Ticker

6/recent/ticker-posts

Tsokaci Kan Yadda Ake Gudanar Da Bincike A Bangaren Adabin Baka

Citation: Muhammad ADAMU & Ibrahim Muhammed OGAH (2024). Tsokaci Kan Yadda Ake Gudanar Da Bincike A Ɓangaren Adabin Baka. Yobe Journal of Language, Literature and Culture (YOJOLLAC), Vol. 12, Number 1. Department of African Languages and Linguistics, Yobe State University, Damaturu, Nigeria. ISSN 2449-0660

TSOKACI KAN YADDA AKE GUDANAR DA BINCIKE A ƁANGAREN ADABIN BAKA

Na

Muhammad ADAMU

Ibrahim Muhammed OGAH

GABATARWA

Adabin Hausawa wani ɓangare ne da aka sa gaba ana nazarinsa a makarantu manya da ƙanana, wanda yake duba abubuwa daban-daban kamar yadda masana suka kasa shi zuwa hanyoyi daban-daban. Manyan masana da suka shahara kan adabin Hausa haɗa da al’adunta, irin su Ɗangambo (1984) da Gusau (2008) sun yi bayani mai gamsarwa a kan cewa adabi hanya ce da al’umma ke bayyana hikimominta da sauran dabaru na sarrafa harshenta. Kamar yadda aka sani, an kasa adabi zuwa gida biyu manya, da akwai adabin baka ko ka ko gargajiya, sannan akwai adabin zamani ko rubutacce, wanda aka samo shi lokacin zuwan baƙƙasar Hausa.

Idan aka ce bincike na ilmi, abu ne wanda yake da hanyoyi da dabaru da ake bi wajen aiwatar da shi. Wato kowane irin bincike yana buƙatar a ɗora shi bisa wasu matakai waɗanda za su daɗa sanya ya zama mai nagarta kuma mai fa’idantuwa. Saboda haka, bincike in ji Odediran (2001) a cikin Bello (2010) ya ce, ‚Bincike Ilmantarwa ce da ake amfani da ita don gano wasu bayanai na ɓoye a kan wata matsala ko batu‛. Don haka a ganinsa bincike rigar sanyawa ce ga duk wani ɗalibi da yake son ya ilmantar a fagen ilmi da ta kamata ta kasance a wuyarsa ko da yaushe.

Wajen gudanar da bincike da ya shafi adabin baka, kamar wanda ya shafi fita fili (gari/wuri) mutum yakan fita da shirin yin cuɗanya da mutanen da kake buƙatar wasu abubuwa daga gare su. Misali, kamar a je ruga don yin bincike kan wasan shaɗi, dole ne sai mai bincike ya mai da kansa kamar su, ya yi cuɗanya da su ta sa irin tufafinsu da cin abincinsu, da sauran abububuwan al’adunsu. Domin ta haka ne, mai gudanar da bincike zai samu biyan buƙatarsa ta cim ma burinsu.

Saboda haka, wannan takarda za ta duba yadda ake gudanar da bincike ne a adabin gargajiya na Hausa, za a fito da hanyoyi da ake bi wajen tafiyar da bincike kan wannan batu da ya zo nan sama, bincike a wannan fage ya bambanta da yadda wasu suka ɗauka. A bincike da ya shafi adabin baka, akwai wasu hanyoyi manya da akan lura da su wajen gudanar da binciken. Da farko za a dubi ma’anar adabi da ma’anar bincike, sannan a hau kan yadda ake bincike a adabin baka.

1.1 MA’ANAR ADABI

Adabin Hausa batu ne da ya jima ana nazarinsa a ɓangarori daban-daban na ilmin al’ummar Hausawa. Masana sun ba da ma’anar adabi ta yadda suka kalli kalmar, wanda asalinta daga kalmar Larabci ce. Duk da cewa ma’anar adabi ta sha duba da aka fito da su domin ganin yadda kowane ya baje kolinsa. Ga abin da suke cewa:

Yahaya da wasu (1992:1) sun ce, “Adabi kalma ce wadda Hausawa suka aro ta daga harshen Larabci suka bayyana nau’o’in azancinsu da fasahohinsu da sauran hanyoyin zaman rayuwa da ita. Adabi a al’ummar ya shafi abubuwan Hausawa da yawa da suka haɗa da halayyar rayuwa da azancin magana da ayyukan fasaha da hikima da sutura da tarihi da waƙoƙi na baka da rubutattu da sauran hanyoyin zaman rayuwa. Domin haka, ta wani gefe ake cewa adabi madubi ne da ake amfani da shi wajen duba rayuwa tun daga haihuwa har zuwa mutuwa”.

Junaidu da wasu (2007:13) suna cewa, “Kalmar adabi asalinta ba ta Hausa ba ce, an aro ta ne daga harshen Larabci. A harshen Larabci ana kiran kalmar da ‘Adab’. Da Hausa ta aro kalmar sai ta mayar da ita ‘Adabi’. Adabi na nufin, wata babbar hanya ce da ɗan’adam yake yin amfani da ita don ya sadar da abubuwan da suka shafi rayuwarsa ko ta farin ciki, ko ta baƙin ciki, da kuma rayuwar ɗan’uwansa ga su ’yan’uwan nasa ko wasu daban. Wato hanya ce ta bayyana al’adu da kuma halayyar rayuwa, irin zaman duniya wanda al’umma suke gudanarwa tun a gadon-gado, wanda suka ɗauko daga iyaye da kakanni, suka riƙe su suna gudanar da su, kuma suke yin alfahari da su”.

Kamar yadda Ɗangambo (2008:1) ya ce, “Kalmar ‘Adabi’, kalma ce da Hausawa suka aro daga Larabci, Adab. A cikin Larabci kansa, wannan kalma ta ginu a kan ma’anoni iri daban-daban a lokuta daban-daban, tun daga jahiliya har zuwa lokacin bayyanar addinin Musulunci. Don haka wannan kalma ta sami ma’anoni iri-iri. Akwai lokacin da kalmar ‘adab’ ke nufin ‚kiran liyafa”. Akwai kuma lokacin da ma’anar ta ɗauki manufar ‘halaye na gari ko ɗabi’u masu kya’ da sauransu. Sannan kuma yana nufin wanda yake da ilmi na fannoni da yawa, da za a iya kiransa adibi da ya shafi halaye na ɗa’a da nagarta a wani lokaci. Saboda haka, adabi kalma ce da aka Hausance ta take nufin ta ginu a bisa ma’anar ilmin nau’o’in azanci da fasaha, na sarrafaffen harshe da ya ƙunshi ƙirƙirarrun fasahohin sarrafa harshe cikin tsarin waƙoƙi da ƙagaggun labarai da wasan kwaikwayo da sauran hikimonin sarrafa harshe: Adabi shi ne hoton rayuwar al’umma wanda yake nuna fasahohinsu da ƙwarewarsu da ci gaban da suka samu wajen iya sarrafa harshensu da ma rayuwar gaba ɗaya”.

Shi kuma Gusau (2011:1) yana cewa, “Sakamakon cuɗanyar Hausawa da Larabawa ta hanyoyi daban-daban ya kawo aka sami kalmomin Larabci suka shiga harshen Hausa. Daga cikin ire-iren kalmomin da Hausawa suka samo daga Larabci akwai kalmar adabi, mai tushe daga adab. Abin da kalmar adabi ke nufi shi ne, adabi wata babbar hanya ce da ɗan’adam yake yin amfani da ita don ya sadar da abubuwan da suka shafi rayuwarsa da ta ’yan’uwansa (iyali ko dangi ko ƙasarsa) ga su ’yan’uwan ko wasu daban. Abubuwan da yakan so ya sadar ɗn nan kuwa sukan shafi wani abu ne da ya daɗaɗa masa zuciya ko wanda ya sosa masa rai ko wanda ya shafi siyasa ko addini ko wayar da kai, wato ilmi. Saboda haka, adabin Hausa, adabi ne wadda ya shafi hikimomi da sarrafa harshe da kuma hanyoyi waɗanda suka shafi tafiyar da rayuwar yau da kullum kuma yakan zama mai yin darasu da hannunka-mai-sanda ko barbaɗa gishiri a rayuwa”.

Saboda haka, idan aka dubi waɗannan ma’anoni da masana suka ba da kan adabi, bori ɗaya suke wa tsafi. Kowane daga cikinsu ya ce, an aro kalmar ce daga harshen Larabci. Sannan kalma ce da take bayani a kan rayuwar al’ummar Hausa tun daga haihuwa har ƙarshen rayuwa. Wannan ya sa adabi kalma ce da take bayani kan dukkan abin da ya shafi rayuwar ɗan’adam.

1.2 MA’ANAR BINCIKE

 Bincike abu mai muhimmanci kuma ba ƙaramar rawa take takawa ba a ɓangaren ilmi, domin shi tsararren tafarki ne da ake amfani da shi ganin an shawo kan wata matsala da niyyar ilmantarwa. Wannan ya sa masana da dama sun yi magana wajen ba da ma’anar bincike, suna cewa:

 Kerlinger (1973) yana mai cewa, “Bincike wata tsararriyar hanya ce da ake bi ko amfani da ita don a gano wata matsala da niyyar yin gyare-gyare ko yin bayanai masu gamsarwa a kan abin da ake bincike a kai don cim ma manufar da aka sa gaba”.

Leedy (1974) ya ba da ma’anar bincike da cewa, “Hanya ce da muke bi don samo tsararren abu da taimakon gwaje-gwaje na zahiri, domin gano amsar tambaya ko kai ga wata matsaya kan wata matsala”.

 Bello (2010) cewa ya yi, ‚Bincike wani muhimmin abu ne a fannin ilmi, wanda ke nuni a kan yadda za a gudanar da nazarin wata matsala ko batu da ya shige wa mai bincike duhu, ta yadda za a fito da shi fili a warware matsalar ko a yi bayani ko zayyano shi ko kintace shi, a yi hasashen abin da zai biyo bayan binciken‛.

 Bunza (2017) yana cewa game da fahimtarsa, ‚Bincike wani abu ne, ta fuskar taliyo, ko diddigin tushensa, da duginsa, tare da ƙwanƙwance silalen mafarinsa. Kalmar ‚bincike‛ tana da alaƙa da tono wani tarihi ko bayani, ta fuskar tambaye-tambayen neman waɗanda suka san shi, ko suka naƙalce shi. A bincike, dole a ba da kambaɗa da cigiya da wakurwar madosa ga abin da ake son a tono ko a gano yadda yake ko yadda ake yin sa ko yadda ya kamata ya kasance‛.

 A bisa waɗannan ma’anoni da masana suka bayar kan bincike, za a ga cewa bincike ba ya yiwuwa sai da matsala. Wannan zai sa a yi ƙoƙarin binciko wani abu daban ko ɗori a kan wanda aka yi a baya. Saboda haka, bincike na da muhimmanci ƙwarai, domin samo amsa ko matsaya kan matsalar da aka gano.

1.3 TSOKACI KAN YADDA AKE BINCIKE A ADABIN BAKA

 Adabin baka wata babbar hanya ce da take nuna tunanin masu shi a cikin irin yanayin da suka faɗa. Wajen gudanar da bincike a kan adabin baka, akan lura ne da yadda shi kansa adabin bakan yake. Domin abu ne wanda ba rubuta shi ake yi ba, sai dai a yi shi a lokacin da ake yin sa. Kamar yadda sunan ya nuna, ya shafi aiwatar da shi ne da baki wato a gargajiyancen al’ada. A bincike irin wannan, akan dubi wasu sassan adabin da za a nazarta, da zai nuna yadda sigogi da nau’o’in bincike ke faɗawa ciki. A adabin gargajiya akwai manyan abubuwa da dole a yi la’akari da su wajen bincike, a san yadda za a gudanar da bincike a kansu, irin su: karin magana, tatsuniya, tashe, makaɗan baka, da sauransu.

Saboda haka, akwai wasu hanyoyi da ake bi wajen nazarin adabin baka, waɗannan hanyoyin sun haɗa da: zaɓen fagen bincike, shirya ginshiƙin bincike, bitar ayyukan da suka gabata ga mai bincike, amfani da na’urar naɗar abu, amfani da intanet, lura da kayan tarihi da ya dace, tsari na tattarowa da naɗar abu, masu sauraro da kallon wasanni da ’yan wasa, duba ayyuka da hanyoyin gudanar da bincike, ra’in da za a bi.

1.3.1 ZAƁEN FAGEN BINCIKE

 Fagen bincik e shi ne tunanin farko da zai zo wa ɗalibin ilmi kan abin da zai nazarta a Hausa. Cikin fannoni uku na nazarin Hausa wanda ya zaɓa, wato fagen sha’awarsa, kuma shi ne fagen da ya keɓanta da shi, ga ba da gudummawarsa. Duk abin da yake so ya yi bincike, ya riƙa kula da babban fagen sha’awarsa take.

 Saboda haka, zaɓen abin da zai yi nazari a kai, zai taimaka wajen samun yadda za a fara hawa kan sauran ko abin da zai biyo bayan wannan batu. Ɗaukar adabin baka a zaman fannin da za a bi, zai dubi wane batu yake sha’awa cikin ire-iren adabin baka, a zaɓi wanda ake son nazari kansa. Hakan zai haifar wa mai bincike ganin inda ya dosa a binciken da zai gudanar. Fagen bincike da aka zaɓa abu ne mai muhimmanci. Misali, Nazarin Wasu Tubala A Waƙoƙin Baka Na Hausa: Duba Ga Waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanƙwairo Muradun, da sauransu.

1.3.2 SHIRYA GINSHIƘIN BINCIKE

Akan shirya abubuwa kamar su sanin ilmin al’adun ƙabilu ko harshensu kafin a kai ga fita fagen binciken. Sai dai akan yi hakan cikin ci gaba da binciken da ake yi, idan kuma ya kasance ba a samu a farkon binciken ba, sai a yi shi daga baya.

Idan kuma ba a san ayyukan da za a yi masu kama ko ra’ayoyi sabbi ba, akan iya faɗawa cikin ruɗani ko wata hanya ta daban, a wajen gudanar da bincike na fita fili ko wanda ake yi a ɗakin karatu. Dole a san muhimman kalmomi da abubuwan da za a binciko.

