Ticker

6/recent/ticker-posts

Cikakken Byanain Yadda Ake Yin Salaatut Tasbeeh

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum malam Yaya ake yin Salaatut Tasbeeh? Mene ne ingancin ta?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

W Alkm Slm W Rhmtul Laah.

Salaatut-Tasbeehi wata Sallah ce mai raka’o’i huɗu wadda ake karanta Tasbihi har sau ɗari uku a cikinta. Lafazin Tasbihin shi ne: ‘SUBHĀNAL LĀH, WAL HAMDU LIL LĀH, WA LĀ ILĀHA ILLAL LĀH, WAL LĀHU AKBAR’.

Ma’ana: Tsarki ya tabbata ga Allaah, kuma Godiya ta tabbata ga Allaah, kuma babu abin bautawa da gaskiya sai Allaah, kuma Allaah ne mai Girma.

Shari’ar Musulunci ta kwaɗaita wa masu Imāni yin wannan sallar. Tana jawo wa musulmi gafarar Zunubansa na farko, da Zunubbansa na ƙarshe, da Zunubbansa daɗaɗɗu, da Zunubbansa sababbi, da Zunubbansa da ya yi cikin kuskure, da Zunubbansa da ya yi da gangan, da Zunubansa ƙanana da Zunubbansa manya, da Zunubbansa na ɓoye, da Zunubbansa na bayyane.

Kuma an so a riƙa yin wannan sallar sau ɗaya a kowace rana in da hali, ko sau ɗaya a kowane mako, ko sau ɗaya a kowane wata, ko sau ɗaya a kowace shekara. Idan kuma ba haka ba, to sai ya yi ko da sau ɗaya a cikin rayuwarsa.

Haka mālaman Hadisi irin su: Al-Imām Muslim, da Al-Imām Abu-Dāwud, da Al-Imām As-Subkiy da Al-Hāfiz Ibn. As-Salāh, da Al-Hāfiz Ibn. Hajr Al-Asqalāniy, da Al-Mujaddid Al-Albaaniy (Rahmatul Laahi Alaihim) duk sun kyautata wannan hadisin saboda yawan hanyoyinsa.

Kamar kuma yadda aka samu wasu malaman irin su: Al-Imām Al-Baihaqiy yana cewa: ‘Abdullāh Bn Al-Mubārak ya kasance yanā yin Salātut-Tasbihi, kuma sashen mālaman ƙwarai (Sahihai) sun riƙa koyonta daga sashensu!

SIFFAR YADDA AKE YIN SALAATUT TASBEEH:

1. Da farko musulmi zai yi shiri irin shirinsa na sallah, ya yi alwala sannan ya fuskanci alƙibla, ya yi niyyar yin Salātut-Tasbihi a zuciyarsa ba a baki ba, yana mai furta kabbarar harama da bakinsa.

2. Zai ɗora hannun damarsa a kan na hagunsa a bisa ƙirjinsa kamar dai yadda tsayuwar mai sallah ta ke, sannan ya karanta Fātihah da Sūrah bayan Du’ā’ul Istiftāhi.

3. Bayan ya kammala karatun Sūrāh, sai ya ce: ‘SUBHĀNAL LĀH, WAL HAMDU LIL LĀH, WA LĀ ILĀHA ILLAL LĀH, WAL LĀHU AKBAR’ sau goma sha biyar (15), sannan ya yi kabbara ya yi ruku’u.

4. A cikin ruku’u bayan ya ƙare zikirorin da aka saba yi, sai ya sake faɗin ‘SUBHĀNAL LĀH, WAL HAMDU LIL LĀH, WA LĀ ILĀHA ILLAL LĀH, WAL LĀHU AKBAR’ sau goma (10). Sai kuma ya ɗago daga Ruku’un.

5. Bayan ya gama zikirorin ɗagowa da tsayuwa da bayan ruku’u sai kuma ya ce: ‘SUBHĀNAL LĀH, WAL HAMDU LIL LĀH, WA LĀ ILĀHA ILLAL LĀH, WAL LĀHU AKBAR’ sau goma (10), sannan ya yi sujada.

6. Bayan ya gama zikirorin da aka saba yi a cikin sujada sai kuma ya ce: ‘SUBHĀNAL LĀH, WAL HAMDU LIL LĀH, WA LĀ ILĀHA ILLAL LĀH, WAL LĀHU AKBAR’ sau goma (10). Sai kuma ya ɗago daga sujadar.

7. A zama tsakānin sujadu biyu zai karanta zikirorin da aka saba yi a wurin kafin ya ce: ‘SUBHĀNAL LĀH, WAL HAMDU LIL LĀH, WA LĀ ILĀHA ILLAL LĀH, WAL LĀHU AKBAR’ sau goma (10). Sannan ya koma ya yi sujada ta biyu.

8. A cikin sujada ta biyu zai karanta zikirorinsa kamar yadda ya yi a sujada ta farko, sannan ya ce: ‘SUBHĀNAL LĀH, WAL HAMDU LIL LĀH, WA LĀ ILĀHA ILLAL LĀH, WAL LĀHU AKBAR’ sau goma (10). Sai kuma ya ɗago daga sujadar ta biyu ya zauna.

9. A cikin wannan zaman da mālaman Fiƙ-hu suke kira Jilsatul Istirāhah babu wani zikiri da ake yi a asali, don haka sai dai kawai ya ce: SUBHĀNAL LĀH, WAL HAMDU LIL LĀH, WA LĀ ILĀHA ILLAL LĀH, WAL LĀHU AKBAR sau goma (10). Daga nan sai kuma ya miƙe tsaye zuwa rakaa ta biyu.

10. A cikin raka’a ta biyu zai yi kamar yadda ya yi a raka’a ta farko, sai kuma ta uku sannan ta huɗu.

A kowace raka’a, zai ga ya faɗi ‘SUBHĀNAL LĀH, WAL HAMDU LIL LĀH, WA LĀ ILĀHA ILLAL LĀH, WAL LĀHU AKBAR’ sau saba’in da biyar (75) ke nan. A cikin raka’o’in huɗu kuma ya samu faɗi har sau ɗari uku (300) kenan daidai!

Allaah ya ƙara mana taimako da himma a kan karatun Hadisi da Aiki da Shi.

Ina ga wannan bayani ya amsa wannan fatawar, in shaa’al Laah.

Wal Laahu A’lam.

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments