Ticker

6/recent/ticker-posts

Gudummuwar wasu Nau’o’in Cimakar Hausawa Ga Lafiyar Mazakuta

Citation: Zauro, D. A. (2025). “Gudummuwar wasu Nau’o’in Cimakar Hausawa ga Lafiyar Mazakuta.” In Ɗunɗaye Journal of Hausa Studies, Vol. 03, No. 02, Pp. 184 – 191. www.doi.org/10.36349/djhs.2025.v03i02.023.

GUDUMMUWAR WASU NAU’O’IN CIMAKAR HAUSAWA GA LAFIYAR MAZAKUTA

Na

Dalhatu Abubakar Zauro

Adamu Augie College of Edu., Argungu, Kebbi State

Tsakure:

Hankalin al’umma da dama a wannan lokaci bai karkata kan nau’o’in cimaka da suke inganta lafiyarsu da kuma waɗanda za su taimaka musu wajen kauce wa shiga cikin matsalolin da suka shafi mazakuta ba. A tsarin gargajiya, abinci ba kawai cika ciki yake yi ba, yakan yi ayyukan magani da kariya da kuma garkuwa ga lafiyar al’umma. Wannan bincike ya mayar da hankali a kan matsayin nau’o’in abincin da Hausawa suka daɗe suna ɗaukar su a matsayin tushen ƙarfi da kuzari ga mazaje. Nazarin ya yi amfani da hanyoyin tattara bayanai na Ziyara da hira da rangadi da tattaunawa da masu magungunan gargajiya wajen lalubo bayanai. Baya ga haka, an ziyarci kafafen sadarwa na zamani kamar facebook da whtasApp wajen farauto wasu bayanai. Maƙalar ta yi amfani da tunanin Hausawa da yake cewa: “Magani a Gonar Yaro” a matsayin hanyar ɗora aiki. Sakamakon bincike ya nuna cewa, cimakar Hausawa tana ɗauke da sinadaran da suke inganta yawatawar jini da sha’awa da kuzari da kuma lafiyar maniyyi ga ɗa namiji. Maƙalar ta ba da shawarar cewa, akwai buƙatar komawa ga hikimar magabata domin inganta lafiyar mazakuta ba tare da dogaro da magungunan Turawa da suka zama tamkar na wucin-gadi ba. 

Keɓaɓɓun Kalmomi: magani, cimaka, lafiyar mazakuta

Gabatarwa

A tsarin rayuwar Bahaushe, abinci da magani abu guda ne. Hausawa na cewa “magani a gonar yaro: wanda bai sani ba ya nome,” suna nufin cewa duk abin da ake nema na lafiya yana cikin abinci da tsire-tsiren da suke kewaye da mutum. Tun kafin zuwan Turawa da kimiyyar zamani, Bahaushe ya daɗe yana amfani da cimaka wajen ƙarfafa jikinsa da kyautata zaman rayuwar aure. Lafiyar mazakuta na da alaƙa da lafiyar jini, jijiyoyi da kuzarin jiki. Yawancin abin da ake kira matsalolin jima’i a yau, Bahaushe na magance su ne ta hanyar amfani da abinci da tsire-tsire ba tare da dogaro da magungunan zamani ba. Wannan maƙalar ta nazarci albasa, gyaɗa, kuɓewa, citta da riɗi, tare da ba gargajiya rinjaye amma da tallafi kaɗan na bayanan zamani.

Tubalan Taken Nazari

A wannan fasali an bayyana ma’anonin muhimman lafuzzan da aka gina taken da su. An yi haka ne saboda mai karatu ya samu zarafin fahimtar inda ka dosa. Baya ga haka, bayyana ma’anonin da aka yi, sun yi wa maƙalar jagora ta yadda ba ta kauce daga kan godaben da aka tsara ta a kai ba. Kalmomin da aka fayyace ma’anoninsu su ne: magani, cimma da lafiyar mazakuta.

