Citation: Usman, MUHAMMAD Ph.D (2025). Amfani Da Karin Magana A Matsayin Kanun Labari Nazari A Kan Littafin Magana Jari Ce Na Abubakar Imam. Yobe Journal of Language, Literature and Culture (YOJOLLAC), Vol. 13, Number 1. Department of African Languages and Linguistics, Yobe State University, Damaturu, Nigeria. ISSN 2449-0660
AMFANI DA KARIN MAGANA A MATSAYIN KANUN LABARI
NAZARI A KAN LITTAFIN MAGANA JARI CE NA ABUBAKAR IMAM
BY
USMAN, MUHAMMAD Ph.D
Tsakure
Karin Magana wani ɓangare ne na adabin
gargajiya na Hausa wanda ake amfani da shi a cikin zantukan yau da kullum.
Ba a banza ake saka karin magana cikin zance ba, akwai dalilai da dama ciki
kuwa har da jawo hankalin mai sauraro natsu da kai ya fahimci saƙonnin dake ƙunshe waɗanda suka shafi yanayin da
ake ciki. Imam ya yi amfani da karin magana masu dama a labarinsa kodai a
matsayin kanun wasu daga cikin ‘ya’yan labaransa ko waɗanda ya saka cikin zantukan
taurarinsa. Waɗanda ya yi amfani da su a matsayin kanun wasu
daga cikin ‘ya’yan labaransa kuwa ya yi haka ne domin ya fito da saƙonnin da karin maganar
suka ƙunsa a sarari domin mai
sauraro ko karatu ya fahimci zahirin saƙonnin ta amfani da abubuwan
da suka abku ga wasu taurarin sakamaon abubuwan da suka aikata walau alheri ko
sharri.
Muhimman kalmomi: Karin Magana da kanun labarai da Magana Jari Ce,
Abstract
Proɓerbs is an important
form of oral literature mostly employed by Hausa people in their daily conɓersations. It is not just used for entertainment but it is mostly
used to send numerous messages that suite the current situations. Imam used
this form of oral literature in his story not only for entertainment but as
heading of some of his frame stories to practically demonstrate the meaning of
the form in order to draw the attention of his reader to the fact that whateɓer one does, be it good or bad, the results of his actions will be
at his door waiting to pay him back as can be seen in the eɗamples from some of the frame stories.
Key words Karin Magana, title and Magana Jari
1.0 Gabatarwa
Magana Jari Ce labari ne da ya yi fice a tsakanin masana da manazarta da
masu sha’awar karanta ayyukan adabin Hausa ko domin ƙara faɗaɗa ilimi ko kuma domin nishaɗi. Adon harshe na daga
cikin tubalan da Imam ya yi amfani da su wajen gina labari kuma ya. Wannnan maƙalar ta yi ƙoƙari ne wajen taskace bajimtar da Imam ya yi ne ta amfani da karin
magana a matsayin kanun labarinsa na Magana Jari Ce. Haka kuma ya yi amfani da
ita wajen raawa
mafi yawa daga cikin ‘ya’yan labaran cikin littafin. Mawallafin ya yi haka ne
domin ya fito da ma’anar karin magana sarari musamman ga waɗanda ba su fahimci muhimman
saƙonnin dake ƙunshe cikin karin magana
ba, akasarin mutane suna amfani da karin magana ne ba tare da sun san zahirin
saƙonnin dake cikinta ba. Za a
iya cewa wannan ƙoƙari da Imam ya yi tamkar fassara ce ya yi tare da misalai
domin mai karatu ko sauraro ya yi karatun ta-nutsu.
2.0 Karin Magana
Masana da manazarta adabi
sun ta kai komo kan ma’anar karin magana. ma fi yawansu, sun yi ittifaƙin cewa abu ne mai wahala a
ce kai tsaye ga wata ma’ana da aka yi ittifaƙi da ita. Amma wannan bai hana kowa tunanin samar da
fahimtarsu ba. Amin (2002) ya ambato ra’ayoyin masana da ra’ayoyinsu suka sha
bamban danagne
da ma’anar karin magana amma
dai za a iya cewa kusan bambance-bambancen ba su taka kara sun karya ba. Hasali
ma, Amin (2002) cewa ya yi idan aka yi la’akari da ma’anonin da waɗannan masana suka bayar na karin magana, duk da bambance-bambance,
za a iya cewa karin magana:
i. Yawanci taƙaitacciyar maganar al’umma ce (mai ma’ana).
ii. Yawanci karɓaɓɓiyar magana ce da
al’umma ta amince da ita.
iii. Magana ce da ke cike da zuzzurfar ma’ana.
iɓ. Magana ce da ba ta
tsufa.
v. Magana ce da ke da ɗandanon daɗi (a kunne).
vi. Maƙasudinta shi ne isar da wani saƙo a kan gaɓa.
Masana irin su Bishop (1922) da Whitting (1931) da Bichi (1977)
da Umar (1978) gaba ɗaya sun yi ittifaƙi cewa abu ne mai wahala
a iya tantance wa tsakanin zancen hikima na kacici-kacici da karin magana.
Whitting (1931) cewa ya yi akasarin masu tattara zantukan hikima na
taka-tsatsan wajen kawo fitaccen bambanci tsakanin karin magana da jumlolin
zantukan hikima. Bada (1995) ya ruwaito wasu masana adabin baka da suka bayar
da gudumuwa wajen bayyana ma’anar karin magana dangane da ƙumshiyarta. Daga cikin waɗannan masana, akwai
Ploppenganer (1969) wanda ya bayar da ma’anar karin magana da cewa ‘Karin
magana zancen hikima ne da ke bayani kan al’amuran rayuwa baki ɗaya. Wilson (1970) a nasa bayanin dangane da ma’anar karin magana,
ya ce karin magana zancen ne cikin hikima na al’ummar duniya. Kelson (1971) ya
ce ‘Karin magana zancen hikima ne da ke fayyace gaskiyar al’amari.’ Shi kuwa
Nwoga (1975) a tasa fahimtar dangane da karin magana, ga yadda ya ce ‘Karin
magana, taƙaitaccen zance ne cikin hikima da ke fito da
falsafar al’ummar zamanin da.’ Haka shi ma Hook (1977) cewa ya
yi ‘Karin magana zance ne da ke nuna hikimar al’umma ta gargajiya.’