Har ilau, yana da muhimmanci ga mai bincike ya san wasu al’adunsu ko tarihin mutanen da zai yi bincike a kansu, kafin ya fita wurin gudanar da bincike. Wato kafin ya je wurin da suke gudanar da wasannin nasu ko abubuwan da suka shafi al’adunsu, sai ya kintsa kansa da sanin yadda suke rayuwa.

Sannan sanin harshensu da kalmomin da suke amfani da su, shi ma zai taimaka ainun. Alal misali, ƙoƙarin sanin yadda za ka gabatar da kanka wajen magana ta baka, domin hulɗa da su a wannan wurin. Yana da sauƙi wajen yin bincike ga wanda ba harshensa ba, yakan iya mai da hankali ko sa kansa wajen ganin ya koyi harshen kan binciken da yake yi, da ma bayan binciken inda sanin harshen zai taimaka a nazarci abin da aka samo a filin. Sai dai wasu na ganin bincike kan adabin baka, kamata ya yi ainihin masu magana da harshen su yi binciken, ko kuma waɗanda suka ɗauki shekaru a cikin wannan al’umma. Amma wannan shawarar, ba a cika amfani da ita wajen gudanar da bincike irin na adabi ba. Misali, masana ilmin adabi daga ƙasar waje, suna buƙatar su sami ilmi mai zurfi kan abin da suke bincike, ya sa ake gudanar da komai tare da su a wajen wasannin ko bukukuwa ko makamancin haka. Domin masu harshen ba su da ƙwarewa ainun a kan dukkan daftari da kalmomin da ake buƙata kan binciken ba.

Bugu da ƙari, yana da kyau a dubi wasu littattafai da za su ƙara haske kan bincike da za a gudanar, ba lallai sai masu yawa ba. Yin hakan ya danganci sha’awa da ake da ita kan batun da aka ɗauka don yin binciken a kansa, da zai kasance a tattauna kafin zuwa filin ko kuma a lokacin da ake filin binciken.

1.3.3 BITAR AYYUKAN DA SUKA GABATA GA MAI BINCIKE

Wannan batu ya shafi duba wasu ayyukan ne da wasu suka taɓa yi a baya. Ba abu ba ne sabo, ganin yadda abubuwa ke kasancewa a duniyar a zamanin nan, yana da kyau a lura a dube su da idon basira. Domin mai bincike zai iya tunanin da wani ya riga shi yin sa, wato kafin ka yi irin aikin da ka yi tunani a kansa wani ya riga ka yi, ba tare da ka ga aikin ba, ba kuma ka ji labarinsa ba. Sannan wani zai iya yin aikinka, ba tare da ya san da shi ba, ko ya gan shi.

Saboda haka, bitar ayyukan da aka taɓa yi zai farkar da mai bincike daga barci ya san inda ya dosa, domin gujewa nanata abin da wani ya yi. Sai a nemo ayyukan magabata a zauna a nazarce su, ana nazari kan kiyaye hujjoji da dalilai da aka sarrafa a wani bincike a kan abubuwan da marubucin ke son ya tabbatar wajen ganin ya ɗora aikinsa a kai. Zai dubi ayyukan ne na sosai, tare da kiyaye manufar mai bincike ko aikin da ke gabansa, domin ya fito da abin da ya je nemowa a cikin ayyukan da ya gano.

Mai bincike ko manazarci ya san a aikinsa na babban digiri, waɗannan ayyukan da suka gabata sun haɗa da kowane irin aiki da aka gabatar gabanin naka. Irin waɗannan ayyukan idan aka ɗauko, ya kamata a bi diddiginsa har sai an gano abin da ake buƙata. A nan, ayyukan da za a yi bitar su sun danganci irin su wallafaffun littattafai da kundaye da aka rubuta a matakin neman ilmi na NCE, Difiloma, Digiri na farko zuwa na uku da sauran digiri, da muƙalu da aka gabatar a tarukan ilmi, muƙalu da aka buga a cikin takardar jerin muƙalu, da mujallu daban-daban, da dai sauran takardu da suka shafi ilmi.

Alal misali, littattafai irin su: Mawaƙa Da Maƙaɗan Hausa, Waƙoƙin Baka A Ƙasar Hausa, Adabin Hausa A Sauƙaƙe, da sauransu. Kundaye akwai kamar su: “Nazarin Falsafa A Waƙoƙin Hussaini Jikan Boka”, “Turke A Waƙoƙin Baka: Nazarin Waƙoƙin Narambaɗa” da makamantansu. Sai kuma muƙalu a cikin irin su: Liwuran Journal of the Humanities, Yobe Journal of Language, Literature and Culture, Harsunan Nijeriya, Zauren Waƙa, da sauran ire-irensu.

