituwar albarkar Allah, sannan ya kawo sunan Allah wanda
yake nuna shi ne yake da haƙƙin
abauta masa shi kaɗai. Bai tsaya a nan ba ya
ci gaba har inda ya siffanta shi da Sarki Jallah Buwayi gagara misali. A ƙarshen ɗiyan sai ya bayyana cewa
Allah ne kaɗai yake bayarwa yau ya bayar gobe. A dunƙule Jikan Boka yana nufin yau da gobe sai
Allah, domin shi ne bai da farko kuma bai da ƙarshe, shi ya azurta halittun farko, shi ke
azurta na yanzu kuma shi zai azurta halittun da za su zo nan gaba. Wannan ya
nuna cewa Allah ba ya buƙatar
kome, amma kowa yana da buƙata a wajensa.
Ya ci gaba da
kawo irin wannan nau’i na tauhidi a waƙarsa
ta ‘Gwamna Goni’ kamar haka:
Jagora: Zuljalali Allah Sarki,
: Sarkin dare da rana jalla.
: Gabar da Yamma Kudu da Arewa,
: To na duba baba ba ya Allah Sarki,
: Baba Jalla huwallazi mannanu,
: Sarkin Isai da Musa da Haruna,
: Bai hana bawa rabo ba Jafaru.
Tauhidi abu ne
da ya yi nisa cikin zuciyar Jikan Boka, ta la’akari da yadda a wannan ɗan waƙa ya kawo abubuwa da dama
da suka ƙunshi tauhidi. Bayan ya yi
wa Allah kirari, sai ya nuna cewa Allah ne kaɗai ke da ikon kawo dare da
rana, waɗanda su ne ɓangarori guda biyu
da ɗan’adam ke rayuwa a ciki, kuma suna da matuƙar muhimmanci da amfani ga rayuwar tasa.
Sannan a ƙarshen ɗan ya kawo Annabawa guda uku wato Annabi Isa da Musa da Haruna, ya
nuna Allah ne Ubangijinsu. Lalle waɗannan manzanni ne na Allah
waɗanda suka yi kira zuwa ga a bautawa Allah shi kaɗai kar a haɗa shi da kowa. A
wannan ɗan waƙa
Hussaini Jikan Boka ya kawo bayanai da suka shafi tauhidi na
rububiyya da na uluhiyya gaba ɗaya.
2.2 Tauhidi-uluhiyyat
(Kaɗaita Allah da bauta)
Shi ne tauhidi
na kaɗaita Allah da ayyukan bayi misali, addu’a da yanka da alwashi da
neman taimako da neman tsari da tawakkali da wanin waɗannan. Wannan nau’i na tauhidi shi ne wanda kafurai suka musanta,
kuma a nan ne aka samu jayayya
tsakanin manzanni da al’ummunsu tun daga Annabi Nuhu amincin Allah ya tabbata a
gare shi har zuwa ga Annabi Muhammadu (S.A.W).
Alhaji Husaini
Jikan Boka a waƙarsa ta “Allah Sarki”
(Bakandamiya) ya tabbatar da cewa, yarda da alƙawarin Allah na daga cikin tauhidi. Haka kuma, yin addu’a da yarda da Wuta da Aljanna gaba ɗayansu tauhidi ne na kaɗaita Allah da bauta kamar
haka:
Jagora: Alƙawarin Allah bai taɓa tashi ba,
: Ja da baya ga rago dattijo.
Jagora: Yadda ka yi mini sai Ziljalalu,
: Jalla shi saka ma shi,
: Da ma ya ba ka gidan Aljanna,
: Baba sai in ce amin.
Tauhidi ba zai
tabbata ga bawa ba har sai ya yarda da alƙawarin
Allah, don haka. Husaini Jikan Boka ke jawo hankalin al’umma da cewa lallai alƙawarin Allah ba ya tashi, wato duk a bin da
Allah ya faɗa a littafinsa na sakamako ga bayinsa gaskiya
ne. A cikin wannan bayani akwai nusarwa ga jama’a cewa su lizimci ayyukan
alkairi, don samun sakamako a lahira. Bayan haka, Husaini Jikan Boka ya yi
addu’a ga wanda yake wa yabo, saboda kyautar da ya yi masa da cewa; da ma Allah
ya ba shi gidan Aljanna. A nan Husaini Jikan Boka ya tabbatar cewa, yana daga
cikin cikar tauhi yin addu’a da kuma yarda da gidan wuta da Aljanna.
Jikan Boka bai
tsaya a nan ba, a waƙarsa ta Ahamad Aruwa ya ci
gaba da kawo tauhidi na kaɗaita Allah da ibada ya
kawo tawakkali, inda yake cewa:
Jagora: Uban Jamila ko ba kai ba,
: Gadon hali kyawun ɗa,
: Kowa ya bar hali, hali zai bar shi,
: Mai tawakkali daga Allah,
: Aikinsa ba ya ɓaci.
