Citation: Abbas, N. I. and Ibrahim, I. G. (2025). “Tsawon Wasali a Harshen Hausa da Harshen Ga’anda: Kamanci da Bambanci.” in Ɗunɗaye Journal of Hausa Studies, Vol. 03, No. 02, Pp. 50– 56. www.doi.org/10.36349/djhs.2025.v03i02.006.
TSAWON WASALI A HARSHEN HAUSA DA HARSHEN GA’ANDA: KAMANCI DA
BAMBANCI
Na
Nazir Ibrahim Abbas
Department of Nigerian Languages, Usmanu Danfodiyo University,
Sokoto
Da
Ibrahim, Ismaila Girei
Department of Hausa, School of Languages, Adamawa State College of
Education, Hong
Tsakure:
Tsawon
wasali wani al’amari ne da ya danganci sauya ma’anar kalmomi a harshen Hausa da
harshen Ga’anda. Manufar wannan bincike ita ce, ƙara
bunƙasa
nazarin kwatancen harshen Hausa da harshen Ga’anda da kuma ƙara
faɗaɗa
nazarin sauye-sauyen sautukan harsunan a cikin ilimin tsarin sauti. An yi
amfani da manya da ƙananan hanyoyi a matsayin dabarun tattara bayanan
da aka gudanar da wannan bincike da su. Haka kuma, an ɗora
binciken a kan Ra’in kai tsaye na yankin tsarin sauti/Ra’in haɗakar
ayyukan tsawon wasali da karin sauti a harshe (Autosegmental Phonology) na
Goldsmith (1976) wajen gudanar da wannan bincike, wanda ya yi bayani a kan
yadda tsawon wasali yake gudana a fagen ilimin tsarin sauti. Aikin ya fito da
hanyar kwatanta tsawon wasali a harsunan biyu. A taƙaice,
takardar ta yi ƙoƙarin fito da kamanci da bambancin da ke
akwai a tsakanin harshen Hausa da harshen Ga’anda. Binciken ya gano cewa,
tsawon wasali yana wanzuwa a cikin harshen Hausa da harshen Ga’anda. Haka kuma,
duka harsunan biyu sun yi tarayya da juna ta fuskar ƙwayoyin
sautuka da kuma wasu nau’o’in tsawon wasali. Bugu da ƙari,
binciken ya gano cewa, ba a bambanta rubutun kalma mai ɗauke
da gajere ko dogon wasali a rubutun yau da kullum na harsunan Hausa da Ga’anda,
bisa dalili a wani lokaci na saukaka wa waɗanda suke karatu su
fahimta.
Keɓaɓɓun Kalmomi: Tsawon wasali da tsarin sauti da sauye-sauyen sautuka
da ma’anar kalmomi da Hausa da Ga’anda
Gabatarwa
Fifikon
da Ɗan’adam
ya samu bisa sauran halittu yana ɗamfare ne da naƙaltar
harshe domin sadarwa. Hasali ma, harshe shi ne linzami na tunani da cigaba,
musamman ma da yake babu mutum biyu da za su yi mu’amala tare cikin manufa
guda, ba tare da sanin halaye da martabar juna ba, ta wannan haujin harshe ya
bambance mutum daga sauran halittu. Bugu da ƙari, al’umma sukan rayu
ne kaɗai
tare da amfani da harshe. Harshe yana taka muhimmiyar raya a cikin al’ummu
mabambanta. Tsawon wasali yana wanzuwa a harshen Hausa da harshen Ga’anda.
Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya (2006:454) ta bayyana tsawo da cewa, kishiyar
gajarta ko dogontaka ko daɗewa ta lokaci. Wasali
kuma, harafi ko alama da ake yi wa harafin baƙi don a sami lafazi
daidai. Saboda haka, tsawon wasali babban jigo ne a fannin ilimin tsarin sauti
wanda yake taka muhimmiyar rawa a al’amari da ya shafi sauye-sauyen sautuka
tare da bambanta ma’anar kalmomi biyu idan suka wanzu a cikin harshe.
