Citation: Nasir Usman NASIR & Hussaini Adamu GAƊAU (2024). Tarsashin Magungunan Gargajiya A Cikin Waɗansu Ƙagaggun Labarai Na Hausa. Yobe Journal of Language, Literature and Culture (YOJOLLAC), Vol. 12, Number 1. Department of African Languages and Linguistics, Yobe State University, Damaturu, Nigeria. ISSN 2449-0660
TARSASHIN
MAGUNGUNAN GARGAJIYA A CIKIN WAƊANSU
ƘAGAGGUN LABARAI NA HAUSA
Na
Nasir Usman NASIR
Hussaini Adamu GAƊAU
Tsakure
Wannan aiki da aka gabatar bincike ne da ya yi ƙoƙarin tattaro wasu ƙagaggun labarai watau littatafan zube da ya yi nutso a
cikinsu don zaƙulo abubuwan da suka shafi magungunan
gargajiya. Babu shakka akwai littatafai da ake gina jigonsu musamman a kan
nau'ukan magunguna gargajiya, inda a ciki ne ake samun yadda ake haɗa wani
siddabaru ko kuma wani sinadari don warkarwa ko illatarwa. A ƙoƙarin tattaro bayanai kuwa, an yi amfani
da hanyar karance-karancen ƙagaggun labarai irin su “Ruwan Bagaja” na Alhaji
Abubakar Imam da “Jiki Magayi” na John Tafida Umaru Zaria da Rupert East da
“Iliya Ɗan Mai Ƙarfi” na Amadu Ingawa da “Shaihu Umar” na Alhaji Abubakar Tafawa Ɓalewa da “Komai Nisan Dare” na Mahmud Barau Bambale da kuma “Duniya Sai
Sannu” na Ado Ahmad Gidan Dabino domin fito da
abin da ake so. A ƙarshe, aikin ya gano sannan ya fito da
yadda ake samun magungunan waraka da cutarwa da na kariya da kuma na neman
biyan buƙatuwar rayuwa a cikin ƙagaggun labarai na Hausa da kuma silar neman magani da
yadda ake haɗe-haɗen magani.
1.0 Gabatarwa
Kowace al’umma a duniya tana da hanyar da take bi wajen
ganin ta kawar da cutar da ta addabe ta ta hanyar amfani da magani, kuma shi
magani abu ne wanda rayuwa ba ta gudana ba tare da an yi mu’amala da shi ba.
Wannan ba ya rasa nasaba da yanayin jikin ɗan’adam na ya wayi gari ba shi da lafiya ko wata mummunar
ƙaddara ko ciwo ya faɗa masa. Kamar yadda (Bunza, 1990, sh 131) ya
nuna kowace al’umma ta duniya tana
da wasu hanyoyi na musamman da suke amfani da su wurin yin magani. Haka, ya
nuna idan aka nazarci magani a al’ummomi
da yawa na duniya za a ga suna da dangantaka da sihirce-sihirce da tsafe-tsafe
da kuma camfe-camfe a al’ummar.
Hausawa suna ɗaya daga cikin mutanen da Allah ya yi musu baiwa wajen sarrafa magungunansu
domin kawar da cuta. Bisa al’ada kowacce sana’ar Hausawa tana da gadaddun
asire-asirenta na magunguna. Waɗannan magunguna suna iya zama na kare masu sana’ar daga wani abu da ka iya
cutar da su. Misali, maƙera daga wuta ko Masunta daga ruwa ko Mahauta daga kaifi da tsini, ko Mawaƙa daga mura da dai
sauransu da dama. Haka kuma, suna iya zama na kare kai da neman zama zakara a
cikin sana’ar ko kuma kariya daga sauran mutane ko kuma cutar da wani. Ibrahim
(2011, sh 230) ya nuna cewa neman waraka da kariya da biyan buƙatun rayuwa da kuma
cutarwa su ne ginshiƙan dalilai guda huɗu da suka tabbatar da wajibcin mu’amala da magani a rayuwar ɗan’adam.
