1) Shin mai azumi zai iya asuwaki?
Amsa:
Mai azumi zai iya asuwaki domin asuwaki baya karya azumi saide a nisanci yin asuwaki da ɗanyan icce.
2) Bruch (Bros) yana
karya azumi?
Amsa:
Na am yana karya
azumi idan an haɗiye shi saboda kamar
ansha wani abu ne.
3) Na yi mafarki
bayan na koma bayan asuba azumi na yana nan ko ya karye?
Amsa:
Azumi yana nan
mafarki baya karya azumi sai idan mutum shi yayi wasa ko kallon abu har ya
fitar da maniyi amma idan mutum yayi mafarki sai da ya tashi yaga maniyi to zai
yi wanka azumin sa yana nan idan kuma bai ga komi ba to azumin sa yana nan ba
zai yi wanka ba.
4) Ina azumi saura
minti 1 a sha ruwa jini ya zo min azumin na ya karye ko yana nan?
Amsa:
Azumi ya karye dalili
kuwa shi ne ba sha ruwa ba kuma lokacin shan ruwa bai yi ba saboda azumi ya
karye wannan azumin babu shi.
5) Ina azumi saida
aka sha ruwa jini ya zo min ya azumin ya ke?
Amsa:
Tambayar guda ce da
ta sama saide wannan ans ha ruwa jini yazo idan ansha ruwa jini yazo to azumi
yayi bai lalace ba saboda saida aka saha ruwa jinin yazo shi.
6) Bayani akan mai
ciki da mai shayarwa za su iya yin azumi ko baza su iya ba?
Amsa:
Mace mai ciki da mai
shayarwa dukan su idan ba za su iya azumi ba to kar su yi idan mai ciki tana
tsoron yaron cikin ya sha wahala haka itama zata sha wahala da mai shayarwa
dukan su za su ciyar idan an sha ruwa ko kafin asha ruwa za su bada kwana guda
na abinci mutum guda wanda baida abinda zai yi buɗa baki shi za su ba idan ba abinci to
a bashi kuɗi shidai wunin wannan
ksr ya wuce ba a ba mutum guda ba.
A takaice mai ciki da
mai shayarwa za su ciyar kuma ba za su rama ba.
7) Mai al'ada zata yi
azumi da sallah ko ba zata yi ba?
Amsa:
Mai jinin al'ada (jinin
haila) idan jini yazo mata har aka yi kwana 7 bai tsayawa ba sai daga baya ya
tsaya ma ta to idan jinin yazo ba zata yi sallah ba kuma ba zata yi azumi ba
sai jinin ya tsaya ma ta za ta yi kuma ba zata ciyar ba bayan sallar azumi ko
bayan Ramadan ta rama adadin wanda tasha.
8) Mace zata iya shan
maganin tseda jinin al'ada dan azumintar azumin Ramadan ko zuwa kiyamul laili?
Amsa:
Eh idan har likita ya
tabbatar maganin baida illa.
Amma babban malamin
mu Sheikh Muhammad Saleh Al-Usaimine Allah masa rahama bai bada shawarar mace
tasha maganin tseda al'ada ba saboda mafi yawa idan suka sha yana rikitar musu
da zuwan jini ko jinin ya ɗauke ya daina zuwa gaba ɗaya.
Dan haka nima bana
bada shawarar Mace mai al'ada tasha magani wai dan yin azumi ko kiyamul laili
wannan Allah ne ya yi ma ƴaƴa mata rangwame dan haka ki hakura haka Allah ya so.
9) Wanda yake ulcer
ko ciwo wanda bai iya hakuri duk awa zaisha ruwa ko abinci ya zai yi)
Amsa:
Na am zai ciyar idan
an tabbatar ba zai samu sauƙi ba ko anyi magani shiru idan ya
ciyar ba sai ya rama ba.
Amma aji tsoron Allah
wasu ulcer su ko ciwon su baha tashi sai Ramadan yazo Allah yana ganin ku dan
haka idan kunyi ƙarya Allah ya sani.
Wansa bai iya azumi
mai rashin wanda zai cutu ko galaɓaita shi ma zai ciyar haka mai rashin lafiya
mai tsanani da mai shayarwa idan tana tsoron yaron ta zai cutu da ita mai ciki
duk za su ciyar amma magana mafi inganci idan sun ciyar ba za su rama ba.
10) Na kwana da
janaba sai na tashi na yi sahur amma banyi wanka ba sai bayan na yi sahur na yi
wankan ya azumi na yake?
Amsa:
Azumin ka yayi kuma
wannan yana samun Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama kamar yadda yazo a
hadisi:
عَنْ
عَائِشَةَ وَأُمُّ سَلَمَة رَضِيَ اللهُ عَنْهُمَا: "أَنَّ رَسُولَ اللهِ
صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ كَانَ يُدْرِكُهُ الْفَجَرَ وَهُوَ جُنُبٌ مِنْ
أَهْلِهِ ثُمَّ يَغْتَسِلُ وَيَصُومُ." (رواه البخارى)
An karbo daga Aisha
da Ummu-Salama (R.A) suka ce, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya
kasance alfijir yana riskarsa yana mai janabar saduwa da iyalansa, sannan ya yi
wanka kuma ya yi Azumi. (Bukhari ne ya rawaito).
Idan mutum ya sadu da
iyalin sa ko kuma yayi mafarki sai kuma ya tashi lokacin sahur zai yi sahur
insa bayan yayi sai yayi wanka yayi sallar sa.
Amma bayan mutum yayi
sahur anyi kiran sallah na biyu baya hallata su sadu da matar sa kuma haramun
ne azumi]ana karyewa kai tsaye kuma kaffara za su su duka.
Allah sa mu amfana da
juna.
Ku yi tarayya cikin
lada wajan yaɗawa domin ƴan uwa su amfana.
*RUBUTAWA:
Ɗan uwan ku a Muslunci:
Ibnul Islam Bachir
Mamane Alhaji Yakuba Abu Muhammad✍️
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.