A ɗayan ɓangaren
duk da cewa, harshen Hausa da harshen Ga’anda, harsuna ne mabambanta, amma
akwai ƙyaƙƙyawar alaƙa da hulɗa
tsakanin Hausawa da Ga’andawa. A ɓangaren ilimin kimiyyar
harshe harsunan guda biyu duk harsuna ne na iyalan Chadi. Harshen
Hausa da harshen Ga’anda suna da alaƙa a tsakaninsu, domin
kuwa harsuna ne daga cikin iyalan
harsunan Chadi (Harshen
Hausa, Yammacin Chadic, harshen Ga’anda kuwa Biu-Mandara waɗanda suka fito daga
tushe ɗaya masu haɗaka da harsunan Afirka da Asiya), (Greenberg (1963); Newman
1980, 2000; Newman 1971; da Al-Musawi 2022).
Edwards
(2007:26) yana da ra’ayin cewa,
Ingilishi:
One of the
most observable ways to classify speech sounds is to divide them into vowels
and consonants. Vowels are produced by a vocal tract that is more or less
unobstructed, the only contact being made by the tongue with the upper and
lower teeth and their corresponding gum ridges.
Fassara: Ɗaya
daga cikin muhimman hanyoyi da ake lura da su wajen rarraba sautukan magana ita
ce, a raba sautukan magana zuwa sautukan wasula da baƙaƙe.
Akan furta sautukan wasula a ƙwararon magana ba tare da
wani samun cikas na iska ba, ko kuma a wani lokaci ƙarƙarwar
ba ta da yawa, kawai dai akan samu haɗuwar harshe da hakoran
sama da ƙasa da kuma shakuɗuwar yawu.
Prasad
(2008:19-21) ya bayyana cewa:
Ingilishi:
A vowel is a
speech sound produced by the unimpeded passage by the breath (modified by the
vocal cord into voice) through the mouth, different vowel sounds (are) being
made by altering the form and position of the tongue and lips. Further says a
vowel sound is of two types: monophthong and diphthong. A diphthong is a
combined form of two vowels. Monophthongs are pure vowels and diphthongs are
gliding vowels. A vowel that does not change in quality may be called a
monophthong; and a vowel sound with a continually changing quality may be
called a diphthong.
Fassara: Sautin
wasali na nufin sautin magana wanda a lokacin furta shi ba a samun tangarɗa
na numfashi ta hanyar baki, sautukan wasula mabambanta akan furta su ta wajen
sauya matsayin harshe da leɓɓa. Masanin ya ci gaba da
cewa, sautukan wasula sun rabu gida biyu; akwai tilon sauti da kuma ‘yar
tagwai. Akan haɗa sautukan wasula biyu ne
su haifar da ‘yar tagwan wasula, a yayin da kuma tilon wasula su ne asalin
wasula.
Wannan
bincike yana da fahimtar cewa, ana furta sautukan wasula ba tare da samun wani
tangarɗa
ko cikas na iska ba. Haƙiƙa, bunƙasa da wanzuwan harsuna
mabambanta a cikin al’umma su suke haifar da yin nazari a kan harsuna biyu
mabambanta a wannan fanni na ilimin tsarin sauti da ma wasu manyan ɓangarori
na ilimin kimiyyar harshe.
Dabarun Bincike
Lura
da cewa, wannan bincike ya yi ƙoƙarin
bayyana yadda tsawon wasali yake gudana a harshen Hausa da harshen Ga’anda,
wajen bunƙasa sauye-sauyen sautuka tare da samar da ɗimbin
kalmomi. Daga cikin dabarun da aka yi amfani da su sun haɗa
da:
(i) Tattaunawa da Hausawa da
Ga’andawa domin samun ingantattun bayanai.
(ii) Tattaro bayanai daga
bugaggun littattafai da maƙalu da mujallu.
(iii) Tattaro bayanai daga
kafar sadarwa ta intanet.
Ra’in Bincike
Masana da Manazarta da dama sun yi ƙoƙarin samar da ra’i wanda zai
dace da tsarin
tsawon wasali a ɓangaren ilimin tsarin sauti. Wannan bincike ya yi amfani da Ra’in kai tsaye
na yankin tsarin sauti/Ra’in haɗakar ayyukan tsawon
wasali da karin sauti a harshe (Autosegmental Phonology) na Goldsmith (1976). Wannan ra’i da farko yana da’awa ne a kan yadda karin sauti yake
gudana, amma daga baya masu ra’in sun faɗaɗa
ra’in zuwa wasu al’amura da suka shafi ilimin tsarin sauti kamar, sautukan baƙaƙe
da sautukan wasula. Wannan ra’i ya sami magoya baya
irin su Rischel (1974)) da Hockett (1955) da Firth (1984). Haka kuma, akwai
Yalwa (2002) da Bobda (2007) da Josiah da Soneye (2011) sun yi amfani da wannan
ra’in a wasu ayyukansu a fannin ilimin tsarin sauti.