Ita kuwa Finnegan (1970:28) cewa ta yi ‘idan aka
yi la’akari da kusancin da ke tsakanin zantukan hikima gaba ɗayansu, to abu ne mai wahala a tantance bambancin da ke tsakanin
karin magana da sauran zantukan hikima.’ Haka shi ma Nyembeze (1974) cewa ya yi
‘abu ne mai wahala wani ya iya nuna bambanci tsakanin karin magana da sauran
zantukan hikima na al’umma.’ A ra’ayoyin waɗannan masana sun zo daidai
dangane da ma’anar karin magana. A zahiri maganar tasu haka take domin idan aka
dubi zantukan hikima na Hausa, za a iske kusan ba abu ne mai sauƙi ba a ce za rarrabe
tsakaninsu. Wato kowane lokaci za a iya aza ɗaya a muhallin ɗayan. Misali idan aka ɗauki wannan baƙar maganar mai
cewa ‘Shakulatin ɓangaro, ungulu ta ga gawar mota.’ Wasu na
iya ɗaukar wannan a matsayin
karin magana a yayin da wasu za su kalle ta a matsayin baƙar magana ko shaguɓe.
Hassan (2009) ya tofa
albarkacin bakinsa a wata maƙala da ya gabatar da cewa adabin baka
musamman ma zantukan hikima irin su karin magana da zambo da habaici da kirari
da sauransu, wani bakandamen fage ne da ke tattare da hikima da falsafar
rayuwar Bahaushe. Ya ce falsafar rayuwa ba ta tsaya ne a kan nishaɗi ko molon ka ba ne kawai,
har ma takan shafi al’amuran tattalin arziƙi da siyasa da yanayin
zamantakewar al’umma. Wannan ya nuna a fili kenan cewa nazarin adabi ya wuce
maganar nishaɗi. Amma kuma marubucin ya
gano cewa sau da yawa ‘yan siyasa na yawan amfani da ire-iren waɗannan karin magana domin
shawo kan al’ummominsu domin ganin ba su tayar da ƙayar baya ba. Ya buga misalai da wasu daga cikin waɗannan nau’o’in karin maganar kamar su:
i.
Idan
dambu ya yi yawa ba ya jin mai.
ii.
Ba
kullum ake kwana a gado ba.
iii.
Da
muguwar rawa gwamma ƙin tashi
Malumfashi da Ibrahim (2014) sun bayyana cewa
kalmomi guda biyu ne aka gina wannan lafazi da su, wato ‘kari’ da kuma
‘magana.’ Sun yi bayanin cewa:
’kari’ na nufin wani ɓangare ko rabi ko karyayye ko kuma rababbe. Alhali kuma ‘magana’
na nufin zance ko furuci ko kalami da mutum kan yi domin a fahimci abun da ke
cikin zuciyarsa. Kenan idan muka dubi batun a yadda yake a zube, za mu ce ba
wani abu ba ne karin magana face zancen da aka yi wa giɓi ko aka karya ko raba shi ko kuma aka kawo wani ɓangare aka yi watsi da waniɓangaren, Malumfashi da Ibrahim (2014)
Bunza (2017:3) ya tofa albarkacin bakinsa a kan
matsayin karin magana inda ya ce:
Karin magana babbar taskar adabi ce ta adana
muhimman abubuwa na kunne ya girmi kaka. A ƙa’idar masana adabi,
karin magana wata taƙaitacciyar ko gajeruwar jumla ce mai ɗauke da babban saƙon da ya fi ta tsawo a zahiri idan za a yi
fashin baƙinsa. Daga cikin karin magana akwai masu ba da
haske a kan bincike da dabarun bincike da ƙwarewar mai aikin
bincike kamar:
i.
Abin
da wayo ya ɓoye hankali ke gano shi
ii. Tafiya da waiwaye tana maganin mantuwa
iii. Matambayi ba ya ɓata
iv. Gani ya kori ji
Wannan bayani da Bunza ya yi, ya ƙara fito da maganar masana cewa karin magana taƙaitaccen zance ne ko gajeruwar kalma ce mai ɗauke da faffaɗar ma’ana da ke bukatar nazari ko zuzzurfan
tunani kafin a gane irin saƙonnin da take ɗauke da su.
A taƙaice, wannan nazarin yana
ganin za a iya cewa karin magana wani taƙaitaccen zance ne na hikima da ke cike da fasaha na iya tsara
magana cikin hikima wadda ba kowa ne zai iya fahimtar saƙo ko ma’anar da ke tattare da ita ba face wanda ya laƙanci harshen da aka gina ita karin maganar da shi. Yawanci akan
gina karin magana ne ta la’akari da wani abu da aka saba da ganinsa mai ɗauke da wani darasi da ya kamata a lura da shi. Ana gina karin
magana da kalmonin da aka saba amfani da su cikin zancen yau da kullum, sau da
yawa ma’anonin kan sauya daga ma’anarsu ta zahiri. Ana amfani da sunayen
dabbobi da tsirrai da garuruwa da kayan amfanin da sunayentufafi da da sunayen
sana’o’i da sunayen muƙamai na sarauta da dai sauran duk wani abu
da ɗan’adam ya sani ya kuma san amfaninsa.
A karin magana akan danganta zance ko aikin da
ake yi kuma ya dace da yanayi ko lokacin da abu ya auku. Misali, idan ana cikin
maganar wani da ake son gani cikin gaggawa, sai kwatsam a gan shi ya zo ba tare
da an aika ɗan saƙọ ba. Nan take sai a
yi amfani da karin magana da ta dace da zuwansa, ‘Faɗuwa ta zo daidai zama,’ Ko ‘Kaya sun tsinke a gindin kaba,’ ko
kuma ‘Ɗan halas ya ƙi ambato.’