Don haka, Manufar wannan maƙala ita ce a zaƙulo da wasu tartsatsin magungunan
gargajya a cikin wasu ƙagaggun litattafai na Hausa domin a fito da su fili ta hanyar amfani da waɗannan dalilai guda huɗu da suka tabbatar da wajibcin mu’amala da magani a
rayuwar ɗan’adam a matsayin mizani.
2.0
Waiwaye Kan Ma’anar Magani
Masana da dama sun yi tsokaci a kan magani. Ciki akwai;
Ingawa (1984, sh 25) ita kuwa ta bayyana ma’anar magani da cewa: “Magani hanya ce ta neman kawar da cuta
kowace iri ko kuma neman kariya daga gare ta ko kuma neman gwanewa ko ƙwarewa kan wani abu".
Bunza (1990, sh 134) ya bayyana ma’anar magunguna
gargajiya da cewa,
“magungunan da Hausawa suka gada kaka da kakanni shekara
aru-aru da suka wuce, kuma Hausawa suna ɗibar waɗannan magunguna a gargajiyance kuma
suna sarrafa su a gargajiyance, wani tasiri a addini ko zamani bai shiga
magungunan ba”. Ya ƙara da cewa, “duk wani abu da aka samu a magungunan za a tarar da gargajiya
ce tsantsarta, idan an ga irin wannan magani ko magunguna Hausawa na amfani da
su ko sun sarrafa su, su ake cewa magungunan gargajiya na Hausawa.
C.N.H.N, (2006, sh 316) ya nuna
magani shi ne, “abin da ake sha ko shafawa a jiki ko a ɗurawa jini don neman samun lafiya.
Shi kuwa Atuwo (2009, sh 177) cewa ya yi, “magani shi ne
sanin wani ilimi na gano cuta da kuma sanin hanyar warkar da ita a gargajiyance
ko a zamanance”.
Amma Nasir da Mu’azu (2021, sh 182)suna ganin, “maganin
gargajiya shi ne yin amfani da itatuwa ko tsirrai ko sassan mutum ko dabba ko
surƙulle don warkar da wata cuta ko neman wani amfani ko gusar da sharri ko
hasada da wani abu saboda biyan buƙata.
A tamu fahimtar, maganin gargajiya shi ne; Amfani da
itatuwa ko tsirrai ko sassan mutum ko dabba ko surƙulle ko asiri ko tsafe-tsafe domin a
kawar da duk wata matsala ko cuta da ta taso ko take shirin tasowa da nufin a
samu waraka.
2.1
Fasalin Magunguna
Magungunan gargajiya masana irin su
Bunza (1990) da Ibrahim (2011) da Sarkin Gulbi (2014) da Abdulrahaman (2017) da
Nasir da Mu’azu (2021) da Abdulahaman (2023) sun kasa su zuwa gida huɗu kamar haka:
2.1.1 Magungunan Warkarwa
Wannan wani nau’i ne na magani da Hausawa
suke amfani da shi wanda ya shafi cututtukan jikin Ɗan Adam waɗanda a zahiri ake iya
ganinsu da waɗanda ba a
iya ganinsu a fili (Abdulrahaman 2017, sh 51).
2.1.2 Magungunan Biyan Buƙatun rayuwa
Magunguna ne waɗanda ake bayarwa ko akan nema don biyan buƙatar rayuwa ko taimakawa rayuwa ta
gudana yadda ake buƙata. Misali, asirran neman auren mace ko mace ta so namiji da na farin jini
da na samun bashi da na kiran kasuwa da na neman mulki ko ɗaukaka da na sarauta da ilimi da sauransu (Sallau,
2010:49).
2.1.3 Magungunan Cutarwa
Magungunan cutarwa suna nufin duk wani maganin da za a yi
amfani da shi don cutar da rayuwar wani mahaluƙi. Irin wannan maganin ne
Abdurrahman (2017, sh 54) .
2.1.4 Magungunan Kariyar kai
Magungunan kariya magunguna ne da ake tanada don kare
jiki daga wasu ƙaddarori da sukan iya aukuwa a kowane lokaci ko kuma don a gano hanyar
kaucewa wahalhalun da ake tunanin fuskanta ko bala’o’i ko musifu (Nasir da
Mu’azu 2021, sh 185)
3.1 Ma’anar Ƙagaggun
Labarai na Hausa
Masana
sun tattauna wajen bayyana ma’anar ƙagaggun labarai. Misali: Yahaya da wasu (1992, sh 65) sun
bayyana shi da cewa; “yan ɗaya daga cikin
rukunin adabin Hausawa na zamani da masana adabin Hausa suka bayyana shi da zube, wanda shi ne na farko a cikin rukunin, kafin waƙa da wasan kwaikwayo.
Shi
kuwa Mukhtar (2016, sh 2) a wata lakca da ya gabatar cewa ya yi; “Shi ƙagaggen labari
cike yake da zantukan hira da nishaɗi,
wanda ba da gaske
ya taɓa faruwa ba, saboda
ana samar da shi ne kawai don nishaɗantarwa”.
Wajen ƙara fito da waɗannan ma’anoni
fili, sai Nayaya da Baba (2018, sh 53) suka bayyana ma’anaonin
a dunƙule da cewa; “Ƙagaggun labarai na Hausa su ne ire-iren labaran da ake samu
a rubuce ko da ka, domin samun abokin hira da ɗebe
kewa ta hanyar karantawa
ko sauraro.”
4.1 Magungunan Warkarwa
Akwai misalan magungunan gargajiya na warkarwa, watau maganin
da ake yi musamman saboda neman sauƙi ko
waraka yayin da aka shiga wani hali na cuta ko jinya.
A cikin littafin Ruwan Bagaja an fito ƙarara an nuna maganin warkarwa. Misali:
“Sarki
ya sa aka kawo mini abinci na ci. Motsin teku ya tashi kurunta ni, sai da na
sha maganin kwana bakwai, sa’annan na warke.” (sh 41).
Wannan abu ya faru ne bayan da Alhaji Imam ya samo ruwan
bagaja yana kan hanyarsa ta dawowa gida inda suka biyo ta wani teku wanda ya
fuskanci barazana matuƙa wadda ta kusa saka
shi kurumta. Amma da ya samu magani ya sha sai waraka ta samu.
Haka kuma a cikin littafin Iliya Ɗan Maiƙarfi an samu inda aka yi
amfani da wani magani na warkarwa.
“wasu
mutane suka zo suka ba wa Iliya Ɗan
Maiƙarfi magani ya sha ya warke, yayin da
aka haife shi ba ya iya ko tashi kuma shekarunsa sun zarta yadda ya kamata ya
fara tafiya. (sh 9).
Akwai wani maganin warkarwa ma a cikin littafin Ruwan
Bagaja, inda a shafi na 6, bayan Malam ya ba da
shawarin a nemo Ruwan Bagaja idan ana so Yarima ɗan Sarki ya warke, sai aka muzanta
shi, ya dawo gida yana kuka. Sai ɗansa Alhaji Imam ya yi zuciya ya tafi neman
Ruwan Bagaja. Ya yi hakan ne don nema wa babansa 'yanci a fada kuma ya samu
nasarar samo wannan Ruwan Bagaja, an yi amfani da shi a matsayin magani sannan
an samu waraka tsaf.
“Na ɗauki tsinke na tsoma cikin kwalbar Ruwan Bagaja, na jefa tsinken cikin
wani ɗan ruwa a kwano, aka ba yaron
ya sha. Da haɗewarsa sau ɗaya sai ya yi farat ya tashi. Nan take ya warke.
(sh 43).