Tsarin Sauti
Tsarin
sauti babban reshe ne, na ilimin kimiyyar harshe. Saura manyan rassan su ne;
ilimin furuci da ilimin ƙirar kalma da ilimin ginin jimla da ɓangaren
ma’ana a Ingilishi kamar haka:
Robins (1967:34) ya zayyana cewa:
Ingilishi: Tsarin sauti (phonology) is
language specific.
Fassara:
Tsarin sauti shi ne, yadda ake samun sauye-sauyen
sautuka waɗanda suka
shafi keɓaɓɓen harshe[1].
Zarruk
(1980:19) kuwa ya bayyana cewa:
Tsarin sauti shi ne siffofin da ke bambanta sauti, da kuma
fasalin dangantakar ƙwayoyin sautin in sun jeru cikin magana mai ma’ana.
Sani
(2011:3) kuwa a nasa ɓangare yana ganin:
Tsarin sauti fanni ne na
ilimin harsuna da ya danganci yadda harshe yake tsara sautuka waje guda su samar da
ma’ana.
Ya ƙara
da cewa, ƙwararre a tsarin sauti na wani harshe ana ce da shi masanin tsarin sauti
na wannan harshe. Tsarin Sauti yana nazartar irin sauye-sauye da ake samu a
dalilin haɗuwar sautuka
a cikin kalma.
Dangane
da abin da ya gabata daga bakin masana ilimin harshe, ana iya cewa, tsarin
sauti ɓangare ne na ilimin kimiyyar harshe da ya
danganci yadda harshe yake tsara sautuka cikin sahu domin bayar da ma’ana.
Tsawon Wasali
Tsawon
wasali (vowel length) babban ginshiƙi ne wanda yake bambanta
ma’anar kalma a cikin tsarin sauti. Dangane da ma’anar tsawon wasali ga abin da
masana suke cewa:
Crystal
(2008:273) ya bayyana tsawon wasali kamar haka:
Ingilishi: Vowel length, in
phonetics is refer to the physical duration of sound or utterances and in
phonology to refer to the relative durations of sounds and syllables when these
are linguistically contrastive; also referred to as quality. Sometimes the term
is restricted to phonological contexts, being referred to as duration.
Phonologically long and short values are conventionally recognized, for both
vowels and consonants.
Fassara: Tsawon wasali a
ilimin furuci na nufin lokaci da sauti kan ɗauka ko furuci, a ilimin
tsarin sauti ana magana ne kan dangantakar wannan lokaci da gaɓoɓin
kalma, wannan al’amari ne a ilimin kimiyyar harshe da ya shafi bambanci. A wani
lokaci tsawon wasali ya taƙaita a kan al’amari na ilimin tsarin sauti
wanda ake bayyana shi da adadin lokaci. A al’amari na ilimin tsarin sauti ana
la’akari da dogaye da gajerun sautukan wasula da baƙake[2].
Matthews
(2007:220) ya bayyana tsawon wasali da cewa:
Ingilishi:
Vowel length
is phonetic or phonological feature, especially vowels. The vowel may either be
short or long and phonological distinction may be realized.
Fassara: Tsawon wasali na
nufin nau’in furuci ko sifar sauyin sauti, musamman ma wasula. Wasali zai
kasance gajere ko dogo, da kuma ta hanyarsa ana samun bambancin ma’ana[3].