Da wannan fassara ne aka aza wannan aiki tare
da ƙudurin ɗaukar labarin Magana
Jari Ce domin kwakkwafe ire-iren saƙonnin da Imam ya bijiro
da su cikin littafin. Littafin ya shahara sosai a idon masana da ɗaliban adabin Hausa har da masu sha’awar karanta habarcen Hausa
saboda a fito da fa’idojin da ke tattare a cikin karin magana da suka shafi
gargaɗi da ilmantarwa da samar da nishaɗi ga mai sauraro da mai furtawa.
Wannan wata dabara ce kamar yadda masana da
manazarta irin su Ɗangabo (2008) da Umar (2010) da Bugaje (2014)
suka bayyana cewa salo ne da ake daukar halayyar wani abu maras rai a bai wa
wata halitta mai rai. Misali:
i. Yaro man kaza
ii. Babba
juji ne
iii.Namiji
dangin barkono sai an tauna ka a san yajinka
Karin
magana ginshiƙi ne wajen fito da fasahar
harshe a cikin zancen yauda kullum. Ana iya cewa tamkar gishiri ne a miya domin
kuwa wata dabara ce da take nuna irin yadda al.ummar da take amfani da ita. Ba
karin magaana ne kaɗai azancin magana da Imam ya yi amfani da ita ba a wannan
labarin, akwai sauran nau’o’in azancin magana irin su kirari da kacici/kacici
da baƙar magana da shaguɓe da sauransu amma dai
karin magana ne ta fi ɗaukar hankalin wannan maƙala, saboda haka a kanta ne
nazarin ya mayar da hankali. Imam ya yi amfani da karin magana a matakai uku a
cikin wannan labaari nasa. Da farko ya yi amfani da ita a matsayin kanun
labarin baki ɗaya inda ya sanya masa suna .Magana Jari Ce. A mataki na
biyu, an kasa labarin zuwa kundaye uku, to haka aka sanyawa kowane kundi suna
da wannan karin magana ta Magana Jari Ce. Sai kuma a mataki na uku inda Imam ya
sakawa taurarin wasu daga cikin ɗiyan labaran karin magana a cikin lafuzansu.
Wani bincike da aka gudanar ya tabbatar da cewa Imam ya yi da karin magana har
guda ɗari biyu da talatin daidai
wannan labari. Usman (2023).
3.0 Maganna Jari Ce
Bayan kammala gasar da ta
haifar da waɗancan litattafai guda biyar
da aka ambata a baya, sai East ya nemi da a ba hukumarsa aron Imam ya zo Zariya
takanas don ya ƙara samar da ƙarin litattafan karantawa a makarantun
elementare na lardin Arewacin Nijeriya. Matakan da aka ɗauka don samar da Magana
Jari Ce, Malumfashi (1995) ya bayar da haske inda ya ruwaito rahoton hukumar talifi na cewa:
An yi amfani da labarai daga wasu
littattafan labarai da tatsuniyoyin sassan duniya dabam-daban aka sake rubuta
su tare da tunanin mai karatu ɗan Afirka. Wannan aiki
(na rubuta Magana Jari Ce) ya samu kammaluwa ne tare da taimakon
malam Abubakar Kagara, (NAK/ANDIOZA, 1936).
Usman (2023) ya ruwaito cewa a wannan labari
na Magana Jari Ce, Imam ya yi amfani da karin magana guda ɗari biyu da talatin (230) daidai, wasu a matsayin kanun ‘ya’yan
labarun da kuma waɗanda ya saka a lafuzzan taurarin ‘ya’yan labarun
da kuma waɗanda shi kansaya yi amafani da su a labarun da
ya buɗe littafi na ɗaya da littafi na biyu
da kuma littafi na uku. Karin magana ta yi tasiri sosai a matsayin wani ginshiƙin tubulin ginin labarin Magana Jari Ce.
Iya zancen hikima tamkar
wanda ya mallaki uwar kuɗi ne a harkar kasuwanci. Kuma kamar yadda ba
kowane mutum ba ne yake iya mallakar jari, haka nan ba kowane mutum ba ne yake
da baiwar iya bayar da labari na hikima, shi ya sa masu iya magana suke cewa:
Wannan maƙalar ta tsakuro karin
magana guda uku domin amfani da su a matsayin misalai.
4.1 ‘Munafuncin Dodo Ya Kan Ci Mai Shi’
Wannan shi ne labari na
goma sha huɗu (14) a jerin ‘ya’yan
labaran da aka bayar a littafi na ɗaya. Labarin yana ɗaukene da irin mummunan
sakamako da mai ƙulla munafunci kan ci karo a ƙarshen al’amari. Gargaɗi ne ga suka wanda ya
fahimci darasin da yake ƙunshe cikinsa. Idan dai kwaɗayin duniya mutum ya sa a
gaba, to ba inda wannan kwaɗayin zai kai shi illa mahalaka kamar yadda
aka gani gun waɗannan mutanen uku.
4.1.2 Ma’anar Karin Maganar Ta
Sarari Da Ta Ɓoye
Munafunci mummunar ɗabi’a ce, Dodo kuwa halitta
ce da Bahaushe ya yi imani da wanzuwar sa kafin zuwan addinin musulunci.
Bahaushe ya kwatanta su ne saboda dukkansu daga ƙarshen al’amari halaka
ma’abucinsu suke yi. Amma Bahaushe na amfani da karin maganar ne da nufin isar
da gargaɗi ga duk mai irin
wannan ɗabi’a ta munafunci da cewa
koda ya ga yana cin nasara yayin da yake ƙulle-ƙullensa, to ya san da sani
wata rana zai halaka yana ji yana gani kamar yadda Dodo yake hallaka mutumin da
ya mallake shi yayin da ya kasa biya masa buƙatunsa. Wannan ayar ta nuna
irin ayyukan da munafukai suke haɗin gwiwa da juna wajen saɓawa umurnin Allah mai girma
da ɗaukaka. Saboda irin wannan
aiki da suke aikatawa sai suka shagala da wanzuwar Allah, to haka shi ma Allah
Ya manta da su baki ɗaya har zuwa ranar tashin ƙiyama. Har ila yau, wannan
ayar ta bayyana yadda Allah Ya manta da masu wannan mummunar ɗabi’a wanda ya nuna
tabbacin hasarar rahama da suka yi tun a duniya. Ita kuma wannan ayar da ta
biyo baya, ta nuna ƙarara irin tanadin da Allah Ya yi wa
munafukai maza da munafukai mata a ranar lahira. Wutar jahannama ce makomarsu
kuma a can za su dawwama har abada.