A nan
mun ga yadda Alhaji Imam ya shiga duniya don nemo Ruwan Bagaja, ya sha faɗi-tashi sosai kafin
ya samo Ruwan Bagaja, amma bai yi ƙasa a guiwa ba sai da
ya samo shi, kuma an yi amfani da shi an warke don haka kwalliya ta biya kuɗin sabulu.
Ga wani
misali a cikin littafin kamar haka:
“Ko da
na huta, suka tambaye ni labarina, duk na kwashe na faɗa musu. Da suka ji
haka, sai suka tausaya min suka ba ni magani, idona ya warke”. (Sh 16).
Wannan
abu ya faru ne lokacin da Alhaji Imam ya gamu da ciwon makanta, Allah kuma ya
taimake shi ya samu magani daga wurin wasu aljanu ‘yan ruwa.
4.2 Magungunan Biyan Buƙatun Rayuwa
Akwai
magungunan biyan buƙatun rayuwa, watau idan wani yana son wani abu sai ya yi ƙoƙarin neman wani
magani don wannan buƙata tasa ta biya. A nan akan nemi asiri don mallake mace
ko mallake miji ko neman wani mulki da dai sauransu. Ga misalai kamar haka:
A
littafin Jiki Magayi inda Malam Shaihu ya yi magani wa Zainabu don ya
mallake ta ya aure ta, kuma ya yi nasarar maganinsa ya samu karɓuwa domin buƙatarsa ta biya. A
shafi na 12, bayan Abubakar ya shiga duniya ya isa wani gari mai suna ‘Zauna
da Shirinka’ suka haɗu da wani boka mai suna “Tausayinka
da Sauƙi’. Wannan ya faru ne sanadiyyar balaguron
neman magani, watau ƙaron kalgo. Misali, inda Abubakar yake cewa;
“Abin da ya kawo ni gare ka, ɓacin rai ne. ni ke da wata yarinya wadda nake so, ita kuma tana sona
gaba da kima, tun muna yara har muka yi girma, ina nan ina tashinta za mu yi
aure. Ina cikin shawara kenan zan sa uwata ta tafi a yi min baiko, sai wani
attajiri na garinmu ana kiransa Malam Shaihu ya ji labarinta. Domin kwaɗayi kawai ya kangara ta, ko da yake yana da matansa
huɗu. Irin wannan mutum bai
kamata ya zauna lafiya ba. Ba shi yiwuwa a gare ni in zauna cikin garin nan.
Ina cikin tambaya har aka gaya mini babu wanda ya fi ka sani magani cikin dukan
ƙasan nan. Saboda
haka na zo gare ka, in ka yarda ka taimake ni in ɗauki fansa a kansu, raina ya huce” (sh 12).
A nan
mun ga yadda Abubakar ya fusata ya neman biyan buƙatarsa, watau ya
shiga duniya musamman domin neman magani.
Baya ga
nan, an sake samun maganin biyan buƙatuwar rayuwa a
littafin Ruwan Bagaja. Misali; lokacin da Alhaji Imam ya bar gida a
hanyarsa ta neman ruwan bagaja. Ya yada zango a wani ƙasurgumun daji inda
ya haɗu da wani tsoho har
ya masa kwana biyu a cikin ƙogo. Da zai tafi ya nemi wannan tsoho
ya masa bugun ƙasa.
“Bayan
mun saba da juna n ace masa ya buga mini ƙasa, ya gaya mini
labarina da labarin niyyata. Ya buga ƙasa y ace, ‘Ruwan
Bagaja dai akwai shi a duniya, amma yana hannun aljanu. Ƙarewa ma ba shi a
wannan ƙasa da muke takawa”. (sh 6).
Shi dai
bugun ƙasa wani nau’i ne na magani da Malaman Tsibbu suka laƙanta. Neman Ruwan
Bagaja kuwa wata buƙata ce da Abubakar Imam yake son biya wa zuciyarsa.
Baya ga
nan, a cikin littafin Komai Nisan Dare an samu maganin biyan buƙata, inda
Tsigarallahu take son samun ciki, wanda hakan ya sa ta bazama neman magani
domin ta samu biyan buƙata na samun ciki.