Wannan
bincike yana da fahimtar cewa tsawon wasali babban reshe ne, na ilimin tsarin
sauti wanda yake magana a kan tsawon daƙiƙoƙi
da gaɓar
kalma kan ɗauka a yayin furta kalma
a harshe. Tsawon daƙiƙoƙin da gaɓar
kalma yakan ɗauka a lokacin furuci
yakan haddasa ma’anar kalma a harsuna mabambanta. Domin karin bayani a kan
al’amari na tsawon wasali a dubi[4] da[5]. *
Tsawon Wasali a Harshen Hausa
Dangane
da tsawon wasali a harshen Hausa kuwa, Newman (2000:400) da Bagari (1986:79) da
Zarruk da Kafin Hausa da Al-Hassan (2005:87) da Sani (1989:28) da Amfani
(2011:139) da (Yusuf (2011:3) da kuma Fagge (2012:23) suna da ra’ayin cewa;
yana nufin yawan lokaci da ake ɗauka wajen furucin kalma
ne, wanda kuma a sanadiyar haka yawan lokacin yakan haddasa sauya ma’anar
kalmomi daban-daban. Bugu da ƙari ana samun wasula iri
biyu ne; gajeru da dogaye, gajerun wasula a Hausa su ne: /i/ da /e/ da /a/ da
/u/ da kuma /o/. Dogayen wasulan Hausa kuwa su ne: /ii/ da /ee/ da /aa/ da /uu/
da kuma /oo/. Wani abun lura kuwa shi ne tsawon wasali kan hau dukkan zubin waɗannan
wasulan na Hausa.
Ga
misalan yadda tsawon wasali yake gudana a harshen Hausa:
|
Kalma |
Ma’ana
a Ingilishi |
Kalma |
Ma’ana
a Ingilishi |
|
/daagaa/ |
struggle |
/dagaa/ |
from |
|
/Φaasa/ |
postpone |
/Φasa/ |
disperse |
|
/duuka/ |
blow |
/duka/ |
all |
|
/daawaa/ |
Guinea-corn |
/dawaa/ |
the bush |
|
/gaarii/ |
flour |
/garii/ |
town |
|
/ʤiimaa/ |
tanning |
/ʤimaa/ |
spend
sometime |
|
/ʤaakaa/ |
stupid
person |
/ʤakaa/ |
any
kind of bag |
|
/s’aakii/ |
sucking
noise |
/s’akii/ |
coarse
part of ground flour |
|
/Φaarii/ |
beginning |
/Φarii/ |
drought |
|
/Φitoo/ |
whistling |
/Φito/ |
ferrying |
|
/baaƙoo/ |
guest |
/Baaƙo/ |
nick
name |
|
/gadoo/ |
bed |
/Gado/ |
name of
a person |
|
/saakee/ |
repeat |
/sake/ |
slackness |
|
/kuuree/ |
male
hyena |
/kuree/ |
makes a
mistake |
|
/taaree/ |
move to
new dwelling |
/taare/ |
gathered |
|
/baabaa/ |
father |
/baba/ |
indigo
dye |
|
/kaaraa/ |
finish
completely |
/kara/ |
increase |
|
/raanaa/ |
day
(emphatic/long) |
/rana/ |
day |
|
/taabaa/ |
touch
repeatedly |
/taba/ |
touch |
|
/gaabaa/ |
front |
/gaba/ |
front/forward |
|
/saasaa/ |
custom/tradition |
/sasa/ |
to
settle |
|
/zaaraa/ |
visit
repeatedly |
/zara/ |
thread
beads |
|
/faadaa/ |
fall
flat |
/fada/ |
palace |
|
/haaraa/ |
new
(emphatic) |
/hara/ |
forbidden |
|
/laabaa/ |
hide
repeatedly |
/laba/ |
story |
|
/maasaa/ |
chew
slowly |
/masa/ |
him/her/it |
|
/kaayaa/ |
goods/property |
/kaya/ |
load/luggage |
|
/raayaa/ |
life |
/raya/ |
raise/bring
up |
|
/zaayaa/ |
waste
away |
/zaya/ |
choose |
Wannan
bincike ya fahimci cewa, a sanadiyar gajarta ko tsawaita sautukan wasula,
kalmomi masu ɗauke da gajerun wasula
suna ɗauke da ma’ana waɗanda suka bambanta da
kalmomi masu ɗauke da dogayen
wasula. Bugu da ƙari wani abin lura a nan shi ne, da gajeren
wasali da dogon wasali kowannensu ƙwayar sauti ne na daban a
harshen Hausa. Bambancin Tsawon wasalin nan yakan kawo bambanci a tsakaninsu.