A ƙarshen wannan ɗan waƙa Husaini Jikan Boka ya
ambaci kamar tawakkali ga Allah, wanda yake nufin dogaro da miƙa dukkan al’amura ga Allah (S.W.T). Mawaƙin yana so ya nuna wa jama’a cewa, dole ne
dukkan Musulmi ya yi dogaro ga Allah ɗaya, domin shi ne mai ba
da kariya daga dukkan sharri, da mugunta, na aljanu, da mutane, da namun daji
da sauransu. Ya ci gaba da cewa mai tawakkali da Allah, aikinsa ba ya ɓaci. Mawaƙin
ya yi imani da cewa duk wanda ya mai da al’amarinsa ga Allah, zai samu nasara
cikin rayuwarsa ta duniya da lahira. A ɓangare guda mawaƙin na ƙoƙarin raba jama’a da
bokaye, da masu tsafi, da ‘yan bori, da masu sihiri, domin su yi riƙo da Allah shi kaɗai.
Husaini Jikan
Boka a waƙarsa da ya yi wa Ahmad
Aruwa ya bayyana tauhidi ta hanyar kawo littattafan da Allah ya saukar ga
manzanninsa don a kaɗaita shi da bauta kamar
haka:
Jagora:
Mai Linjila mai Dala’ilu,
: Mai Attaura
ga Ƙur’ani,
: Ga ma’ana ko
ga Tauhidi.
Mawaƙin ya lissafo manya-manyan littattafai da
Allah ya saukar waɗanda suka zama wajibi a yi
imani da su, domin suna cikin rukunan imani guda shida. Husaini Jikan Boka ya
nuna waɗannan littattafai saukakku ne daga Allah, Linjila littafi ne da
aka saukar wa Annabi Isa (A.S.), Attaura kuma ga Annabi Musa (A.S), sannan Alƙur’ani an saukar da shi ga Annabi Muhammadu
(S.A.W). Dole ne Musulmi ya yi imani da waɗannan littattafai kamar
yadda ya yi imani da Allah, da Mala’iku, da Annabawa, da ranar alƙiyama, da ƙaddara mai kyau da maras kyau. Ta hanyar sanin littafin da Allah
ya saukar ne ake sanin Allah, da sanin yadda za a bauta masa shi kaɗai ba tare da an haɗa shi da kowa ba.
Idan aka yi la’akari
da waɗannan misalai da suka gabata za a fahimci cewa, Husaini Jikan Boka
ya ba da gagarumar gudummawa ga al’umma wajen nusar da su hanyar kaɗaita Allah da ayyukan bayi, wato tauhidin uluhiyya. Inda ya kawo
addu’a, da tawakkali, da riƙo
da littattafan da Allah ya saukar domin a kaɗaita shi da bauta.
2.3 Tauhidi-Asma’u
Was-Siffat. (kaɗaita Allah da sunaye da
siffofi)
Wannan yana
nufin miƙa wuya (Imani) ga dukkan
abin da ya zo a cikin Alƙur’ani
mai girma da Hadisai ingantattu na daga sunayen Allah da siffofinsa, waɗannan da ya siffanta kansa da su, ko manzonsa ya siffanta shi da
su, a kan haƙiƙan
(tabbaci). Ga misali a cikin waƙarsa
ta Shehu Na Shehu, inda ya ambaci wasu daga sunayen Alla kamar haka:
Jagora: Zuljalali Allah Sarki,
: Shi za shi ba ka bai ma gori.
Jagora: Yau ya ba ka gobe shi ƙara,
: Sai Ziljalalu ya mannanu.
A
waɗanan ɗiyoyin Husaini Jikan Boka
ya kawo tauhidi na asma’u wassifa da tauhidi na kaɗaita Allah da. Ya Ambato sunayen Allah mai girma huda biyu wato,
Zuljalalu da kuma Allah. Waɗanna sunaye ne daga cikin
sunayen Allah ɗari ba ɗaya, wanda kalmar Zuljalal na nufin Allah shi ne mai
kammalalliyar ɗauka, Alƙur’ani sura ta 55, aya ta 78. Kalmar Allahu
kuma na nufin abin bauta Alƙur’ani
sura ta 20, aya ta 8. Waɗannan sunaye babu mai amsu
sai Allah shi kaɗai, don haka wajibi ne
kowane musulmi ya yi Imani da haka. Wannan ya sa Husaini Jikan Boka yake amfani
da su musamman, wajen buɗe waƙoƙinsa.
Ga su kamar haka:
Jagora: Shi za shi ba ka bai ma gori.
: Yau ya ba ka gobe shi ƙara,
: Sai Ziljalalu ya mannanu.
Jagora: In Allah ya ba ka dole a ba ka,
: In ya hana ka ba mai ba ka.
Sannan
mawaƙin ya ci gaba da bayani
kan tauhidi na kaɗaita Allah da ayyukansa
inda ya nuna, babu wanda zai ba ka yau gobe, ya ƙara maka, sai Ziljalalu. Kuma ya nuna cewa in Allah ya
ba ka dole a ba ka, in ya
hana ka, babu mai ba ka. A wannan ɗiyoyin waƙa Husaini Jikan Boka yana nufin wajibi ne
Musulmi ya yarda da Allah ya yi imani da shi ya dogara da ya nema a wajansa ya
bi dokokinsa ya hanu da haninsa, don shi kaɗai ne mai ba shi arziki da
lafiya da haihuwa. Kuma shi ne yake jarrabar sa da talauci da rashin lafiya da
rashi haihuwa da sauransu.