Magani

Daga bayanan Bergery, Ahmad, Bunza da Inuwa, za a iya cewa: “Magani shi ne, duk wata hanya ko abu da ake amfani da shi domin riga-kafi, karewa, rage raɗaɗi, kwantar da cuta, ko warkar da ita gaba ɗaya. Wannan ya haɗa da hanyoyin gargajiya ko na zamani, na zahiri ko na ɓoye. Kazalika, yana iya haɗawa da hanyoyin sihiri, siddabaru, ko wasu dabaru da ake amfani da su wajen neman warkarwa, kariya, ko ma ɗaukaka ta daraja a wasu al’adu.”

Bisa ga luguden waɗannan ayyukan na magabata da aka yi, wannan nazari yana kallon magani a matsayin duk wata hanya da aka yi amfani da ita ta zahiri ko ta ruhi, ta gargajiya ko ta zamani domin warkarwa ko rage tsananin cuta, kare jiki daga kamuwa da cuta, ko kawo jin daɗi da kwanciyar zuciya ga ɗan’adam ko dabba ko kuma wani tsiro.

Cimaka

A harshen Hausa, kalmar cimaka tana nufin abinci ko abin sha da ake ɗauka domin ƙarfafa jiki, ƙara kuzari, da tabbatar da lafiyar ɗan’adam, kuma a fahimtar Hausawa tana ɗaya daga cikin muhimman ginshiƙan rayuwa. A al’adance, cimaka ba wai cikar ciki ba ce kawai, har ma tushen ƙarfafa jiki, ƙwaƙwalwa, da iyawar ɗan’adam wajen gudanar da aikace-aikacen yau da kullum. Wannan ra’ayi ya samo asali daga fahimtar gargajiya wadda ta ƙunshi karin maganar da yake cewa “abinci magani ne”, alamar dangantakar abinci da ƙarfin lafiya. Hausawa na rarrabe cimaka zuwa ta ƙarfi, ta lafiya, da ta natsuwa, waɗanda suke taka muhimmiyar rawa wajen inganta ƙarfin jiki, ɗorewar aiki, da daidaituwar tunani ga ɗan’adam.

Binciken kimiyya yana nuna cewa, rashin ingantacciyar cimaka na iya janyo raguwar kuzari, raunin garkuwar jiki, da matsalolin natsuwa, waɗanda ke rage ƙarfin aiki da lafiyar gaba ɗaya. Wannan ya yi daidai da rahotannin ƙungiyoyi kamar UNICEF (2022) da ke bayyana tasirin rashin abinci mai gina jiki ga lafiyar manya. Don haka, a tsarin zamantakewar Hausawa, cimaka na wakiltar ginshiƙi mai mahimmanci ga lafiyar namiji, kasancewar ita ce tushen ƙarfinsa, kwarjininsa, da ingantacciyar rayuwarsa ta yau da kullum.

Lafiyar Mazakuta

A wannan gaɓar lafiyar mazakuta tana nufin yanayin da mazakuta take cikin cikakkiyar ƙoshin lafiya. Wato, tana iya yin ayyukanta na fitsari, jima’i da taimakawa a haihu yadda ya kamata, ba tare da wata matsala ta jiki ko ta tunani ba.

A taƙaice lafiyar mazakuta ita ce haɗin daidaiton lafiyar jiki, jijiyoyi, jini da ƙwaƙwalwa wajen tabbatar da cewa:

i. Mazakuta tana iya miƙewa yadda ya kamata.

ii. Tana iya fitar da maniyyi a lokacin da ya dace.

iii. Ba a jin zafi ko ganin kumburi ko rauni a lokacin fitsari ko jima’i.

iv. Babu cututtuka kamar su sanyi, raunin gaba ko karewar mazakuta.

Hanyoyin Gudanar da Bincike

Binciken ya dogara da fahimtar Hausawa cewa “gaskiya ita ce nagartar namiji”, don haka dole bincike ya kauce wa jita-jita da bayanan banza. An bi wannan ƙa’idar ta hanyar amfani da hanyoyi nagartattu da suka haɗa da:

i. Tuntuɓar masana maganin mazakuta na gargajiya domin tabbatar da sahihancin bayanai.

ii. Zantawa da mutanen da suka fuskanci matsalolin mazakuta, duk da al’adar ɓoye sirri, domin a samu ra’ayoyi daga ɓangarori biyu, wato, mai magani da mai sha.

iii. Neman bayanai daga jami’an lafiya na zamani domin daidaita hangen bincike.

iv. Duba ayyukan baya da masana suka gudanar domin sanin matsayinsu da kuma daidaita mafari.

v. Amfani da wayar hannu, kafofin sada zumunta, da Google wajen cike giɓi a wuraren da ba a samu bayanai kai tsaye ba. Wannan tsarin ya tabbatar da cewa binciken ya kasance bisa gaskiya, tsari, da daidaitattun ƙa’idojin ilimi.