1.3.4 AMFANI DA NA’URAR NAƊAR ABU

Amfani da na’urar naɗar murya ko ɗaukar hoto ko bidiyo zai dace duk da cewa ma mai yiwa akwai shi da tsada. A bincike da ya shafi adabin baka, ana buƙatar yin amfani da na’urar naɗar abu da ajiyarsa yana da fa’ida wajen gudanar da binciken. A yau ana amfani da gani da idanu da sauraro, wani lokaci da na’urar bidiyo wajen al’amurar al’adun gargajiya, amma amfani da na’urar naɗar murya da alƙalami da takarda na da muhimmanci. Domin ga mai bincike a irin wannan ɓangaren, na’urar naɗar murya a wannan zamani, ba zai zama da wahala ba, domin na’urar ƙarama ce, ga sauƙi, ga kuma inganci, ga sauƙin sarrafawa, ga sauƙin kula da ita, tana da ƙarfi, sannan tana ɗaukar murya ko daga nesa. Akwai wasu dalilan da ya sa amfani da na’urar naɗar abu yana da fa’ida a bincike irin na adabin baka. Su ne kamar haka:

a. Wajen yin muhawara kan sa a samu murya kai tsaye da kuma hujjoji da za a bada.

b. A wasu ɓangarori na adabin gargajiya kamar ɗaukar murya ko amfani da gangar jiki, sai an buƙaci wannan na’ura domin daga baya za a zauna a yi nazarinsa.

c. Amfani da na’urar kan sa aikin ya yi sauri, ga rashin wahala, ba kasala wajen tattaro bayanai.

d. Na’urar kan yi taimako, domin abubuwan adabin baka, ba masu jimawa ba ne, yin hakan kan sa a adana, a isar ko yi nazarinsa. Wani lokaci dole a yi haka don a adana.

Saboda haka, manazarta ko masu bincike a ɓangaren adabin baka yana da muhimmanci su yi amfani da na’urar naɗar murya ko ɗaukar hoto a fagen bincike domin amfanin nan gaba. Duk da ma sai an kula da na’urar sosai, amma ba abin damuwa ba ne har idan za a mai da hakali a kansa.

Akwai wasu na’urori da mafi yawanci ake amfani da su wajen yin bincike a fili. Farko, abin za a yi a wurin kan zama tattaunawa da kuma amfani da na’ura. Akan shirya wasu ’yan tambayoyi da kuma neman izini, kusan su ne ginshiƙan abubuwa da za a buƙata wajen gudanar da bincikenka, domin kar a samu matsala idan aka ta shi amfani da na’urar. A wannan wuri akan yi abubuwa kamar su; yin rubutu, da ɗaukar hoto, naɗar murya, da ɗaukar hoto na bidiyo kamar fim ko majigi, da sauransu. Akan yi amfani da irin su; rekoda, kamaran hoto, kamaran bidiyo, wayar salula, da makamantansu.

1.3.5 AMFANI DA INTANET

Duk da cewa adabin baka abu ne da ake aiwatar da shi ta baka (baki), amma fa ana rubuta shi a kan takarda. Zamani ya kawo abubuwan da dole mai bincike sai ya yi amfani su, domin a yau babu yadda za a gudanar da bincike mai ma’ana ba a shiga duniyar ilmi a yi abota da intanet ba. Wannan ya sa dole mai bincike ko manazarci ya sa rigar zamani in yana son zamani ya karɓi saƙonsa hannu biyu. Domin a yau ana samun rubuce-rubuce da aka yi kan waƙoƙin baka, wasannin gargajiya, tatsuniyoyi, maganganun azanci, labarun gargajiya, duk a cikin shafukan intanet daban-daban wanda ’yan gida da waje suka ɗora domin gudanar da bincike ga manazarci a fagen adabin Hausa.

Mai nazari ya kamata sai ya mai da hankalinsa yana hawa kan intanet domin nemo shafukan da suka dace da aikinsa. Masana sun nuna akwai shafuka masu yawa da aka ɗora a kan intanet da mai nazari zai binciko ko taskace abubuwan da yake so wajen inganta bincikensa. Ana iya samun mujallun ilmi da wallafe-wallafe da suke da alaƙa da adabin baka da masana da manazarta suka rubuta suka ɗora a kan intanet. Alal misali, wajen nazarin waƙar baka, za a samu hanyoyin da za a bi wajen nazarin ta, ba lallai sai an yi amfani da littafi ba, idan kuma babu littafin a kusa, da sauran ire-iren adabin bakan.

Saboda haka, mai bincike ya san da cewa, yau duniyar intanet a ko’ina sananniya ce, domin tana da muhimmanci ƙwarai da gaske. Intanet zai samar maka da abubuwa masu yawa da kake buƙata, har da irin ayyukan da aka yi irin naka domin gujewa aiki iri ɗaya. Akwai ayyuka bila-adadin a cikin intanet kan adabin baka a yau, waɗanda za su taimaka wa mai bincike samun ingantaccen aiki mai karɓuwa. Intanet ba abin jefarwa ba ne ga mai bincike na babban digiri, a san da haka, amfani da shi ya zama dole.