4.1.2 Sharhin Labarin
Wannan labarin ya fito da
illar munafunci a fili inda aka ga sakamakon ƙulle-ƙullen makirci saboda cutar
da wani ya koma kan mai ƙullawa. Tun da farko waɗannan mutane guda uku ba
amintattatu ba ne ga al’umma, abin da suka sa a gaba shi ne cutar da al’umma
masu neman na kansu domin neman rufa wa kansu asiri. Babban darasin da aka koya
a wannan labarin shi ne kar mutum ya sake ya bi son zuciya ko ya zama mai haɗama kan abin duniya. Waɗannan samari sun kasance
mahandama da babakere wajen son abin duniya. Da a ce sun haɗiye haɗamarsu, kowa ya haƙura da abin da ya samu, da
sun ci gaba da rayuwa, watakila ma su yi tunanin barin wannan muguwar sana’a,
amma son zuciya ya kai su ga rasa rayuwarsu.
Shi kuwa Kaɗo dayake ba mugu ba ne,
kuma Allah ya sa kuɗin duka rabonsa ne, sai ya dawo ya iske kuɗin cikin kwanciyar hankali,
ya kwashe kayansa ya koma gida rayuwa ta canza duniya ta dawo sabuwa. Saboda
haka, a kullum ana so zuciyar mutum ta zama tsarkakka cikin kyakkyawan tunani.
Wannan ita ce mafita ga duk mai son ya samu alheri cikin rayuwarsa. Amma duk
wanda ba shi da wata manufa sai ƙulla makirci da husuma a cikin al’umma, to
babu makawa ƙarshensa zai kasance nadama
ne wadda ba za ta amfane shi ba duniya da lahira. Waɗannan ɓarayi su uku, tun da farko
ba su zaɓarwa kansu sana’a da za ta
kai su gaci ba, sun ta’allaƙa ne kan cutar al’umma ta hanyar tare hanya
su ƙwace musu dakiyoyinsu da
duk wani abu da suka mallaka. A maimakon su yi amfani da ƙarfinsu su nemi halas, sai
suka zaɓi amfani da ƙarfi su cutar da jama’a.
Dayake duk mugun da bai yi mugunta wa kansa ba bai cika mugu ba, sai ga shi
daga ƙarshe, sun ƙullawa junansu makirci
wanda shi ne ya zama ajalinsu su ukun duka. Kamar yadda aka karanta, duk wanda
ya ɗauki wannan mummunar ɗabi’a, to ko ya so ko
ya ƙi, haka ko makamancin
haka ƙarshensa zai kasance, kuma
ya je lahira ya ci karo da fushin Allah maɗaukakin Sarki.
Akwai darussa masu
muhimmanci a wannan labarin. Daga ciki akwai mai tayar da mutum daga barci
musamman wanda ya kasance babu komai a zuciyarsa illa kwaɗayin tara abin duniya ta
kowane hali. Rashin godiya ba abin koyi ba ne. Da waɗannan samari sun dangana da
abin da kowa zai samu idan aka yi rabon nan to da sun sun tsira da rayukansu.
Amma haɗama da mugun nufi sun ja
masu hasarar dukiya da rayukansu. Allah Ya kyauta.
4.2 ‘Iya Gani Iaya Ƙyalewa’
Shi kuwa wannan labarin
wani maharbi ne da ya iske wani maciji cikin halin ƙunci, wato dutse ya danne
shi macijin kuma ya rasa yadda zai yi ya kuɓuta. Macijin ya roƙi wannan maharbi da ya
taimaka masa ya ture dutsen nan domin ya kuɓuta daga halaka. Maharbin
ya jinjina ya kuma koka kan halin halittun zamani, kar taimako ya zama ƙari. Macijin nan ya yi alƙawarin ba zai cutar da
mutumin nan ba. Amma abin mamaki, ture dutsen nan da ke kan macijin nan yake da
wuya, sai ya kawo wa maharbin nan sara da niyar ya kashe shi. Daga nan ne aka
tafi neman alƙalan da za su yanke hukunci
kan wannan rashinamana ta maciji.
4.2.1 Ma’anar Karin Maganar Ta
Sarari Da Ta Ɓoye
Duk abin da bai shafe
mutum, to mafi a’ala ya bar shi kar ya sake ya saka baki ciki. Saka baki a
al’amarin da bai shafe ka ba na iya zama maka matsala ƙatuwa da za ta dame ka koma
ta zame maka hanyar halaka. Zaman lafiya shi ne barin abin da bai shafe ka ba.
Turawa ma suna da makamanciyar wannan karin maganar, ‘let a sleeping dog lies.
Hikimar Bahaushe a nan idan
idon mutum ya kai kan wani abu da bai shafe shi ba, to duk yadda za a yi kar ya
sake ya sa bakinsa aciki saboda ya tsira da mutuncinsa da kimarsa. Shiga harkar
da ba ta shafi mutum ba al’amari ne mai haɗari sosai da zai iya kai
shi asarar lafiyarsa ko ma ransa baki ɗaya.