Hanyar Ɗora Aiki

Manufar kawo hanyar ɗora aiki ita ce, a yi amfani da tunanin magabatanmu a matsayin jagora ga ayyukan bincike. Wani abin armashi game da haka, an samu ayyuka da dama da suka yi amfani da azancin magabatanmu a matsayin hanyar ɗora aiki, kuma suka ci nasara. Misalin irin waɗannan ayyuka sun haɗa da: Bunza, (2019 da 2023) da Sani (2022) da Dalha (2024) da sauransu da dama. Dalilin kenan da ya sanya aka yanke shawarar amfani da hanyar ɗora aiki a wannan nazari; saboda zai taimaka wajen yin jagora ta yadda za a fito da samako nagartacce. Bisa ga haka, wanna nazari, an ɗora shi a kan tunanin Hausawa da suke cewa: “Magani a Gonar Yaro: wanda bai sani ba ya nome.” An yi amfani da wannan tunani ne saboda ƙunshiyar maƙalar yana yi wa al’umma hannunka-mai-sanda ne a kan cewa matsalolin da suke damun su magungunansu na nan kusa da su a cikin gidajensu. Sai dai kash! Ba kowa ne yake da masaniyar hakan ba. Sakamakon maƙalar tana nuna cewa, abincinmu maganinmu. Shi ne ya sa aka yi amfani da wannan karin magana a matayin matashiya. Hausawa suna cewa, rashin sani ya fi dare duhu.

Cimakar Hausawa a Matsayin Magungunan Cututtuka da Larurorin Mazakuta

Cimaka a nan tana nufin duk wani nau’in abinci ko abin sha da Bahaushe yake amfani da shi don maganin yunwa ko ƙishurwa, ko don marmari da wasu biyan buƙatu na yau da kullum. Hausawa suna da nau’in abinci da yawa da matsayinsu ya zarta na a ci a ƙoshi ko a ji daɗi kawai, don kuwa suna da ɓoyayyen amfani ta fuskar magani. A wannan nazarin an yi ƙoƙarin lalabo wasu daga ciki.

Albasa

Albasa, wani irin tsiro mai yaji dangin mabunƙasa ƙasa da ake miya da shi, ko lawashinsa, (CNHN, 2006:11)Albasa tsiro ne ko kuma kayan lambu da ake amfani da shi sosai a girki da kuma wajen magani.

i. A nemo albasa a yanka ta madaidaita, sai a saka a kofi mai marfi, sannan a zuba tafasasshen ruwa a rufe. Ana so ruwan ya kai adadin mintuna goma zuwa sha biyar (10-15) a ƙalla. Ana shan wannan ruwan kwatankwacin mintuna talatin (30) kafin a je ga iyali. Falsafar da take cikin amfani da wannan magani ita ce, albasa tana wanke dukkan dattin da yake maƙale a mara ko a ciki kamar yadda take wanke cutar da take cikin jini.[1] Wannan ne zai ba mazakuta damar yin aiki yadda ya kamata.