Shi kuwa bambancin ma’ana jigo ne a ɓangaren ma’ana da tsarin
kalmomin nahawu (grammar) a harshen Hausa. Za a fahimci hakan kamar
yadda aka bayyana cikin misalan da suka gabata. Duk da cewa binciken bai yi
magana a kan ɓangaren tashin sauti ba,
galibi wannan batun ya fi shafan harsunan Turanci, kalmomi ne masu nuna
karfafawa. A harshen Hausa akwai Sani (2013) mai ra’ayin cewa, tashin sauti kan
iya auku a Hausa.[6]
Dangane
da dokar tsawon wasali: Idan aka samu kalma sai a samu a cikin kowane gaɓar
kalma, gajeren wasali ko dogon wasali ya gabaci sautin baƙi
ko ya biyo bayansa. Misali: /f+a+a+s+a/ → /Φaasa/ da /f+a+s+a/ → /Φasa/.
Tsawon Wasali a Harshen Ga’anda
Tsawon
wasali a harshen Ga’anda yana ba da gagarumar gudumawa wajen bambanta ma’anar
kalma. Wasula nau’o’i shida ne a harshen Ga’anda. Waɗannan
wasula sun haɗa da: /a/, /e/, /u/, /o/ /i/ da /ǝ/[7].
Tsawon
wasali a harshen Ga’anda, yakan auku ne a kan sautukan wasula guda uku kawai
daga cikin shida kamar haka: /aa/, /ee/ da /ii/. Tsawon wasali ba ya hawa a kan
sautukan wasulan /u/, /o/ da /ə/ a harshen Ga’anda bisa
dalili na kalmomi ba sa ɗaukar tsawo a harshen
Ga’anda a yayin furucin kalmonin[8]. Misali: /kufa/ (kogi) da /ɓo/
(zo) da /tə/ zafi. Ga yadda tsawon wasali yake gudana a
harshen Ga’anda.
Ga
misalan tsawon wasali a kalmomi da ke biye da kuma kalmomin da suke ɗauke
da gajerun wasula:
|
Kalma |
Ma’ana |
Kalma |
Ma’ana |
|
/waa/ |
yaro
(boy) |
/wa/ |
sai
(except) |
|
/yaanda/ |
faɗa (fight) |
/yanda/ |
saƙa (weave) |
|
/tǝltaa/ |
hawa
(ride) |
/tǝlta/ |
ɗauka (take) |
|
/yeera/ |
ɓarawo (thief) |
/yera/ |
ruwan
sama (rainfall) |
|
/wenichee/ |
idanu
(eyes) |
/weniche/ |
tabarma
(mat) |
|
/mii/ |
a bakin
(in front of) |
/mi/ |
mene ne
(what?) |
|
/wiita/ |
dare
(night) |
/wita/ |
tafiya
(journey) |
Kamancin Harshen Hausa da Harshen Ga’anda ta Fuskar Tsawon Wasali
Harshen
Hausa da harshen Ga’anda duk sun yi tarayya ta fuskar tsawon wasali a cikin
tsarin sautukansu. A dukkan harsunan biyu suna bambanta ma’anar kalmomi masu
takwarorin rubutun samuwar tsawon wasali. Misali: /daawaa/ (guineacorn) da
/dawaa/ (bush) da /gajeeree/ (short person) da /Gajeere/ (name of someone). A
harshen Ga’anda /sǝrta/ (iyaka) (boundary) da /sǝrtaa/
(doka) (rule) da /fichee/ (biri) (monkey) da /fiche/ (toka) (ash).
Bambancin Harshen Hausa da Harshen Ga’anda ta Fuskar Tsawon Wasali
Harshen
Ga’anda ya bambanta da harshen Hausa ta fuskar samuwar wani nau’in wasali na /ǝ/
a cikinsa wajen samar da wasu kalmomi a harshen. A harshen Hausa ana
samun dogaye wasali a kan dukkan sautukan gajerun wasulan harshen. Misali: /aa/, /ii/, /ee/, /uu/ da /oo/ wanda
hakan ya sa an ƙara samun wanzuwar kalmomi masu bambancin ma’ana
da yawa a harshen. Al’amuran akasin haka yake a harshen
Ga’anda, domin dogayen wasula a harshen Ga’anda kan auku ne, a kan uku daga cikin gajerun wasulan harshen kaɗai, wato /aa/ /ee/ da /ii/[9].
