𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalaamu Alaikum Wa Rahmatul Laah. Malam, da gaske ne cewa wai akwai hadisin da Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce, ba zai yi shekaru dubu biyu (2000) a ƙasa ba za a yi Tashin Ƙiyamah?
TASHIN ƘIYAMAH
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus Salaam
Wa Rahmatul Laahi Wa Barakaatuh.
A gaskiya ban san
wannan hadisin ba, sai dai ko in mun tuntuɓi malamai.
Daga baya an nuna
mini kuma na ga:
Al-Imaam As-Suyuutiy
(Rahimahul Laah) a cikin Al-Kashfu An Mujaawazati Hazihil Ummatil Alfa ya
ambaci cewa:
فَقَدْ
كَثُرَ السُّؤَالُ عَنِ الْحَدِيثِ الْمُشْتَهَرِ عَلَى أَلْسِنَةٍ ، أَنَّ
النَّبِيَّ - صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ - لَا يَمْكُثُ فِي قَبْرِهِ أَلْفَ
سَنَةٍ
Haƙiƙa! Tambaya ta yawaita
a kan hadisin da ya shahara a kan waɗansu harsuna cewa: Annabi (Sallal Laahu
Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ba zai zauna a cikin ƙabarinsa tsawon
shekaru dubu ɗaya ba.
Sai kuma ya bayyana hukuncinsa
a kan wannan riwayar, ya ce:
وَأَنَا
أَجِيبُ بِأَنَّهُ بَاطِلٌ ، لَا أَصْلَ لَهُ
Kuma ni ina bayar da
amsa cewa: Shi lalatacce kuma ɓataccen hadisi ne, ba shi da wani asali.
Kuma Al-Imaam Ibn
Al-Qayyim (Rahimahul Laah) a cikin Al-Mannaarul Muneef Fis Saheeh Wad Da’eef ya
faɗa, a inda yake bayar
da amsa a kan wata fatawa cewa:
وَسُئِلْتُ:
هَلْ يُمْكِنُ مَعْرِفَةِ الْحَدِيثِ الْمَوْضَوعِ بِضَابِطٍ مِنْ غَيْرِ أَنْ
يُنْظَرَ فِي سَنَدِهِ
Kuma an tambaye ni:
Shin ko zai yiwu a iya sanin hadisin ƙarya ƙirƙirarre ta amfani da
waɗansu ƙa’idoji,
ba tare da an kalli isnadinsa ba?
Shi ne a cigaba da
bayar da ƙa’idojin ya faɗa a shafi: 80 ya ce:
وَمِنْهَا:
مُخَالَفَةُ الْحَدِيثِ صَرِيحَ الْقُرْآنِ ، كَحَدِيثِ مِقْدَارِ الدُّنْيَا ،
وَأَنَّهَا سَبْعَةُ آلَافِ سَنَةً ، وَنَحْنُ فِي الْأَلْفِ السَّابِعَةِ
Kuma daga cikin su: A
samu hadisin yana saɓawa a fili ƙarara da Alqur’ani,
kamar hadisin tsawon shekaru duniya, wai cewa shekaru dubu bakwai ne, kuma wai
muna a cikin dubu na bakwai ɗin ne!
Daga nan ne kuma ya
ce:
وَهَذَا
مِنْ أَبْيَنِ الْكَذِبِ ، لِأَنَّهُ لَوْ كَانَ صَحِيحًا لَكَانَ كُلُّ أَحَدٍ
عَالِمًا أَنَّهُ قَدْ بَقِيَ لِلْقِيَامَةِ مِنْ وَقْتِنَا هَذَا مِئتَانِ
وَأَحَدَ وَخَمْسُونَ سَنَةً
Kuma wannan yana daga
cikin mafiya bayyanar ƙarairayi, domin idan da riwayar ingantacciya ce, to kuwa
da kowa ya san cewa abin da ya rage daga lokacin nan namu zuwa Ƙiyama shekaru ɗari biyu ne da hamsin
da ɗaya!
Sannan kuma Al-Haafiz
Ibn Katheer (Rahimahul Laah) ya faɗa a cikin An-Nihaayah Fil Fitani Wal Malaahim
cewa:
لَمْ
يَصِحَّ عَنِ الرَّسُولِ أَنَّهُ لَا يَمْكُثُ فِي الْأَرْضِ قَبْلَ السَّاعَةِ
أَلْفَ سَنَةٍ ، وَلَمْ يُحَدِّدِ الرَّسُولُ مُدَّةً مُعَيَّنَةً لِقِيَامِ
السَّاعَةِ
Bai inganta daga
Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ba cewa, shi ba zai
zauna a cikin ƙasa kafin Sa’ar Ƙiyama na tsawon
shekaru dubu ɗaya ba. Kuma Manzon
Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) bai iyakance wani lokaci
ayyananne na tsayuwar Sa’ar ba.