ii. Akan nemo albasa matsakaiciya a yanka ta ƙanana-ƙanana, a ƙwalɗtafarnuwa kimanin ƙwara huɗu (4), ita ma a yanka ta ƙanana. A nemo kanunfari kimanin ƙwara goma (10), a markaɗe su waje ɗaya a juye su a kofi ko wani mazubi, sai a zuba babban cokali ɗaya (1) na zuma mai kyau, a juya. Ana son a sha wannan haɗin mintuna talatin (30) kafin saduwa da iyali. yana ƙara ƙwazo da girman mazakuta.[2]

iii. Za a nemo albasa matsakaiciya, a yanka ta ƙanana-ƙanana. A samo citta ɗanya matsakaita guda uku (3) su ma a yanka su ƙanana, a haɗe su waje ɗaya a markaɗe, a tace a sa a kofi, a zuba cikin babban cokali ɗaya (1) na zuma a motsa a sha rabin kofi da yamma. Yana ƙara girma da ƙarfin mazakuta.[3]

iv. A nemo albasa mai girma, a wanke ta da kyau, sai a ɓare ɓawan jikinta na sama. Ana son a samo wuka a yanke hancinta na sama da kuma na ƙasanta a mazauninta, sai a yanke kashi ɗaya bisa uku (1/3) na albasar, a yi wa ciki rami, a saka wuta a caccaki cikin da kyau. A nemo zuma mai kyau a zuba a cikin ramin albasar, sai a rufe da guntun albasar da aka yanke a sama. Ana buƙatar a nemi abin da za a ba albasar zafi ba tare da ta jiƙe da ruwa ba ko da na tsawon minti (1-2). Idan an ciro albasar sai a zuba zumar da ke ciki a cokali, sai a sha tun da safe kafin a karya kumallo. Baya ga haka, ana shan wannan magani daidai lokacin da bai wuce mintuna talatin ba kafin a je ga iyali. Haɗin yana ƙara ƙarfin mazakuta, yana kuma sa daɗewa lokacin saduwa.[4]

Hikimar da take cikin amfani da albasa a matsayin mahaɗin magani ita ce, bincike ya nuna cewa, albasa tana taimakawa sosai wajen tunkaɗa jini zuwa sassan jiki daban-daban da kuma cikin zuciya. Baya ga haka, cin albasa yana hana jini daskarewa a waje ɗaya. Ma’ana, tana tsinka jini, wanda hakan yana saka jini kewayawa ko’ina a jiki cikin sauƙi. Shigar jini cikin mazakuta akai-akai yana matuƙar taimakawa wajen ƙara masa girma.[5] Haka kuma, tafarnuwa da kanumfari da citta da ake amfani da su a matsayin mahaɗan maganin larurorin mazakuta, an lura cewa, suna maganin ciwon sanyi wanda yake taimakawa matsalolin mazakuta. Don haka ake amfani da su saboda kasancewarsu mahaɗan da suke daƙile cutar sanyi. Wannan ne dalilin da ya sa ake yawan ambatar su a matsayin mahaɗan maganin larurorin mazakuta na Hausawa.[6]

Gyaɗa

Gyaɗa, wani tsiro mai ‘ya’ya a ƙasa, da ke cikin ƙwanso, ana amfani da ‘ya’yan don yin ƙuli-ƙuli da man-ruruwa da sauransu. ‘Y’yan suna da garɗi, musamman idan an soya, (CNHN, 2006:185)

i. A nemo gyaɗa wadda aka ɓare, amma ba a soya ta ba, sai a saka a wani abu mai marfi. Idan an saka ta, za a zuba ruwa daidai yawan yadda gyaɗar za ta ɗan nutse a ruwan; sai a bari ta jiƙe idan ta yi kamar sa’o’i goma sha biyu (12). Daga nan sai a sha ruwan kafin a ci abinci da safe. Wannan haɗin magani yana matuƙar ƙara wa namiji kuzari a wajen saduwa.[7]

ii. A nemo gyaɗda dabino da riɗi, sai a haɗe su waje ɗaya a niƙe. Idan sun zama gari, sai a riƙa hambuɗar garin ana raka shi da ruwa mai ɗimi. Ana shan wannan magani tsawon mintuna talatin (30) kafin a je ga iyali. Wannan haɗin yana ƙara kuzari da ɗebe jin gajiya wajen saduwa da iyali.

iii. Ana nemo gyaɗa da ganyen shuwaka a riƙa taunawa (ana ci) tun da safe kafin a karya kumallo. Wannan hanya tana ƙara wa mazakuta ƙarfi da kuzari.[8]

iv. A nemo gyaɗa a murje bayanta, a hure yadda ake yi in za a ci, sai a sami namijin goro guda ɗaya (1) a haɗe su waje ɗaya a taune a haɗiye. Ana son a yi haka a ƙalla sau biyu a wuni. Haɗin yana matuƙar ƙara wa namiji kuzari da hana saurin kawowa.