1.3.6 LURA DA KAYAN TARIHI DA YA DACE

Kamar yadda wannan batu yake, ana ganin ba shi da alaƙa da bincike da ake yi a fili. Dukkan kayakin bincike da aka yi daga ɗakin tarihi da ɗakin karatu ko littattafai ne, yana da muhimmanci ƙwarai da gaske, a san cewa yana taimakawa ma a bincike na adabin baka. Ai an tattaro su ne da kuma rubuta ko juya su bayan an samo bayanai daga filin bincike, ta amfani da hanyoyin bincike da ake bi wajen bincike na adabin baka. Babban muhimmin abu shi ne, a san tushen abin da za a binciko. Saboda haka, a ɗauki tushensu duk daga bayanai ne da aka tattaro ko aka harhaɗa a baya daga amfani da wasu hanyoyi kamar su, na’urar naɗar abu da sauransu. Muna da irin waɗannan wurare ko ɗakuna da ake ajiyan kayakin tarihi da za a duba, akwai kamar su; ɗakin tarihi na Kaduna, gidan Makama a Kano, gidan Ɗan Hausa, da dai sauransu.

1.3.7 TSARI NA TATTAROWA DA NAƊAR ABU

Wannan hanyar ta danganci yadda shi mai bincike ya tsara aikinsa, kan iya zama shiga a yi da kai, ko kallon masu yi, ko yin hira ko ganawa ta yin tambayoyi, ko yin aikin dalla-dalla a fili, da zai kasance na wani ƙanƙanin lokaci ko lokaci mai tsawo cikin ziyarce-ziyarcen da za a yi. Babban fa’idojinsa ko iyakansa na da amfani sosai.

Ana amfani ne da tambayoyi nan take, akwai lokaci da wuri na naɗar ko kallon wannan abu a wajen bukukuwan, inda mai binciken ya samu damar yin haka. Misali, tatsuniyoyi, azancin magana ko yin waƙoƙi a wajen aiki. Duk waɗannan tsarin kan samu nasa maganganun da aka yi da kuma tasirinsa.

Sai dai lokaci da wuri kan hargutsewa mai bincike, ana buƙatar ya yi la’akari da amince da wasu sharuɗa fitattu. Domin wasu nau’o’in adabin bakan akan yi su a kowane lokaci, kamar aiki, waƙoƙi da bukukuwa, mafi yawanci akan yi su ne da rana ko safe. Sai dai sanannu su ne waɗanda ake yi lokacin hutawa, da yamma, hutu ko lokacin da aka samu sarari ko sakewa a cikin shekara. A wannan lokacin ne manya kan samu damar gudanar da irin waɗannan wasannin gargajiya, wanda manazarci zai samu damar gudanar da bincikensa a kan gaɓa (daidai). Wannan yana nufin manazarci sai ya shirya yin gwaji ko jarraba abin da suke yi a wannan lokacin, wato kamar cikin dare, wanda shi ne lokaci da ya zama muhimmi ga mutanen, domin ba lallai ba ne a shirya irin waɗannan wasanni a lokacin da zai dace da na mai bincike. Wani lokaci akwai doka kan faɗan yaushe da wurin da za a yi wani nau’in adabin gargajiya, ko zai kasance ko akasin haka a kan gudanar da wasannin. Saboda haka, mai bincike ya kamata ya samu sanin irin waɗannan lokutan a wurin magabata domin samun damar yin bincikensa.

Ta wannan hanyoyin mai bincike zai samu ’yancin naɗar murya ko hoton bidiyo ko kuma ɗaukar hoto, domin amfani da shi nan gaba bayan ya nutsu. A baya an yi magana a kan irin wasannin da ake yi a fili, mai bincike ba zai samu damar aikata dukkan abubuwan da suke yi a lokaci guda ba, sai ta naɗar abin da suke gudanarwa. Yin hakan zai samar da hanya mai sauƙi ga mai bincike ya sami abin da yake so cikin nutsuwa da inganci a filin wasan. Saboda haka, yana da muhimmanci a san irin tsarin da za a bi a tattaro da kuma naɗar bayanai da wasanni ko bukukuwa na gargajiya. Abin nufi a nan shi ne, binciken kan danganci irin su wasan shaɗi, wasan kalankuwa, tatsuniya, dambe, tashe, waƙoƙin yara, waɗanda suke buƙatar neman izini da ma lokaci da manazarci zai bi su.

1.3.8 MASU SAURARO DA KALLON WASANNI DA ’YAN WASAN

Mafi sauƙin abin da mutum zai yi a ɓangaren nau’o’in adabin baka shi ne, ya shiga a dama da shi. Wannan shi ne zai zama babban abin da yake son ya cim ma buri a wajen gudanar da binciken. Akan fara wasannin da lura da kula da dukka waɗanda suke cikin masu yin wasannin, wanda yake kawo ci gaba.