“Bayan
da ta samu kimanin kwana arba’in da gama aiki da magani, sai ta samu ciki. Ta
haifi ‘yan biyu mace da namiji, aka saka musu suna Jamila da Jamilu.” (sh 61).
Wannan
ciki da ta samu ta sanadiyyar neman magani ne a wurin boka Zuru a ƙasar Masar. Shi kuwa
ya haɗa mata magani da
fitsarinta, ya haɗa da wasu layu da ƙunshin magani da
turare da goro ya bata. Sanadiyyar haka ta samu ciki har ta haihu.
4.3 Magungunan Cutarwa
Cutarwa
ita ce yi wa wani mugunta ko wani abu da zai iya cutar da shi ta sanadiyyar
amfani da magunguna wadda ake kira asiri.
Akwai
tartsatsin magungunan gargajiya a cikin ƙagaggun littatafai,
misali idan muka ɗauki littafin Jiki
Magayi, inda Abubakar ya samo ƙaron kalgo ya haɗa da magani da shi,
ya cire gashin Kyauta ɗan Malam Shehu, inda
daga nan ya susuce ya kama shashanci. Ga yadda abin ya faru a shafi na 22,
sakin layi na 1, bayan Abubakar ya yi faɗi-tashi na wahalhalun dukan da ya sha a gurin
wasu mutane da aka biyo ɓarawo an ɗauka cewa shi ne.
sannan bayan ya warke ɓarayi ‘yan
fashi sun tare shi har suka karɓe masa kuɗi da abin hawa sannan suka yanke masa kunne ɗaya. Amma duk da haka
bai haƙura ba, sai marubucin yake ba da labarin cewa;
“Duk wahalan nan da ya sha zuciya tasa ba ta
girgiza ba, sai daɗa ƙeƙashewa ta yi, dukan
hankalinsa yana kan rama muguntar da aka yi masa, yana ta tafiya kwance tashi
har ya kai Sanga. Kullum a zuciyarsa yakan ce, “ba ni dai komawa gida
kome wahala, sai na samo ƙaron kalgon nan, bisa ikon Allah”.
(sh 22)
A nan, ana ƙoƙari fito da wahalar
da Abubakar ya sha ne wajen nemo magani don ɗaukar fansa kan abin da aka yi masa duk da
irin wahalar da ya yi ta sha, amma bai sare ba.
Sai
kuma, a shafi na 25, sakin layi na 5, inda Abubakar ya ga haske har ya nufi ɗauka sai ya ga baƙin kumurci ne
(Maciji) kawai sai ya faɗi daga baya inda ya
ji murya ana tambayarsa wane karambani ne ya kawo shi cikin wannan daji. Bayan
ya gama labarin, sai kuma Aljanin yake cewa;
“Samari, ko da mu ba domin alheri ake nemanmu
ba sai don mugunta. Da ka zo gare ni tuni da fari da dukan wannan wahala ba ta
same ka ba. Dukan muguntar da kake so na taimake ka da ita, amma ban da alheri,
domin mugunta ce halina, wanda kuma ya yi nufin yin ta shi ne abokina”.
(sh 25)
A nan
dai ana bayyana yadda ake shan wahala ne yayin neman magani musamman ma maginin
cutarwa. Mun ga yadda Aljani ya ɗaure wa Abubakar gindi, kan zai taimake shi
don ya ɗauki fansar abin da
aka yi masa. A taƙaice dai Abubakar bai yi haƙuri ba, har sai da ya
ɗauki fansa fiye da ma
abin da aka yi masa. Bayan Abubakar ya samo ƙaron kalgo (Magani),
ya kai wa Tausayinka da Sauƙi ya haɗa masa magani ya ce ya yanki gashin
kan kyauta ya haɗa da maganin to shike
nan an gama da shi. Ga inda ya cika aiki, a shafi na 29, a sakin layi na 6 inda
mawallafin yake ba da labari cewa:
“Rannan da dare ƙafa duk ta ɗauke, sai Abubakar ya
tashi, ya wanke hanunsa da maganin nan da Tausayinka-da-Sauƙi ya ba shi, ya fita
sai gidan Malam Shaihu, ya shiga shamaki ya ga ɗakin da kyauta yake. ya shiga, ya iske
duk suna barci. Sai ya kware jikinsa, ya shafe shi da hanunsa. Ya ɓallo almakashi daga
ratayensa, ya datsi gashin kansa, ya fita abinsa”.