Kuɓewa (Guro)

Kuɓewa, tsiro ne mai tsawo da ake shuka domin samun ‘ya’ya masu laushi da ɗan zare. Ana yawan amfani da ita wajen dafa miya. ‘ya’yan kuɓewa kan yi tsawo kaɗan, suna da siffa siriri ko ɗan kauri. Idan an yanka su, suna sakin wani ruwan danƙo wanda yake sa miya ta yi ɗan ɗauri.

i. A nemo kuɓewa guda biyar (5), a cire hancinta a yanka ta ƙanana-ƙanana, a wanke ta sosai a saka ruwa kimanin lita biyu (2) sai a tafasa. Idan an sauke a tace, sai a nemo zuma kwatankwacin roba ɗaya (1) sannan a zuba kuɓewar a ciki a motse da kyau a sha kofi ɗaya (1) safe da yamma. Wannan haɗin yana magance ƙanƙancewar mazakuta ta halitta ko ta wata larura. Sai dai an nuna akwai haɗari idan aka sha wannan haɗin fiye da wata ɗaya.[9]

ii. A nemo irin kuɓewa a shanya. Idan sun bushe, sai a soya irin a niƙe su. Ana son a rinƙa zuba cokali ɗaya (1) na garin a ruwan shayi, a sha sau biyu (2) a rana har na tsawon kwanaki ashirin da ɗaya (21). Wannan maganin ko mazakuta ta mutu ta daina tashi, in dai aka yi amfani da shi yadda aka kawo a nan, mazakutar za ta dawo aiki da izinin Allah.[10]

iii. A nemo ‘ya’yan kuɓewa da ‘ya’yan yakuwa, a soya su sama-sama, sai a haɗe su waje ɗaya a dake/markaɗe. Idan sun yi laushi, sai a rinƙa yin shayi ana sha. Haɗin na ƙara wa ɗa namiji kuzari.

iv. A nemo kuɓewa ɗanya guda uku (3) matsakaita, sai a yanka a ciro ‘ya’yan cikinta, su ake buƙata. Daga nan sai a samu ƙwarar tafarnuwa biyu (2) a kwalɗɓawan da ke sama, sai a markaɗe ta zama gari, a haɗe su waje ɗaya, a zuba a tukunya, a saka ruwa kofi ɗaya, sai a tafasa, in an sauke a sha da safe kafin a karya kumallo. Ana son a yi haka har na tsawon kwanaki bakwai (7). Za a sami ƙarfi da kuzari har ma da magance matsalar ƙanƙancewar mazakuta da saurin kawowa.[11]

Citta

Citta, wani tsiro mai ‘ya’ya mai yaji, wato, citta mai yatsu, (CNHN, 2006:78).

i. A nemo citta da tafarnuwa ƙwara uku (3) kowane, sai a fere bayan su da kyau a wanke, a saɓe ko a markaɗe su tare. Daga nan sai a tafasa ruwa a zuba ganyen shayi ƙwara biyu (2), sannan a saka citta da tafarnuwar da aka markaɗe, a bar su sai sun tafasa. Bayan nan sai a tace, a sha tsawon mintuna talatin (30) kafin a je ga iyali. Haɗin yana magance matsalolin raunin mazakuta.[12]

ii. A nemo citta ƙwara uku (3) a jajjaga, a samo tafarnuwa ƙwara uku (3) ita ma a jajjaga ta. Sai a nemo lemun tsami ƙwara guda (1) a yanka shi gunduwa-gunduwa, a zuba ruwa a tukunya a saka su tare a tafasa. Idan an sauke, sai a sha sau biyu a rana. Haɗin yana wanke mara da ƙara wa mazakuta kuzari.[13]

iii. A nemo citta ɗanya ƙwara uku (3) matsakaita a girma, da albasa matsakaiciya a yanka ta ƙanana-ƙanana a markaɗe su da kyau a tace. Bayan an gama tacewa, sai a zuba zuma cokali ɗaya (1) a motsa. Ana shan adadin rabin kofi safe da yamma. Wannan haɗin yana ƙara girman mazakuta.