Wasanni da akan shiga a yi kan ba da dama a samu sani kan abin da ake bincike a kai, wanda za a sami mutane masu yin wasannin cikin yawa ko kaɗan. Ana kuma lura da shekaru da jinsi da muƙami, horon da aka samu da darajan mutum da ƙwarewarsu a lokacin yin bincike. Sannan a samu sunan mutum da darajarsa da tarihinsa wanda yana da muhimmanci a wannan ɓangaren. Bayan nan, akwai waɗanda suka ƙware sosai wajen gudanar da wasanni, da kuma waɗanda suka bambanta ta wajen sana’o’insu da sani a kan ayyukansu. Ya kamata a tsara wasu tambayoyi da za a buƙace shi, kamar; Wa za a ɗauka mai gudanar da wasa kuma ta wace hanya, ko zai hau kan adabin da al’adun gargajiya, da tunawa da ire-iren gwanin, ko naɗar abu? Sanin tambayoyi nan da za a yi na taimakawa a filin bincike.

Yanayin shiga cikin wasan ko kuma zama mai sauraro, wani lokaci ba a ɗaukarsa da muhimmanci a wajen gudanar da binciken, domin ana ganin kamar ba su da amfani. Sai dai a wajen bincike suna bambanta da juna, an ba da wasu abubuwan da ya suka bambanta su kamar haka:

a. Masu sauraro sukan ba da gudummawa ɗan kaɗan wajen rubutu a filin bincike.

b. A waƙa masu sauraro akan yi da su a irin waƙoƙin da ake yi a tatsuniyoyi ko lamuran addini.

c. Shiga a dama da kai a wajen yin tatsuniyoyi (ba da tatsuniya) ya bambanta da wajen sauraron tatsuniyar, domin idan aka yi haka ka taimaka wajen sauraro.

d. Waƙoƙin da ake yi wajen niƙa ko lokacin jan kwale-kwale ko waƙoƙin da ake yi a lokacin gudanar da wasanni. Waɗannan suna taimakawa wajen samun ilmi na yadda za a tunkari aikin bincike kan adabin gargajiya.

1.3.9 DUBA AYYUKA DA HANYOYIN GUDANAR DA BINCIKE

Wani muhimmin abu shi ne samar da ayyukan da aka yi kan adabin baka. Domin tunanin nemo irin waɗannan ayyukan kan sa a samu batu wanda zai dace da ra’ayinka na gudanar da bincike. A baya an ɗauki wannan batu kara zube wajen neman bayanai da aka tattauna da ya zama wani sashe na bincike da hanya ta wakilcin abin da aka binciko. Saboda haka, ginshiƙin yin bincike manufarsa a samar da ayyukan da aka yi a karance su, a samu abubuwan da ake buƙata. Wannan zai sa a san irin littattafan da za a duba sannan a ɗauke su wajen ganin an nazarce su. Babban abin da ake buƙata a wajen nazarin ko bincike da ya shafi labaran gargajiya na al’umma, irin waɗannan su ne littattafai da aka fi amfani da su wajen samun tatsuniyoyi, hikaya, almara da makamantansu a ciki. Domin ayyukan da aka yi cikin littattafan nan, sun faro ne tun lokacin da aka yi bincike ta cuɗanya da masu adabin da al’dunsu. Saboda haka, nazari na al’adun da labarun gargajiya da fasahohin baka an tattaro su ne aka zuba su cikin littafi don karantawa, shi ne mafarinsu.

Bayan nan, sai hanyoyin da aka bi wajen gudanar da wannan bincike. Kamar yadda bayanai suka gabata, na yi bayani cewa idan binciken ya shafi fita waje ne, can inda ake ƙoƙarin binciko abin da ake buƙata, lallai ne sai manazarci ya shiga kocakam an dama da shi. Sannan dole ne ya yi cuɗanya da su wajen sanin abin da zai daɗaɗa musu da kuma wanda zai zama akasin haka. Akwai kuma karance-karance da ziyarce-ziyarce da za a gudanar kafin a fara yin binciken, misali, fita zuwa wasu garuruwa da binciken ya faɗa a kansu kafin zuwa a yi cikakken bincike. Karance-karance kuwa, ya shafi irin ayyukan da aka taɓa yi kan binciken da ake son aiwatarwa, masu dangantaka na ƙut-da-ƙut da ma na kusantaka.

Sannan akwai amfani da na’urori kamar na naɗar murya wato rekoda, akwai na ɗaukar hoto da na naɗar hoton da murya (bidiyo). A kuma samu lokaci daga bisani a juya dukkan abin da aka samo a kan takarda domin a yi nazarinsu ɗaya bayan ɗaya. Bincike na adabin baka yana buƙatar a fita wajen nemo bayanai, domin ya fi ba da cikakken abin da ake buƙata domin cim ma manufa, kan wanda ake yi a ɗakin karatu.