Sai kuma ya ce (shafi
na: 6 a lissafin Shaamilah):
فَأَمَّا
مَا يُورِدُهُ كَثِيرٌ مِنَ الْعَامَّةِ مِنْ أَنَّ النَّبِيَّ - صَلَّى اللهُ
عَلَيْهِ وَسَلَّمَ - لَا يُؤَلِّفُ تَحْتَ الْأَرْضِ فَلَيْسَ لَهُ أَصْلٌ .
وَلَا ذُكِرَ فِي كُتُبِ الْحَدِيثِ الْمُعْتَمَدَةِ ، وَلَا سَمِعْنَاهُ فِي
شَيْءٍ مِنَ الْمَبْسُوطَاتِ ، وَلَا شَيْءٍ مِنَ الْمُخْتَصَرَاتِ ، وَلَا ثَبَتَ
فِي حَدِيثٍ عَنِ النَّبِيِّ - صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ - أَنَّهُ حَدَّدَ
وَقْتَ السَّاعَةِ بِمُدَّةٍ مَحْصُورَةٍ ، وَإِنَّمَا ذَكَرَ شَيْئاً مِنْ
أَشْرَاطِهَا وَأَمَارَاتِهَا وَعَلَامَاتِهَا . اهـ
Amma dai abin da masu
yawa daga cikin gama-garin mutane suke riwaitowa wai Annabi (Sallal Laahu
Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ba zai yi shekaru dubu a ƙarƙashin ƙasa ba, wannan kam ba
shi da wani asali. Kuma ba a ambace shi a cikin littaffan hadisi da ake dogaro
da su ba. Kuma ba mu ji shi a cikin wani abu daga cikin manyan littaffai ba,
haka ma ko a wani abu daga cikin taƙaitattun littaffan
ba. Kuma bai tabbata daga Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ba
cewa shi ya iyakance lokacin aukuwar Sa’ar Ƙiyama da wani lokaci
iyakantacce. Kaɗai, ya ambaci wani
abu ne kawai daga cikin alamominta.
Daga waɗannan bayanai za mu
gane cewa:
Akwai riwaya da ta
shahara a bakunan waɗansu mutanen da ba
malaman hadisi ba cewa: Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ba zai
yi shekaru dubu ɗaya a ƙasa ba Al-Ƙiyama za ta tsaya!
Sai dai wannan riwaya
ba ingantacciya ba ce, riwaya ce ƙirƙirarriya, ta ƙarya kawai, kamar
yadda Hafizai masana hadisi irin su Ibn Katheer da Ibn Al-Qayyim da As-Suyuutiy
(Rahmatul Laahi Alaihim) suka yi bayani.
Me yiwuwa ganin cewa
shekaru dubun sun wuce da rasuwar Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa
Sallam) amma har yanzu Ƙiyamar ba ta tsaya ba, shiyasa waɗansu suka sake ɗauko waccan riwayar
kuma suka yi mata kwaskwarima, suka mayar da ita: Shekaru dubu biyu!
Allaah ya kiyaye.
Amma abin da Allaah
Subhaanahu Wa Ta’aala ya ce dai shi ne:
یَسۡـَٔلُونَكَ
عَنِ ٱلسَّاعَةِ أَیَّانَ مُرۡسَىٰهَاۖ قُلۡ إِنَّمَا عِلۡمُهَا عِندَ رَبِّیۖ لَا
یُجَلِّیهَا لِوَقۡتِهَاۤ إِلَّا هُوَۚ ثَقُلَتۡ فِی ٱلسَّمَـٰوَ ٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۚ
لَا تَأۡتِیكُمۡ إِلَّا بَغۡتَةࣰۗ یَسۡـَٔلُونَكَ كَأَنَّكَ حَفِیٌّ عَنۡهَاۖ قُلۡ
إِنَّمَا عِلۡمُهَا عِندَ ٱللَّهِ وَلَـٰكِنَّ أَكۡثَرَ ٱلنَّاسِ لَا یَعۡلَمُونَ
Suna tambayar ka akan
Sa’ar Ƙiyama wai yaushe ne lokacin aukuwar ta? Ka ce: Kaɗai, iliminta yana
wurin Ubangijina ne. Babu mai iya bayyanar da ita ga lokacinta sai dai shi
kawai. Ta yi nauyi a cikin sammai da ƙasa. Ba za ta zo muku
ba sai dai afke kawai. Suna tambayar ka kamar dai kai masani ne a kan ta. Ka
ce: Iliminta yana wurin Allaah ne, sai dai kuma yawancin mutane ba su sani ba.
(Surah Al-A’raaf: 187)
Sannan kuma Manzon
Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:
« مَا
الْمَسْئُولُ عَنْهَا بِأَعْلَمَ مِنَ السَّائِلِ »
Wanda aka tambaye shi
a kan ta bai fi wanda ya yi tambayar sani ba. (Sahih Muslim: 102)
Wannan kaɗai ya isa dalili da
zai nuna rashin ingancin wancan hadisin.
Allaah ya saka wa
malamai da ɗaliban hadisi da
alkahiri a duk inda su ke, kuma ya ƙara mana kyakkyawar
fahimta a cikin addininmu.
Wal Laahu A’lam.
Sheikh Muhammad
Abdullaah Assalafiy
Zauren Fatawoyi Bisa
Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.