iv. A nemo citta ƙwara biyu (2) a wanke ta da kyau a fere bayan a markaɗe. A samo rabin albasa matsakaiciya, ita ma a markaɗe. Kazalika, kunkunba ita ma a markaɗe rabin ta, sai a yamutse su da kyau a tace ruwansu. Daga nan sai a nemo cokali ɗaya (1) na zuma mai kyau a saka a motse. Ana son a sha minti talatin (30) kafin a je ga iyali. Haɗin yana ƙara ƙarfin mazakuta.[14]

Riɗi

Riɗi, wata tsiro ce mai ɗan ƙaramin tsawo da ake nomawa saboda tsabanta, waɗanda ake amfani da su a matsayin abinci, mai da magani.

i. A nemo riɗi da aya a haɗe su waje guda, A samo citta a yanka shi ƙanana-ƙanana a zuba ciki a markaɗe da kyau. Ana son a ɗibi cokali ɗaya babba a saka zuma cokali uku (3), sai a sha sau uku (3) a rana. Wannan haɗin yana ƙara girman mazakuta, yana sanya sha’awa mai yawa, yana ƙara ruwan maniyyi, sannan yana sanya kuzari.[15]

ii. Akan nemo riɗi da dabino da kanumfari da ‘ya’yan kabewa, sai a haɗe su waje ɗaya a niƙe su da kyau. Ana son a ɗibi babban cokali ɗaya a sa a nono ko madara a sha tsawon mintuna talatin (30) kafin a je ga iyali. Wannan haɗin yana maganin ɗaukewar sha’awa.[16]

iii. A nemo man riɗi mai kyau kamar kofi ɗaya (1), sai a samu garin jirai (ƙaro) kamar cokali biyu da rabi (2 ½). Ana son a ɗora man riɗi a wuta ya yi zafi, sai a zuba garin jiran a ciki a gauraya sai ya narke, sannan, a sauke shi a zuba a kwalba. Idan ya huce sai namiji ya riƙa shafawa a kan mazakutarsa. A kula! Ban da ƙofar mazakutar. Wannan haɗin yana ƙara tsawo da kaurin mazakuta ne.[17]

iv. Ana nemo riɗi tare da mayar da shi gari. Bayan haka ana samo aya a markaɗe ta zama gari, sai citta ita ma a mayar da ita gari. Ana haɗe su waje ɗaya, sai a zuba madara a bar su sai sun tsima sannan a tace a zuba zuma cokali ɗaya (1). Ana shan ƙaramin kofi kafin a karya kumallo da kuma da yamma bayan an ci abinci.[18]

A kimiyance riɗi yana ƙarfafa mazakuta da lafiyar jima’i, don kuwa yana ɗauke da magnesiumzinc da vitamin E, waɗanda suke taimakawa wajen ƙara yawo na jini zuwa mazakuta da ƙarfafa jijiyoyin mazakuta da taimakawa wajen tsayuwar azzakari mai ƙarfi da ɗorewa.[19]

Sakamakon Bincike

Sakamakon da wannan binciken ya fito da shi ya haɗa abubuwa da dama kamar haka:

i. Binciken ya gano cewa abincin Hausawa suna iya zama a gurbin magungunan cututtuka da larurorin mazakuta.

ii. An gano nau’o’in cimakar Hausawa guda biyar (5) da suka fi tasiri wajen inganta lafiyar mazakuta: albasa, gyaɗa, kuɓewa, Citta da riɗi.

iii. Kowane daga cikin waɗannan abincin yana ɗauke da muhimman sinadarai da suka haɗa da: masu ƙara kuzari da sha’awa, masu buɗe jijiyoyi da ƙara gudanawar jini, masu rage gajiya da motsa sha’awa. Kazalika suna ƙara samar da jini da juriya, masu ƙarfafa ƙwayoyin halittar ɗa namiji da lafiyar jijiyoyi.

iv. Hanyoyin haɗa waɗannan nau’o’in abinci sun tabbatar da alaƙarsu da ƙara kuzari da lafiyar mazakuta.

v. Binciken ya gano cewa akwai haɗin kai tsakanin fahimtar gargajiya da binciken kimiyya na zamani, wanda hakan yake tabbatar da ingancin amfani da abinci wajen kula da lafiyar mazakuta ba tare da dogaro da wasu magunguna na daban ba.

Shawarwari

i. A ci gaba da amfani da cimakar gargajiya cikin ma’auni, don inganta lafiyar mazakuta.

ii. A wayar da kai ga matasa game da illolin amfani da ƙwayoyin ƙarin ƙarfi ba tare da shawarar masana ba.

iii. ƙara bincike kan sauran cimaka kamar rogo, masara, kifi, zuma, dabino, namijin goro da aya da sauransu.

iv. A haɗa cimaka da abinci na yau da kullum domin kare lafiyar mazakuta.

Kammalawa

Binciken ya nuna cewa, waɗannan abinci na Hausawa suna da tasiri sosai wajen lafiyar mazakuta da saduwa. Suna haɗa fa’idar gargajiya da ta kimiyya, kuma amfani da su na yau da kullum yana iya zama hanyar magance matsalolin jima’i ba tare da dogaro da magungunan zamani ba. A cikin nazarin, an kawo irin taimakon da albasa da gyaɗa da kuɓewa da citta da kuma riɗi suke bayarwa wajen warkar da cutukan da suke shafuwar mazakuta ko kuma inganta amfaninta.

Manazarta

Abdullahi, A. (2015). Maganin Gargajiya da Al’adun Abinci a Arewacin Najeriya. Kano: Arewa Research Press.

Akhigbe, R. E. (2013). Tasirin Albasa (Allium Cepa) ga Hormones na Haihuwa a Maza. Journal of Medicinal Food, 16(10), 894–900.

CNHN, (2006). Ƙamusun Hausa Na Jami’ar Bayero. Wallafar Cibiyiar Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero Kano. Zaria: Ahmadu Bello University Press.

Kamtchouing, P., Mbongue, F. G. Y., Dimo, T., & Jatsa, H. B. (2002). Nazarin Tasirin Citta (Zingiber Officinale) ga Hormones na Namiji. Asian Journal of Andrology, 4(4), 299–301.

Mayo Clinic. (2023). Penis Health: Identify and Prevent Problems. Mayo Foundation for Medical Education and Research. Retrieved from https://www.mayoclinic.org/

Mohammad, A., & Ibrahim, M. (2020). Nutritional and Medical Value of Sesame (Sesamun Indicum L.): A Review. International Journal of Nutrition and Food Szciences, 9(2),49-56.

Umar, S., & Musa, H. (2021). Abincin Gargajiya na Hausawa da Lafiyar Haihuwa: Dubi ta Ethnonutrition. African Journal of Ethnobiology, 18(2), 55–64.

UNICEF. (2022). The State of the World’s Children 2022: Children, Food and Nutrition. New York: United Nations Children’s Fund.

Word Health Organization (WHO). (2021). Sexual Health and Reproductive Rights: Men’s Sexual Health. Geneva: WHO Press.

 

Shafukan Intanet da aka yi Amfana da Su

1. Asibitin Gargajiya (Traditional Medicine Clinic) www.facebook.com

2. Auwalu Abdulƙadir Kademi a shafin Gidan sanin Itatuwa da Ciyayi Ta Fannin Asararu. whatsApp: 09136478815

3. Bashir Suraj Adam tiktok.com@bashirsurajadam

4. Dr. Hafiz Kano Sarkin Maganin Nigeria. www.facebook.com

5. Dr. Nagwale Traditinal Medicine. www.facebook.com Don neman ƙarin bayani ana iya kiran wannan numba. 08162990107

6. Maijalalaini. Facebook.com www.maijalalaini.com ko a kira numbar waya: 08137482786

7. Sirrin riƙe miji, (2023, Dec. 22) www.Facebook.com.

 

Mutanen da Aka Gudanar da Hira da Su

 

Suna

Shekaru

Wuri

Rana

1.

Bashar Abdullahi Bunza

51

Unguwar Malamai Bunza

02/03/2025

2.

