𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Shin Mace Mai-Ciki za ta iya yin Jinin-Al'ada ko batayi? Sannan a Shari'ance meye hukuncin wannan jinin in taga ya zo mata??
𝐀𝐌𝐒𝐀❗
Alal-Haƙiƙa Malamai sun yi Saɓani tun adacan
harkuma zuwa wannan zamani damuke cikinsa, dangane da hukuncin jinin da Mace
Mai-Ciki za ta gani, ansamu maganganun Malamai kamar Ƙauli-2 dangane da
wannan Mas'ala.
1. Ƙauli nafarko shi ne,
Malaman da ke Mazhabin MALIKIYYA da SHAFI'IYYA, da kuma irin su
Shaykhul-Islam-Ibn-Taimiyya tareda Shaykh-Salihul-Usaimin, Sunaganin cewa Mace
Mai-Ciki tana iya yin Jinin-Al'ada, daga cikin Dalilansu sunkafa Hujja dacewa
antambayi A'isha-Matar-Mαиzoи Aʟʟαн( Sallallahu Alaihi
Wasallam) cewa idan Mace Mai-Ciki taga jini ya za ta yi? Sai tace za ta dena
Sallah harsai taga jinin yaɗauke, kuma suka ce a Babin-Al'ada Mace tafi Namiji ƙwarewa aharkar domin
ita daga jikinta jinin yake fita Saɓanin Namiji, Sannan kuma suka ce A'isha tafaɗi wannan maganane
agaban wasu daga cikin Sahabbai kuma babu wanda ya yimata Inkari (musu) akan
hakan, danhaka suka ce idan Mace Mai-Ciki taga jini to in dai har jinin ya zo
matane adaidai lokacin da tasaba Jinin-Al'ada yana zuwa mata Sannan kuma ya yi adadin
kwanakin da tasaba yana yi yaɗauke suka ce to Jinin-Hailane, ko kuma ya kasance jinin ya
zone da irin Siffar Jinin-Haila kamar yadda Aηηαвι( Sallallahu Alaihi Wasallam)
yake cewa:
" ﺇﻥ ﺩﻡَ
ﺍﻟﺤﻴﺾ ﺃﺳﻮﺩ ﻳﻌﺮَﻑ "
MA'ANA: Lallai
Jinin-Haila baƙine kamar yadda akasanshi.
Danhaka Jinin-Haila
yakanzo da Siffofi kamar haka: Launin-Baƙi-Baƙi, Mai-Kauri, Mai-Ƙarni, sannan kuma
galibi Mace takanji wasu alamu kafin jinin ya fita, danhaka ke nan in dai Mace
taga waɗanna Siffofi to
Jinin-Hailane ya zo mata ko da kuwa tana da ciki.
2. Ƙauli nabiyu kuma shi
ne, Malaman da ke Mazhabobin HANAFIYYA da kuma HANABILA da mafi yawa daga cikin
Malamai Ahlul-Ilmi, suna ganin cewa babu yadda za'ayi a ce Mace Mai-Ciki ta yi Jinin-Haila,
daga cikin Dalilansu sunkafa Hujja da wata ruwayar da'aka sake samu daga wajen
ita A'isha ɗindai tana cewa idan
Mace Mai-Ciki taga jini to kawai za taci gaba dayin Sallartane, Sai wannan
yanuna cewa ashe Sahabbai ba su yi Ijma'i akan wannan Mas'alarba kamar yadda
wasu suka faɗa, Sannan suka sake
kafa Hujja da Hadisin da Mαиzoи Aʟʟαн ( Sallallahu
Alaihi Wasallam) ya ce da Umar-Ɗan-Kaɗɗab lokacin da ɗansa Abdullahi-Ɗan-Umar yasaki
Matarsa tana cikin Jinin-Haila, sai Aηηαвι( Sallallahu Alaihi
Wasallam) ya ce da Umar-Ɗan-Kaɗɗab:
" ﻣﺮﻩ ﻓﻠﻴﺮﺍﺟﻌﻬﺎ
ﺛﻢ ﻟﻴﻄﻠﻘﻬﺎ ﻃﺎﻫﺮﺍ ﺃﻭ ﺣﺎﻣﻼ ، "
MA'ANA: (Ya kai Umar)
ka umarceshi (Abdullahi-Ɗan-Umar) dacewa yadawo da'ita (harsai ta yi tsarki)
Sannan daga baya inyaso sai yaketa (amatsayin) mai tsarki ko kuma mai ciki.