4.2.2 Sharhin Labarin
Karya alƙawari wani mummunan aiki ne
da zai iya jawo wa mai wannan hali shiga uku da sanewar amintaka daga wanda aka
karya wa alƙawari koma al’umma
baki ɗaya. A mafi yawan lokuta,
son zuciya shi ke kai wasu su karya alƙawarin da suka ɗauka da kansu ba tare da an
tilasta masu ba, amma kuma daga baya idan sun samu biyan bukatarsu, sai su rufe
ido gam su karya alƙawarin da suka ɗauka da kansu. Wannan shi
ne abin da ya faru a tsakanin maharbi da macijin da maciji. Maharbin nan yana
kyakkyawar niyya game da macijin da ya samu dutse ya danne, amma shi kuma
macjin sai ya kasance mai mai karya alkawari. A labarce, wannan labarin ya bayyana
wa mai karatu ko sauraro irin mu’amala da ke akwai a tsakanin mutane da
dabbobi. Doki da Biri sun bayar da munanan kalamai dangane da mutum, suna ganin
maciji ya kashe mutum shi ne daidai saboda irin yadda suke ganin muguntar
mutum. Amma sai cikon alƙali na uku, wato kare ra’ayinsa ya sha banban
da na ‘yan uwansa, ya nuna hikima da sanin ya-kamata. Wannan hukunci da ya
yanke shi ne ya kuɓutar da maharbi ya kuma koma da maciji angulu loma kan
masheƙiya. Wannan wani saƙo ne da ya kamata duk wanda
ya ji wannan labari ya ɗauki darasi, idan ka yi alƙawari, to ka cika koda kuwa
akwai wata ƙulallaiya a tsakaninka da
wanda ka yi wa alƙawarin domin ba a kan ƙulallaiyar ka ɗauki alƙawarin ba. Bugu da ƙari, labarin na nuna wa
al’umma cewa duk abin da za ka yi, to ka yi saboda Allah, shi kuwa Allah zai
taimake ka ta inda ba ka zato.
5.1Alheri Danƙo Ne Ba Ya Faɗuwa Ƙasa Banza’
Wannan kuwa labarin wani
saurayi ne mai son aikata alheri. A kullun hannunsa a sake yake wajen
kyautatawa al’umma. Ya gaji dukiya mai yawa daga mahaifinsa, Allah kuma ya nufe
shi da zama inuwa ga kowa da kowa . Alherinsa na zuwa ga duk wanda Allah ya ciyar
ba sai wanda ya sani ba. Har fatake yake nemowa daga kan hanya ya kawo su
gidansa ya ciyar da su. Wannan aikin alherin da ya gudanar da dukiyarsa, ya
jawo masa alherin da ba ya lissafuwa.
5.1.1 Ma’anar Karin Maganar Ta
Zahiri Da Ta Ɓoye
Wannan karin maganar tana
nuna cewa duk wanda ya aikata aikin kirki to babu shakka zai samu kyakkaywan
samakamako a rayuwarsa.A wannan karin maganar, Bahaushe ya kwatanta alheri da
danƙo. Danƙo dai wani abu ne da ake
amfani da shi wajen liƙe abu biyu a waje guda. Idan danƙo ya faɗi a ƙasa, ba za a iya ɗakko shi ba ba tare da
ya ɗebo ƙasa a jikinsa ba. Hikimar
Bahaushe a nan ita ce duk mai aikata alheri, daidai yake da yadda danƙo yake, wato aikin nan da
ya yi na alheri ba zai tafi a banza ba, sai ya samu mafi kyawun sakamako abin
da alherin da ya fi aikin alherin da ya yi. Ana amfani da wannan karin
maganarwajen ƙarfafa gwiwar al’umma da ta kasance masu aikata kyawawan
ayyuka domin ci gaban al’umma.
5.1.2 Sharhin Labarin
Labarin nan ya taɓo irin sakamakon da duk
wani mai aikkata alheri yake samu. Hassan dai tun da Allah ya sa ya samu
mallakar dukiyar da mahaifinsa ya bar masa a matsayin gado, ya nuna halin
tausayi ga marasa shi. Kullun tunaninsa shi ne ta wace hanya ce zai taimakawa
mabuƙata. Ko lokacin
da ‘yan uwansa suka nemi su ba shi tsoron da talauci, bai girbiza ba, ya
ci gaba da taimakon da ya saba. Abokansa sun amfana da dukiyar da Allah ya ba
shi. Dayake Allah na iya gwada bawansa a duk lokacin da ya so, ya kuwa gwada
Hassan da karayar arziki, duk dukiyarsa ta ƙare, ya shiga halin ƙaƙa-ni-ka-yi. Abokai da dangi
duk suka watse suka bar shi cikin talauci kamar bai taɓa mallakar ko sisi ba.
Allah mai yin yadda ya so a
lokacin da ya so, ya sake buɗawa Hassan wata kafar arziƙin, suniya ta dawo sabuwa.
Lokacin da ya ga Allah ya maido masa da arziƙinsa, sai ya yanke shawara
ya sake matsuguni tunda ya ga yadda mutanen garinsu suka juya masa baya a
lokacin da dukiyarsa ta karye. Da ya sake gari kuma bai fasa abin alherin da ya
saba ba. Ya kan gayyato fatake ya ciyar da su. Aikin alherin nan da yake yi ne
ya jawo hankalin Sarkin wannan ƙasa, suka zo shi da wazirinsa suka ga irin
taimako da Hassan yake yi wa al’umma. Shi kuwa Hassan bai san ko suwaye ba.
Aikin alherin nan ne ya jawo Sarki ya naɗa shi wawan Sarki, ya samu ɗaukaka a wajen Sarki da
jama’ar ƙasa baki ɗaya.
Karin maganar ta yi daidai
da ƙumshiyar labarin idan aka
yi la’akari da halin kirki da aka gani a wajen Hassan. Kyauta da taimakawa mabuƙata a duk lokacin da Hassan
ya samu dama ta zama hanyar rufin asirin da Allah ya ba shi da ɗaukaka fiye da shi abin da
ya kasance yana yi wa jama’a.
Hausawa na cewa ‘Alheri
gadon ƙaya.’ Duk mai aikata
alheri tabbas zai ga sakamako mai kyau ko ba-daɗe, ko ba-jima. Idan dai
Allah Ya taimake ka ka zanto mai kyakkyawar zuciya, ka zama babu abin da yake
cikin zuciyarka illa taimakawa mai neman taimako, to ka sha kuruminka, in Allah
Ya so daga ƙarshe sai ka ga sakamakon
alheri ya zo maka a lokacin da ba ka zaton hakan. Wannan ne ya faru da Hassan.