Ɗanjumma Nahaliƙu Sanyinna

43

A Garin Sanyinna

20/04/2025

3.

Hajiya Jagaba (Ungozoma)

83

A Gidanta, Unguwar Yagidare Zauro

17/11/2024

4.

Haliru Usman Nigar

37

A Shagonsa, Bakin Tashar Argungu

14/11/2025

5.

Haruna Muhammad Ɗan Tunga

42

Tsohuwar Kasuwa Sakkwato

 22/05/2025

6.

Ibrahim Dalhatu (Gura)

39

Bakin Gadar Kangiwa Argungu

25/12/2024

7.

Ibrahim Musa Geza

43

A Garin Geza Kamba LG

20/09/2024

8.

Isyaku Tanimun Kangiwa

41

A Cikin Garin Kangiwa Arewa LG

19/10/2024

9.

Kabiru Muhammad Mashayabo

52

A Kasuwar Bodinga

16/05/2025

10.

Malam Muhammadu Ɗan Malam

60

Unguwar Yabon Sarkawa Yauri

08/08/2024

11.

Mande Ɗan’amo Sabiyal

52

A Bakin Kasuwar Ambursa Birnin Kebbi LG

27/08/2025

12.

Nafi’u Na’allah Kangiwa

40

Bakin Kasuwar Kangiwa Arewa LG

02/02/2025

13.

Suleman Abubakar Yeldu

43

A Gidansa, Garin Yeldu Arewa LG

20/02/2025

 



[1] Hira da Malam Muhammadu Ɗan Malam Mai Shekara 60 a Unguwar Yabon Sarkawa Yauri Ranar 08/08/2024

[2]Hira da Mande Ɗan’amo Sabiyal Mai Shekara 52 a Bakin Kasuwar Ambursa Ranar 27/08/2025

[3]A shafin Dr. Nagwale Traditional Medicine. Facebook.com Don neman ƙarin bayani a kira 08162990107

[4]Hira da Isiya Tanimun Kangiwa Mai Shekara 41 a cikin Garin Kangiwa Ranar 19/10/2024

[5]A shafin Asibitin Gargajiya (Traditional Medicine Clinic) facebook.com

[6]Kimiyya ta tabbatar da cewa Albasa tana ɗauke da sinadarai masu inganta zagayawar jini, tana ƙara kuzari da shaawa. Tana kuma ƙara testosterone (Akhigbe, 2013).

[7]Hira da Ɗanjumma Nahaliƙu Sanyinna Mai Shekara 43 a Garin Sanyinna Ranar 20/04/2025

[8]Hira da Kabiru Muhammad Mashayabo Mai Shekara 52 Mai Sayar da Karas Bodinga Ranar 16/05/2025

[9]A Shafin Maijalalaini. Facebook.com www.maijalalaini.comko a kira numbar waya: 08137482786

[10]A shafin Bashir Suraj Adam tiktok.com@bashirsurajadam

[11]Hira da Hajiya Jagaba Ungozoma Mai Shekara 83 a gidanta da ke Yagidare Zauro Ranar 17/11/2024

[12]Hira da Nafi’u Na’allah Kangiwa Mai shekara 40 Bakin Kasuwar Kangiwa Ranar 02/02/2025

[13]Hira da Ibrahim Musa Geza Mai shekara 43 a garin Geza Kamba Ranar 20/09/2024

[14]Hira da Suleman Abubakar Yeldu Mai shekara 43 a garin Yeldu Ranar 20/02/2025

[15]A shafin Dr. Hafiz Kano. Facebook.com

[16]A shafin Sirrin Riƙe Miji (2023, Dec. 22). www.facebook.com

[17]Hira da Bashar Abdullahi Bunza Mai Shekara 51 Unguwar Malamai Bunza Ranar 02/03/2025

[18]A shafin Dr. Nagwale Traditinal Medicine. www.facebook.com

[19]A cikin Mohammad, A., & Ibrahim, M. (2020). Nutritional and Medical Value of Sesame (Sesamun Indicum L.): A Review. International Journal of Nutrition and Food Szciences, 9(2),49-56

 Dundaye Journal

Post a Comment

0 Comments