Sakamakon Bincike
Wannan
bincike ya gano cewa, tsawon wasali yana wanzuwa a harshen Hausa da harshen
Ga’anda. Haka kuma, harshen Hausa da harshen Ga’anda sun yi tarayya ta fuskar
samuwan ƙwayoyin sautukan wasula /a/ da /i/ da /e/ da /u/ da kuma /o/.
Sannan, da kuma wasu al’amuran tsawon wasali. Misalan kamancin tsawon wasulan
harsunan sun haɗa da: /aa/, /ee/ da /ii/, domin
nau’o’in dogayen wasulan */uu/, */oo/
da */əə/ ba su wanzuwa
a harshen Ga’anda. Bugu da ƙari, wannan binciken ya
gano cewa, tsawon wasali yakan bambanta ma’anar takwarorin kalmomi a wajen
rubutu a harshen Hausa da harshen Ga’anda.
Kammalawa
Wannan
binciken ya yi ƙoƙarin bayyana yadda tsawon wasali yake
gudana a harshen Hausa da harshen Ga’anda a ilimin tsarin sauti. A cikin
binciken bayan da aka yi shimfiɗa, an kawo ma’anar tsarin
sauti bisa fahimtar masana. Bugu da ƙari, binciken ya kawo
dabarun bincike da ra’in bincike da ma’anar tsawon wasali. Haka kuma, binciken
ya bayyana yadda tsawon wasali yake gudana a harshen Hausa da harshen Ga’anda,
tare da kawo kamanci da bambancin sauye-sauyen sautuka cikin tsawon wasali a
harshen Hausa da harshen Ga’anda.
Manazarta
Al-Musawi, U. I.
(2022). Kwatancin Bukukuwan Hausawa da na Kabilar Ga’anda. Unpublished M. A. Dissertation. Department of Languages and Linguistics, Jalingo: Taraba State University. Taraba State Nigeria.
Amfani, A. H. (2011).
Hausa Phonology. In Yusuf, O. (Ed). Basic Linguistics for Nigerian
Languages. Pp. 139-145. Ijebo-Ode: Linguistic Association of Nigeria.
Ijebu-Ode Shebiotimo Publications.
Bagari,
D. M. (1986). Bayanin Hausa: Jagora ga mai Koyon Ilimin Bayanin
Harshe. Rebat Moroc: Imperimerie Elmaarif Aljadida.
Bobda, A. S.
(2007). Some Segmental Rules of Nigerian English Phonology. English
World Wide.
CNHN.
(2006). Кamusun Hausa na Jami’ar Bayero. Wallafar Cibiyar Harsunan
Nijeriya. Zaria: Ahmadu Bello Printing Press.
Crystal, D. (2008). A
Dictionary of Linguistics and Phonetics. (Six Edition). London:
Blackwell Publishers.
Edwards, H. (2003). Applied
Phonetics (the Sounds of American English). Thomson Delmar Learning.
Fagge,
U. U. (2012). Hausa Language and Linguistics. Zaria: Ahmadu Bello
University Press.
Firth, J. R.
(1984). History of Linguistics. West Yorkshire. England.
Greenberg,
J. H. (1963). Classification of African Languages. London: Macmillan Press.
Goldsmith, J.
(1976). Autosegmental and Metrical Phonology. Blackwell Publishers.
Hockett, C. F. (1955). A
Manual of Phonology. Meoir II of the International Linguistics Journal
of American (IJAL). Indiana University Press.
Ibrahim,
G. (2015). Tone and Vowel Length in the Hausa Verbal Nouns. A Journal
of Languages and Literatures (JALAL) Vol. 6 No. 1. Pp 21-34.
Josiah, U. E. da Soneye,
T. (2011). Peculiar Pattern of Juxtapositional Assimilations in Educated
Nigerian Spoken English Variety. Lingustik online, 70 (1) https://doi.org/10.13092/10.70.1746.
Katamba, F. (1989). An
Introduction to Phonology. London: Longman Press.
Matthews, P. H. (1997). Oxford
Concise Dictionary of Linguistics. Oxford: University Press.
Newman, P. (1980). Classification
of Chadic within Afro-Asiatic. Leiden Universitaire Pers.
Newman, P.
(2000). The Hausa Language. An Encyclopedic Reference Grammar. London:
Yale University Press.
