𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaikum malam khamis Muna godiya sosai. Allah ya saka muku da alkhairi Ameen. Tambaya ta anan shi ne Yaushe ne lokacin buɗa baki (shan ruwa) kuma wacce addu'a ake yi lokacin buɗa baki?
LOKACIN BUƊA BAKI DA ADDU'A BUƊA BAKI
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus Salam
Warahmatullahi Wabarkatuhu.
Lokacin buɗa baki yana tabbata
ne da zarar rana ta faɗi. Dalili kuwa shine,
hadisin da aka karbo daga Malik, daga Abdurrahman ɗan harmala al Aslami,
daga Sa'eed ɗan al Musayyabi, ya
ce: Lallai Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam, ya ce: "Mutane baza su
gushe ba suna cikin alkhairi matuƙar za su gaggauta yin
buɗa-baki"
Muwatta Malik (640)
Yana daga cikin
sunnah ta Manzon Allah sallallahu alaihi wasallama yin gaggawa wajen buɗa-baki idan ya kai
azuminsa, har ma yake kwaɗaitar damu cewa mu ma
muyi koyi dashi wajen yin gaggawar buɗa-bakin sabida tarin alkhairin dake cikin yin
hakan.
Haka hadisin da aka
karbo daga Abdullahi Ibn Abī Auf ya ce: "ya kasance tare da Manzon Allah
Sallallahu alaihi Wasallam a lokacin tafiya suna azumi, sai rana ta faɗi, sai Manzon Allah
Sallallahu alaihi Wasallam ya ce da wani daga cikin sahabbansa ya sauka ya
shirya musu kayan buɗa baki sai sahabin ya
ce: "Ya Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam da sauran rana, akayi haka
har sau uku, Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam na cewa dashi ya shirya
musu abin buɗa baki. Daga karshe
bayan sun kammala sai Annabi Sallallahu alaihi Wasallam ya ce: “Idan kuka ga
dare ya gabato daga nan (wato rana ta faɗi), haqiqa mai azumi ya buɗe bakinsa (ana nufin
koya sha ruwa ko bai sha ba)
Bukhari da Muslim suka
ruwaito shi.
Daga Ansa bn
Malik(RA) ya ce: Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ya kasance yana yin
buɗe baki kafin ya yi
sallah da danyen dabino, idan bai samu danyen dabino ba sai yayi da busassun
dabino, idan kuma bai samu busasshen ba, sai ya kurɓi wasu kurɓi na ruwa".
Tirmidhi ya ruwaitoshi.
Idan ka kai azuminka,
ka jaraba fara yin buɗa-baki da dabino, ko
ruwa, tabbas za kaga amfanin hakan, domin shawara ce daga bakin wanda ba ya
cutarwa.
Amma don ka yi buɗa-baki da wani abu saɓanin dabinon ko ruwa,
wannan ba laifi kayi ba, domin ai Manzon Allah sallallahu alaihi wasallama ba
umurni yake ba ka ba a cikin wannan hadisin, shawara ce dai kawai ya ba ka,
amma za ka iya yin buɗa-bakinka da duk abun
da kake sha'awar ci idan lokacin buɗa-bakin ya yi.
«ADDU'AR BUƊA BAKI»
ذَهَبَ
الظَّمَأُ وَابْتَلَّتِ الْعُرُوقُ، وَثَبَتَ الأَجْرُ إِنْ شَاءَ اللَّهُ
FASSARA: Ƙishirwa ya tafi, an
yayyafawa jijiyoyi ruwa, kuma lada ya tabbata in Allah ya so.
(Abu Dawud)
ADDU'A IDAN MUTUM
YA YI BUƊA BAKI A GIDAN WASU MUTANE:
أَفْطَـرَ
عِنْدَكُم الصّـائِمونَ وَأَكَلَ طَعامَـكُمُ الأبْـرار، وَصَلَّـتْ عَلَـيْكُمُ
الملائِكَـة.
FASSARA: Allah ya sa masu
azumi su yi buɗa baki a wajenku,
kuma Allah ya sa nagartattun bayi su ci abincinku, kuma Allah ya sa Mala'iku su
yi muku addu'a.
(Abu Dawud 3/367, Ibn
Majah 1/556)
Mai azumi a lokacin
da zai yi buɗa baki (kafin ya ci
ko ya sha wani abu) addu'arsa karɓabbe ne ba a mayar da shi.
(Tirmidhi)
Ƴan uwa haƙiƙa addu'armu a wajen
buɗa baki karɓaɓɓiya ce, saboda haka
muyi addu'o'i muna masu sakankancewar an karɓa mana, amma mu sani cewa Allah baya karɓar addu'ar wanda
zuciyarsa rabkananniya ce mai wasa daga ambaton Allah.
Allah Ta'ala ya amsa
mana.
Zauren Fatawoyi Bisa
Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
ƘARIN BAYANI
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.