A yayin da ya dage wajen aikin alheri, tun yana ainihin garinsu, har ‘yan
uwansa ma sun so su raba shi da taimakon mabukata, amma ya ƙi. Allah Ya jarabce shi da
karayar arziƙi, ya zamanto ba shi da
komai, abincin da zai ciyar da iyalinsa ma babu. Ya zama abin zunɗe a wajen ‘yan uwa da
abokai. Kwatsam sai Allah Ya sake buɗa masa wata hanyar. Karayar arziƙi da ya samu a baya ba ta
hana shi ci gaba da taimakon mabukata ba, amma sai ya sake gari domin ganin
yadda mutanen garinsu suka kasance masu yi masa dariya a lokacin da ya samu
karayar arziƙi. Hassan ya ci gaba da
taimakon al’umma a garin da ya koma har ma hukuntan garin suka san ahlin kirkin
da yake aikatawa a garin. Wannan ne ya jawo Sarkin garin ya kusance shi domin
ya ga irin aikin alherin da Hassan yake yi da idanunsa. Ganin yadda Hassan yake
taimakawa al’umma ne ya sa Sarkin ya jawo shi a jika har ma yi masa sarauta a
garin. Haka masu iya magana suka ce ‘Idan Allah Ya taimake ka kaikuma ka
taimaki na baya gare ka.
6.1 Naɗewa
Babu shakka Imam ya yi
bajinta wajen fito da manufar Bahaushe dake ƙumshe cikin karin maganarsa
ta amfani da su a matsayin tubalin ginin labarinsa mai ƙumshe da tarbiyya da nasiha
da gargaɗi da hangen nesa ga al’umma
cikin raha da annashuwa.Wannan dabara ta taimaka wajen ƙara fito da martabar
harshen Hausa a idon duniya musamman ta fuskar adabi da harsunan al’ummomin
duniya ya zama ɗaya daga cikin sanadin da harshen Hausa ya samu gindin
zama a tsakanin manyan harsunan nahiyar Afirka.
Wannan salo da Imam ya yi
amfani da shi, ba haka kawai ya ƙirƙiro shi ba, yana da manufa, manufar kuwa ita
ce ya ankarar da al’umma irin muhimmancin da karin magana take ɗauke da shi a gare su ta
wajen tsaftace zamantakewa da faɗakawa da kuma nishaɗantarwa. Imam ya fito da
kyawun tunani dake ƙunshe cikin harshen Hausa a dunƙule masu ɗauke da kyawawan manufofi
da suke gyara halin mutum da kuma maganganun dake tsoratar da duk wani mai
aikata laifi a sarari ko a ɓoye. Haka kuma akwai karin maganar dake ƙoƙarin ƙarfafa gwuiwa da zaburar da
al’umma cewa babu wani abin kirki da yake samuwa sai fa idan an tashi tsaye da
nema. Akwai misalai da yawa da za a iya hakaitowa a cikin labarin musamman waɗanda suke ɗauke da kanun karin magana.
Idan an fahimci karin
maganar da Imam ya yi wa labarin kanu da shi, wato ‘magana jari ce,’ sai a ga
cewa ko shi kansa Imam ɗin, ya cancanci a jingina wannan karin magana
da shi. Dalili kuwa shi ne iya maganar ne ya zama silar ɗaukakar da Allah Ya ba shi.
Tarinsa ya nuna shi haziƙi ne tun kafin ma ya shiga makarantar boko,
wato tun lokacin da yake gaban mahaifinsa a garinsu Kagara. Ya yi karatun
addini mai zurfi a gaban mahaifinsa inda har harshen Larabci ya koya. Hazaƙarsa ne ma ta sa aka ɗauki shi aikin malanta a
yayin da ya kammala makarantar sakandare ta Katsina a matsayin malamin harshen
Ingilishi. Imam mutum na farko da masaurautar Katsina ta naɗa a matsayin sakataren
majalisar sarkin Katsina.
Manazarta
Abdullahi, I.M. (1995)
“Wasu Tubalan Ginin Littafin Magana Jari Ce”, Sashen
Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usman Ɗanfodiyo, Sakkwato.
Amin, M.L. (2002) “Hausa Metaphysical
World Ɓiew’: A paremeological Eɗpression. An unpulished Ph. D Thesis submitted to the Department
of African Languages and Cultures, A.B.U.Zaria.
C.N.H.N (2006) Ƙamusun Hausa.
Kano: Jami’ar Bayero.
Hassan S. (2012) “Ba a
mugun Sarki sai migun bafade’ Tsokaci daga Magana Jari Ce no
3 (There is no wicked King but a wicked courtier) Fiescript in honour of
Professor Ɗalhatu Muhammad Zaria.
Department of African Languages and Cultures, Ahmadu Bello University, Pp
376-386.
Imam, A. (1980) Magana Jari Ce. Zariya:
Northern Nigerian Publishing Company.
Imam, A. (1946) Tafiya Mabuɗin Ilimi: Zariya: Northern
Nigerian Publishin Company.
Jami’ar Bayero Kano (2013) Sababbin
Kalmomi: Ingilishi zuwa Hausa, Littafi Na Biyu. Zaria: Ahmadu Bello
University Press Limited.
Jez, B. (2003) Foreign
Influences and their Adaptation to the Hausa Culture in Magana Jari Ce by
Abubakar Imam in Studies of the African Languages and Cultures, No 33, 2023,
Stanislaw Pilaszewicz, University of Warsaw.
Mahuta, I. (1980) “Nason Alfulaila wa
laila cikin adabin Hausa, misalai daga Magana Jari Ce. B.A.
Hausa Usman Danfodio University, Sokoto.
Malumfashi, I. (2009) Adabin Abubakar Imam. IBM Printers,
No 11 Muri Road,Kaduna.
Malumfashi da Marafa (2014) Ƙamusun Karin Maganar Hausa. Garkuwa Publishers, Kaduna, Nigeria.
Mora, A. (1989) (ed): Abubakar Imam’s
Memoirs. Zaria: Northern Nigerian Publishing Company.
Musa, A. (1993) “Karin Maganar Magana
Jari Ce, Kundin Neman Digiri Na Farko, Sashen Harsunan Nijeriya da Afirka,
Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya.
Suleiman, I.I. (1990) “Morality in Imam’s Magana
Jari Ce, A Departmental Seminar Paper at Department of Nigerian and
African Languages, Ahmadu Bello University, Zaria.
Usman, M. (1998) “Tarsashin Adabin Baka A Magana
Jari Ce, Kundin Digirin Tsakiya, Sashen Harsunan Nijeriya da Afirka,Jami’ar Ahmadu Bello
Zariya.
Usman, M. (2014) “Man as A Greedy Being: A case
study of some stories in Magana Jari Ce. Journal of Liberal Arts, Department of Nigerian
Languages, Kaduna State University,Kaduna.
Usman, M (2023) “Karin
Magana A Tunanin Bahaushe Nazari Daga Magana Jari Ce
Na Abubakar Imam. Sashen Harsuna Da Aladun Afirka, Jami,ar Ahmadu
Bello Zariya
Wali, Z.N. (1976) “Nazari A Kan Littafin Magana
Jari Ce. Kundin Digirin Farko,Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar
Bayero, Kano.
Rataye
Litafi na 1.
1.
Magana
jari ce
2.
Ba
a fafe gora ranar tafiya
3.
Magana
jar ice
4.
Matambayi
ba ya ɓata
5.
Gobe
ma rana ce
6.
Baƙo da Tukura duka
Umbutawa ne
7.
Baya
ba zane
8.
‘Ana tsoron Inna’ in ji ‘ya’yan
mayya
9.
Banza
ta koriwofi
10.
Gani
ga wane ya ishi wane tsoron Allah
11.
Allah
abin tsoro, mutum ma abin tsoro n
12.
Rai
dangin goro ne, ban iska yake so
13.
Da
Tukura da Baƙo duka Umbutawa ne
14.
Ta
faru ta ƙare, an yi wa mai
dame ɗaya sata
15.
Sauri
ya haifi nawa
16.
Wayon
a ci an kori kare daga gindin ɗinya
17.
Mai
hali ba ya barin halinsa
18.
A
bar kaza cikin gashinta
19.
Zuwa
da wuri ya fi zuwa da wuri-wuri
20.
Gaba
siyaki baya damisa
21.
Yau
da gobe ba ta bar kome ba
22.
Ta
faru ta ƙare, an yi wa mai
dame ɗaya sata
23.
Kowa
ya daka rawar wani ya rasa turmin daka tasa
24.
Kau-da-bara
ba ta ci sai an haɗa da gociya
25.
So
hana ganin laifi
26.
In
ajali ya yi kira ko ba ciwo a je
27.
Kunar
baƙin wake
28.
Gani
ya kori ji
29. Duk abin da mutum ke
aikatawakomai daɗewa zai ga sakayya
30.
Kome
ka shuka shi za ka girba
31.
‘Yan
zamani sanin ku ba sanin halinku ba
32.
Abin
da ya yi Goje, shi ya yi Ƙaura
33.
Mai
rai ba ya rasa motsi
34.
Cin
danƙo har da su kaza
35.
Dabara
ita ce yaƙi ba ƙarfi ba
36.
Sarkin
yawa ya fi Sarkin ƙarfi
37.
Sarkin
yawa ya fi Sarki ƙarfi
38.
Soyayya
gamon jini
39.
Tsohon
doki sai mai shi
40.
Ungulu
ta koma gidanta na tsamiya
41.
Ba
a san inda rana za ta faɗi ba
42.
Aikata
alheri ga kowa sakayyarka na gun Allah
43.
Raina
kama ka ga gayya
44.
Raina
kama ka ga gayya
45.
Ɗan hakin da ka raina shi
ke tsole ma ido
46.
Ɗan-Adam tara yake bai
cika goma ba
47.
Baki
shi kan yanka wuya
48.
Abin
da ya ci Domaba ya barin Awai.
Littafi na 2
1 Ƙarfe duka ƙarfe ne amma ko cikin
karafaakwai azurfaakwai tagulla
2 Maza
dangin gujiya ne sai an fasa akan san bidi
3 In an bi daga-daga, na ƙurya ka sha kashi
4 In
laila ta ƙiya sai a koma basha
5 Cin ƙwan makauniya
6 Ta
safe ta raggo, in safiya ta yi sai mu mutanen Sarki
7. Da muguwar rawa gwamma ƙin tashi
8. Ba
kullun ake kwana a gado ba
9. Gidan
ma-ƙi-gudu da kara a kan nuna
10. Gani
ya kori ji
11. Me
ya raba dambe da faɗa?
12. Dare ɗaya Allah ka yi Bature
13. Kowa
ya bar gida gida ya bar shi
14. An
yi ba a yi ba kenan, juyin gatar fara
15. Sa’a
ta fi manyan kaya
16.
Akwai
ranar ƙin dillanci, ranar da
akuyar mai gari ta ɓata
17.
Abokin ɓarawo ɓarawo ne
18.
Bakin
da Allah Ya tsaga ba Ya hana mashi abinci
19.
An ƙi cin biri an ci
dila
20.
A ɓoye wa abokin kuka
mutuwa?
21.
A
bari ya huce shi ke kawo rabon wani
22.
Me
ya gama kifi da kaska?
23.
Zaman
duniya iyawa ne, kowa tasa ta fisshe shi
24.
Zato
zunubi ko da ya zama gaskiya
25.
Ɗan kaciya in bai ci kaza
ba, ai ba ya yin bara
26.
Sata
gidan ɓarawo rance
27.
Kowa
da kiwon da ya karɓe shi, maƙwabcin mai Akuya ya sai
kura
28.
Ana
zaman ƙarya, baƙauye ya zo birni ya
tambayi masussuka an ce babu
29.
Ka
zama dungu, a bar ka ana ƙyamar ka, a yanke ka ba a samun sabo
30.
In
ka ji makaho ya ce ‘a yi wasan jifa,’ ya taka dutse ne
31.
Kora
da hali ya fi kora da kara
32.
Ruwa
baya tsami banza
33.
Yaro
da gari abokin tafiyar manya
34.
Ko
kura ta tsufa ta fi gaban kare
35.
Ba
kullun ake kwana a gado ba
36.
Baki
shi kan yanka wuya
37.
Rashin
sani ya fi dare duhu
38.
Ƙuda wajen kwaɗayi a kan mutu
39.
Wuri
ya ja wuri
40.
Kwaɗayi mabuɗin wahala
41.