(sh 29)
Daga
wannan lokaci, shi kenan halayen kyauta suka sauya, ya zama ɓarawo har ya kai ga
matakin babban ɗan fashi inda shi ne
ma ya sa aka kashe babansa da kansa. Wannan fansa da Abubakar ya ɗauka ta yi tsauri
sosai. Amma a wani fannin hakan zai iya zama faɗakarwa ga masu addu’a
da ba ta dace ba yayin da suke buƙatar wani abu a gurin
Ubangiji. Wannan misali ya bayyana mana yadda ake haɗa magani musamman
domin cutarwa cikin wannan littafi.
Har wa
yau, a littafin Ruwan Bagaja an yi amfani da magani na cutarwa a lokacin
Alhaji Imam ya shiga neman aure, inda ya kasa abokan hamayyarsa. Ba kowa ne
yake jure irin wannan ƙalubale ba.
“Da sun
hange ni sun shiga zagina ke nan. Mai tsina na yi, mai zagi na yi. To, ni da
nake baƙo lalle sai in kame bakina, gama fa shi ya fi. Abu dai ya
tsananta, har suka yi makircin da suka ƙwace mini matar. Suka
yi mini magani na makance.” (sh 14).
Bugu da
ƙari,
a cikin littafin Dunya Sai Sannu magauta da mahassada sun cutar da
Ja’afaru ta hanyar yi masa asiri wanda sanadiyyar haka duk lokacin da ya ɗauki zare da allura
zai yi ɗinki sai ya daina
gani. Misali;
Bayan
sun bi duk hanyar da za su bi domin su ga ya daina samun abokan hulɗa basu ci nasara ba,
sai kawai suka durfafe shi da asiri, babu ji babu gani”. (sh 14).
Lura da wannan abu da ya wakana, za a iske magauta sun
cutar da Ja’afaru ba don komai sai kawai dan yana samun abokan hulɗar cinikayya. Wannan ya nuna ƙarara an cutar da shi ta
hanyar yi masa magani na asiri domin ya daina gani da idanunsa da zarar ya ta
shi gudanar da sana’arsa ta ɗinki.
4.4 Magungunan Kariyar kai
Kariyar kai na nufin riga-kafi kan wani abu da ka iya tasowa
ko kaucewa ɓacin rana ko wasu bala’o’i ko ƙaddarori da ake ganin za su iya aukuwa a kowane lokaci.
An samu maganin kariyar kai a cikin
littafin Shaihu Umar, inda Makau ya buƙaci Maharbi ya ba shi wasni ɗan
asiri wanda zai iya kuɓutar da shi daga haɗari.
Ga abin da suka yi;
Saura
ina so in tambaye ka wani ɗan asiri wanda yake zan yi in kuɓuta daga haɗari wand azan haɗu da shi kafin na isa
maƙarfi.
Sai Maharbi ya kawo ‘yar laya mai sasari ya ba shi.” (Sh 12).
Idan
aka nazarci waɗannan bayanai da suka
gabata a tsakanin Makau da Maharbi za a tarar lallai akwai maganar maganin
kariyar kai.
Akwai maganin kariyar kai a littafin Jiki Magayi, inda
Baban Tausayinka da Sauƙi yake bayar da laya
wa Abubakar don kare kansa daga wasu miyagun abubuwan da za su iya faruwa da
shi yayin neman ƙaron kalgo.
Misali:
Baban Tausayinka da Sauƙi ya ba wa Abubukar
layu ya ce masa kar ya yarda ya rabu da waɗannan layu, sannan idan yana tafiya kar ya
waiwaya ko da ya ji ana yi masa magana in har ba ya isa dajin da ƙaron kalgon yake ba.
A nan
an ba wa Abubakar ne waɗannan layu domin
neman kariya daga miyagun da za su iya cim masa a hanyarsa ta zuwa neman Ƙaron Kalgo. Don haka
wannan ma tarsashi ne na magungunan gargajiya a cikin wannan littafi na Jiki
Magayi.
An sake
samun maganin kare kai a cikin littafin Ruwan Bagaja. Misali; Malam Zulƙe wani tauraro ne na
cikin labarin inda ya sha gwagwarmaya wanda ta sanadiyyar haka ya sa ya nemi
maganin kariya domin gudun ɓacin rana.
“Gari
na wayewa Sarki na jin labarin. Nan da nan ya aiko aka ɗunguma da su. Da dare
na sami labari Zurƙe ya yi layar zana ya tsere.” (sh 25).
A nan, gardama ce ta kaure
tsakanin Malam Zurƙe da matarsa a kan wani damin
kaya da aka kawo wa matarsa a tunaninta mijinta ne Malam Zurƙe ya kawo mata da dare, alhali kuwa Alhaji Imam
ne. Da shigowarsa gida yake cewa matarsa ya yi sa’a Ƙwara ba su harbe shi ba, kuma yau ba a abin da
ya samo. Matar ta ce ai kayan da ka kawo da dare ma sun isa. Ko da aka buɗe damin kaya sai aka tarar da gawa a ciki. Mata ta ce shi ne, shi ko ya
ce ba shi ba ne. Sarki ya sa aka kawo su, nan da nan Malam Zurƙe ya yi amfanin da layar zana ya ɓace.
Layar zana wata laya ce ko wani abu da za a haɗa mutum ya dinga amfani da shi lokacin da yake buƙatar kada mutane su gan
shi wato hanyar ɓata (Bunza, 2006:51).
5.0 Kammalawa
Tabbas ƙagaggun labarai na Hausa suna taka muhimmiyar rawa wajen
fito da wasu al’adun Hausawa na gargajiya. Cikin al’adun kuwa ana samun yanayin
zamantakewarsu da sana’o’insu da bukukuwansu da magungunanansu na gargajiya da
makamantansu. Kamar yadda bayanai suka gabata, wannan aiki ya bayyana abubuwan
da suka shafi tarsashin magungunan gargajiya a cikin ƙagaggun labarai na Hausa, inda
takardar ta fito da nau’ukan magunguna da aka fasalta a ilmance, watau Magungunan Warkarwa da Magungunan Biyan Buƙatun rayuwa da Magungunan Cutarwa da Magungunan Kariyar kai duk a cikin wasu ƙagaggun labarai. Aikin ya fito da wasu magunguna da ake
amfani da su a cikin wasu ƙagaggun labarai na
Hausa kamar littafin Ruwan Bagaja da Jiki Magayi da Iliya Ɗan
Mai Ƙarfi da Shehu Umar da Komai Nisan Dare da kuma Duniya Sai
Sannu.
MANAZARTA
Abdullahi, I. S.S. (2000). “Magani Da Siddabaru Cikin
Rubutattun Ƙagaggun Labarun Hausa: Keɓaɓɓan Nazarin Littattafan
Gasar Shekarar 1933 da 1978 da 1980”. Kundin digiri na biyu. Sakkwato: Jami’ar
Usmanu Ɗanfodiyo.