Newman, R. M. (1971). A
Case Grammar of Ga’anda. Unpublished Ph.D Thesis. Los Angeles: University of
California.
Prasad, T. (2008). A
Course in Linguistics. Prentice Hall of India Press.
Rischel, J. (1974). Topic
in West Greenlandic Phonology: Regularities Underlying the Phonetic Appearance
of Word forms in a Polysynthetic Language. Copenhagen: Denmark
Akademisk Forlog.
Robins, R. H. (1967). General
Linguistics. An Inroductory Survey. London: Longman Press.
Sani, M. A. Z.
(1989). Jagoran Nazarin Tsarin Sautin Hausa. Kano: Benchmark
Publishers Limited.
Sani, M. A. Z.
(2011). Gamayyar Tasrifi da Tsarin Sautin Hausa. Zaria: Ahmadu
Bello University Press.
Skinner, N. (1977). A
Grammar of Hausa for Nigerian Secondary School and Colleges. Zaria:
Northern Nigerian Publishing Company Limited.
Udoh, I. I. L.
(2003). An Introduction to Phonemic Analysis. Uyo: Fruities
Publications Limited.
Yalwa L. D. (2002).
Autosegmental Account to Some Hausa Tonal Processes, in Algaita Journal
of Current Research in Hausa Studies Vol. 2 No. 1, pp. 26-46. Kano:
Benchmark.
Yusuf, M. A.
(2011). Hausa Grammar: An Introduction. Zaria: Ahmadu Bello
University Press.
Zarruk,
R. M. (1980). Lafazin Hausa a Taƙaice. Zaria: Institute of Education Ahmadu Bello University.
Zarruk, R. M. da Kafin
Hausa, A. A. da Al-Hassan, B. S. Y (2005). Sabuwar Hanyar Nazarin
Hausa. Don Кananan Makarantun Sakandare Litttafi na Biyu. Ibadan:
University Press.
Waɗanda aka yi hira da su
|
S/N |
Suna |
Shekaru da Jinsi |
Rana |
Wuri |
|
1. |
Luka Peter |
60 (M) |
12/01/2025 |
Gabun |
|
2. |
Lucy Jabas |
53 (F) |
15/01/2025 |
Ga’anda |
|
3. |
Alice Poga |
30 (F) |
20/01/2025 |
Boga |
|
4. |
Timothy Jonathan |
55 (M) |
27/01/2025 |
Ga’anda |
|
5. |
Sulaiman Ahmad |
53 (M) |
01/02/2025 |
Ga’anda |
[1] Fassarar
mai bincike.
[2] Fassarar
mai bincike.
[3] Fassarar
mai bincike.
[4]Udoh,
I. I. L. (2003:42). An Introduction to Phonemic Analysis. Uyo:
Fruities Publications Limited.
[5]Skinner,
N. (1977: 2-3). A Grammar of Hausa for Nigerian Secondary School and
Colleges. Zaria: Northern Nigerian Publishing Company Limited.
[6]Sani,
M. A. Z. (2013). Maraka Yanki a Tsarin Sautin Hausa. Zaria: Ahmadu
Bello University Press.
[7] Wannan
bincike ya ƙara tabbatar da cewa tsawon wasali da karin sauti suna wanzuwa a
harshen Ga’anda, abun la’akari shi ne, a wannan harshe ba a sanya tsawon wasali
da alama ta karin sauti a kan kalma da nufin bambanta kalma, kamar yadda wasu
harsuna suke yi. Misali: harshen Yoruba da kuma harshen Igbo.
[8] Mai
bincike ya yi hira da wasu majiya harshen Ga’anda a ranaku mabambanta, su suka
tabbatar da wannan. Misali:12/01/2025 da 20/1/2025 da 27/1/2025 da 1/2/2025. Su
ne: Luka Peter da Lucy Jabas da Alice Poga da Timothy Jonathan da Sulaiman
Ahmad.
[9] Mai
bincike ya yi hira da wasu majiya harshen Ga’anda a ranaku mabambanta, su suka
tabbatar da wannan batun. Misali: 12/01/2025 da 15/01/2025 da 20/1/2025 da
27/1/2025 da 1/2/2025. Su ne: Luka Peter da Lucy Jabas da Alice Poga da Timothy
Jonathan da Sulaiman Ahmad.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.