Jagora: Kan da rai da rabo,
: Yau kan babu rai rabo yau babu.
Haka
zalika Husaini Jikan Boka ya ci gaba da bayyana kaɗaituwar Allah, inda ya nuna kowane rai da Allah ya halitta ya
sanya masa arzikinsa. Dan haka yake cewa in har mai rai yana halin rayuwa to
yana tare da rabo, wannan ya ƙunshi
duk abin da mutane da tsintsaye da dabbobi da ƙwari suke rayuwa da su, da suka haɗa da; abinci da ruwa da sutura da mahalli da yawan kwanakin rayuwa
da duk wani abu da ɗan’adam zai mallaka. Mawaƙin ya bayyana cewa Allaha yakan ba wa halitta
rabo ne a yayin da yake halin raye, amma da zarar rai ya yi halinsa to rabo
ya ƙare. Abin da mawaƙin ke nufi shi ne, babu wani mai rai da zai
mutu, face kafin yam utu sai iya rabon da Allah y a ba shi sun ƙare. Wannan yana karantar da al’umma cewa, su
bar baƙin ciki da hassada
da ƙyashi da zagon ƙasa da ƙeta a tsakaninsu, domin kowa rabonsa yake ci.
Jagora: Na Shehu na Shehu,
: Gobara daga kogi,
: Ba mai tare ki sai Lillahi,
: Sai Ziljalalu shi kan tare ta,
: Na shehu ka
san daidai.
A
wannan ɗan waƙa
Jikan Boaka ya fito da iko da ƙudura
da ɗaukar Allah (S.W.A), inda yake cewa gobara daga kogi ba mai tare
ta sai Lillahi. Mawaƙin yana nufin duk wani
abin da ya gagari ɗan Adam ko fi ƙarfin tunaninsa ba zai gagari Allah ba. Don
haka mawaƙin ya yi amfani da misali
mai kama hankali inda ya ce, ‘gobara daga kogi’, kowa ya san kogi wuri da yake
cike da ruwa, ruwa kuwa shi yake kashe wata, idan aka ce ga wuta daga cikin
ruwa lalle zai zama abin mamaki, babu shakka hankalin mutum zai tashi domin
abun ya fi ƙarfinsa sai dai Allah. Don
haka mawaƙin yana faɗakarwa tare da nusarwa ga al’umma da su kiyaye dokokin Allah su yi
masa ɗa’a, lallai shi ne mai taimakonsu cikin abin
da ya fi ƙarfinsu.
3.0 Kammalawa
Mawaƙi Husaini Jikan Boka ya tabbata mutum ne da
ya tasirantu da addini kamar yadda aka gini gurare da dama cikin waƙoƙinsa
yadda faɗakarwa kan tauhidi ya mamaye da yawa daga cikin waƙoƙin.
A wannan takarda an lalumo fannoni na tauhidi guda uku daga cikin waƙoƙin
na Husaini Jikan Boka, wato tauhidi na rububiyya (kaɗaita Allah da Ayyukansa) da na uluhiyya (kaɗaita Allah da Ibada) da na Asma’u Was-siffat (kaɗaita Allah da sunayensa).
Manazarta
Altine,
H. (1983). “Aliyu Ɗandawo
Da Waƙoƙinsa”. Kundin Digiri na Farko, Jami’ar Usman Ɗanfodiyo, Sakkwato.
Asimina,
S. M. S. (1989). “Attauhidu Walfiƙhu
Wat-tajwid Lil-Faslir Rabi’u Al-Ibtida’iyyat. MahfulzatilWizaratil Ma’arif.
Saudi Arabiyya.
Bunza,
U. A. (2001). “Taɓa Kiɗi Taɓa Karatu: Tauhidi A Bakin
Makaɗan Bakan Hausa”. Kundin Digiri na Farko, Jami’ar Usaman Ɗanfodiyo, Sokkwato.
Bunza,
U. A. (2013). “Wa’azi A Bakin Gambo Dogo Mai Kalangu”. Cikin Mujallar Makaɗi A Mahangar Manazarta. Jerin takardun da aka gabatar a taron ƙara wa juna sani kan Tubar Muahammadu
GambonMai Kalangu, Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sokoto. ISBN. No: 978-8082-02-5.
Gumel,
M. A. (1992). “Tarbiyya Da Dangoginta A Waƙoƙin Makaɗan Baka Na Hausa”. Kundin
Digiri na Farko, Jami’ar Bayero, Kano.
Gusau,
S. M. (1993). Jagoran Nazarin Waƙar
Baka. Fisbas Media Serɓices, Kaduna.
Gusau, S.M.
(1996). Makaɗa Da Mawaƙa Na Hausa. Fisbas Media Serɓices, Kaduna.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.