Allura
ta tono garma
42.
Kowa
ya ɗebo da zafi bakinsa
43.
Kowa
ya yi ƙaryar dare gari zai
waye
44.
Baki
shi kan yanka wuya
45.
Ta
faru ta ƙare an yi wa mai
dame ɗaya sata
46.
Ba
kullun ake kwana a gado ba
47.
Allah
Ya yi masa gyaɗar dogo
48.
Banza
ba ta kai zomo kasuwa
49.
Raɓa na raukar raɓa
50.
Akwai
ranar ƙin dillanci ranar da hajjar mai
gari ta ɓata
51.
Ana wata ga wata, ana kuɗin ƙasa gari ya watse
52.
Ba
a mugun Sarki sai mugun bafade
53.
An
yi gudun gara an faɗa zago
54.
Kama
da wane ba wane ne ba
55.
Ta
Malam ba ta wuce amin
56.
Na
gaba ya yi gaba na baya sai labari
57.
Komai
ta tafasa ta ƙone
58.
Sarkin
yawa ya fi sarkin ƙarfi
59.
Ba
kullun rana take Juma’a ba
60.
Hankali
ke gani ido gululu ne
61.
Abin
da ya koro ɓera ya faɗa wuta ya fi wutar zafi
62.
Mahaƙurci mawadaci
63.
Yau
da gobe sai Allah
64.
Mahaƙurci mawadaci
65.
Komai
ta tafasa ta ƙone
66.
Bayan
wuya sai daɗi
67.
Gaba
da gabanta maibaggu ya ga haƙorin uwarzana
68.
Kunne
ya girmi kaka
69.
Kowa
ya bar naman kura ba zai sa kura ta bar nasa ba
70.
Son
a sani yaji da kwarin miji
71.
Gajin
haƙuri shi ya kawo mai aka
shuka
Littafi na 3
1. Magana jari ce
2.
Aiki
da zato zunubi ne ko ya zama gaskiya
3.
Girma
da arziƙi ita ta sa jan sa da
abawa
4.
Bara
na yi wake bana na yi harawa
5.
Yaro
ko da ganin birni ya san ya fi garinsu
6.
Kada
kaza ta yi murna don ta ga ana jan hanjin‘yar uwa tata
7.
Jifa
in ta wuce kanka ko kan wa ta faɗa
8.
Hauka
da naɗe-naɗe, mutuwa ta ga ladan
9.
Idan
bori gaskiya ne ya faɗa rijiya
10.
Kashin
birbiri da faɗuwa da naɗewa
11.
A
bar kaza cikin gashinta
12.
Ɓatan ɓakatantan
13.
Na
san a rina, an saci zanen mahaukaciya
14.
Ba
rabo ba, ɗan wabi ya mutu
15.
Na
san a rina an saci zanen mahaukaciya
16.
Girman
kai rawanin tsiya
17.
Rabo
rababbe, tsuntsu daga sama gasasshe
18.
Gaba
damisa baya siyaki
19.
Da
muguwar rawa gwamma ƙin tashi
20.
Sauri
shi kan haifi nawa
21.
Zuwa
da wuri ya fi zuwa da wuri-wuri
22.
Tsintar
dami a kala
23.
Ba
ta rinu ba ta yi shuɗi
24.
Yi
wa shakiyyi shakiyanci gyaran akayau ne
25.
Yau
ci nan sha nan kura ta kashe mai gwaiwa
26.
Shan
ruwa ya fi barinsa
27.
Akwai
ranar ƙin dillanci ranar da
akuyar mai gari ta ɓata
28.
Wuri
ya ja wuri
29.
Zomo
ba ya fushi da makashin sa sai maratayi
30.
Kowa
ya ci ladan kuturu dole ya yi masa aski
31.
Munafunci
dodo ya kan ci mai shi
32.
Komai
ta fanjama fanjam
33.
Baki
shi kan yanka wuya
34.
Mai
rabon shan duka ba ya jin kwaɓo sai ya sha
35.
Mayar
da mashi ran gaba tsoro ne
36.
Ramuwar
gayya ta fi gayya zafi
37.
Tsugune
ba ta ƙare ba an sayar da kare
an sai biri
38.
Tsuntsu
mai wayau a ƙoto ake kama shi
39.
Rama
cuta ga macuci ibada
40.
Idan
mutum ya ce zai haɗiye gatari sai a sakar masa ƙota
41.
Da
hannu kan san girma
42.
Ƙashin bakin tukunya ka
shiga ka ƙi fita
43.
Tsintattar
mage ba ta mage
44.
Zomo
ba ya fushi da makashinsa sai maratayinsa
45.
Ga ƙoshi ga kwanan yunwa
46.
Tsuguni
ba ta ƙare ba an sai da kare an
sai biri
47.
Dalilin
kaza kaɗangare kan sha ruwan
kasko
48.
Sa’ar
Sarki ta fi fatauci, ta ko fi a duka gona noma
49.
Rasin sani ya fi dare duhu
50.
Garin
baƙo kowa Sarki
51.
Duk ƙoƙarin kura yana ga haƙoranta
52.
Kora
da hali ta fi kora da kara
53.
Gamo
da Katar
54.
Zato
zunubi ko ya zama gaskiya
55.
Mai
arziƙi ko a kwara ya sayar da
ruwa
56.
Yaro
da gari abokin tafiyar manya
57.
Taron
Kwara da Ama
58.
Da
birin da ke dawa da wanda ya yi makuwa duk dawa za su kwana
59.
Riga-kafin
mugunta rashin yi wa wani
60.
Randa
kina ɗaka Allah na ba ki ruwa
ki sha
61.
Duk
wanda
ya ji ƙan wani Allah Ya ji kan
sa
62.
Mutum
dangin gwanda ne, ba ya jimirin
zungura
63.
Kowa
ya ce yana iya haɗiye gatari sai a sakar masa ƙota
64.
Bakin
da Allah Ya tsaya ba Ya hana masa abinci
65.
Duk
bori ɗai ake wa tsafi
66.
Tsuntsu
duka dai na cin kashi amma na angulu ake gani
67.
Cin
danƙo har da su kaza
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.