1.3.10 RA’IN DA AKA ƊORA AIKI

Wannan ɓangare yana magana ne a kan wasu ra’o’i da masana ilmin adabi suka fito da su da kan iya hawa kan abin da ake bincike a kai. Ra’i yana nufin wata dabara ce ta wani masani ko wasu masana da aka kawo ko fito da shi fili wajen amfani da shi ana nazarin harshe ko adabi ko al’adu. A hakan akan samu ƙungiyar masana da manazarta inda sukan ayyana wasu ra’o’i a kan adabi da ake dubawa a yi amfani da su.

Saboda haka, masana da manazarta sun ƙarfafa amfani da ra’i musamman a nazarin adabi, domin hankalinsu ya fi karkata a ɓangaren. Wannan ya sa, ana buƙatar idan mai bincike ya tashi gudanar da aiki ya dubi wani ra’i da yake da dangantaka da wannan aikin nasa. Shi ne a kowane irin bincike da ya faɗa kan adabi, za a ga an ɗauki wani ra’i daga wata mazahaba da aka ɗora aiki a kai. Wannan shi ma yana ƙara ƙarfin binciken da ake yi, da ake ganin idan babu shi bincike bai cika ba ainun. Hakan ya sa yana cikin hanyoyi da ake bi wajen gudanar da bincike na adabi. Misali, akan sami ra’i daga mazahaba irin su; Zahiranci, Mararanci, Tubarkalla, da sauransu. Akwai ra’i kamar ra’in Ɗangambo ko Gusau ko Balarabe, da makamantansu.

2.0 KAMMALAWA

Bincike dai yana da ire-irensa kamar yadda masana suka faɗa, akwai bincike na tarihi da bincike na bayani da bincike na gwaji da dai waɗanda ba a rasa ba. Bello (2010). Amma wajen gudanar da bincike da ya shafi adabi, akan yi la’akari da irin binciken da za a yi, domin a adabin ma akwai na gargajiya da kuma na zamani. Saboda haka, bincike na adabin gargajiya an ga yadda ake yin sa, ganin hanyoyi da ake bi wajen nemo bayanai don samun sakamako mai kyau da zai ba da abin da bincike yake bu ata. A hanyoyin da aka samo akwai; zaɓen fagen bincike, ginshiƙin bincike, bitar ayyukan da suka gabata ga mai bincike, amfani da na’urar naɗar abu, amfani da intanet, lura da kayan tarihi da ya dace, tsari na tattarowa da naɗar abu, masu sauraro da kallon wasanni da ’yan wasa, duba ayyuka da hanyoyin gudanar da bincike, ra’in da aka bi. Irin wannan bincike yana buƙatar lokaci mai tsawo da kuma juriya da haƙuri da nutsuwa, domin ganin an cim ma buri. Bincike na sha’awa ganin yadda ake dagewa a ga an fahimci irin al’adu da wasanni da labarun gargajiya na wata al’umma don a samo bayanai. Wannan shi ne yadda ake gudanar da bincike a ɓangaren adabin baka. 

MANAZARTA

Bello, A. S. (2010) Dabarun Gudanar da Bincike A Hausa. Kaduna: Effectiɓe Media Serɓices, Printers/Publishers.

Bunza, A. M. (2017) Dabarun Bincike (A Nazarin Harshe Da Adabi Da Al’adun Hausawa). Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.

Ɗangambo, A. (1984) Rabe-Raben Adabin Hausa. Zaria: Amana Publishers Ltd.

Ɗangambo, A. (2008) Rabe-Raben Adabin Hausa (Sabon Tsari). Kano: K.d.g Publishers.

Finnegan, R. (1984) Oral Traditions and The Ɓerbal Arts: A Guide To Research Practices. London: Academic Press.

Gusau, S. M. (2008) Dabarun Nazarin Adabin Hausa. Kano: Benchmark Publishers Ltd.

Gusau, S. M. (2011) Adabin Hausa A Sauƙaƙe. Kano: Century Research and Publishing Ltd.

Junaidu, I. da Wasu (2007) Darussan Hausa A Kammale Don Ƙananan Makarantun Sakandare 1. Ibadan: HEBN Publishers Plc.

Kerlinger, F. W. (1973) Foundation of Behaɓioural Research (2nd Edition). New York: Holt Rinehart and Winston Inc.

Leedy, P. D. (1974) Practical Research: Planning and Design. New York: Macmillan Publishers.

Yahaya, I. Y. da Wasu (1992) Darussan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandare 1. Ibadan: University Press Ltd. 

 Yobe Journal of Language, Literature and Culture (YOJOLLAC)

Post a Comment

0 Comments