Abdulrahman, M.A (2017). “Cuta da Magani a Abincin
Hausawa: Nazari Kan Ciwon Sukari”. Kundin digiri na biyu, Sashen Harsunan
Nijeriya. Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Abdulrahman, M.A. (2023). “Nazarin Kimiyyar Magungunan
Ciwon Daji da Hanta da Hawan Jini a Mahangar Al’adar Hausawa”, kundin digiri na
uku, sashen nazarin harsunan Nijeriya da Kimiyyarsa. Gadau: Jami’ar Jiha.
Atuwo, A.A. (2009) “Ta’addanci A idon Bahaushe Yaɗuwarsa da Tasirinsa A wasu ƙagaggun Rubutattun labarun Hausa.”
Kundin digiri na uku. Sakkwato: Sashen Harsunan Nigeriya.
Bambale, M.U.(1994). Komai
Nisan Dare. Kaduna: Northern
Nigeria Publishing Company Limited, Zaria.
Ɓalewa, A.T. (1966). Shaihu Umar. Zaria: Northern Nigerian Publishing
Company Limited.
Bunza, A.M. (2006). Gadon
feɗe Al’ada. Lagos: Tiwal Nigerian Limited.
Bunza, A.M. (1990). “Hayaƙi Fid da na Ƙogo, Nazarin siddabarn da Sihirin
Hausawa”. Kundin Digiri na Biyu, Sashen Harsunan Nijeriya. Kano: Jami’ar
Bayero.
C.N.H.N (2006). Ƙamunsun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press.
Gidan
Dabino, A.A. (1997). Duniya Sai Sannu. Kano: Gidan Dabino Publishers.
Ibrahim,
S.S. (2011). “Awon Maganin Gargajiya a Littafin Ruwan Bagaja”, a cikin Algaita, Vol. 2 No. 1. Pp
230-237, sashen koyar da harsunan Nijeriya. Kano: Jami’ar Bayero.
Imam,
A. A. (1966). Ruwan Bagaja. Zaria:
Northern Nigeria Publishing Company Limited.
Ingawa,
A. (1984). Iliya Ɗan Maiƙarfi. Zaria: N.N.P.C
Ingawa,
Z.S. (1984). “Magungunan Hausa Don Mata”, kundin digiri na farko, sashen koyar
da harsunan Nijeriya. Kano: Jami’ar Bayero.
Mukhtar,
I. (2016). Fahimtar Tsarin Harshe a Cikin Matanin Zance Na Ƙagaggun
Labarai.
Takardar Da Aka Gabatar A Ranar Marubuta Hausa Na Duniya karo na farko, a ranar
26 Maris, 2016. Mambayya House, Kano.
Nasir,
N.U. da Mu’azu, A. (2021). “Gudunmawar Magungunan Gargajiya Wajen Aiwatar da
Ta’addanci a Cikin Al’ummar Hausawa”, a cikin Ɗunɗaye Journal of Hausa
studies vol 2, no 4, pp 180-193,
sashen harsunan Nijeriya. Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Nayaya,
I.G da Baba, I. (2018). “Kura-kurai A
Rubutun Hausa: Nazari A Kan Wasu Littattafan Adabin Kasuwar Kano”, a
cikin Yobe Journal of Language, Literature and Culture. Volume 6, pp 52-61,
sashen harsuna da kimiyya. Damaturu: Jami’ar Jihar Yobe.
Sallau, B. A. (2010). Magani a Sha a Yi Wanka a Buwaya.
Kaduna: M.A Naji Professional Printers.
Sarkin Gulbi, A. (2014). “Magani a Ma’aunin Karin
Magana”. Kundin digiri na uku, Sashen Harsunan Nijeriya. Sakkwato: Jami’ar
Usmanu Ɗanfodiyo.
Tafida, J.U. da East,
R. (2007). Jiki Magayi. Zaria: Northern
Nigerian Publishing Company.
Yahaya, I. Y. da Ɗangambo,
A. (1986). Jagoran Nazarin Hausa. Zaria: Northern
Nigerian Publishing Company.
Yahaya, I.Y. da Wasu (1992). Darussan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandare. Littafi Na Ɗaya. Ibadan: University Press
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.