Da kuma Hadisin da
Aηηαвι( Sallallahu Alaihi Wasallam) Yake cewa:
" ﻻ ﺗُﻮﻃَﺄُ
ﺣَﺎﻣِﻞٌ ﺣَﺘَّﻰ ﺗَﻀَﻊَ ، ﻭَﻻ ﻏَﻴْﺮُ ﺫَﺍﺕِ ﺣَﻤْﻞٍ ﺣَﺘَّﻰ ﺗَﺤِﻴﺾَ ﺣَﻴْﻀَﺔً، "
MA'ANA: ba a saduwa
da (baiwar da aka ribaceta awajen yaƙi) idan tana da ciki
harsai in ta haife abin da ke cikinta, hakanan ba a saduwa da (baiwar da
akasayeta) wacce ba ta da ciki harsai anjira ta yi (istibra'i) da zuwan jinin
haila sau ɗaya.
Sannan kuma suka ce
Shari'a ta sanya a yi Istibra'ine ta hanyar yin jini ɗaya, ita kuma Idda ta
hanyar yin tsarki-3, amma sai aka ce ita Mace Mai-Ciki Iddarta shi ne tahaife abin
da ke cikintane kawai kamar yadda Aʟʟαн( ﷻ) Yake cewa:
" ﻭَﺃُﻭﻟَﺎﺕُ
ﺍﻟْﺄَﺣْﻤَﺎﻝِ ﺃَﺟَﻠُﻬُﻦَّ ﺃَﻥ ﻳَﻀَﻌْﻦَ ﺣَﻤْﻠَﻬُﻦَّ "
MA'ANA: (Matan)
dasuke da ciki sukuma Iddarsu shi ne lokacin dasuka haife abin da ke cikinsu.
Sannan kuma Malamai suka
ce ai Mace tana iya gane cewa tasamu cikine tahanyar yankewar Jinin-Hailarta,
kuma da a ce Mai-Ciki tana Jinin-Haila, to da itama sai yazama hukuncinta ya zo
daidai da waɗanda basu da ciki ya
yin da aka sakesu, kuma kowa yasani cewa idan akasaki Mace da ciki ko da ta yi Jini-3
ba zai yiwu a ce shi ke nan taƙare iddartaba, dole sai in ta haihaife
abin da ke cikinta sannan taƙare Iddarta.
Bayagahaka kuma suka
ce asali dama jini yana fitowane daga mahaifar Mace a sakamakon cewa bakomai a
cikin mahaifar, to amma daga lokacin da Mace tasamu ciki gaba ɗaya wannan jinin
antoshe masa wurin zamansa a mahaifar, kuma har ilayau wannan jinin shi ne
za'amayar yazama abincin shi wannan Ɗan-Tayin da ke cikin
mahaifar ita wannan Mata.
Wannan shi ne bayani
aɓangaren abin da
yashafi Shari'a ke nan, amma aɓangaren abin da yashafi kiwon lafiya abisaga bincike na
Likitanci gaba ɗayan Likitoci sun yi
Ijma'i akancewa abu ne dayake mai matuƙar wahala aga
Mai-Ciki ta yi Jinin-Haila, danhaka Malamai suka ce idan Mai-Ciki taga jini ya
zo mata, to idan jinin ya zone kafin ta haihu da kwana-2 ko 3, to wannan
Jinin-Haihuwane, amma idan Mai-Ciki taga jini kuma ba daf da haihuwa ya zoba to
kawai na cutane, amma ba Jinin-Haila ba ne, danhaka za taci gaba ne dayin
dukkan wata Ibadabarta.
Ko Shakka babu cewa
wannan maganar tafi inganci kamar yadda mafi yawa daga cikin Malamai suka
rinjayar da Ƙaulin cewa Mace-Mai-Ciki ba ta Jinin-Al'ada.
шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ
Doмυп пεмαп ƙαяıп
вαчαпı sαı αdυвα
шαɗαппαп ʟıтαттαғαı
καмαя нακα:
" ﺍﻹﺧﺘﺒﺎﺭﺍﺕ
" ( ﺹ 30 )
" ﺷﺮﺡ ﺍﻟﻤﻤﺘﻊ
" ( 1/469 )
" ﺗﻨﻘﻴﺢ
ﺍﻟﺘﺤﻘﻴﻖ " ( 1/414 )
" ﺍَﻟْﻤُﻐْﻨِﻰ
ﻟِﺈِﺑْﻦِ ﻗُﺪَﺍﻣَﺔ " ( 1/262 )
AMSAWA
Mυѕтαρнα Uѕмαи
08032531505
Zauren Fatawoyi Bisa
Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.