Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Cin Yankan Kirista

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Kiristoci ne suka yanka Dabba daga Coci Suka kawo mana shin ya halatta mu ci? Shin cin yanke-yanken Kiristoci a wannan zamani namu na yau yana halatta, duk kuwa da cewa hanyoyin yanka a wurinsu sun yawaita, watau kamar yin amfani da injuna, da kuma abubuwa masu daskarar da kwakwalwa a wurin yankan?

𝐀𝐌𝐒𝐀

Cin yanke-yankensu yana halatta, matukar dai ba a san da cewa an yanka dabbar ne ta hanyar da ba ta dace da Shari'a ba, saboda asalin lamari shi ne halaccin cin sa, kamar dai yankan Musulmi, saboda faɗin Allah Maɗaukaki:

وَطَعَامُ الَّذِينَ أُوتُوا الْكِتَابَ حِلٌّ لَكُمْ وَطَعَامُكُمْ حِلٌّ لَهُمْ

Da abincin waɗannan da aka ba su littafi halal ne yake a gare ku, kuma abincin ku halal yake gare su. (Surah Al-Maa’idah: 5).

Ya halatta muci yankan da Kirista ko Yahudawa suka yanka. Amma da sharadi kamar haka:

1. Ya zamto yankan basu yishi domin wanin Allah ba. Saboda faɗin Allah (swt):

حُرِّمَتْ عَلَيْكُمُ الْمَيْتَةُ وَالدَّمُ وَلَحْمُ الْخِنْزِيرِ وَمَا أُهِلَّ لِغَيْرِ اللَّهِ بِهِ وَالْمُنْخَنِقَةُ وَالْمَوْقُوذَةُ وَالْمُتَرَدِّيَةُ وَالنَّطِيحَةُ وَمَا أَكَلَ السَّبُعُ إِلَّا مَا ذَكَّيْتُمْ وَمَا ذُبِحَ عَلَى النُّصُبِ وَأَنْ تَسْتَقْسِمُوا بِالْأَزْلَامِ ۚ ذَٰلِكُمْ فِسْقٌ ۗ الْيَوْمَ يَئِسَ الَّذِينَ كَفَرُوا مِنْ دِينِكُمْ فَلَا تَخْشَوْهُمْ وَاخْشَوْنِ ۚ الْيَوْمَ أَكْمَلْتُ لَكُمْ دِينَكُمْ وَأَتْمَمْتُ عَلَيْكُمْ نِعْمَتِي وَرَضِيتُ لَكُمُ الْإِسْلَامَ دِينًا ۚ فَمَنِ اضْطُرَّ فِي مَخْمَصَةٍ غَيْرَ مُتَجَانِفٍ لِإِثْمٍ ۙ فَإِنَّ اللَّهَ غَفُورٌ رَحِيمٌ

An haramta muku mũshe da jini da nãman alade da abin da aka ambaci sũnan wanin Allah a gare shi, da mãƙararriya da jefaffiya da mai gangarõwa da sõkakkiya, da abin da mãsu dãgi suka ci, fãce abin da kuka yanka, da abin da aka yanka a kan gunki (shĩ ma an haramta). Kuma kada ku yi rabo da kibiyoyi na cãca wannan fãsiƙanci ne. A yau waɗanda suka kãfirta sun yanke ƙauna daga addininku. Sabõda haka kada ku ji tsõronsu kuma ku ji tsõroNa. A yau Nã kammalã muku addininku, Kuma Nã cika ni´imaTa a kanku, Kuma Nã yarda da Musulunci ya zama addini a gare ku. To, wanda aka sanya wa lalũra a cikin yunwa mai tsanani, bã yana mai karkata zuwa ga wani zunubi ba, to, lalle ne Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai. (suratul Ma'idah aya ta 3).

2. Ya zamto sunan Allah suka ambata ya yin da za su yanka dabbar. Idan suka yanka da Sunan Jesus ko Holy spirit ko sunan wani pastor, to ba za a ci ba. Allah (swt) yana cewa:

وَلَا تَأْكُلُوا مِمَّا لَمْ يُذْكَرِ اسْمُ اللَّهِ عَلَيْهِ

Kada ku ci daga abin da ba a ambaci sũnan Allah ba a kansa. (suratul An'am ayah ta 121).

3. Ya kasance abin da suka yanka ɗin baya daga cikin irin dabbobin da Allah ya haramta mana. Misali, alade ko kare ko jaki ba zai halatta aci ba ko da sun yanka shi tare da ambaton sunan Allah.

Amma bai halatta Musulmi ya ci abin da 'yan addinin Buddah ko hindu suka yanka ba. ko da sun ambaci sunan Allah ya yin da za su yanka dabbar.

Sheik Uthaimeen ya ce cikin littafinsa Ash-Sharhul Mumtii 12/148:-

ﻓﺎﻟﺤﺎﺻﻞ: ﺍﻥ ﺍﻟﺬﻱ ﻋﻠﻴﻪ ﺟﻤﻬﻮﺭ ﺍﻫﻞ ﺍﻟﻌﻠﻢ ﺍﻥ ﻣﻦ ﺗﺪﻳﻦ ﺑﺪﻳﻦ ﺍﻫﻞ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻭﺍﻧﺘﺴﺐ ﺍﻟﻴﻬﻢ ﻭﻟﻮ ﻛﺎﻥ ﻳﻘﻮﻝ ﺑﺎﻟﺘﺜﻠﻴﺚ ﻓﺎﻧﻪ ﺗﺤﻞ ﺫﺑﻴﺤﺘﻪ، ﻭﻳﺤﻞ ﻧﻜﺎﺣﻪ

Ma'ana: ((A takaice dai: Abin da majoratin masu ilmi suka ce shi ne duk wanda ya yi Addini da addinin Ahlul kitabi, ya kuma danganta kansa zuwa gare su ko da kuwa yana cewa Allah uku ne, to lallai ne cin wannan yankan halal ne, kuma auren su halal ne)).

Sa'annan Al Imamul Dabarani, Abul Dar'da, wata an yi masa Fatawa akan cin Yankan Kirista, suka ce masa Kiristoti ne suka yanka Dabba daga Coci Suka kawo mana shin ya halatta mu ci? sai da ya girgiza kansa ya ce Allah yafe mana, sai ya tambaye su shin su ɗin ba Ahlul-Ƙitabbi ba ne? Sai suka ce ahlul-ƙitab ne, sai ya ce ai Abincin su halal ne, sabida haka cewar ba a San ya suka yanka ba a Ina suka yanka, duk wannan ba hujja ba ne na nuna Haramcin cin sa ba. Kawai in kana Bukata ka ci in ba ka Bukata ka bari, shi ke nan shin ba Allah ya halatta mana cin abin Yankan su ba? Mun yi bayanin Ayar jiya a Dayan Fatawar mu, sa'annan Duk Imaninka duk Tsarkinka duk Kyan-Kyaminka, shin mun Kai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam ne? Duk Ayar da mutum zai karanta ko ya fassara ka tsaya ka dubi ya rayuwar Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) yake?

Har kullum Ahlus Sunnah wal Jama'ah a duk inda suke suna gina Addinin su ne a kan abin da ya tabbata daga Alkur'ani Mai girma da kuma ingantattun hadithan Annabi mai tsira da amincin Allah masu daraja. Amma saɓanin su, su kan gina Addinin su ne kawai a kan abin da ya dace da son zuciyar su.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments